Showing 459001 words to 462000 words out of 479911 words
jikinsa ta ce "Kai ka san wata fanka, dama abin da ka ke nufi kenan, ka ke gaya mini zafi ka ke ji kwanaki, ko?" Ɗaga mata gira ɗaya ya yi yana murmushi.
Ta ce "Bari na duba girki"
Ya jinjina mata kai, ya sake ɗaga hoton Jauhar yana kallo, daga bisani ya mayar da shi in da yake.
Suna karyawa yana tsokanarta, wai a ina ta iya girki har haka, shi ya zata ba ta iya komai ba, kawai ajebo ce.
Dariya ta yi ta ce "Haba dai, boarding fa nayi har high institution, ace ban iya girki ba, girki yana cikin abubuwan da sukan sakani nishaɗi, da kuma kwalliya.
Abba ne baya son make up, girki kuma sai na ga ina so nake yi, Abba ya hana sakani girki, idan ba ni na yi ra'ayi nayi ba"
"Yar gatan Abba, gaskiya yana ji da ke sosai, dama har Jauhar shi ne ya riƙeta"
"Shi kansa ya yi wannan nadamar ai"
Ua jinjina kai ya ce "Maybe da shi ne ya riƙeta, da ba zan santa ba, Allah dai ya riga ya gama tsara komai, hakan ma mun gode masa"
Wayarsa ta fara ringing, ya ɗaga ganin lambar Abbu.
Suka gaisa, Abbu ya ce "Ina zamu yi, idan mun shigo Abuja?"
"Wai zuwa za ku yi?"
"Eh zuwa za mu yi, tun da kai ba ka ga ya dace ka sanar mana abin da ya faru ba"
"Abbu ka yi haƙuri, na yi hakan ne dan kar na ɗaga muku hankali"
"Koma menene gamu a hanya dai"
"To bari na turo maka adress ɗin"
Ya sauke wayar ya ce "Wai su Abbu su na hanya, ko wa ya gaya musu abin da ya faru, gashi an ta so su, next week na so mu koma gida fa"
Nabila ta ce "Sai a ɗora girki, kafin su ƙaraso, amma sai an yi cefane"
"Zaki iya kuwa, na ga jikin naki sai a hankali"
Murmushi kawai ta yi ta tashi tsaye, ta ce "Zan iya mana"
*****
Wani irin gumi ne yake tsatsafowa Indabo, cikin hasala ya ce "Wai wace irin Naja'atu kuma, ina ruwana da wata naja an kaita prison, iya ruwa fid da kai kawai a wannan gaɓar.
Nan na ɓoyeta, na saka ake yi mata visa a ɓoye, ta bar ƙasar amma abun bai yiwu ba, wannan jarabben yaron maye, ya kawo mana farmaki, gashi gidan jaridar da aka bawa kwangilar yaɗa labarin, an maka su a kotu kuma tara za a caje su mai yawan gaske. Ko dai mu biya musu, ko su tona mana asiri.
Gashi ba ni da tabbacin rundunar soja, za su ƙi faɗar ainihin abin da ya faru, dan su wanke Viper, gashi ministan tsaro ɗan uwan kankarofi ne, balle a sasanta komai yayi magana da su"
"Ka kwantar da hankalinka, zuwa jibi war haka, ka bar ƙasar nan, kujerar sanatan ka haƙura, ace ka tafi neman lafiya, idan Allah ya sa komai ya lafa sai ka dawo, koma ka yi zamanka a can".
Ayshercool
08081012143
*MASU JIRAN ƘARFE A WUTA COMPLETE DOCUMENT, ZA KU IYA PAYMENT A YANZU, A CIKIN SATIN NAN ZAI KAMMALA 1K VIA 0009450228
AISHA ADAM JAIZ BANK SAI SHAIDAR BIYA TA 08081012143
Yakice gumi Indabo ya yi, yana jinjina kai cike da gamsuwa.
Zakiyya kuwa, hankalinta ya kwanta bayan ganin hafsa ta koma gidan Alhaji mu'azzam, babu irin huɗubar tsiyar da ba ta yi mata ba kafin auren. Ta koma ta sakankance, hafsa zata din ga dumbuzo abin da ta samu ta din ga kai mata, domin kuwa har ta fara tsara irin rayuwar da za ta yi, a matsayinta na surukar ƙaramin minista a Nigeria.
Babu irin huɗuba da dabarun ha'inci, da ba ta koyar da hafsa ba, haka ba ta fasa shige-shige ba, cike da fatan a karon farko hafsa ta haifo ɗa namiji, domin idan kankarofi ya mutu su samu dukiya, domin kuwa yaransa mata ne. Amma tun da hafsa ta bar gidan, wata kusan shida, ko Kanon ma ba ta tako ba, sisi ba ta turawa Zakiyya ba.
Ta din ga kiranta a waya, a kan ta aiko da kuɗi, a sake bi mata malamai ayi maganin uwargidansa, kuma a kama mata shi, amma ta ce ita baya bata ko sisi.
Hafsa ta sanya wa ranta, a wannan karon ba zata yi asarar kuɗinta ba, babu wani mushiriki da zai sake cin sisinta, saboda ta mallake Alhaji mu'azzam.
Ta yi amfani da shawarar Jauhar, da ta bata tun tana raye, ta kama addu'a, da miƙawa Ubangiji lamarinta, tare da yi masa biyayya dai-dai iyawarta, sai kuma uwa uba gyara da take yi, yadda yakamata ba tare da ta yi abin da zai cutar da lafiyarta ko imaninta ba.
Sai dai mai rai ba a rasa shi da motsi, duk da irin kula da tattalin da Alhaji mu'zzam yake yi mata, ba shi da isashshen lokacinta, kuma har zuwa yanzu ya kan bi abin da matarsa uwargidansa take so, bai fiye son ɓata mata ba, gashi kusan kowane lokaci cikin aiki yake ba shi da lokaci.
A wannan karon ba ta yi yinƙurin yin fito na fito da uwargidansa ba, dan taga alamar baya son hakan, kuma ita rayuwa yar siyasa ce, a gabansa babu abin da ya yi mata zafi, da ko sako zancen matar, a bayan idonsa kuwa ba ta jurewa idan ta kira ko ta yi yinƙurin ci mata mutunci.
Kuma dai-dai gwargwado kankarofi yana sakar mata kuɗi tayi yadda take so, ko kyauta zata yi a gidansu, Baba take aikawa kuɗi, ta san koba komai kowa zai amfana a kan ace Anty kawai take bawa, dan ta san ƙarshen kuɗin a yawon bin bokaye zai ƙare.
Daf da azahar su Abbu suka iso gidan su Nabila, kafin nan tuni ta kammala abincin karɓar su.
Abbu ne da Baba da kuma Major suka zo tare.
Nabila ta yi farin cikin zuwansu sosai da sosai, sai dai Major yayi ta faɗa a kan yadda ba su faɗi abin da ya faru ba.
Major kawai kallon Nabila yake yi, yadda ta fututtuke da ba ta son auren, amma tayi ƙalau da ita.
Sun daɗe a gidan, sai da Major ya zaga a cikin barrack ɗin, suk sai juniors ɗin sa a aiki, duk sun yi retire.
Daga nan suka je gidan Alhaji mu'azzam, suka wurin hafsa, ita ma kamar ta taka dan murna, iyaye akwai daɗi.
Sai dai ba su daɗe a gidan hafsa ba, saboda yamma suka kama hanyar kano.
Nabila na kitchen tana ta ƙoƙarin yin wanke-wanke, Viper ya shiga kitchen ɗin ya tarar da ita.
"Sannu"
Ta kalleshi ta ce "Yauwwa"
"Ki na iya aikin a haka?"
Ta ce "Eh mana, me ka gani?" Yayi murmushi ya ce "Bakomai, dama dai shekaranjiya suka zo, yau na so nima na yi zaman jinya, anyway sannu Abla, na so na yi appreciating iskar fankar jiya unfortunately....
Katse shi ta yi da "Ni dai na ga ta kaina da wannan fankar"
Ya jingina da jikin bango, ya ce "Na yi ƙoƙari fa Abla, shekara ta nawa ina zaune haka, kodaye ba na gane komai sai 'yan kwanakin nan"
"Dan Allah vi ka ƙyale ni da zancen fankar nan"
Dariya ya yi ya ƙarasa kusa da ita, ya saka hannunsa a sink ɗin, yana tayata wanke kwanukan.
****
Abdul shi yake kai Ramma makaranta, haka idan an tashi, idan kuma yana da ayuuka da yawa da kanta take tafiya.
Mama sam ba ta son kaita makarantar nan da yake yi, tafi so ta tare, saboda gudun abin da aka iya faruwa, dan haka ta ya tan kunnen ramma, a kan lallai gara ta tare, can su ƙarata kar su ɗaukko mata magana a titi.
Allah ya taimaki Abdul, hankalin Indabo ba ya jikinsa, hatta ita mahaifiyarsa ba ta cikin hayyacinta, amma shi sam hakan bai dame shi ba, yadda zai gina rayuwarsa da ta rahama yake yi.
Surutun abin da ya faru da Bunkure kuwa, ya ci gaba da zaga wa lungu da saƙo, gaba ɗaya mutane suka din ga Allah wadai da yadda ta daɗe tana cutar jama'a.
Viper kuwa bai bari Nabila ta yi girki ba, ordern abinci ya kuma yi musu, yana ta lallaɓata.
Bayan sallar isha'i, ya kira Walid, yayi sa'a kuwa ya ɗaga.
"Mai laya"
"Mai zamani, ya gida ya ƙanwata?"
Viper ya ce "Lafiya ƙalau, tun ɗazu nake kiranka, su Abbu sun zo fa yau, har da sirikaina"
Walid ya ce "Kash, amma wallahi da na san za su zo, biyo su zan yi"
"Ai gara da baka sani ɗin ba, ka zauna ka kula mini da ƙanwata, tun la'asar na kiraka ai baka ɗaga ba"
"Sai magariba na ga missed call ɗin naka, muna asibiti ne, Shahida ba ta jin daɗi tun asuba muke can, sai magariba muka dawo"
Viper ya ce "What? Muhsin haka muka yi da kai? Daga aura maka yarnya ka haɗata da aiki, wane irin abu ne haka?"
Walid ya ce "Innalillahi me zamani meye haka wai? Fura ta sha ta ɓata mata ciki, take ta amai da gudawa muka tafi asibiti fa"
"Ba wani nan, laulayi ne, matsalar aurawa tuzuru yarinya kenan, gamo da kasawa sai wannan al'amari, to ni dai idan namji ne ayi mini takwara"
Kashe wayar Walid ya yi, jin abin da Viper yake yi masa.
Nabila kuwa sai kallon Viper take yi, dama haka yake da tsokana har haka, kuma yana yi yana wani mazewa, kamar ba daga bakinsa suke fitowa ba.
Shahida kuwa dariya take yi wa Walid, yadda ya dage yana yi wa Viper rantse-rantse.
"Wallahi my kana bani dariya, ya san kunya ka ke ji, shiyasa yake yi maka wasu abubuwan, ka fiye kunya, ni har dariya ka ke bani"
Yayi murmushi ya ce "Ai na fuskanci tsokanar ta wa yake yi kawai"
"My ka san sai yanzu na san Yaya Al'amin yana wasa da dariya, wallahi da ko kallona ba ya yi, ban taɓa zaton yana wasa da dariya ba"
Walid ya yi murmushi, yana shafa gefen fuskarta, ya ce "Ki daina tuna bayan nan, amma Viper mussaman lokacin marigayiyya, bayan ta fara saita mu, yana wasa da dariya, kin san rayuwar ta mu ce, duk sai a hankali sai godiyar Allah. To ya ki ke jin jikin naki yanzu?"
"Da sauƙi, amma ba zaka yi mini wayo ba, ni duk ka daina jin kunyar tawa yanzu"
"Ai mai zamani gaskiya ya faɗa, da ya ce matsalar a ba wa tuzuru aure kenan, bai iya cin ƙwan makauniya ba"
Tare suka yi dariya, cike da nishaɗi da jin daɗi.
Nabila kuwa ta ɗauka, yau za ta sake, ta samu isasshen bacci, dan tun da ta fara jinyar Viper, ba ta samun bacci, ta zata ya samu abin da yake so, zai bari yau ta yi bacci.
Amma sai ta riski abin da ba tayi tsammani ba, dan kusan gara jiya da yau, dan jiyan ƙyaleta kawai ya yi, yadda yake nanata zancen fankar nan, sai da ya tabattar mata da gaske tsawon lokacin da ya ɗauka, yana zaune haka ya dame shi, dan ta gazgata yadda yake ba wa fanka muhimmanci.
Ɓangaren Abdallah Liti, barkwancinsa ya sanya yake da mutane sosai a kasuwa, amma hakan bai hana shi yin faɗa da muzurai wasu lokutan a kasuwar, dan ma idon Abbu yana hana shi yin wani abun.
Sai dai Abbu yana jin daɗin aiki da su sosai da sosai, ba su da ƙyuya ko kaɗan, kuma ya sha jarraba amanar su, ba tare da sun sani ba, amma ko kusa ko da wasa babu wanda ya taɓa yinƙurin cin amana.
Sai da ya ƙara dana sanin ɗaukar su Abba ya ɗora su a kan harkokin sa, suka din ga ɗurka masa sata, suna cutarsa. Da su Al'amin ya riƙe, da yanzu dukkanin su, sun tsaya da ƙafrsu.
Sai dai ya yanke shawarar zai tallafa musu sosai da sosai, su tsaya da ƙafafuwan su, dan ya san bai isa ya biya su, wahalar da suka yi da ɗan sa ba.
Samunsu a kasuwar, ya sanya wasu lokutan ko zuwa baya yi, sai ya zauna a gida ya ɗan huta, ko yaje wasu sha'anunnunkan, za su kular masa da komai babu cuta ko cutarwa.
Idan yana cikinsu, sai ka ɗauka shi ne ya haife su, har shawara ya kan yi da su a kan harkar kasuwanci, bai yi da abokan sana'arsa ba, saboda su ba za su cuce shi ba ko su yi masa hassada ba.
Abbun ne yake tsokanar liti ya ce "Abdallah, kai haryanzu babu wadda ku ka daidaita ne? Su sun yi aure sun bar mini kai a haka fisabilillahi, yakamata ka motsa kai ma na aurar da kai"
Liti ya ce "Ai abbu wadda nake so ɗin kamar tafi ƙarfina, gani nake kamar ba za a bani ba" yayi maganar cikin damuwa.
Walid sai hararsa yake yi, yadda yake sakin jiki yayi hira da Abbu shi ba ya iyawa.
Abbu ya ce "Haba dai, ni da ina da wata 'yar ai da na baka, amma meyasa ka ce ta fi ƙarfinka?"
Jiki a sanyaye ya ce "To ai ana ganin ni ba mutumin kirki bane ba, ba kowa zai iya jihadin da ka yi ba Abbu"
"In ji waye ya ce maka ba mutumin kirki ba? Wannan wani abu ne da aka yi shi ya wuce, kuma yanzu Alhamdilillah, babu abin da za mu cewa Allah sai godiya. Kuma gaka da sana'a ka shiryu yanzu ba kamar da ba, in sha Allah za a baka, yar gidan waye idan ma baban naka ba zai tambayar maka ba, ni sai na wuce maka gaba"
Liti ya ɗan yi shiru ya ce "Ƙanwar matar mai zamani ce, wata Walida a gidan su take, 'yar major ce"
Abbu ya ce "Au to ashe ma 'yar gida ce, shi ne ka ke ta damuwa"
"Ina jin tsoro ne, gani nake kamar ba zai bani ba, kuma Walid ma cewa ya yi na nemi wata, ba lallai a bani wannan"
"Ita yarinyar kun daidaita? Kana zuwa wurinta ne?"
Ya jinjina masa kai alamar eh.
"An gama, ka fara tarin abin da ya sauwwaƙa ba zai gagara ba in sha Allah" washe baki liti yayi cikin matsanancin farinciki, Walid kuwa kamar ya mare shi, saboda ba ya jin kunya ko kaɗan yake wannan maganganun da Abbu.
Shahida ta je har gida gaida Abbu, ta yi masa farfesun kaza, taje gaishe shi, sai da ta tuna masa da jauhar, lokacin azumi ta saka Al'amin a gaba suka zo musu sannu da shan ruwa.
Rahila kuwa, ko kallon kirki ba ta yi wa Shahida ba, duk yadda shahidan ta din ga raɓarta, amma ta din ga hantararta, tana ƙarewa auren zagi.
****
Viper har tausayin Nabila yake ji, domin yanzu zaman ɗari-ɗari takeda shi, saboda yadda ya addabeta, har ta fara yi masa zancen, tun da ya ji sauƙi, zata koma Kano, hutunta ya kusa ƙarewa, ya ce ba za ta koma ba, shi ma an kusa sallamar shi, zai je hutu, sai su tafi tare.
Har murna take yi idan ya ɗan fita baya nan, ta samu ta ɗan sake.
Da ya dawo kuwa ta shiga fargaba da tashin hankali.
Da safe wurin ƙarfe tara da mintuna, Viper ya zuba wa Nabila ido da ta kasa tashi, take ta lumshe ido, alamar bacci bai isheta ba.
"Abla yau ba zamu karya bane ba? Yunwa nake ji fa"
Ta buɗe idonta da kyar, ta ce "Tun wurin 8 fa na tashi, na yi niyyar ɗora breakfast ɗin, kai ka hana ni, kuma ga wani irin bacci da nake ji" tayi maganar tana ci gaba da lumshe idanunta.
Ya saka hannunsa, ya shafi fuskarta, ya yi ƙasa da muryarsa ya ce "Na sani ki na haƙuri, amma ki ƙara kin ji 'yar sugar na, duk da wasu lokutan ki na yi mini bore, but am appreciating jazakillahu bil janna" ɗan ƙara sunkuyar da kai tayi, cike da jin nauyin sa, dan haryanzu tana jin nauyinsa sosai da sosai. Sannan ta jinjinawa ƙoƙarin sa, irin yadda ta din ga shishishige masa dan ta dawo da shi hanya, da keɓewar da suka din ga yi, amma ko da wasa bai taɓa yinƙurin yi mata abin da bai dace ba, wanda hakan ne ya sanya ta ƙara sakin jiki da shi sosai.
Maganar sa ce ta dawo da ita hayyacinta ya ce "Kin san wani abu kuwa?"
"A'a sai ka faɗa"
"Liti ne ya zo mini da wata magana, wai wata sisternki yake so, na manta sunanta, wadda muka tarar da baba uwani a wurinki a asibiti"
Ta buɗe idonta ta ce "Wai Walida?"
"Yes ita, wai sonta yake yi, amma ki na ganin Abba zai ba shi aurenta kuwa? Tun da kin ga ga tarihin rayuwar mu"
Nabila ta ce "Me zai hana, Walida tana da sauƙin kai, kuma ba ta da dogon buri ita da Anty mamanta"
Viper ya ce "Ina fatan ba zaki yi ramuwar gayya abin da yayi miki ba, ki saka a hana shi ita ba"
Nabila ta ce "Haba dai, ai wannan ya wuce, ai in dai tana son shi shikenan, mu dama fatanmu kullum idan aka samu wanda ya tuba ya daina ɓarna, al'umma su karɓe shi, a mutunta shi, in sha Allah ba zai gagara ba"
Viper ya ce "Mun gode sosai da sosai my sugar girl"
Dariya ta yi tana tashi zaune ta ce "Wai kun gode, kamar an yi wani abu"
"Bari idan muka karya, zuwa eleven, sai mu je na kai ki gidan hafsa"
Cikin murna ta ce "Amma na ji daɗi sosai da sosai, na gode Vi"
"Never mind, mu je ayi wanka, sai mu yi breakfast ɗin"
Ta ji daɗin zuwanta gidan hafsa, ko ba komai, ta rage zaman kaɗaici.
Ta din ga tsokanar hafsa wai anya ba ciki ne da ita ba, saboda yadda ta yi ƙiba.
Hafsa ta ce "Wallahi ba wani ciki Nabila, jiya na gama period kwanciyar hankali ce kawai da cin abinci, ni abin ya fara damuna ma,wata shida ko ɓatan wata ban yi ba"
"Kai hafsa, me aka yi da maza kwata kwata yaushe aka yi auren? Dan Allah kar ki ɗaga hankalinki"
Hafsa ta rausayar da kai ta ce "To, amma ina son yara Nabila, dan Allah ki yi mini addu'a, ka da Allah ya jarrabe ni da rashin haihuwa, ina son yara sosai da sosai"
Nabila ta ce "Dan Allah kar ki damu kanki, komai rabo ne kuma lokaci ne, daga yin auren ai yayi wuri ki fra wannan maganar" tayi ta kwantar mata da hankali, daga nan kuma suka ɓuge da hira, wanda galibi hirar ta karkata ga yanayin zamantakewar aure bawa junansu shawarwari, da zancen kayan likitar mata maman dr . Wadda cikin ikon Allah, magungunanta suka ɗaga darajarsu a idon mazajensu fiye da yadda suke tunani, ita mace ai yar