Showing 207001 words to 210000 words out of 479911 words
tun a duniya Abdul yasar"
Duk da ya ji zafin maganganunta amma sai cewa yayi "Ko wanda ya raɗa mini sunan nan, bai kai ki iya faɗar sunan ba Rahama, Abdul yassar"
Kallonsa tayi tana kuka, haushin kanta yakamata da lokacin da yake waya, ba ta yi ihu a wayar ta ce a taimaka mata ba sace ta yayi. Yanzu ko wayarsa ta ɗauka ba zata iya operating ɗin ta ba, kuma ba ta da lambar wanda ta haddace balle ta kira.
***
Abba yana zaune yana kallon labarai a Aljazeera, Nabila ta shiga da sallama, yana kashingiɗe, ya tashi zaune yana murmushi ya ce "Barrister, kin yi mini wuyar gani da yawa fa, kullum na dawo kina aiki, baki dawo ba aiki ya hana mini arfana sukuni"
Tayi murmushi ta ce "Abba ni kaina ina kewarka, bana samun zama, yanzu na shiryu ai, ina aiki sosai da sosai, na san addu'a ka ke yi mini"
Ya ce "Kullum Addu'ata a kanku take, mussaman ke arfana, Allah ya yi miki jagora a dukkan lamuranki".
"Eh mu ma Allah ba zai tagayyara namu ba" Umma tayi maganar tana harar Nabila.
Nabila ko a jikinta ta ce "Abba dan Allah abu na zo roƙonka"
Ya ce "Ina jinki ƴar albarka"
"Abba dan Allah mota nake so, wallahi wahala nake sha samun napep, ayi ta haɗani da maza, ga zirga-zirga na yi ta kashe kuɗin mota, kuma haryanzu ni ba na yi wa client ɗina charges mai yawa"
Yayi dariya ya ce "Nawa ki ka tara?"
Tayi shiru sannan ta ce "Ina da 400k"
Ya kwashe da dariya ya ce "400k, sai dai a gyara miki tsohuwar honda ta"
Cikin shagwaɓa ta ce "Haba Abba, big girl kamar ni, da tsohuwar mota, ka taimaka Please"
"Babu komai, za a sai mota in sha Allah, amma da sharaɗi ba na son yawon babu gaira babu dalili, kuma ke zaki din ga zuba manki, ba zan sai mota na din ga cacar mai ba"
Cikin takaici Umma ta ce "Major mu fa? Muna zaune zaka saya wa Arfa mota, wannan wane irin rashin adalci ne?"
Ya kalleta ya ce "Da walida zan saya wa mota, ba zaki faɗi haka ba, ku fa da me? Ga mota nan ana kai ku unguwa a ciki, meye na kishi da 'yar cikinku? Ku daina haɗa kanku da ita, kun san abun da nake nufi".
Arfa ta tashi ta ce "Abba sai da safe" ta juya zata fita, ta yi wa Umma gwalo, a ranta ta ce "Saura ma babar su DSP idan ta ji, sai dai ku mutu".
Ta koma bedroom ɗin ta tana murna, ta ɗauki wayarta, Viper ya faɗo mata a rai.
Lambarsa da ta saka a wayarta, ta lalubo, ta zubawa ido, murmushi ta yi, ta kira lambar ta saka a kunnenta.
Yana zaune a kan katifa, yana ta shan sigari, zubawa lambar ido yayi, ya gaji ya ajiye wayar, ya cigaba da abun da yake gabansa. Ba ta gaji ba ta din ga kiransa babu ƙaƙƙautawa, har sai da ya hasala, ya ɗaga wayar, amma bai yi magana ba.
"Har na kusa fushi sannan ka ɗaga, na san da 'yar madara ce, ko ba ta san mai lambar ba, zata ɗaga kuma za ta saurareni, haka zalika zata yafe mini laifin da na yi mata. Akwai abubuwan koyi sosai da sosai a rayuwar ta, da ya ci ace ko ba duka ba, ka yi koyi da wasu, ba ta wulaƙanta ɗan Adam da tana yi, da ba ta riƙe ka da amana da tausayawa ba. Ina sake roƙonka yafiya, da kuma fatan samun haɗin kanka, ka ƙarasa mini labarinka da kanka, ina sha'awar kasancewa wani ɓangare na labarin nan, mai ban tausayi da ratsa zuciya Viper, sai da safe" tun da ta fara maganar, ya sunkuyar da kai, ya saki sigarin da take hannunsa, ya sunkuyar da kai hannunsa yana rawa. Ta gama maganar ta katse wayar, amma ya kasa ajiye wayar.
Sai da liti ya dafa shi ya ce "Maza yane?" Ya ɗago idanunsa ya kalli liti.
"Kamar Muryar wannan shegiyar yarinyar na jiyo a wayar, duk Walid ne da wannan sheɗancin"
Ya cigaba da ƙurawa Liti ido, babu abun da yake fata, banda ya zubar da hawaye ko na mintuna biyar ne, amma ko na sakan ɗaya ya kasa tsawon shekarun nan.
Murya a sanyaye ya ce "Liti"
"Na'am mai zamani".
"Ina kewar jauhar sosai"
Walid da da yayi musu shiru, dan ya lura daga Viper har liti haushin sa suke ji, amma maganar da Viper yayi yanzu ta sanya jikinsa ya yi sanyi, tausayin Viper ya ƙara kama shi.
"Da yanzu yarona ya isa shiga makaranta, wataƙila ma ta kuma haifa mini wasu"
Walid ya taso, ya dawo gaban Al'amin, ya riƙe hannunsa ya ce "Ka ƙara haƙuri mai zamani".
"Zuwa yaushe? Ko na ɗauki fansa kamar yadda nake buri da fata, kashe kaina zan yi saboda ba ni da wata makoma, idan kuwa hakan ba zai samu ba, zan koma in da na fito na ƙarasa rayuwata".
"Dan Allah maza ka daina irin wannan maganganun, kana karya mana zuciya wallahi " liti yayi maganar cikin damuwa.
Viper ya girgiza kai ya ce "Ba zaka gane ba"
Kawai ya gyara ya kwanta, gaba ɗaya suka kewaye shi suna kallonsa.
Nabila kuwa kallon wayar ta cigaba da yi, ta ce "Allah ya bani nasara a kanka, ya bani ikon taimaka maka".
Kira ne ya shigo wayarta, ta ɗaga ta saka a kunnenta, ta yi sallama.
"Wa'alaikum Salam da 'yar ƙwalisa".
"Wa ke magana?"
Yayi murmushi ya ce "Bawan Allah ne"
"To, ai kowa ma bawan Allah ne, wanne daga ciki?"
Yayi gyaran murya ya ce "Wani case ne da ni, nake so a taimaka mini"
Nabila ta yi hamma ta ce "Office zaka zo, ba ta waya ba" ta katse kiran, dan a zatonta irin samarin nan, ne masu kiran wayar mata anyhow, duk da Muryar wannan ba ta yaro ba ce.
Wani nannauyan bacci, yayi awon gaba da ita wanda babu abun da take yi ban da mafarkin Viper, dan sai da ta kusa makara yau.
Kwanaki uku da zuwanta wurin su Viper, ba ta sake zuwa ba, she's very busy, tana ta off and down na tattara hujjoji, duk da ana ta taɗiyeta, duk in da za ta bi ta samo shaida, sai a rufe, sai da aka aike da dattijon nan gidan kaso.
Gashi sai tayi ta sintiri a hanata ganinsa.
Kamar uba da ɗa haka Walid yake ta lallaɓa Viper ya ci abinci, sai dai ya cakala ya bari, ba ya cin abinci.
Private numbrn nan da ake kiransa da ita ce, ta kira shi, wayar tana ta ringing liti ya ce "Maza ka ɗaga mana"
"Me zan ce?"
Walid ya ce "Ko ba ka da abun cewa, ka ɗaga kawai"
Ganin ba shi da niyyar ɗagawar, ya sanya Walid ya ɗaga ya sakata a hansfree.
"Aminu Viper, kwana biyu. Ashe ta dawo maka da wayar. Alamu sun nuna kwana biyu ka yi sanyi, Kodayake kai sai an sakankance ka ke ɓarna. Gargaɗi nake sake yi maka, ka nesanta yarinyar nan da ga gareka, za a iya cutar da kai ta hanyarta".
"Ni nake da ikon yanke hukuncin abun da yake daidai da rayuwata, babu wanda ya isa ya juya mini rayuwa yadda nake so, ka cigaba da ɓuya ko ka bayyana kanka, zan yi abun da nake ganin shi ne dai-dai da rayuwata.
Mutumin yayi murmushi ya ce "Aminu Viper, shikenan idan ka ƙi ji, ba zaka ƙi gani ba ai"
"Babu abun da ban gani ba, dan haka na shirya ganin koma menene" ya katse wayar.
Liti ya ce "Duk walid ne ya janyo komai, ni na san a rina, wannan yarinyar idonta kawai zaka kalla ka gane munafuka ce"
Kallon da Viper yayi masa ne, ya sanya shi yin shiru, Walid yayi dariya ya ce "Ayi dai mu gani, za a gane waye mai gaskiya tsakanina da ku".
Liti ya ce "Ba wata gaskiya da ka ke da ita, ka dakatar da mu daga making moves, wallahi mun kusa fita operation kwanan nan"
"Ku fita yaƙi ma ba operation ba"
Haka liti da Walid suka kusa yin faɗa.
Tun ana gobe Nabila zata je wurin Naja'atu Bunkure, suke waya da sumayya, take bata ƙwarin gwiwa, a kan za ta iya, kar ta ji tsoro.
Da safe sai da ta fara zuwa wurin aikinsu, ta samu barrister Habib, shi ma ya ƙara mata ƙwarin gwiwa, da yi mata fatan alkhairi.
Cikin ƙasaita take fiya a farfajiyar office ɗin, har ta ƙarasa, mutane ta tarar jingim. Wanda galibin su mata ne, suna jiran shiga wurin Barrister Naja'atu Bunkure.
Kai tsaye Nabila ta shiga wurin sakatariyarta, ta nuna mata ID card ɗin ta, nan da nan ta bawa Nabila wurin zama, na ciki na fitowa ta yi mata iso zuwa wurin Barrister Naja'atu.
Tun a hanya take maimaita "la hula wala ƙuwwata illa billa". Har ta shiga wurin Bunkure.
Tayi sallama, ba tare da ta ɗago ta kalli Nabila ba ta amsa mata, ta ƙarasa ta zauna ba tare da an yi mata umarnin hakan ba.
Kayan jikin Nabila kawai ta kalla, ta fuskanci ba kalar gajiyayyun da suke zuwa wurinta bane ba.
Ta gyara zaman gilashin fuskarta ta na kallon Nabila.
"Sannu da aiki ma" Nabila tayi maganar tana murmushi.
"Yauwwa sannu"
Nabila ta ɗaga mata id card ɗin ta ta ce "I am barrister Nabila Yusuf maitama"
Bunkure ta jinjina kai ta ce "You look familiar to me"
Nabila ta jinjina kai ta ce "Na yi mamaki ma, da ki ka iya tuna kamar kin sanni, saboda na san jama'ar ne da yawa. Ni abun da ki ka yi mini ba zan taɓa mantawa ba har abada"
Bunkure ta ce "Ohh really"
"Yeah and i have a promise to fulfil, a dalilin abun da ki ka yi mini"
Ta kashingiɗa da jikin kujerarta ta ce "That's very good, ina son mutane masu yarda da kansu, ba na buƙatar sanin me nayi miki, ko kuma wani alwashi ki ka yi ba, ga ki ga bunkure Allah ya ida nufi "
Nabila ta ce "Na ji daɗi da ki ka ce Allah, dan kuwa shi ne gaba da komai, na gode sosai barrister"
"Mentioned not"
Nabila ta gyara zamanta ta ce "Yauwwa, ba komai ne ya kawo ni ba, na zo ne a kan wani case, duk da ba mu haɗu a court ba, an kai wanda nake depending prison, amma ban ganki a court ba sai wakilanki"
Bunkure ta ƙarewa Nabila kallo, sannan ta ce "Wane case ki ke magana a kai?"
"Yarinya da aka yi wa fyaɗe, ki ka ce kin tsaya mata, ni ce lawyer wanda ake ƙara, na je wurin 'yan sanda ana ta yi mini yawo da hankali, ina son doctors report, kuma ina son zan ga yarinyar zan yi magana da ita".
Naja ta yi wa Nabila kallon baki da hankali sannan ta ce "Kin san a gaban wa ki ke?"
"I am barrister Nabila, ba ruwana da a gaban wa nake, ina neman hujja ne da zan kare client ɗina"
"Nawa suka baki, ki ka samu ƙwarin gwiwar yin wannan kasadar? Zan ninka miki, ki ajiye case ɗin, kafin ki kunyata a idon duniya "
"Watch your words, it can be use against you a kotu, kin san me nake nufi, you are also a lawyer"
"Who the hell are you?" Bunkure ta yi maganar tana tashi tsaye, Nabila ma ta tashi tana sake ɗaga mata id card ɗin ta "Sai da na fara gabatar miki da kaina, sannan na gaya miki meya kawo ni.
Ko dai ki bani abun da nake buƙata kawai, ko kuma na fasawa duniya wacece ke?"
"Ni ɗin? Yaushe ki ka yi grduating, da me ki ke taƙama ki ke jin karanki ya kai tsaikon da zaki tunkare ni kina gaya mini maganar da ki ka ga dama?"
Nabila ta girgiza kai ta ce "Cikin dukkanin girmamawa ta seniority a aiki, nake faɗar duk abin da nake magana a kai. You were my mentor before, abun da ki ka yi mini ya tabattar mini you are green snake under green grass. Keep your eyes open, Barrister bunkure, zan iya baki mamaki a lokacin da baki zata ba. Zan cigaba da bibiyar case ɗin ramma, da ƙoƙarin wanke wanda nake karewa har sai na yi exposing ainihin gaskiya ko da kuwa ita ce ajalina" tun da ta yi face to face da ita, ta ji duk wata fargaba da tsoron da take ji sun kau.
Ta ɗauki jakarta, ta fita daga office ɗin.
Tsaki Bunkure ta yi ta daki tebur, ta ɗauki wayarta, ta danna ta kara a kunnenta.
"Yauwwa barrister Kabir ya kake?"
"Lafiya ƙalau manyan ƙasa ya aikin?"
"Normal ne, wacece Nabila a ma'aikatanka?"
Ya ce "Lafiya kuwa? Ya aka yi ki ka santa?
"Wacece ita, a id card ɗin ta na ga a wurinka take aiki"
Ya ce "Barrister Nabila, a law firm ɗina take".
"Ta zubawa kanta fetur a jiki, tana kuri, idan na ƙyatta ashana, ba ita ba har kai, zaka ƙone ƙurmus ka ja mata kunne, ɓera ba ya taka rawa a gaban mage, ko da kuwa tana kan gargara ne"
Kabir ya ce "Subhanallah, me ta yi?"
"Ka bincike ta, ba na bari ayi mini kuskure biyu, ko yinƙurin yi aka yi, ina daƙile duk wani abu da zai kawo mini cikas".
Kabir ya ce "Na fahimta, ki yi haƙuri dan Allah zan yi magana da ita, zan kuma ja mata kunne" ta ajiye wayar tana tsaki.
Cike da annashuwa ta fito daga wurin, tare da jin kanta tamkar ta yi facing ɗin babban abun tsoronta.
Ta tsaya a gefen hanya, ta ciro wayarta, ta kira Viper, ya ɗaga sai dai bai yi magana ba.
"Hello, ya jiki? Na san ba zaka yi magana ba, dama so nake na ji ya jikinka, na so zuwa na ganka amma rana tayi sosai, zan je wani wuri ne, ka kula da kanka sosai" ta katse wayar, ji yayi tamkar ya aikata wani uban zunubi, ya din ga bin wayar da kallo, yana tunanin yarinyar nan tana da hankali kuwa?.
Gida ta tafi cikin matsanancin farinciki, duk da ba su kwasheta da daɗi ba ita da.
Gida ta tafi ta yi wanka, ta ɗauki wayarta ta kira sumayya, amma line busy.
Ta ajiye wayar ta kwanta tana bacci.
***
Shiru shiru Abdul bai je kiran iyayensa ba, yana nan yana fama da kansa, kuma ya hana duk abokansa zuwar masa gida.
Duk da Allah ya isa, da fatan mutuwa da ramma take yi masa, hakan ba ya hanata tausaya masa, idan ciwon ciki ya murɗe shi, har mamaki take yi da ya ce mata ulcer ce, dan ita ta ɗauka yunwa ce take kawo ulcer, yaran masu kuɗi ba sa yi.
Da daddare yana kwance a kan gado, tana zaune a ƙasa tana karanta wani novel na turanci, da ta ɗauka a falonsa, duk da ba wani ganewa take yi ba, amma yana ɗebe mata kewa.
Tana ji aka kira shi a waya, ya ce yana zuwa, ya tashi ya fita.
Bayan ya fita, ta ɗaukko pillow, ta ajiye a ƙasa ta cigaba da karatunta.
Hamma da take ta yi ba ƙaƙƙautawa ne ya sanya ta gane bacci take ji sosai, ta tashi za ta rufe ƙofar ɗakin, kasancewar ya bar key ɗin ta ciki, dan ciwon cikin nan da yake yi, ta samu sassauci daga akuyancinsa.
Sai dai ta buɗe ƙofar falon ba ya nan, ta fito ta wuce kitchen, ta daɗe a kitchen, ta zubawa fridge ido, komai akwai na morewa rayuw a gidan, amma gaba ɗaya ba ta jin daɗinsu, saboda ƙazantacciyar rayuwar da take ciki.
Ta sha ruwa mai sanyi, ta cika cikinta, ta fito falo, sai dai abun da ta tarar ya sanya gabanta mummunan faɗuwa.
Cikin hanzari ya ture Nina daga jikinsa, ya yi tsilli-tsilli da ido, yana kallon ramma.
"Abdul wacece wannan?"
"Amm maid ɗina ce, mai aikina ce".
"Kamar yaya, ina solomon ɗin, shi zaman me yake yi? Me ka ke yi da mace a zaune a gidanka? Abdul kar ka raina mini hankali mana, karuwa ka ajiye Abdul?"
"Kar ki sake ce mini karuwa, ni ba karuwa ba ce, ke ce karuwa amma shi ki tambaye shi yadda aka yi na zo gidan nan?" Ta yi tsaki za ta tafi.
"Abdul ka yi mini magana wace banzar ce wannan?"
Abdul ya miƙe ya ce "ya isa haka, ki je gida za mu yi magana "
"Ban gane ba, ka gaya mini wacece wannan?"
Bayan ramma ya bi da sauri, Nina ta biyo shi, amma yana shiga ɗakin, ya mayar da ƙofa ya rufe da key ta ciki.
Ramma tuni ta kwanta wani abu mai zafi ya tsaya mata a rai.
"Rahma, ki tashi mu yi magana dan Allah, zan yi miki bayani" tayi masa shiru ta ƙi motsawa.
"Dan Allah ki tashi ki ji, zan yi miki bayani"
Ramma ta waiwayo sosai ta kalleshi ta ce "Ba ni zaka yi wa bayani ba, Allah zaka yi wa bayanin abun da kake aikatawa ba tare da tsoronsa ba. Ni baƙincikina, muzanta rayuwata da ka yi ne da wulaƙanta ni.
Ka yi zina da wasu, ko wankan janaba baka yi, ka zo ka kuma afka mini, wannan wace irin rayuwa ce, Abdul yasar ka gama da rayuwata, wallahi ko baka kashe ni, ina son kashe kaina na huta, dan dai kawai ina tunanin makomata ne, amma ka cuceni wallahi" tayi maganar hawaye na ta gangarowa ta gefen idonta.
Hannu ya sa yana share mata hawayen, amma ya kasa ce mata komai.
Ya numfasa ya ce "Kina ji na?"
"Dalla ƙyale ni, ba abun da zan ji, ni ƙyanƙyamika ma nake ji, mazinaci ƙazami mara tsoron Allah"
Duk da yadda maganganunta suka yi masa zafi, amma ya daure ya ce "Dan Allah Rahma ki daina kirana da mazinaci, kalmar nan na yi mini ciwo sosai. Wallahi tun a kanki ban sake zina ba, yanzu ba abun da ki ke tunani ba"
Aikuwa kamar ya tunzura ta, ta tashi zaune ta ce "Ni abun da ka ke yi mini menene? Na faɗa na kuma" ta sauka daga kan gadon tana huci, cikin ɓacin rai.
***
Naja'atu kuwa tana zaune a bakin gado, tana ta haɗa ƙwayoyi a cikin roba, ta na zuba ruwa a ciki, shiru ta yi tana tunanin maganganun da Nabila ta gaya mata, mamakin ƙarfin halin yarinyar take yi, yadda ake shakkarta da shakkar yin gaba da gaba da ita, ita wannan yarinyar zata yi wa cin mutunci haka. Me take nufi da za tayi exposing ɗin ta. Ta daki teburin gabanta ta ce "Wai ma wacece ita?" Ta yi wata ajiyar zuciya ta ɗaga kai, ta shanye ƙwayoyin cikin robar nan da ta narka.
Nabila ce zaune tare da