Showing 225001 words to 228000 words out of 479911 words
ƙirjinta.
"Wallahi Abdul ka ɗuma asara, kai a duniya abu ɗaya Allah ya saka maka a cikin kanka ne? Haba mana"
"Future governor ki ke gaya wa haka? Zan fa hanaki first lady, kodayeke wadda zan aura ce zata zama first lady, ke kuma maid ɗin ta" tayi shiru, tana tauna cornflakes.
"Ki lallaɓa ni na dawo da wuri"
A fusace ta ce "Kar Allah ya sa ka dawo ɗin, in sha Allah ka tafi kenan, ko jirgin ya faɗi, kai kaɗai ka mutu"
Yayi dariya ya ce "Kin ga sai ki mutu kekaɗai a gidan nan ba, dan babu wanda ya san na ajiye ki a ciki. Gara ki yi sauri ki janye addu'ar ki, idan kina son ki fita"
Ajiye kofin tayi, ta fashe da kuka, har da sheshsheƙa.
Ya ce "Is ok, ke ce ba ayi miki abu, sai ki yi ta tsine mini, ina jin pain fa, am sorry ya isa haka, haba your excellency" maimakon ta yi shiru, sai ma ta ƙara sautin kukan, nan da nan ya rikice, ya hau bata haƙuri, amma tayi disconnecting kiran, ta cigaba da kuka.
Ta ɗauki wayar, tun da ya tafi, take gwada kiran lambobi daban-daban, amma ba ta tafiya sai ta sa kawai. Ta dudduba ko ina, ko da hanyar da za ta iya guduwa, amma babu ga wata irin kewar mama da sani ƙaninta da take yi.
Su liti tamkar za su yi hauka, gaba ɗaya suka rikice, da Viper bai kwana a gida ba, duk in da suke tunanin za su ganshi ba su same shi ba. Har gidansa Walid ya je, ya haura ta katanga, ya shiga amma ba su same shi ba, gashi madakin da aka ce ya zo yana unguwar, shi ma yayi ɓatan dabo, an neme shi an rasa.
Gaba ɗaya hankalinsu ya tashi, mussaman liti, amma saboda tsananin ƙi faɗi, yaƙi yarda ya karɓi laifin, Walid ya din ga yi musu luguden ashariya daga shi har ɗan mama, suka yi masa shiru suka ƙi kula shi.
A sukwane Nabila ta tashi daga wurin aiki, bayan cin karo da batun faɗan daba a tsakanin yaran madaki da na Viper, sai dai babu ɗaya daga cikin su da ya zo hannu, tsakanin Viper da madaki, al'ummar unguwar na cigaba da zaman ɗar-ɗar, sakamon rashin tsaro.
Ofishin Nasir ta tafi, babu sanarwa sai ganinta yayi, sai da hankalinsa ya tashi ya ce "Arfa lafiya kuwa?"
Ta ciro wayarta ta nuna masa posting ɗin.
Ya ce "To wannan ne ya saka ki ka taho har nan?"
Ta ce "Eh, na yi zaton baka sani bane"
Ya girgiza kai ya ce 'No, na sani"
"To yaya ake ciki?" Ya ɗan tsareta da idanunsa sannan ya ce "Ni duk kin ruɗa ni, ko kece ke binciken nan, sai haka Arfa. Na je, sun yi faɗan daba, amma babu tabbacin yazo".
"Baka kama shi ba kenan?" Ya jinjina mata kai alamar eh.
"To ko yaran nasa ba ka kama ba?"
"Lokacin da muka je, sun yi sun watse" wata irin ɓoyayyiyar ajiyar zuciya ta yi, sannan ta ce "To shikenan, ai ban zaci ka gani ba, shiyasa na zo da kaina, bari na tafi"
Nasir ya ce "Yanzu mussman ki ka baro aikinki ki ka zo kawo mini rahoto, arfa mai abun mamaki, zauna na gama abun da nake yi, na rage miki hanya"
Ta ce "A'a yi aikinka, ina da wurin zuwa" ta lallaɓa shi ta fice.
Sai dai hankalinta ya rarrabu kashi-kashi, voice ɗin nan da aka turo mata, babbar shaida ce da zata shiga kotu da ita da ƙwarin gwiwar ta.
Abdul ya kira saif a waya, ya tambaye shi yaya ake ciki ya ce masa "Wallahi Abdul babu labarin matar nan, duk wani bincike da yakamata na yi na yi, amma shiru babu labari".
"Lahaula wala ƙuwwata illa billa, Saif akwai matsala me zan ce wa yarinyar nan idan ta gano mahaifiyarta tayi ɓatan dabo, bayan babu irin magiyar da ba ta yi mini ba, a kan na mayar da ita"
"To wannan kuma kai ta matsewa, tuntuni da ka san abun yi a kanta da duk ba a kawo nan ba"
Abdul ya ce "Dole na gano in da mahaifiyar rayya take, idan ba haka ban san kalar tsinuwar da za ta yi mini ba"
Saif ya ce "Ban gane tsinuwa ba, tsine maka take yi?"
"Manta kawai" ya kashe wayar, ya din ga kiran wayar ramma, saboda tun jiya da safe da tayi kukan nan, ba ta sake ɗaga wayarsa ba, hankalinsa yayi mummunan tashi, ya fara tunanin ko wani abun ne ya sameta, kar ya je ta yi wa kanta illa, dan da wuƙaƙe a kitchen, kuma tana yawan iƙirarin cewa zata kashe kanta.
Kusan awanni ashirin da huɗu suka shuɗe, Nabila ba ta samu Viper a waya ba, can ɓangaren su Walid ma, hankalinsu ya kasa kwanciya, saboda yawon neman Viper.
Har ta je wurin aiki, ta kasa sukuni, kawai ta yanke shawarar zuwa gidan da yake.
Tana sauka daga abun hawa, wata mota ƙirar helux baƙa, ta fito daga hanyar, duk da wurin mota ba ta iya bi, tayi ta tunanin yaya aka yi mota ta bi ta wurin, ta ƙarasa gidan, tun a tsakar gida take sallama, amma shiru babu wanda ya amsa, ta nufi ɗakinsa, ta ganshi a kwance a kan katifa, gefensa ga wuƙarsa da wayarsa da ledar magunguna, yana sanye da riga baƙa armless, da dogon wando shi ma baƙi, ga damtsensa an yi masa ɗinkin rauni, da sauran wurare a jikinsa.
Cikin hanzari ta ƙarasa tana faɗin "Subhanallah"
"Viper meyasameka?" Sai dai kamar gawa, ta ƙare masa kallo, an yi masa askin uwar sumar da take kansa, an yi masa gyaran fuska tare da rage masa gashin da ya taru a fuskar sa. Yayi wani irin ƙayataccen kyau, hatta kayan jikinsa ba ƙaramin kyau suka yi masa ba. Wayarta ta ciro ta din ga ɗaukarsa a hoto.
Ta daddaki gefen katifarsa ta ce "Viper, bacci kake yi ne? Garin yaya ka ji raunuka haka?" Sai dai shiru ko motsi baya yi.
"Me ka sha har haka ne? Ko sai na ce Master zaka tashi?" Babu tsammani ta ga yana motsawa a hankali.
"Madarata" Nabila ta ce "Too yau kuma?"
Yayi murmushi idanunsa a lumshe ya ce "Ai a duniya babu wanda ya raina ni, daga ke sai Walid, kin daina jin tsorona gaba ɗaya zan kama ki ne" murmushi yake yi sosai, wanda hakan ya bayyanar da tsantsar shauƙi da soyayyar da yake yi mata.
Surutansa ya cigaba da yi ya ce "Yakamata na gaya miki wani abu, da yakamata ace kin sani, amma sai kin haihu tukuna, saura kuma ki isheni da tambaya na san halinki" ya buɗe idonsa a hankali, ya kalli Nabila da ta zuba masa ido, ya miƙa hannunsa ya riƙo nata ya ce "Zan gaya miki me na je yi Lagos ne" sai kuma ya saki hannunta yana girgiza kai.
"Laaa, ke ya aka yi ki ka dawo da shi, Walid ƙaraso ka ga" liti yayi maganar yana shigowa ɗakin.
Gaba ɗaya su ukun suka shigo, suka kewaye ta.
"Da gidan uban wa ki ka kai shi?"
Ta kalli Liti ta ce "Kamar yaya?"
"Gidan uban wa ki ka kai shi?"
A ƙule ta ce "Gidan ubana, tayaya zan iya ɗaga wannan shirgegen ƙaton"
"Ƙarya ki ke yi haɗa baki aka yi da ke aka ɗauke shi, wannan kayan na jikinsa ma ba nasa bane ba macuciya"
Walid ya ce "Ya isa dan Allah, Barrister nemansa muke ko sama ko ƙasa bamu ganshi ba, a ina ki ka gano shi?"
Ta ce "Wallahi yanzu na zo, bana samunsa a waya, yanzu na zo kawai na tarar da shi a kwance, wallahi ban san ma neman sa ku ke yi ba, duba wayarsa zaka missed calls ɗina da yawa. Amma dai naga wata baƙar helux ta fita daga hanyar nan, ban san ta ina suka biyo ba, na riƙe lambar motar a kaina"
Walid ya ce "Karki damu, na yadda da ke"
"Wallahi mai laya, ka cigaba da sakankancewa da yarinyar nan, sai tayi dalilin an kashe ku tukuna"
Liti ya ƙarasa gaban Viper ya durƙusa a kansa, cikin zafin nama, viper ya danƙi wuƙarsa ya saita ta a cikin liti yana wani irin huci.
Liti ya buɗe baki ya ce "Ni zaka sa wa russia Viper?"
A hankali ya ƙara buɗe idonsa, ya hankaɗe liti gefe ya ce "Na zata madaki ne" sai kuma ya kalli jikinsa, ya kalli kayansa, ya kalli damtsensa ya ga ɗinki, ya kalli Nabila ya kalli ɗakin ya ce "Ke a ina muka rabu da ke?"
Ta ce "A titi, bayan ka dire daga adaidaita sahu".
"Me ki ka yi mini?"
Nabila ta ce "Au kaima ni ka ke zargin na sace ka kenan?"
Walid ne ya yi masa bayanin abun da ya faru, ya lalubi wayarsa da sauri yana duddubawa.
"Don't endanger your life again, madaki is still not your mate, da sauran lokaci" ya ajiye wayar ya sunkuyar da kansa, da yayi masa nauyi yana tuno abun da ya faru a ranar.
Nabila ta kalli Walid ta ce "Yay walid, yayana yana zuwa wurin sayar da shayinku, kuma akwai jami'ansa a farin kaya suna zuwa, kayi taka tsantsan, yanzu aikinsa a kanka yake. Kuma ka kula da wanda suke zuwa wurin sosai, kar wani information yayi leaking a wurin"
Liti ya ce "Munafuka, wadda take kwarewa ɗan uwanta baya ne, ku ke tunanin kuma ba zata bar ku ba wataran. Shegen yayan naki azzalumi, ƙugu kamar gatari"
Nabila ta ce "Allah ya isan sa, kuma ni ba munafuka ba ce, kuma wallahi idan baka kiyayeni ba, zan kuma sakawa a kama mini kai, sai igiya tayi saura" tayi maganar tana hararsa ta ɗauki jakarta.
Ta durƙusa a gefen Viper ta kai bakinta, kunnensa ta ce "Viper, zan tafi zan je wani wuri, zamu yi waya, ka samu ka ci abinci, kar ka takurawa kanka da tunani da yawa, kar ka sha ƙwayoyin da za su yi maka illa. Saboda muna son ganinka cikin ƙoshin lafiya da ni da 'yar madara, na ji ka ce zaka gaya mata wani abu, to nima sai ka gaya mini, tun da nice amarya. Kayan nan sun yi maka kyau sosai da sosai, ka ci abinci kayi salla ka huta, ka bar wayarka a buɗe zamu yi magana dan Allah, ka yi mini addu'a zan cigaba da shari'a da su bunkure, take care dear" ya ɗaga kai ya kalleta, taƙi kallonsa tayi waje.
Liti ya ce "Makira, duk makircinki sai ya koma kanki". Ta galla masa harara ta tafi.
***
Abdul yana ta kiran ramma, har ya fitar da ran zata ɗaga, yaji ta ɗaga muryarta ƙasa-ƙasa.
"Bacci ki ke yi ne?"
Ta ce "Eh"
"Eyya sorry na tashe ki, nake ta kiranki a waya amma ba kya ɗagawa, lafiya dai ko?"
"Haushinka nake ji ne, zan iya ɗuɗɗura maka ashar, shiyasa bana ɗagawa"
Yayi dariya ya ce "Yanzu kin huce?"
"Eh"
"To masha Allah, kin tashi lafiya?"
"Eh"
"Duk muryarki wani iri, anya lafiya kuwa?"
Ramma ta ce "Ba wani lafiya, ni na gaji da zaman gidan, nikaɗai kamar mayya sai tv da haushin karnuka, ni ba prisoner ba".
Abdul ya ce "To yanzu ya ki ke so ayi?"
"Ni koma yane ayi"
Ya ce "To shikenan, zan dawo gobe in Allah ya kaimu"
"Ba sati ka ce zaka yi ba?"
Ya ce "A'a hankalina yaƙi kwanciya ne, zan dawo gobe in Allah ya kaimu "
Ramma ta ce "To Allah ya tsare"
"Kin fasa in faɗi a jirgin, kar in dawo?"
"A'a jirgin ya faɗi kai kaɗai ka mutu"
"Muguwa ba Amin ba"
"Ban kai ka mugunta ba ai"
Yayi dariya ya ce "Sai anjima".
***
Washegari ya kama ranar da Nabila zasu cigaba da shari'ar mai gadi, ta shiga office ɗin ta, ta tarar da wani file a ajiye a kan teburinta, har ta fara masifar na meye wannan aka ajiye mata a kan tebur.
Ta nemi wuri ta zauna, ta ɗauki wayarta, ta shiga social media ta rubuta, kuraye masu fatar akuya, an kusa walƙiyya mu ga kowa" ta yi tagging ɗin Naja bunkure.Washegari ya kama ranar da Nabila zasu cigaba da shari'ar mai gadi, ta shiga office ɗin ta, ta tarar da wani file a ajiye a kan teburinta, har ta fara masifar na meye wannan aka ajiye mata a kan tebur.
Ta nemi wuri ta zauna, ta ɗauki wayarta, ta shiga social media ta rubuta, kuraye masu fatar akuya, an kusa walƙiyya mu ga kowa" ta yi tagging ɗin Naja bunkure.
M karofi ya kirata, ya din ga yi mata surutu, da neman ta bashi damar zuwa gidansu, ta ce masa yanzu aiki take yi, bayan sun yi sallama, ta ja file ɗin tana dubawa.
Sunan Naja'atu Bunkure ne a sama, sannan aka fara bayanin tarihin rayuwarta tiryan-tiryan, har zuwa fara aikinta, yadda ta taso cikin rayuwar ƙunci da wahala, yadda ta zama lawyer, bayan fyaɗe da aka yi mata da ƙanan shekaru, gaɓar da Nabila ke son ganin meyafaru, a nan aka tsaya. Ta daki tebur, ta din ga jujjuya file ɗin tana tunanin waye wannan ya kawo mata file ɗin nan, da kyar idan ba shi da alaƙa da wanda ya tura mata voice message ɗin nan.
***
DSP Nasir yana zaune yana rarraba ido a ƙaton falon, da ko ina sanyin A.C ne ke ratsa shi.
Babu tsammani mutumin ya fito, ya samu wuri ya zauna, cikin girmamawa Nasir ya ce "Barka da wannan lokaci sir"
"Yauwwa barka, DSP Nasir Yusuf maitama, ɗan uwan barrister Nabila Yusuf maitama" ya ɗago ya kalle shi.
"Na san zaka yi mamakin kiran da nayi maka ko?"
Nasir "Ƙwarai sir, na san ni dai babu wani abu da ya taɓa haɗa ni da kai, amma ka saka a nemo ni, kuma ga sunana ka kama, da na ƙanwata"
Indabo ya gyara zamansa ya kalli Nasir ya ce "Nabila!"
Cikin rashin fahimta ya ce "Me tayi?"
Ayshercool
08081012143
55
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
Arewabooks ayshercool7724
Cikin rashin fahimta, Nasir ya ce "Amma Yallaɓai me tayi ne?"
Indabo yayi murmushi ya ce "Bari mu ɗan ajiye batun ta a gefe. Aminu Viper, wanda aka fi sani da mai zamani a baya, kai ne incharge of bincike da ƙoƙarin kama shi haka ne?"
Ya jinjina kai ya ce "Eh sir"
"Na san kana fuskantar matsin lamba, daga wurin na sama da kai, a kan lallai ka kama Viper. Duk da abun mamaki ne, a baya yana tsare a prison lokaci guda yayi ɓatan dabo sama da shekara guda ana nemansa".
Nasir ya ce "Haka ne sir"
Indabo ya sassauta muryarsa ya ce "Akwai jiƙaƙƙiya tsakanina da Viper, wanda barazana ne ga siyasata da mutuncina. Saboda haka na yanke shawarar yin gaba da gaba da kai mu tattauna wataƙila kafi bawa aikin muhimmanci, tun da na samanka kawai nake gani, kai bamu taɓa haɗuwa ba, kuma Alhamdilillah sai na yi sara a kan gaɓa"
ya ajiye masa wata jaka ya ce "Ga wannan ka sha mai, sannan akwai fuloti mai rai da lafiya a unguwar tudun yola da takardunsa a ciki, wannan zai zama wani ɗan hasafi, ko in ce ihsani domin ƙara maka ƙwarin gwiwa, idan aiki ya kammala, ina da kyakykyawan Albishir gareka, muddin Viper ya zo hannu, ko ma ya bar duniyar baki ɗaya ina da ƙarin Albishir gareka. Ɗana na shirin zama deputy governor a garin nan, zaɓe mai zuwa. Kuma ka san kujerar da nake kai, ka san ma'anarta. Zan iya yi maka alƙawarin zama CP na jihar nan, kai koma na yi maka babban muƙami a ƙasa. Akwai kyautar mota irin ta sanatoci, da gwamanti kan yi gwanjon su, gida ko fili sai wanda ka zaɓa. Kar ka yi dogon tunani, ba wai cin amanar ƙasa zaka yi ba, taimakon kai da kai ne, kai ma ka taimaki gobenka, idan ba haka ba, a haka zaka ƙare kana yi wa ƙasar da ba ta san muhimmancin ka ba bauta, ka gama babu wani allowance ɗin kirki ka ƙare rayuwarka a tagayyare" Nasir yayi shiru yana ajiyar zuciya.
"Sai magana ta biyu, Nabila ƙanwarka, akwai wasu abubuwa muhummai a tattare da ita. Abu na farko na sanya rayuwarta a matsayin tarkon da zan kama Viper ba tare da ta sani ba, duk da hanyar tana tangarɗa, amma tabbas ina ƙoƙarin kama Viper ta hanyar ta, ko da kuwa hakan yana nufin salwantar da rayuwarta ne"
Cikin mamaki da rashin fahimta ya ce "Kamar yaya?"
"Kamar yadda nake gaya maka, ai ba ta hannunku kawai nake nemansa ba, dan haƙa ƙwazonka, da nemo Viper shi ne zai kuɓutar da rayuwarta, haka zalika ka taka mata burki a kan shari'ar da take yi, na son yin gaba da gaba da Naja'atu Bunkure, saboda yin hakan tamkar yin fito na fito da ni ne, idan ba haka ba, wallahi rayuwarta zata salwanta a banza, ba zan taɓa bari sunana ya ɓaci a banza ko asirina ya tonu ba"
Nasir ya ce "Amma sir, dole sai an shigar da Nabila cikin wannan lamarin?"
"Dole ne, muddin kana son rayuwarta, make her withdraw the case, ta fita daga shari'ar nan"
Nasir yayi sassanyar ajiyar zuciya ya ce "Zan duba naga menene abun yi"
Indabo ya ce "Yauwwa, a ƙoƙarta, zaku tafi da P.A ɗina, za ayi wa motarka full tank, ka sanya ido sosai a kan yarinyar nan"
Nasir ya tashi ya ce "Thank you sir"
Indabo yayi murmushi ya ce "In dai muna tare, ka din ga samun damrmaki kenan, ai ba a zama haka DSP" ya jinjina kai ya juya ya fita, kansa yana wani irin nauyi.
***
Cikin hanzari Nabila ta fito daga office ɗin ta, ta kalli mai goge-goge ta ce "Baba, akwai wanda ya shiga office ɗina kafin na zo ne?"
Ya ce "A'a, shara kawai na yi na goge miki, na fito"
"Kai ka ajiye mini wani file a kan tebur?"
Ya girgiza kai ya ce "A'a, ban tarar da komai ba da na goge teburin" ta jinjina masa kai ta koma, tana cigaba da mamakin waye haka?.
Ta window ta leƙa taga zuwan barrister Habib, tayi sauri ta fita, a ƙofar office ɗin sa ya tarar da ita ya ce "Ya dai? Tara ko bashi, ki ka tsaya mini a ƙofar office" tayi murmushi ta ce "Babu ɗaya, nemanka nake yi ruwa a jallo ne"
Ya saka mukulli ya buɗe, suka shiga, ya ce "Allah ya sa ba wata shirirtar ba ce? Nima ina nemanki dama"
"Haba barrister, sai ka ce wata 'yar yarinya, is a very serious issue"
Ya dubeta ya ce "To yanzu dai, ki yi haƙuri, na fara karyawa tukuna"
Noƙe masa kafaɗa