Showing 306001 words to 309000 words out of 479911 words

Chapter 103 - K.A.W Complete Hausa Novel

01 Jan 2025

6920

ni, dan ban aikata laifin komai ba"

Tuni yan gidan suka tattaru a falo, domin jin meyake faruwa, suke ta wannan uwar hayaniya da yammacin Allah.

Sai dai jin turka-turkar da ake yi, ya sanya su mamaki ba kaɗan ba, jin abun da Nabila ta aikata, gaba ɗaya sai suka haɗe mata kai, suka din ga jifanta da miyagun maganganu, na cin zarafi.

Mama ta kada baki ta ce "Ai na san a rina, an saci zanin mahaukaciya, ba dai major ya ɗaukaketa ya nuna ita ce ya a gidan nan ba, an zo dai-dai in da nake son a zo, ɗan sa da ya haifa bai ja masa abun kunya ba, wata a banza gashi ta jawo masa, Allah ya sa ba yawon ta zubar take yi ba da sunan aiki, ban da haka, ya za ayi ta din ga hulɗa da ɗan iskan gari da ake nema ruwa a jallo, ta ce shi zata kare mutumin da yayi kisan kai ɗan ta'adda".

"Allah ba zai nuna mini yawon ta zubar a rayuwata ba, da ni da 'ya'yan gidan nan, in Allah ya yadda, babu wanda zai yi yawon ta zubar"

"Maman ki ke gaya wa haka Nabila?" Yayi maganar yana nuna ta da yatsansa.

Ko a jikinta ta ce "Zata iya kallon sauda, ko su siyama, ta ce suna yawon ta zubar? Ko yi suke na san ɓoyewa zata yi ba zata faɗa ba, sai ni 'yar Allah ba ni da ba ita ta haife ni ba, ai na daɗe ina yi mata kawaici kai ma ka sani" Baba magaji sai haƙuri take bayarwa, Nabila kuwa bakinta yaƙi mutuwa, da sun faɗa take mayar musu, mama ta ce wa Nasir, ya rabu da ita ya jira major ya dawo, ya ɗauki duk matakin da yakamata a kanta, kar ya matsa tayi masa wani Sharrin amma duk abun da yakamata ayi mata na doka, a ɗauki mataki a kanta.

***
"Abdul, so kake sai baƙin ciki ya kashe ni, ya kashe mahaifinka, mu bar maka duniyar ka rayu kai kaɗai ko? Tun da aka ce masa an mayar da jafar amurka, hankalinsa yaƙi kwanciya, wataƙila hukuncin kisa ne a kansa, jininsa yayi mummunan hawa, an bashi hutu ma zaman majalisar nema yake ya gagare shi, kai ana ta fama ka samu ka zama deputy governor ɗin nan, yanzu ko maganar bikinka ka daina yi, yau an ƙara watanni uku a kan lokacin bikin, amma ko ka bibiya meyafaru ya ake ciki? Babu ruwanka saboda ka ajiye yar mutane kana lalata da ita, so kake sai asirinka ya tonu mu shiga uku baki ɗaya, da wanne ka ke son mu ji? Wancan case ɗin ko kuma naka da ake ta bibiyarka ana lallaɓaka ka ke rashin mutunci?"

Ya girgiza kai ya ce "Mummy, ba haka bane ba, wallahi tsoro nake ji na fito da rahama, na san babu lallai abun ya tsaya a iya bayar da shaida a kotu, ina tsoron daddy ya yi mata wani abun, kin san halin sa, idan kuwa aka kuma cutar da ita, ba zan iya yafewa kaina ba, saboda nayi nadamar abun da na aikata"

"Ka yi nadama amma ka ajiye musu yarinya, ka ke lalata da ita? Wace irin nadama ce haka?"

Ya ɓata fuska ya ce "Ni ajiyeta kawai nayi, ba lalata nake da ita ba"

"To yanzu dai na ji, amma tana ina? Ni ka gaya mini, nayi maka alƙawarin babu wanda zai cutar da ita, har mahaifin naka ma, ba zan bari ya cutar da ita ba"

Ya ce "Gaskiya Mummy na san lallaɓa ni ki ke yi, kiyi mini wayo, amma na san tsaf zaki bayar da ita"

Ta ce "Laaa ƙarya nake yi maka kenan Abdul?"

Ya girgiza kai ya ce 'To, zan dai dawo in gaya miki, amma ba yau ba, bari na tafi Asibiti zan je"ya tashi ya ɗauki jakarsa.

"Ba zaka je ka duba mahaifin naka ba?"

Abdul ya ce "Zan je, yanzu na kusa makara ne, kuma ina zuwa zai yi mini zancen yarinyar nan, sai na dawo tukuna" ya fice daga ɗakin.

***
Viper ya ƙurawa madaki ido, da duk yayi wani iri, babu wannan kwarjinin da ban tsoron da yake da shi, babu shaye-shayen ƙwayoyin da ya saba, gaba ɗaya sai tsufansa ya fito sosai da sosai.

"Madaki, yanzu na tabatta har labarin madaki ya shafe, Viper ba zai bar zuciyarka ba, ko dan wannan ƙafar da aka yanke, kodayeke taimakonka nayi, ni na fika imani, ba dan haka ba, wannan ƙafar cin jikinka zata cigaba da yi.
Na turo lawyer ta, ku yi magana, amma ka ƙi, ni ba ta taka nake yi ba, kai ka san kasheka ba wahala zai bani ba, da kai da muƙarabbanka, amma ba ta kai nake yi ba, zan yi amfani da kai ne, na dangana da Indabo, dan haka ka shirya yin magana ko baka shirya ba?"

"Ban shirya ba, kuma ba zan shirya ba, kayi kaɗan mai zamani, haryanzu ba ka kai in da zaka ga bayana ba, maƙiyina bai isa ya ga bayana ba"

Viper ya ce "Baya kuwa na riga na ganshi, tun da da hatimin sunana zaka mutu a gadon bayanka, na san duk abun da zan yi maka, ba zan huce ba madaki, ni zuciyata ka yi wa illa, amma zan iya kamantawa. Kar ka manta lakwari ma yana hannuna, sannan shi ya ji wuyar da ya shirya yin magana, dan haka ko ka yi magana, ko kar ka yi tare zata kwaɓe muku, idan yayi tamkar ka yi ne"

Ya ciro wani jan gari, mai fatsi-fatsi a cikin yar leda, ya ɗago wa madaki shi, ya ce "Da irin wannan, ku ka yi amfani wurin hanani kataɓus, ku ka yi mini illa ko?" Madaki yayi shiru, yana bin hannun Viper da kallo.

"Bari na yi maka amfani da ita, na ga wani irin hali na shiga kuma wane irin nishaɗi ka ji, lokacin da kake cin zarafina" Viper ya miƙe tsaye, Madaki ya zazzaro ido, amma Viper haka ya sheƙawa madaki garin nan.

A take kansa ya fara juyawa, ya shiga girgiza kansa.

Viper ya ce "Ina son ku ɗauke shi, ku kai shi kusa da tsohuwar dabata, in da yaran nan da yake cin zarafi yake yi wa kisan gilla, wanda ya sanya tsananin tsoronsa a zukatansu, idan dare yayi ku yasar da shi a can, gari ya waye su ganshi a wurin, da ƙafa ɗaya su tabattar da cewa alkadarin sa ya karye, ƙaryarsa ta ƙare.

***
Nabila na kwance, ƙirjinta na ta bugawa, jiran dawowar Abba kawai take yi, ba ta san me Nasir zai gaya masa ba, ba ta san a yaya zai karɓi maganar ba. Tana ta maimaita "la haula wala ƙuwwata illa billah" bacci ne ya fara fizgarta, ta ji tsayuwar motar Abba, wajen ƙarfe goma na dare, zumbur ta tashi ta tsaya, ta tafi window tana leƙe-leƙe, har wurin goma na dare, shiru ba ta ji an kira ta ba.

Ta ɗauki wayarta, ta kira Viper, bugu ɗaya ya ɗaga, ya ce "Ya ake ciki?"

"V am scared" tayi maganar tana fitar da numfashi cike da tsoro.

"Meye yake baki tsoron?"

"Ban san me Abba zai ce mini ba, tsoro nake ji, Abba bai iya fushi ba, bana tunanin zai fahimce ni cikin sauƙi, na shiga uku" tayi maganar tana fashe masa da kuka.

"Shhhhh, Abla" ta ji kiran sunan har tsakiyar zuciyarta.

"Mmm"

"Shi ramin ƙarya ƙurarrre ne, duk yadda ki ka kai ga ɓoyewa, dole sai ya fasu wataran, shiyasa na kawo ƙarshen zargin da yayanki yake yi miki. Haɗuwar da muka yi da ke, sai da aka gaya masa, yana bibiyarki ko ta ina tasa mafitar kawai yake nema. Ki nutsu ki cigaba da addu'a, babu abun da zai faru in sha Allah, you are my only hope as i told you before, idan ki ka karaya ni ya zan yi?" Yayi maganar cikin rarrashin da bata taɓa tunanin ya iya ba.

"Ba zaka gane ba, amma zan cigaba da addu'a, sai da safe" ta kashe wayar tana dafe ƙirjinta, saboda yadda yake bugawa.

***
P.A ne ya shiga bedroom ɗin Indabo, bakinsa ɗake da sallama, ya amsa masa ya ƙarasa ya zauna, ya ce "Barka da wannan lokaci"

"Barkanka dai P.A"

"Ya ƙarfin jiki kuma?"

"Jiki Alhamdilillah, da sauƙi sosai, maybe gobe in Allah ya kaimu zan shiga Abuja"

P.A ya ce "Yakamata ka ɗan dakata da shiga Abujan nan?"

Ya kalli P.A ya ce "Saboda me? Hutuna ya ƙare ai"

"Ƙishin-ƙishin na ji, maganar kuɗin scholarship ɗin da na harkar sadarwa, balli na daf da tashi, EFCC zata bincike ku" zumbur indabo ya tashi zaune ya ce "Kai a ina ka ji?"

P.A ya ce "Majiya mai ƙarfi, amma ka kira shugaban marasa rinjaye, a wurin P.A ɗin sa na ji maganar, kuma ba jita-jita bane ba"

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, P.A wai ya aka yi abubuwa suke ta taɓarɓarewa ne haka?"

P.A ya ce "Nima abun ya fara bani tsoro, amma ka dudduba ka bincika mu ji"

"Ai ni har bana son kiran waya, duk wanda na kira akwai kalar masifar da zai gaya mini. Kuɗin nan fiye da rabi duk a kan ƙoƙarin ganin jafar ya fito ne, idan ba hali sai na lallaɓa na mayar, amma zan yi magana da ministan sadarwar da na ilimin, mu tattauna, koma dai na saka su bincika mana".

"Bayan nan, mutane fa suna ta surut a kan program ɗin da yarinyar nan take yi, na walƙiyya wallahi mutane sun fara dawowa daga rakiyarmu, na rasa uban da yake ba ta wasu information ɗin da take faɗa a kanmu"

"Kaga P.A, dan Allah ka ƙyale ni haka, gaba ɗaya maganganunka ba alheri yau, tashi ka tafi dan Allah"

P.A ya ɗan yi shiru, sannan ya tashi ya fita.

***
Yanayin da Abba ya fito falo, ya tabattar musu da ba lau ba, fuskar nan a murtuke babu annuri.

Ya kalli baba magajiya ya ce "Kira wo mini Nabila" sai da suka kalli Abba, jin ya ambaci Nabila, maimakon Arfa da ya saba kiranta.

Nabila na kwance baba magajiya ta shigo ta sameta, ta ce "Arfa, babanki yana kiran ki" sai da ƙirjinta ya buga da ƙarfi, ta yi ajiyar zuciya ta ce "To, gani nan zuwa" baba magajiya ta fita daga ɗakin.

Da ƙyar Nabila ta tashi, ta nufi falon, ƙirjinta na ta bugawa da sauri.

Kusan kowa ya hallara a falon, ita kawai ake jira.

Ta ƙarasa ta durƙusa a gaban Abba, ta ce "Abba gani"

Mama ta ce "Munafuka ga ladabin kura"

Umma ta ce "Ki yi shiru, karya haɗa da ke".

"Dama irin tarbiyyar da na baki kenan? Ki je ki dinga bibiyar 'yan iska a waje?"

Gabanta ya faɗi, ta ɗaga kai ta kalli Nasir ta koma ta sunkuyar da kai.

"Har muka yi zaman kudancin Najeriya, muka gama ki ka yi jami'a, duk baki lalace ba sai yanzu? Ina ke ina bibiyar ɗan daba, ɗan ta'adda kuma ɗan iska da hukuma take nema? Kin zama 'yar iska lalacewa ki ke so ki yi ko, ko ma in ce ki ka yi?"

Falon yayi tsit, baka jin sautin komai, ƙarar gudun A.C, sun yi cirko-cirko suna kallon Nabila.

Tuni ta fashe da kuka, jin yadda maganganun Abba, ke dukanta.

Abba ya ce "Nasir ya gaya mini komai, da duk bana yadda, yanzu sakamakona kenan a wurinki ko? Sakamakon tarbiyya da ilimin da na baki kenan, ki ƙare a ɓoye mai laifi, azo kama shi a haɗa da ke, ki tozarta ni ki zubar mini da mutunci"

Cikin ƙulewa mama ta ce "Wane sakamako ka ke saka ran samu daga tsintacciyar mage, ai ba zata taɓa mage ba, shiyasa nayi ta ƙoƙarin ankarar da kai tun a baya, uban wani ba ya zama na wani, yanzu duk da fifikon da ka nuna mata, bai hanata nuna maka, ita 'yar kunama ce ba, duk gidan nan babu wanda yake janyo maka magana sai ita, yayanka suna zaune lafiya amma ita kullum cikin ɗaga mana hankali take"

Baba magajiya ta ce "A'a fa, dan Allah ki sassauta maganganun nan, sun yi tsauri da yawa"

Nabila kuwa da a zahiri ta nuna tashin hankali da nadama, cikin zuciyarta kuwa babu alamar hakan, ta yakice gumin fuskarta da yake ta tsatstsafo mata ta ce ""Abba ba mummunan sakamako bane ba, abin da ka tarbiyyantar da ni a kai ne, gaskiya ita ce nake tsaye a kai. Yakamata ayi mini adalci aji ta bakina, ba a goyi bayansa kawai ba ace ni ce bani da gaskiya ba. Wallahi Abba ni ba bibiyar yan iska nake ba, aikina kawai nake yi".

Mama ta ce "Har wata gaskiya ce da ke....

Abba ya ɗaga mata hannu, ya dakatar da ita, ya ce "Ya isa haka, ki tashi ki je, bana ko son ganinki, ki je ki yi abun da ki ke ganin shi ne dai-dai, tun da a kan gaskiyar ki kike"

Cikin tashin hankali ta ce "Abba baka son ganina fa ka ce, me aka gaya maka har haka a kaina ya sanya ka yanke mini wannan hukuncin "

"Abun da ki ka aikata aka gaya mini, muddin kina neman zaman lafiya da gudun ɓacin raina, dole ki bawa ɗan uwanki cikakken haɗin kai, ya gudanar da aikinsa, ki fita daga wannan lamarin, kafin a saka ki cikin masu laifi a kama da ke.
Duk wahalar da yaron nan yake yi, kina ji kina gani, amma kika ja bakinki ki ka yi shiru, har barazana ake yi masa na kora, muddin bai kama mutumin nan ba, amma ki ka zagaye ki ka je ki ka ƙulla alaƙa da shi, kin fara bani tsoro Arfa"

Cikin matsanancin tashin hankali ta ce "Amma Abba ni kuma menene makomata? Yakamata ka ji ta bakina abba, na karɓi aikin nan ka fahimce ni Abba"

Bai tsaya sauraronta ba ya ce "Sai dai kin nuna mini ba ni na haife ki ba, na gode" yayi gaba zai bar falon.

Cikin tashin hankali, ta riƙe ƙafarsa ta ce "Haba Abbana, idan har zan rayu kana fushi da ni, me yayi mini saura a duniya? Ka yi haƙuri zan yi abun da ka ce" ta yi maganar tana kuka mai ratsa zuciya, tana sheshsheƙa kamar ta shiɗe, amma ya fizge ƙafarsa yayi gaba.

Yana bari falon, tamkar su cinyeta ɗanya, suka yi kanta da surutu, kowa na tofa albarkacin bakinsa.

Tashi ta yi tsaye, ta goge hawayenta, cikin ko in kula, ita ma ta bi wata hanyar ta bar musu falon, cikin sigar kwa ci kanku.

Ɗakinta, ta shiga ta buɗe drower, ta fito da wasu takardu ta zube su a kan gado, ta kunna system ɗin ta da take caji a gefen gadon, lokaci guda kuma ta ɗauki wayarta tana dannawa.

Jin motsin mutum a bayanta, ya sanya ta waiwaya da sauri.

A tsaye ta ganshi bakin ƙofa, fuskarsa babu walwala balle annuri.

Mayar da hankali ta yi, za ta cigaba da danna wayarta, Nasir ya tako zuwa gabanta, ya tsaya ya ƙare mata kallo sannan ya ce "Kin shirya aikata abun da Abba ya umarce ki ko kuwa? Ina zan kama Viper"

Cikin hanzari ta tari numfashin sa ta ce "Ban ce shirya ba, kuma ba zan shirya ba, daga nan har gaban abada,ka je can ka neme shi, yaya Nasir ka fita ka rabu da ni dan Allah".

Cikin matuƙar mamaki yake bin ta da kallo, "Yanzu duk kukan da ki ka yi a falo, ƙarya ki ke yi kenan?"

A hasale ta ce "Ina ruwanka, idan ma kukan ƙarya ne ko na gaske, ka yi aikinka in yi nawa. Ba dai ka je ka gaya masa ƙarya da gaskiya abun da ka ke so ba? Shikenan, amma kar ka sake yinƙurin shigar mini aiki, idan ba haka ba komai yana iya faruwa, wallahi ba zan fasa abun da na yi niyya ba, idan kuma ka cigaba da takura mini, zan baka mamaki ka taka a hankali kar ka faɗo cikin aikina"

Hannu ya saka, ya ɗagota daga kan gadon ya ce "Menene zai faru, wani irin mamaki zaki bani? Me zai faru nake son ki gaya mini. Kina da hankali kuwa Nabila? Kin san doka amma kina taka ta yadda ki ke so? Da me ki ke taƙama ne haka? Sai da na zauna na nutsu, nake tunani, kenan duk hanyoyin da nake bi, dan na samu na kama mutumin nan, ke ce ki ke toshe su ko? Ki ke taka doka yadda ki ke so Nabila"

Ta waro masa idanunta ta ce "Doka ko? Ni  iya takata na yi, kai kuma cin zarafinta ka ke ƙoƙarin yi, ka ƙyale ni babu ruwanka da ni, ka yi naka aikin na yi nawa duk wanda yayi galaba shikenan. Idan ka ga dama ka je ka sake gayawa Abba abun da duk yayi maka a kaina, wallahi babu gudu babu ja da baya, ban fara dan ina saka ran dainawa ba, ba tare da na yi nasara ba. Ka rabu da ni muje a kan Sharrin da ka yi mini, ina bin ɗan daba a waje" hankaɗata yayi kan gadon, yana wani irin huci, zuciyarsa na yi masa zafi, yayi wata irin ƙwafa yana bin ta da kallo. Cikin hanzari ya fice ya bar mata ɗakin, saboda idan ya cigaba da tsayuwa, zai iya yi mata abun da ba shikenan ba. Ta yinƙura ta tashi zaune tana haki, tana kallon ƙofar da ya fita.

Yana fita ta dafe kanta, saboda yadda yake wani irin sara mata, ta kira Sumayya a waya, sai da ta kusa katsewa sannan ta ɗaga.

"Salamu alaikum"

"Wa'alaikum Salam, sumayya dan Allah kina ina ne?"

"Gida, ban daɗe da dawowa ba ma"

"Dan Allah idan kin huta ki zo gida, ina son na ganki, ina cikin matsala ne, ba zama a bari na fito ba"

"Subhanallah, wace irin matsala kuma?"

"Ni dai ki zo dan Allah"

"Shikenan, bari na canza kaya na zo kawai"

***
Tamkar an ɗora masa gingimemen dutse a kansa, haka ya buɗe idanunsa da ƙyar, ya na ƙoƙarin tashi, ya ce "Masa oga kar ka tashi, ka huta tukuna"

Madaki ya ɗaga kai da kyar, ya ganshi a dabarsa ya ce "Ya aka yi na zo nan?"

"Yaran mai zamani ne, suka kawo ka, suka ce wai gaka nan ajiya, zai waiwayeka, amma oga ya na ganka da ƙafa ɗaya, sai nemanka muke yi da kai da lakwari babu wanda ya san in da kuka shiga?"

Ya kalle shi ya ce "Akwai wanda suka san na dawo?"

"Eh mana, su fidda na kogo, duk suna nan aka kawo ka, labari ma ya fara zagawa cewar an cire maka ƙafa ɗaya"

"Wani

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login