Showing 213001 words to 216000 words out of 479911 words

Chapter 72 - K.A.W Complete Hausa Novel

01 Jan 2025

6148

mini da yarinyar 'yar tofa ce, wai wani gari yaloko, amma bai san ina ba a tofa. Ni ban san ina ne ma tofan ba, balle na nemi gidan su yarinyar".

Barrister Habib ya yi shiru sannan ya ce "Kin tabattar a tofan ya ce miki take? A yalokon?"

Ta jinjina masa kai alamar eh.

"To shikenan, ki bani kwanaki i will get back to you. Amma ki daina garaje, ki din ga bin komai a hankali"

Ta ce "To" ya din ga rarrashinta, har ta huce, ta tashi ta koma office ɗin ta".

***

Tun da Abdul ya dawo, yake cika yana batsewa, ramma ko kallo bai isheta ba, ta cigaba da sabgoginta, ko abinci bai ci ba, ya nemi wuri ya kwanta.

Haushi ya ishe shi, gaba ɗaya ba ta tasa take yi ba, karatun littafinta ne kawai a gabanta, babu tsammani ta ji ya fizge littafin hannunta.

Ta kalleshi ta ce "Lafiya?"

"Wai ke wace iri ce ne?"

Ta kalleshi ta ce "Kamar yaya?"

"Ke baki damu da ki ga mutum cikin damuwa ba, ki tambayi meyafaru ba?"

Ramma ta ce "To ina ruwana da abun da ya dameka? Ni banda damuwar da ka saka ni a ciki? Bani littafina malam".

Abdul ya ƙura mata ido, ta tashi zaune ta miƙa masa hannu ta ce "Bani dan Allah".

"Me ki ke ganewa a ciki ne?"

Ramma ta ce "Ko ba na ganewa, ai gara na karanta littafin, da kallon fuskarka ma, bani littafina malam" ta yi maganar tana haɗe rai.

Wayarsa da take vibrating ya ciro, ya saka a kunnensa.

"Yau Yakamata ka shigo Asibiti, yau zaka yi wa patient ɗin ka tiyata fa"

Ya ɓata fuska ya ce "Yau ne amma baku tuna mini ba, ni na manta gaba ɗaya".

"An yi booking ɗin su, da wanda za su ganka, kusan wata biyu suna jira, ba su samu ganinka ba"

"Zan kira Doctor Anas,ya je yayi am sick, ba zan iya tiyata ba"

"Amma doctor... Cikin hargowa ya ce "Shut up, abun da na ce za ayi"

"To shikenan" ya ajiye wayar, ramma ta ce "Dama kai likita ne?"

"Ban sani ba, sai yanzu ki ga damar kula ni, saboda baki da imani, ki na kallo ko abinci na kasa ci".

"Kar Allah ya sa ka ci mana, kai har ka na bakin cewa wani bashi da imani Abdul yasar? Hala tsabar imanin ne ya sa kazo ka yi mini kurkuku a nan?"

"Ke fa taimakonki nayi, haka ki ka zo kalli yadda ki ka yi ƙiba, ki ka yi kyau, sai ma mun ci gwamnati, zaki fi haka ƙiba" yayi maganar yana taɓa damtsenta.

"Ni meye nawa idan ma kun ci gwamantin, in sha Allah ma ba zaku ci ba, ace a rasa wanda za su jagoranci al'umma, sai mutanen banza masu lalata yaran mutane " ya ce "Ok, Ai ba a wurinki muke nema ba"

"In sha Allah ba zaka ci ba, ko ƙuri'a ɗaya ba zaka samu ba"

Abdul ya ce "Ke ki ka sani, na je na ga yarinyar da aka ce zan aura, kyakykyawa nutsatiyya, tabbatar Allah ba ya karɓar addu'arki"

Da sauri ramma ta kalleshi ta ce "Nutsatiyya, ai ba zaka taɓa auren macen kirki ba, sai wadda wani ya lalata kamar yadda ka yi. Ai ko ka ganta a nutse ma, in sha Allah irinka ce zaka aura. Ba zan yi fatan Allah ya baka lalatacciyar 'ya ba, dan ba ita tayi mini ba, amma in sha Allah sai ka auri lalatacciya" tayi maganar tana hawaye.

Abdul ya ce "A'a gaskiya ba lalatacciya kamar ke ba, Nutsatiyya ce sosai, idan na aureta kar ki damu, ba zamu rabu ba, ai ana mugun tare tun da kin zama 'yar hannu kema.

Ta ce "Kai da Allah, kuma in sha Allah sauran wani zaka aura"

Abdul ya ce "Nima saurana wani zai aura, balle ba zamu iya rabuwa da juna ba, mun riga mun saba, ni zan iya aure, amma ke ba zaki iya ba, kawai mu cigaba da rayuwarmu a haka rahma".

Hawaye wani na bin wani ta ce "In sha Allah, sai Allah ya kuɓutar da ni daga hannunka azzalumi kawai" Abdul tamkar jin daɗin tsinuwar da ramma take yi masa yake ji, ta zage shi tayi masa Allah ya isa, amma hakan ko a jikinsa, sai ma cigaba da tunzurata da yake yi ya ce "Ohhh kishi a fili, ki dai yi a hankali, kar ki yi zurfi a soyayyata, 'yan mata ne da ni burjik"

"Eh tun da ga ka bunsuru ba" ta tashi tsaye tana kuka.

Ya ƙyaƙyace da dariya ya ce "Bunsuru ya ajiye akuya ta mussaman a gidansa ba" kalmar akuyar tayi mata ciwo, kawai ta fita daga ɗakin ta bar shi, yana ƙyaƙyata dariya.

***

Indabo yana ta shiri zai koma Abuja, hutunsu na majalissa ya ƙare, ga shirye-shiryen da ake yi na fara zaɓen fidda gwani, wanda yake ta fafutuka a tabattar da yarjejeniyar da suka yi na ba wa Abdul takarar mataimakin gwamna. Sai dai sai fama yake da shi, idan yayi nan sai yayi can.

Naja'atu Bunkure ce ta kira shi a waya, ta ce masa tana office ɗin sa na gidansa, tana son ganinsa.

Ya san muddin ta yi masa zuwan gaggawa ba bu sanarwa, akwai damuwa ne, dan haka ya ajiye abun da yake yi, ya fita.

Ya shiga ya zauna yana faɗin "Naja'atu masu ƙasa ya ake ciki ne?"

Ta kalleshi ta ce "Ina Abdul?"

"Oho masa, yana can tasa shiririta ya tattara ya koma gidansa da zama"

"Akwai ƙura fa"

Indabo ya ce "Wace irin ƙura kuma?"

"Yaya yayi da yarinyar da ya yi wa fyaɗe?"

Indabo ya ce "Mun yi magana da shi, ya ce mini ya kasheta"

"Ka tabattar da hakan kuma? Akwai matsala fa. Wata shegiyar yarinya ta zo office ɗina, wai na bata bayanan in da aka tsaya da maganar yarinyar, wai zata tsayawa mai gadin nan, hankalina ya kasa kwanciya jikina yana bani, ba itakaɗai take wannan abun ba, akwai abun da ta taka, duk da na kira law firm ɗin su na yi musu warning, amma jikina yana bani akwai wata a ƙasa, kar ta zurafafa ta gano wani abu, dan yarinyar a tsaye take babu alamar kunya a tare da ita".

Indabo ya ce "Kin daɗe kina magance matsaloli da rigingimun da Abdul yake ɗaukkowa, amma ya aka yi na ga karaya a tare da ke yau?"

"Ba karaya nayi ba, ka san hausawa sun ce, rana dubu ta ɓarawo, ɗaya tak ta mai kaya, na so ƙarasa aikin da kaina, amma ka ce na bari zai yi maganin abun, ka nemo ɗanka ka tabattar da bai bar wani trace ba, gobe in Allah ya kaimu zan tafi conference ɗin da shugaban ƙasa ya tura mu, dan haka ba zan samu damar zuwa gidan su yarinyar ba, dan haka ka nemo shi"

Indabo ya ce "Naja'atu, idan aka samu matsala the blame will be on you, sakacinki ne"

Naja ta girgiza kai ta ce "Sakacinku dai, na yi iya yi na ni, yadda ku ka yi da shi, ka sanar da ni"

Indabo cikin hanzari, ya ɗauki wayarsa yana kiran Abdul, sai dai wayar taƙi shiga gaba ɗaya.

Nabila har wata ramar dole tayi, saboda zirga-zirga, gashi kwana biyu ba ta je wurin Viper ba, gashi tana cikin damuwa da tsananin son ganinsa.

Gaba ɗaya yanzu ba ta doguwar shawara, kafin ta tafi gidan Viper, yau ma haka babu tsammani sai ganinta suka yi rana tsaka.

Duk suka bi ta da kallo, ta kalli Walid ta ce "Ina wuni"

"Lafiya ƙalau"

"Ya mutumina, ina fatan yana lafiya?"

Walid ya ce "To da sauƙi dai, yana ciki"

Liti ya ce "Wallahi ba zata shiga ba, ke ware, ni fa ban yarda da yarinyar nan ba".

Nabila ta kalli liti ta ce "Ka kiyaye ni fa, ba ruwanka da ni, ba wurinka na zo ba, wurin Viper na zo, zan duba lafiyar sa kuma mu yi magana"

Walid ya ce "Dan Allah liti ka daina haka, mana wai me ta yi maka ne, ta bayar da haƙurin abun da tayi ai"

Liti ya ce "Ni fa ba a iya yaudarata cikin sauƙi, fita malama, ba zaki ganshi ba"

"Ba zan tafi ba sai na ganshi, ba ruwanka da ni".

Ya zazzaro mata ido zai yi magana, ya ji an hankaɗe shi daga bakin ƙofa, Viper ya fito yana ƙanƙance idanunsa.

Suna haɗa ido, ta sakar masa murmushi, mai cike da nuna farincikin ganinsa, duk kallon na sa tsoro yake bata.

Liti ya ce "Mai zamani mai hakan yake nufi? Kai ma ka yarda da wannan munafukar, ita fa ta saka aka kama maka ni, aka rufe ni so take sai an kama ka fa".

Walid ya ce "Kai ɗin uwar me ka ke tsinana masa?"

Duk bai kula su ba, ya taka ya fito ya ɗauki brush da toothpaste, ya matsa.

"Ina kwana" tayi maganar tana bin bayansa. Bai amsa ba, ya durƙusa yana wanke bakinsa.

Wayarta da take ta vibrating ta ciro, ta saka a kunnenta ta ce "Hello"

"Ke Sumayya ce"

"Ohh sumy, kullum cikin sauya lamba kamar 'yar yahoo?"

"Malama kwana nawa ina nemanki a waya ban same ki ba, kuma baki neme ni ba"

Nabila ta ce "Sorry na yi laifi"

Sumayya ta ce "Yaya ku ka yi da Naja'atu baki gaya mini ba"

Nabila ta ce "Ke zan zo gida na baki labari, ina wani abun ne yanzu, dan na kusa rubuta resigning na ajiye musu tsiyar su, na fuskanci Naja'atu Bunkure gaba da gaba, naga gani take ita wata jan wuya ce, ko ban kaita ƙasa ba sai na razanata" gaba ɗaya suka zuba wa Nabila ido, cikin hanzari Viper ya ɗago ya zubawa Nabila ido, ta katse wayar ta ce

"Meyafaru ku ke kallona ne?"

"Naja'atu Bunkure" ya maimaita yana kallon idon Nabila.

Cikin rawar baki, saboda tsorata da kallon da yake yi mata ta ce "Ka santa ne?"

"Mu je waje mu yi magana"

Ayshercool
08081012143

52
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724


Jikinta ne ya hau tsuma, saboda irin kallon da yake yi mata, yayi gaba da nufin ta bi bayan shi, amma ta ƙi, ya tsaya ya waiwayo yana kallonta, ta kalli Walid, ya gyaɗa mata kai alamar ta bi shi.

Kamar mara gaskiya haka ta bi bayansa, sai da suka ɗan yi nesa da gidan kaɗan, sannan ya waiwayo ya kalleta ya ce "Me ki ke nema a wurina?"

Ta kalleshi ta sunkuyar da kai. "Ki yi mini magana, me ki ke nema a wurina? Meyasa ki ke sintirin zuwa in da nake? Idan so ki ke a kama ni, ki kawo su su kama ni mana, wace irin yarinya ce ke ne?"

Yadda yake maganar cikin hargowa, sai da ta ja da baya, saboda tsoro.

"Talk! Me ki ke so, waye ya turo ki?"

"Ni ba wanda ya turo ni" ta yi maganar cike da tsoro.

"Me ki ke nema?"

A sangarce ta ce "Ni ka daina yi mini magana a haka, tsorata ni ka ke yi, ni ban san me zan ce maka ba"ta yi maganar tana kawar da kanta gefe.

Ya tsareta da idanunsa, ita kuma taƙi ɗagowa, ta sunkuyar da kanta ƙasa tana haɗe fuska cikin tsoro.

Ya sunkuyo dai-dai tsawon ta ya ce "Ki bani amsa" tayi shiru ta ƙi magana.

Hakan ya ƙara hasala shi, ya buga ƙafarsa ya ce "Ki yi magana kan na saka ki yi ta ƙarfin tsiya"

Cikin rauni ta ce "Na gaya maka, ni babu wanda ya turo ni, ni na turo kaina, kuma ni tsoro ka ke bani ban san ta ina zan fara ba, tsorata ni ka ke yi"

Ba ta ƙarasa maganar cikin nutsuwa ba, ta ji hannunsa a wuyanta. "Naja'atu Bunkure, meye alaƙarki da ita? Ita ki ke yi wa aiki a kaina, da ita da Indabo ko?" Ba ta yi masa magana ba, sai idanuwanta da suka yo waje, ga hawaye na bin fuskarta, sai dai kallon da ta yi masa, ya sanya ƙirjinsa bugawa da ƙarfi, ya saketa ya ja da baya, yana dafe saitin zuciyarsa.

Dai-dai lokacin Walid ya ƙaraso ya ce "Viper meyasa ka ke haka ne? Ban sanka da cin zarafin mata ba, meyasa ka ke ƙoƙarin farawa yanzu?" Ya nuna Nabila da yatsansa, amma ya kasa magana sai haki yake yi, saboda zuciyarsa ta ƙi nutsuwa. Ta ƙura masa ido, tana kuka.

Kawai ya juya ya bar wurin, Walid ya ce "Sannu, kin ga abun da nake guje miki a kansa ko? Shiyasa na ce ki daina zuwa anyhow. Mun gode da gudunmawarki ga ɗan uwanmu, amma ki daina zuwan nan, ina tsoron yayi miki illa wataran".

Ta girgiza kai ta share hawayenta ta ce "Ina da kafiya wasu lokutan, haryanzu ban ji cewar zan karaya ba, da ya bi ni a sannu, da zan yi masa bayanin abun da ya haɗa ni da Naja'atu Bunkure. Kawai ji nake ya zame mini wajibi na taimake shi, ina son sanin ƙarshen labarinsa, har cikin zuciyata nake son ba shi gudunmawa, na yi masa uzuri, wataran ba zai yi mini haka ba, bari na tafi. Ayyuka sun yi mini yawa ne sosai, amma ina nan zan je wurin likitan ƙwaƙwalwar, zan kuma dawowa"

Walid ya girgiza mata kai ya ce "Rayuwarki fa, ke kanki zaki jefa kanki cikin hatsari"

Nabila ta share hawayenta ta ce "Kar ka damu da ni, shi ɗin a ceto rayuwar sa da hankalinsa, a ƙwato masa hakkinsa, ba a san amfanin da zai yi wa al'umma nan gaba ba, ina son kamo bakin zaren lamarin ne, bari na tafi" ta juya ta tafi.

Walid ya girgiza kai, duk haryanzu bai tabattar da manufar Nabila a kan Al'amin ba, amma a jikinsa yake jin ba zata cutar da shi ba.

Ya koma gidan su, ya tarar da Al'amin ya cika yayi fam, ya kalle shi ya ce "Mai zamani ba ka kyautawa gaskiya, shi yaƙi ɗan zamba ne, ko da turotan aka yi, sai ka bari mu bi komai a hankali, haka Ƙanwata tayi ta fama da kai, da wannan zafin zuciyar ta ka, ƙarshe ta zame maka sanyin idaniyarka. Ka din ga bin komai a hankali, bamu san mai gobe za ta haifar ba, kar ka daki kwano. Ina son mu ƙara zurafafa bincike a kanta, wanda na yi bai gamsar da ni ba"

"Mai laya"

"Viper"

"Ka ƙyale ni da maganar yarinyar nan"

Walid ya ce "Ba zan ƙyaleka ba, sai ka fuskanci gaskiya Viper".

Nabila tana tafe, tana mamakin dalilin da ya sanya Viper yake son kasheta wasu lokutan, amma meyasa ya rikice haka da ya ji ta ambaci Naja'atu Bunkure?.

Gaba ɗaya al'amuran case ɗin Viper sarƙaƙiyarsu ta yi yawa, a labarin da Walid ya bata, ba ta ji in da Najar tayi masa wani abu ba, kodayeke haryanzu labarin bai kammala ba.

Gida ta yi niyyar tafiya, dan kanta ciwo yake yi mata, amma kwana biyu ba ta haɗu da sumayya ba, kuma gashi ba ta bata labarin karonta da Naja'atu ba, dan haka ta kira nufi gidan radiyon su Sumayya.

***
Ramma na zaune na karyawa take kallon Abdul, yadda ya sha kunu, yana video call da wani likita, yana yi masa bayani, a kan wani result na patient da ya turo masa, yanayin yadda yake bayanin ya tabattar mata da ya san abun da yake yi. Sai da ya gama sannan ya rufe tab ɗin, ya kalleta ya ce "Kalli gabanki kar ki lashe ni"

Ta kwaɓe baki ta ce "Ban ga abun lasa a jikinka ba, jiki duk najasa".

Cikin ko in kula ya ce "Haka dai ki ke zaune da ni" tayi guntun tsaki, ta cigaba da tauna a hankali.

Can ta sake kallonsa ta ce "Abdul yasar"

Ya ce "Your excellency"

Ta ɓata fuska ta ce "Ba na son wata your excellency".

"Ke ba abun alfaharinki bane ba, ace ke yarinyar deputy governor ce ba"

"Malam ka daina zaƙewa ba zaka taɓa ci ba, ai shugaba nagari ake fata, kai idan ka zama shugaba ai ina ga sai ka halatta zina, tun da gaka bature, yahudawa ne abun koyinka"

Ya girgiza kai ya ce "A'a iskancin nawa bai kai nan ba"

Ramma ta ce "Ga wanda bai sanka ba ba, ni tambayarka zan yi, wai dan Allah da gaske kai likita ne? Mamaki nake yi" yayi mata banza yana shan tea.

"Taɓ, kura da fatar akuya, ba su san har giya ka ke sha ba, ashe wataran zaka yi kisan kai, ko ma in ce kana yi. Saboda irinka wasu mazan suke raka mata asibiti, dan tsaf zaka yi wa matan mutane ɓarna tun da ka saba" yadda ya dire kofin yana kallonta ne ya sanya ta sha jinin jikinta.

"Meyasa ba ki da ɗa'a?"

"Saboda ɗa'a muhalli ne da ita, nan kuma ba wurin da ya dace na nuna ta bane"

Ya jinjina kai ya ce "Haka ne, duk matar da na yi lalata da ita, ita ta kawo mini kanta, kar ki ƙara yi mini irin haka"

"Nima ni na kawo maka kaina kenan ko? Baka da kunya ko kaɗan, sai dai idan ka gama kumburin ka fashe, har abada mutumin banza ka ke a idona, 'ya mace ba ta taɓa mantawa da wanda ya kawar mata da mutunci, ko da kuwa ta hanyar aure ne, balle ta mummunar hanya, irin wadda ka yi mini, wallahi ban da zuciyar musulunci da tuni na kashe kaina na huta, kaf danginmu babu mazinaci, amma ni kalle ni yanzu. Tsaki yayi, ya tashi ya zai fice.

"Wallahi duk in da zaka je, Allah ya isata, na nan na bibiyarka har kabarinka" Dummm ƙirjinsa ya buga, ya waiwayo yana kallon ramma da ke ta uban kuka.

Bai taɓa dana sanin aikata duk wani laifi da yake yi ba, sai a kan fyaɗen da ya yi wa ramma. Galibin saɓon da yake yi, tsakaninsa da Ubangiji ne, ba a taɓa tsayawa gaba da gaba, ana tsine masa da yi masa Allah ya isa ba, ya sha attempting ya mayar da ita, amma sai ya ji ba zai iya rabuwa da ita ba, kuma kamar yadda take yawan faɗa, ya riga ya gama lalata mata rayuwa, ba za ta yi daraja a idon jama'a ba.

Motarsa ya shiga, ya tarar da wayoyinsa a ciki suka kwana, a buge ya dawo jiya tab ɗin sa ce kawai a cikin gidan, missed calls ɗin mahaifinsa babu adadi, ga na Naja'atu Bunkure, banda na mahaifiyarsa. Tunani yake yi ko lafiya ake yi masa wannan uban kiran hakan, shi ya san bai yi wani laifin ba balle ace.

Haka ya ja mota, ya nufi gidan su, yana jin yadda Allah ya isan ramma, ke ƙara

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login