Showing 339001 words to 342000 words out of 479911 words

Chapter 114 - K.A.W Complete Hausa Novel

01 Jan 2025

6057

je? Kar ka yi wani wurin"

"Za a zo a ɗauke ni, ki tafi kawai tare da su Walid zamu tafi".

Cikin damuwa ta ce "Kar na tafi fa su kama ka".

"Babu hannun da zai iya kama wannan ƙarfen ba, ku tafi kawai" Nabila ta tafi tana waiwayensa.

Tsananin mamaki ya kama Nasir, kenan Nabila son mutumin nan take yi, abin da ya gani a idonta, tsantsar soyayya ce.

Ya tsura mata ido, har ta shiga mota, ita da sunayya su ka bar wurin, murtala ya hau babur ɗin sa ya tafi, Viper mayar da idanunsa kan Nasir ya ce "Malam, akwai mutanen da suke ajiyar Allah ne, duk tsanar nan da ka yi mini, na riga na fi ƙarfinka, babu yadda zaka yi da ni, takura mata da hura mata wuta a kaina, da ƙuntata mata a kaina, ba zai haifar maka da komai ba, sai zunzurutun ƙiyayyarka a wurinta. Ka san meyasa dalili biyu ne, a yanzu a wannan duniyar da nake ciki tafi kowa sanin waye ni, kuma babu wani abu da take tausayi kamar ni, kuma ka san menene ma'anar tausayi a wurin mace. Abu na biyu kuma wannan, mussaman saboda na haɗu da kai na baka, na cigaba da yawo da shi".

Ya zaro envelope daga aljihunsa, ya ce "Na bata saƙo, ta kai muku gida, kun yi burus da ita, kun yi mata furucin ta je ta nemi mahaifinta, na gaya maka na fiku buƙatar ta, kuma lokaci yayi da zan biyata ladan aikin da tayi mini, ko kun shirya hakan ko baku shirya ba, dan haka shawara ta rage ga mai shiga rijiya".

Ya danƙawa Nasir envelope ɗin ya ce "Gashi nan, mu haɗu a zama na gaba, ko kotu, ko a mafitar makomar Nabila" ya juya ya nufi in da su Walid suke.

Nasir ya rasa meyasa baya iya kataɓus idan yana gaban Viper, yayi ta ci masa mutunci yana tsaye yana kallon sa.

Liti kamar yayi kuka, ya ce "Ɗan mama, ɗan kut...... Saboda hauka da yarinta, ya ja an kama shi, uban waye ya gaya masa zaman wurin nan lafiya ne? Allah kaɗai ya san izayar da zasu yi masa, yanzu za a haɗa shi da masu kisan kai, na jakai zasu din ga naɗa masa wallahi wawa kawai"

Viper ya ce "Mu tafi"

"Mu tafi ina mu bar wannan banzan?"

Walid ya ce "ashe dai kana son sa?"

"Ba wai son sa nake yi ba, tausaya masa kawai nake yi, gaba ɗaya gaɓo ne"

Viper ya dafa kafaɗar liti ya ce "Duk cikin plan ne, ka kwantar da hankalinka, ba abin da zai same shi in sha Allah"

***
Sumayya suna tafe a hanya, suna hira da Nabila, ta ce "Subhanallah, Nabila kin ga wata ƙira ta manya, ga mulki wai kuma ɗan daba, gaskiya ya ci sunansa Viper, bala'i"

"Ya maganar mahaifinsa da ki ka yi mini?"

"Na gaya masa saƙonki ai"

Nabila ta ce "Idan mun gama da wurin su ramma, zan ganshi"

Sumayya ta ce "Da gaske, zaki haɗa shi da Vipern?".

Nabila ta ce "Eh, zan haɗa su, zan yi uniting uba da ɗa, ko me hakan zai janyo kuwa"

"Kina nufin akwai matsala kenan?"

Nabila ta ce "A'a karki damu"

Da hanzari Ramma ta ƙarasa suka rungume juna da Nabila, Nabila ta ce "Rahama, barka da arziki ban samu na zo na duba ki ba"

"Bakomai Anty, na gode sosai da sosai Allah ya saka miki da alkhairi"

Nabila suka gaisa da maman ramma, ta ce "Rahama ga masoyiyyar ku, Sumayya T ladan"

Ramma ta ce "Anty sumayya ya aiki?"

Sumayya ta ce "Alhamdilillah, ya fargaba kuma, Allah ya kiyaye gaba"

Maman ramma suka gaisa da barrister Habib ma, tana tayi masa godiya, ta ɗaukko wa Nabila takarda, an yi stapling ɗin ta, ta ce "Gashi aka kawo, tasatasan da aka yi wa ramma ne, da aka ɗebi jininta, bayan an kawota, aka ce kar a buɗe ke za a bawa, tun da ke ce lauyanta"

Nabila ta karɓa ta na faɗin "Ai yana daf da zuwa hannu, mun gama sbirya komai ta buɗe takardar tana dubawa, komai na ramma lafiya ƙalau, sai dai ga tes ɗin ciki ya fito rangaɗau".

"Ina fatan babu matsala dai ko? Babu ƙanjamau ko wani abu?"

Nabila ta yi ajiyar zuciya ta ce "Eh komai lafiya, amma rahama ɗan zo mana"

Ramma ta tashi suka koma gefe, ta kalli ramma ta ce "Rahama kin san kina da juna biyu?"

Ramma ta jinjina kai alamar eh.

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un"

"Dan Allah anty kar ki gaya wa mama"

"Rahama dole a mata, dole ta sani fa"

Cikin kuka ramma ta ce "Dan Allah ki rufa mini asiri"

Ta kamo hannun ramma suka dawo falon, ta kalli mahaifiyar ramma ta ce "Maman ramma, da gaske kin tabattar ya aureta?"

Jiki a sanyaye ta ce "Haka wan babanta ya gaya mini, meyafaru?"

"Akwai matsala, sakamakon nan ya nuna akwai ciki fa"

Sosai Nasir yake gudu, cikin matsanancin tashin hankali, ganin hoton da Viper ya bashi, hotonsa shi da jauhar.

Ko rufe motar bai yi ba, ya fita ya faɗa cikin gida.

Sai da Abba baya nan, ya din ga kallon hoton, cikin fargaba, kenan wannan ce ake dambarwa a kan kisanta? Saboda yanayin yadda suka yi hoton, ya tabattar da mata da miji ne. Lallai akwai gagarumar matsala.

"Wai wannan wane irin mutum ne? Kenan ya san komai, shiyasa yake ziga Nabila? Akwai Matsala......

Ayshercool
08081012143

82
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa


*BRIGHT PENS SECOND BATCH*

Ku kasance da littatafan bright pens, second batch.
*ƘARFE A WUTA (AYSHERCOOL)*
*MUTALLAB (NIMCYLUV)*
HADARIN GABAS (NAZEEFA NASHE)*
*ZAYTOON (ZEE KUMURYA)*




Nasir ya cigaba da jujjuya hoton, ya fita ya tafi sashen mama, ya tarar da ita tana cin abinci, amma ya rasa me zai ce mata.

"Lafiyarka kuwa?"

"Eh lafiya ƙalau, shigowa nayi kawai mu gaisa"

"Kuma sai na ganka a haka kamar mara gaskiya, gaisawar da muka yi da safe fa?. Amm ya ake ciki ne? Ka haɗu da ita ɗin?"

Ya jinjina kai ya ce "Eh mama, mun haɗu ƙarewar rashin kunya, tare suka je da gayen"

"Hmm ai na sha gaya wa mahaifinku, gurbin ido ba ido bane ba, ai yanzu gashi nan ya fara gani. Ni dai ka yi iya yinka kar yarinyar nan tayi galaba a kan ka"

Ya jinjina mata kai kawai ya fita.

Wiwi ramma take kuka, mamanta ta ce "Ramma, kin munafunce ni, na ce miki babu abin da yaron nan yayi miki, ki ka ce mini eh, amma kawai sai na tsince ki da ciki? Baki kyauta mini ba"

Ramma cikin kuka ta ce "Dan Allah mama ki yi haƙuri, bana son ki shiga damuwa ne"

Barrister Habib ya ce "Hajiya, ina ga mu bi komai a hankali, Nabila menene watannin cikin, kuma kwana nawa da ɗaura musu aure, tun da an ce ai lokacin da ya saceta da ciki, ya ci ace zuwa yanzu ta haihu.

Ramma tayi wiƙi-wiƙi da ido tana kuka.

"Kiyi magana dan ubanki"

Nabila ta ce "Yi mata a hankali, rahama meyafaru da wancan cikin?"

Ramma ta kasa magana, ta cigaba da kallon mahaifiyarta da ta hasala.

Nabila ta yi ta rarrashinta, amma taƙi magana fafur.

Sumayya ta ce "Nabila, ku bi a hankali, zata yi magana, amma yanzu yakamata a rabu da ita, zuwa lokacin da zata samu nutsuwa tayi magana"

Maman ramma ta ce "Har zuwa yaushe kenan, dan girman Allah ku yi mini rai a cire cikin nan"

Barrister Habib ya ce "Haba Hajiya, baki bari an cire na farko ba sai wannan, dan Allah kar ki takura mata, ki ce sai ta yi miki bayani ko makamancin haka, ki yi haƙuri"

Maman ramma ta dafe fuskarta tana hawaye, ta ce wannan wace irin wulaƙantacciyar rayuwa ce, an cutar da ni an wulaƙanta iyalina"

Nabila ta ce "Mama jarrabawa ce, kowa da yadda Allah ya tsara masa, muddin muka taɓa cikin nan, zamu iya shiga matsala, tun da da izinin wakilinta ya aureta, babbar damuwar mu a nan shi ne, ayi masa hukuncin abin da ya aikata mata, amma ki yi haƙuri dan Allah"

Nabila ta cigaba da rarrashin ta, tare da taimakon su sumayya.

Sai da suka gama da mahaifiyar ramma sannan suka fito, suna ta jajanta lamarin, Sumayya ta ce zata tafi gida, Barrister Habib kuma zai mayar da Nabila, Nabila ta ce "Sumy, ki turo mini lambar mahaifin Viper please"

Sumayya ta ce "Ok, amma ni haryanzu baki gaya mini tayaya ki samu alaƙa da matarsa ba"

Nabila ta girgiza kai ta ce "Ai ni yanzu na daina dagewa lallai idan na faɗi abu sai an yadda da ni, lokaci zai warware komai"

"Shikenan, ba zan matsa miki ba, zamu gani, amma Nabila nayi mamakin ganin Viper, lallai ya ci sunansa Viper, wallahi na zata zan ga wani karabutin mutum kawai, kalleshi masha Allah, lallai wannan su suke yin dabar gaske"

Nabila ta ce "Malama ya daina daba fa, ki daina zancen dabar nan Please, ya tuba"

Sumayya tayi murmushi ta ce "Allah ya baku haƙuri, sai mun yi magana"

"Ok, bye" suka yi sallama.

****

Sannu a hankali ta cigbaa da zaro kwalaban maganin tari, da satchet ɗin magungunan mura a ƙarƙashin gadonsa, kwalabe sun kusa ashirin, jikinta sai tsuma yake yi.

Da kyar ta iya amsa sallamar da Shahida take yi a tsakar gida, ta fito jiki a sanyaye tamkar munafuka.

"Mama ya dai? Na ganki kamar a tsorace meyake faruwa ne?"

Alama ta yi wa shahida da hannu da ta shigo, ta ƙarasa cikin ɗakin Abba, ta nuna mata tulin kwalaben maganin tari masau hatsarin gaske.

Shahida ta dafe kai ta ce "Mama kin gani ko? Na daɗe ina gaya miki amma kin ƙi yarda"

Rahila ta ce "Duk laifin babanku ne, tun da ya kore shi daga kasuwa shi da Nazifi, ya rasa abin yi ya shiga wani hali, ni da nake ta fatan nayi masa aure"

"Mama Abbu fa ba shi da laifi, yayi iya ƙoƙarin sa a kansa, ya zai zauna da su, suna cutarsa"

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, na shiga uku ni Rahila"

"Ina Amira ne?"

Tamkar ta fashe da kuka ta ce "Amira yau kwananta biyu bata gidan nan, ban san in da take ba, na yi wa babanku ƙaryar tana gidan Yaya, Shahida na shiga uku"

Jiki a sanyaye ta ce "Mama baki shiga uku ba, ni fa daga kotu nake, na kai Anwar ƙara ya sauwwaƙe mini, ba zan iya ba na gaji" A razane ta ce "Ya sauwwaƙe miki? Shahida baki da hankali, a wannan ƙadamin da ake ciki zaki kaso aurenki, ya ki ke so nayi, sai duniya tayi mini dariya?"

"Mama, kin kasa gane in da na dosa, wai so ki ke sai na halaka ne, saboda kawai yana da kuɗi, nayi haƙuri fa iya haƙuri, ke fa uwata ce, haƙurina ya ƙare, Allah da zan iya tunkarar Abba, da sai na tunkare shi na sanar masa".

"Shahida uban naki zaki tunkara da wannan maganar? Saboda baki da kumya?"

Cikin tsiwa ta ce "Idan ba irin Amira ki ke so na zama ba ki ƙyale ni dan Allah"

Rahila ta kwantar da murya ta ce "Ki rufa mini asiri Shahida, shi wannan ya fara shaye-shaye, waccan bin maza, shi Nazifi ya gudu kudu neman kuɗi, ban ma san a duniyar da yake ba, ke kaɗai ce a ɗakin aure nake jin daɗi, kar ki gurguɗe auren nan, ki ƙara tona mini asiri, ba ya ce miki yana neman magani ba? Baki san me Allah ya ɓoye a lamarin nan ba, ga tarin dukiya yana da ita, sai ki ga ke kin haihu da shi, ki haifi namiji, wannan dukiyar ta zama tamu"

Ta kalli Rahila cikin takaici ta ce "Na haihu ta yaya, mama shekara uku fa, wane irin magani ya kasa nema a kan sauran matan da ya rabu da su? Ashe aurensa tara ni ce ta goma ya ɓoye mana, ga shaye-shaye ga cin mutunci har da duka wasu lokutan, wallahi ba za a kashe ni da raina ba, gara na auri talakan tulus in samu nutsuwa da kwanciyar hankali" Rahila ta ɗora hannu a ka, ta din ga kurma ihu, tana kukaz Shahida ko a jikinta, ta tashi ta shige ɗaki ta bar ta.


***

Abin duniya duk ya damu liti, da yayi juyi ya ga babu ɗan mama sai yayi ta tsaki, da daddare ma kasa bacci yayi, sai tsaki yake yi.

Walid ya ce "Sarkin gida"

"Mai laya"

Walid ya ce "Wai ya ne?"

"Wallahi tunanin yaron nan nake yi, Allah ya sa ba suna can suna jibgarsa ba, ka san ba imani ne da su ba, kuma ga sauron wurin nan"

Walid ya yi dariya ya ce "Allah liti, kai ne kake tunanin halin da ɗan mama yake ciki? Dama ka damu da shi har haka?"

Liti yayi tsaki ya ce "Wallahi ban san ya aka yi ya shiga raina haka ba, ka san ya iya ladabin makirci, wallahi da ya dawo wurinmu, rashin Nura ya sanya nake yin sa"

Viper ya yi gyaran murya ya ce "Ka yi haƙuri duk laifina ne, amma in sha Allah ba zai wulaƙanta ba zai fito"

"Idan ma cewa kayi ba zai fito ba, ya tafi kenan dai-dai ne Ogana"

Viper ya ce "Zai ma fito, ni kaina nayi mamakin yadda ya shiga raina, Allah sarki ɗan uwana Nura, Allah ya sanyaya makwancinsu da shi da mahaifiyata, da Sadik, da uban gidana dodo, da kuma matata a bar ƙaunata, da dukkanin wanda muka rasa" suka amsa masa da Amin.

Liti dai bacci gagararsa yayi, sai tsaki ya din ga yi yana juyi.


Gidan da Nabila take, aka gabatar mata da wata macen soja, a matsayin mamallakiyar gidan, ba ta gari ne ya sanya Nabila take zaune a gidan tare da masu aikinta.

Nabila ta zata zata ga matar masifaffiya, kasancewar an ce soja ce, amma taga ba haka ba, tana da matuƙar kirki da sauƙin kai.

Nabila ta din ga jujjuya lambar mahaifin Viper tana son ta kira, amma tana tsoron tijarar Viper, kasancewar ya gargaɗeta a kan haka, tana cikin tunanin, sai ga kiran Viper sai da ta kusa katsewa ta ɗaga ta ce  "SPY"

"Idan ki ka sake suka ji abin da ki ke faɗa, zasu iya kashe ki, ban da ogana da ya zo wurnki da su Walid, babu wanda ya san kin san ni waye"

"Yanzu har su Oga Walid basu sani ba"

Ya ce "Mmmm"

"Taɓ, sannu"

"Yauwwa, ya rahama da mamanta? Ina son zuwa da gaske kamar yadda ki ka ce, na ga halin da suke ciki"

Nabila ta ce "Akwai matsala, ciki ne fa da rahama"

"What ciki ta yaya?"

"Ya za ayi in sani, ciki dai, maman hankalinta ya tashi sosai da sosai, ta ce sai an zubar, wallahi na rasa yadda zan yi, gashi ta ƙi magana rahaman, muna son mu ji, kafin ya aureta cikin ya samu ko bayan ya aureta, amma na fi kyautata zaton bayan auren ta samu cikin, duk da bamu san meyafaru da wancan cikin ba da ta samu bayan ya mata fyaɗe"

Viper ya haɗiye takaici, ya tsani ya ga an ci zarafin mace, mussaman mahaifiyar ramma da aka watsa mata yara gaba ɗaya babu wani wanda ta amfana an watsa rayuwar su, kuma abin mamakin uba da ɗa ne suka lalata mata rayuwar yara"

"Bani adress ɗin in da suke zan je" yayi maganar a kausashe cikin damuwa.

"Ka bari muje tare, ina ga idan rahaman ta ganmu tare, ta yi magana, kayi haƙuri na san ranka a ɓace yake, amma babu yadda muka iya da ƙaddara" yayi shiru yana huci.

A raunane ta ce "Viper"

"Mmmm"

"Idan na mutu baka sadani da mahaifin jauhar ba, wanda nake kyautata zaton ina da alaƙa da ita ba, ba zan yafe maka ba"

Dummm haka ya ji maganar Nabila ta dira a tsakiyar zuciyarsa.

Viper "Kin san me ki ke faɗa kuwa? Ta ina ki ke da alaƙa da jauhar?"

Tuni ta fara kuka ta ce "Abubuwa da yawa, na fara sarewa, tun kan na ganka nake mafarkinka, bayan ban sanka ba, ban taɓa ganinka ba, ina da ciwon Athma da take gada nayi daga mahaifiyata, ita ce take da ciwon, familyn su na Jalingo da yawansu, Asma ciwonsu ne, ita ma ka ce ciwonta ne. Akwai abubuwa da dama, ba zan ɓoye maka ba, Wallahi idan Allah ya karɓi rayuwata baka sada ni na mahaifina ba, ba zan yafe maka ba" ta ƙarasa maganar tare da kashe wayarta.

***
Abba ya kalli Nasir ya ce "Nasiru, ya aka yi ne, an ce tun ɗazu ka ke nemana, na je wani wuri ne, ya aka yi?"

"Na haɗu da Arfa"

Abba ya ɗan yi sak, sannan ya ce "Tana lafiya" ya jinjina masa kai alamar eh.

"Haryanzu ba ta yi regreting abin da tayi ba kenan, shirun da nayi mata da zuru duk bata saduda ba kenan?"

"Babu alama, tare da ɗan daban suka je CID jiya"

"What? Aka ce mini tana barrack wurin yarinyar nan Halima goza, ina sane da duk halin da take ciki ai"

Nasir ya ce "Tare dai na gansu, tare da wasu 'yan daban ma, da sumayya"

Abba ya yi shiru cikin takaici, wai 'yan daba.

"Nabila ba ta da hankali, kuma bana tunanin zata yi shi, zan je na taho da ita, duk wadda za ayi sai dai ayi, basarwa kawai nake yi, amma hankalina yana kanta"

"Abba" ya kalli Nasir.

"A harabar wurin, ga abin da shi wanda take karewar ya bani"ya miƙawa Abba envelope.

Cikin matsananciyar faɗuwar gaba, ya kalli Nasir ya ce "Hoton da ta kawo mini wancan karon dama ba Photoshop bane?, Har na fara tunanin waye ya gaya mata wani abu"

"Abba ka san babu wanda ya isa yayi fatali da umarninka a cikin gidan nan"

Muryar Abba har rawa take ya ce "Shi wannan ɗin waye a jikin hoton?"

"Shi ne gayen, matarsa ce, ita ce ake shari'ar a kanta ai, ake zargin ya kasheta"

A zabure Abba ya tashi tsaye jikinsa yana rawa ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, kuma Nabila saboda mahaukaciya ce, ta tsaya masa take fafutukar a wanke shi, Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Nasir kira mini Nabila a waya yanzun nan".

Nasir ya ciro wayarsa daga aljihunsa, ya kira lambar Nabila, amma line busy.

Ya ce "Abba line busy" Abba jikinsa na ta ɓari, ya ciro ta sa wayar, ya jefawa Nasir, ya ce "Kira ta maza" sai dai tun tana cewa line busy, aka ce wayar a kashe take.

"Abba ta kashe wayar"

"Nasiru, tashi ka ɗaukko mota mu tafi barrack"

"Abba a daren nan, wajen gari ne wurin"

"Ka tashi na ce!" Yayi maganar cikin tsawa.

"Abba dan girman Allah kayi haƙuri, ka san ba zasu bari mu shiga yanzu ba, dan Allah ka yi haƙuri sai Allah ya kaimu gobe

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login