Showing 474001 words to 477000 words out of 479911 words

Chapter 159 - K.A.W Complete Hausa Novel

01 Jan 2025

6091

ita nata ya kusa shiga watan haihuwa.


Ramma na gida ta dawo daga makaranta, tana ta sauri ta gama abin da take yi, ta san Abdul ko ya dawo, ko ya aiko a ɗaukar masa abinci.

Kiran waya ta gani, da baƙuwar lamba, ta ɗaga tare da yin sallama.

"Matar doctor Abdul ce?"

"Eh nice"

"Ok, dan Allah maza ki taho Asibiti, Doctor ne ya yanke jiki ya faɗi"

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un" ta furta jikinta yayi wani irin sanyi.




Ayshercool
08081012143

Jikin ramma tsuma ya din ga yi cikin matsanancin tashin hankali da damuwa, fargabarta Allah ya sa ba wani mummunan abin ne ya faru da shi ba, dan kuwa yanzu a duniya tana matuƙar buƙatar Abdul a cikin rayuwarta.
Ko rasa shi tayi, ta san abu ne mai wahala samun mijin da zai tsaya a kan lamuranta kamarsa.

Hijjabi kawai ta zura ta fice daga gidan ta tafi asibitin da ya ce mata zai je ganin marasa lafiya.

Har an bashi ɗaki, yana kwance ana ƙara masa ruwa. Cikin tashin hankali da damuwa, take tambayar meyasame shi.

Wani likita yake yi mata bayani "Bamu sani ba, ya gama ganin marasa lafiya, aka kira shi a waya, ba mu san me aka ce masa bai fi mintuna sha biyar ba ya faɗi, amma ya farfaɗo ɗazu har yake ta kiran sunanta, aka yi masa allurar bacci.

Ta ɗauki wayarsa, ta saka thumb print ɗin ta, ta buɗe wayar.

Call log ɗin sa ta duba, ta ga wanda suka yi waya ta ƙarshe da shi Honorable speaker ta gani.
Ta kalle shi, ta san ba zai wuce a kan maganar mahaifinsa ba ne ba.

Tausayin sa ya kamata, ta matsa kusa da shi tana shafa kansa, yanzu da ya nutsun nan, har wani kyau ya yi na musamman.

Rashin ji da gagara ba su da wani amfani.

Aka kira sallar la'asar, ta shiga banɗaki ta yi alwala, tana fitowa taga Mummy da Anty Jidda a ɗakin.

Mummy ta ce "Ga shaiɗaniyar yarinyar nan"

Jidda ta kalli ramma, yarinyar da take mata aiki,  wahalalliyar 'yar ƙauye tayi ƙiba, fatar nan tayi kyau.

"Ramma, ke nake gani haka?"

Ramma ta dake ta ce "Eh, nice anty Jidda, kin yi zaton tozarcin da ki ka yi mini Allah zai wulaƙanta ni ne? Ai shi Allah yana kishin bawansa"

"Ramma ni ki ke gaya wa haka?"

"Ai ba tun yau ba, na daɗe ina fatan Allah ya haɗa ni da ke, na gaya miki abin da yake raina. Duk bauta da wahalar da nake yi miki da yaranki, iftila'i ya same ni a gidanki, ki nuna baki sanni ba, in haɗu da ke ma, ki ka toshe kowacce irin kafa, ki ka wulaƙanta ni, aka hana mu shiga gidan ma, babu wata magana mai daɗi ko rarrashi, saboda ni baitil mali ce mara galihu. To da yake shi Allah ba yadda ba ya juya lamuransa ai yanzu ku na gani, ko iftila'in zawarci ma ya ishe ki"

Buɗe baki suka yi su na kallon ramma.

Ko a jikinta ta sake cewa "Wallahi darajar mijina ki ka ci anty Jidda, amma niyya na yi na roƙi Allah ya sa yi wa 'yar ki abin da aka yi mini, a kan idonki ki ji abin da ni da uwata muka ji, sai dai kash ƙaddara ta riga fata, yaranki ba su suka yi mini laifin ba, kuma wanda ya yi laifin ya yi tuba na haƙiƙa, kuma na yafe masa har gaban abada, amma ba dan haka ba ba zan gushe ba ina yi miki fatan Allah ya jarrabeki ke ma, ko alhakin mai gadinki da aka kashe, ya isheku nauyi".

Mummy ce ta fara zage-zage, ramma kuwa ta tayar da salla, tare da jin sassauci a zuciyarta ko ba komai yau ta amayar da wani abu da yake ci mata zuciya.

Wani likita ne ya zo yayi musu magana, a kan ko su yi shiru ko su fita, Abdul yana buƙatar hutu.

Anty Jidda dai azabar mamaki ya hanata magana, kallon ramma kawai take yi, yarinyar da magana ma wahala take yi mata, amma ita ce ta zama haka take gaya mata magana.

Ramma ce ta hango Abdul yana motsi, ta tashi ta nufe shi da sauri, su Mummy ma suka yi kansa.

"Doctor, meyafaru ne? An kira ni aka ce mini ka faɗi"

Babban abin da ya ƙular da Mummy bai wuce yadda yake kallon ramma ba, ko ya nuna ya gansu.

"Rahama, embassy na Nigeria sun yi iya yin su an shiga an fita, ba za a iya fitar da Daddy ba, za a gurfanar da shi a gaban kotu" yayi maganar muryarsa na rawa.

Salati suka saka gaba ɗaya, dan su ba su ma sani ba sai yanzu.

Ramma ta riƙe hannunsa ta ce "Ka yi haƙuri Abdul, kowace rai akwai kalar jarrabawar da Allah subhanahu wata'ala yake yi mata, ka yi haƙuri.

Mummy ta ɗora hannu a ka ta fashe da kuka, ta ciro wayarta tana dannawa, Jidda na ta ba ta haƙuri, ramma a ranta ta ce "Allah ya ƙara, kaɗan ma ku ka gani, ni kam Allah ya ƙara shirya mini kai ya kare mini kai da ci gaba da aikata duk wani mugun aiki.

A zahiri kuma ta ci gaba da rarrashinsa, tana kwantar masa da hankali.

*****
Rahila Allah ya taimaketa, aka sallamota daga asibitin masu rangwamen hankali, sai dai duk tayi wani iri, tsufanta ya fito sosai da sosai.

Shahida ta zauna ta yi ta mata nasiha a kan tayi haƙuri, ta kwantar da hankalinta, kar ta ɗorawa kanta kishi, idan ba haka ba ta bari Abbu ya saketa ba ta da wurin zuwa ta zauna.

Shi kuwa Abbu, hankalinsa ya kwanta, Al'amin ɗin sa ya zama mutum, ya nutsu ya shiryu, ga maman ramma sam ba ta da damuwa da hayaniya, su na zamansu lafiya.

Abdul ya takura a asibiti shi a sallame shi, da aka sallame shi su ka koma gida, ko fita baya iya yi, abinci ma sai ramma tayi da gaske yake iya ci.

Ta kira mama ta gaya mata, mama ba ta taɓa zuwa gidan ramma ba sai lokacin, suka je tare da Abbu.

Duk da da sauran pain ɗin abun da Abdul ya yi musu a zuciyarta, amma sai da ya bata tausayi.
Ta din ga jinjina girman ikon Allah, ganin katafaren gidan da rammar ke ciki, komai na jin daɗin rayuwa dai-dai gwargwado akwai shi.

Su ka jajanta musu, Abbu ya yi ta yi masa nasiha, tare da nusar da shi muhimmancin addu'a da kuma juriya.

****
Nabila kuwa na ta rainon cikinta, da aka raba kayan jauhar, kayan jariran da suka saya, ya faɗo a rabon Nabila, ya tambayeta ta na so ko a sayar a bata kuɗin, ta ce kayan take so.

Major buni-buni, sai ya zo gidan Nabila ya dubata, cikin nan yayi girma sosai da sosai.
Gaba ɗaya ta zauna a gida ta daina fita, saboda duk wanda ya ga cikin sai ya yi magana.

Liti ya saka babansa a gaba, tun da ya ga ya san Major, yake ta yi masa nacin, yaje ya tambayar masa auren Walida, amma babansa yaƙi ya ce sai ya ga kamun ludayinsa sai ya ƙara hankali.

Abbu ya samu mahaifin liti ya ce masa shi ne yake tare da su a kasuwa, liti ya yi hankali sosai da sosai, kuma shekarunsa ja suke yi.

Da kyar ya amince ya yi wa Major maganar, amma ya yi masa bayanin komai.

Major ya ce "Ai ɗanka nawa ne prof, kuma tun da shi ma ya shiryu haka muke so, in dai yarinyar ta na son sa, Ubangiji Allah ya tabattar mana da alkhairi, dama tuntuni  yayarta Nabila ta fara yi mini zancen, idan kun shirya ku zo ayi magana kawai"

Liti har gida ya je ya gaya wa Nabila Major ya amince ya bashi auren Walida, tare da ƙara yi mata godiya, bisa ƙoƙarin da ta yi masa.

Cikin Nabila na ganin gata, domin kuwa tuni a wannan karon ma Viper ya fara sayayyar kayan jariri, idan ya tambaye ta zaɓi, sai ta ce ita duk abin da ya saya shikenan, ita dai damuwarta ta rabu da cikin nan lafiya.

Shahida ce ta fara haihuwa, matar Walid, daga kai ta asibiti cikin dare tana ciwon baya, aka ce ai ta kusa haihuwa, abin har mamaki ya bashi.

Viper ba ya gari, Nabila kuma ta yi nauyin da ba za ta iya fita ba, Walid baki yaƙi rufuwa, wai shi ne ya zama uba, Allah ya bashi ɗa namiji.

Liti har ya fishi murna, kamar ɗansa, ya din ga bin sa yana cewa "Saura ka saka masa sunan Viper, alhalin gani, sunana zaka saka masa"

"Kai a wa?"

"Ni a baban yaron mana, dan Allah Walidi ka saka masa sunana Abdallah, na san rashin m ɗinka, tsaf zaka saka masa sunan Viper, dan muraran ka ke nuna fifikon ka fi son sa a kaina"

Kafin suna Viper ya zo gari, Nabila ta so ta bishi ta je ta ga yaron, amma ya ce ba zata fita a din ga tanka ta ba.

Viper kamar ya tafi da yaron, ya din ga addu'a Allah ya nuna masa na sa haka shi ma.
Yayi masa addu'a sosai da sosai yaron.

Walid ya sanya sunan mahaifinsa Umar.

Dubu ɗari Viper ya bawa Walid, ya ce masa yayi haƙuri, abubuwa ne sun yi masa yawa.

Yanayin jikin Nabila, ya sanya Major ya tura Baba magajiya ta zauna da ita.

Sai dai idan Viper yana nan 'yar kallo take zama, sai dai ta yi ɗan aikace-aikacen gida. Hatta wanka sakata yake a toilet ɗin ƙurya ya wanketa, undeas ɗin ta, idan ta cire duk shi yake wanke mata.

Shi kansa ba ƙaramin tausayi take bashi ba, idan ta zauna shi ma cikin nasa zaman yake yi.
Zama sai da dabara, tashi sai da dabara, haka bacci ma, gashi tun da ya ƙara tsufa, take fama da matsalar numfashi, dan ma ba ta da yawan complain, sai dai shi ya fuskanci akwai matsala.

Sanin alaƙar da take tsakanin Sumayya da Nabila, ya sanya mijinta ba ya damuwa, da yawan zuwa gidan Nabila da take yi, duk wanda ya ganta sai ya tausaya mata.

Duk shagwaɓa da rigimar Nabila idan ba ta da lafiya, yanzu babu, sai dai idan an yi mata sannu ta yi murmushi kawai, gaba haka kurum take jin ta sare, kamar mutuwa za ta yi idan ta zo haihuwa.

Duk da ita ce abin tausayi, amma tana tausya wa Viper sosai da sosai, bawan Allah sai ya zauna ya zuba mata ido, duk motsinta tausayinta yake ji, da ta motsa zai tambayeta me take buƙata, me take so.
Har nauyinsa take ji, ta ce tana buƙatar wani abu.

Ana haka mama uwargidan baban su Nabila, Allah ya karɓi rayuwarta, duk unguwa ba in da zancen jinyar wulaƙancin da 'ya'yanta su ka yi mata bai je ba.
Nabila tana ji tana gani, babu roƙo da magiyar da ba ta yi ba, Viper ya ce sai dai ta yi addu'a daga gida, ba zata je ko ina ba.

Mutuwarta ta ƙara razana Zakiyya, ta din ga ganin saura ita.

Watan jaririn Walid biyu, Nabila ta fara naƙuda, tun cikin dare suka tafi Asibiti, amma har garin Allah ya waye ba ta haihu ba.

Tun da aka gaya wa Major da sassafe sai gashi a asibitin, ya zo ya tarar da su da Viper da baba magajiya, an fito da Nabila tana zagaya wa, ta samu wuri ta zauna a jikin Viper saboda ta gaji da zagayen.

Viper na gaida shi, amma bai ji ba, hankalinsa na kan Nabila, ya riƙe hannunta ya ce "Sannu Arfa na, ya jikin?"

"Da sauƙi Abba"

"Allah ya rabaki da cikin nan lafiya, ki ci gaba da addu'a kin ji, muna taya ki"

Ta jinjina masa kai, mai haɗe da yaƙe.

Duk wanda ya wuce ya ga Nabila, sai ya sake waiwaiwayawa ya kalli cikin nan.

Shahida ta kira wayar Nabila, dan tun yammacin jiya ta kirata take tambayarta, wai ya mutum yake gane naƙuda yake yi.

Viper ne ya ɗaga ya sanar mata su na Asibiti.

Shahida ta gaya wa Walid, lokacin bai fita kasuwa ba, ya cewa liti ya wuce kasuwa, zai fara biyawa ya duba Nabila, liti ya ce "Saboda ka rigani ganin ɗan mai zamani ko? To baka isa ba"

A asibitin suka haɗu, Walid jikinsa yayi sanyi, dan bai manta yadda Shahida ta din ga fama ba.

Liti ya zata abin wasa ne, ganinsu a zaune a harabar wurin a kan kujera, har tana shan shayi.

Wata Nurse ta fito ta ce mata ta daure, ta tashi a mayar da ita labor ward a sake dubata.

Da Nabila ta miƙe sai da gaban liti ya faɗi, tare da mamakin yadda aka yi tayi rayuwa da wannan cikin, duk da da hijjabi a jikinta.

Su na tafe idan ciwon ya motsa sai ta rirriƙe Viper, tana yarfa hannu tana ambaton Allah.

Liti ya ce "Walid gaskiya tafiya zan yi, idan ta haihu ka kira ni a waya,na ci gaba da zama a nan kuka zan yi, wallahi na zata haihuwar ba wahala"

Walid zai yi magana ya ga da gaske hawaye ne a idon liti, wanda liti da bakinsa yake cewa shi fa sai a shekara ko ƙwalla bai yi ba.

Wasa-wasa har Baba sai da ya zo asibitin, Nabila ba ta haihu ba, Viper ji yake kamar ya tayata ciwon, tun da cikin nan ya samu a wahala take.

Idan ta gaji, sai ta fashe da kuka, sai dai Viper ya yi ta rarrashinta, yana ba ta haƙuri.

Har sai da ya cewa Abdul, ko ayi mata tiyata kawai.

Abdul ya ce "Dan Allah ka yi haƙuri, lokaci ne zata haihu da kanta in sha Allah, haka kowace mace take ji. Babu tangarɗa a laborn dan haka a ƙara haƙuri.

Sai da ta kusa daf, sannan aka ce Viper ya fita waje, ya din ga sintiri a bakin ƙofa, yana addu'a, sai dai ya din ga tuna Jauhar, yana fargabar Allah ya sa kar wani abu ya samu Nabila da yaran.

Doctor Abdul Yasar, ma'aruf Indabo, shi ya karɓi haihuwar Nabila, ta sha wahala sosai da sosai. Dan bayan da jaririn ya faɗo, sai da ta kuma wani ciwon sannan ta biyun ta faɗo.
Hamdala ta din ga yi, tana yi wa ma'aikatan godiya, saboda gudunmawar da su ka bata.

Abdul ya ɗora mata jariran a kan ƙirjinta, ta rungume su, kawai ta fashe da kukan murna.

"Ya haiyyu ya ƙaiyyum ya zuljalalu wal ikram, ya Ubangijin Al'arshi ya Allah duk mai neman haihuwa in dai alkhairi ce , Ubangiji Allah ka bashi yara masu albarka, Allah ka bashi yara masu jin ƙai ababen alfahari ga addinin musulunci, Allah duk mai nema ka bashi, kamar yadda ka azurta Annabi Zakariyya Alaihissalam a lokacin da ya roƙeka. Allah na gode maka da wannan ni'ima, Allah ka raya mini yarana, ka shirya mini su"

Su ka din ga amsawa Nabila da Amin.

Viper ne kaɗai a wurin da labor room yake, su Major su na can waje.

Nabila ta sha ɗinki ciki da waje, ta ji yadda gaba ɗaya ɗakin ya cika da ƙarnin ƙazantar haihuwa, amma daga Abdul har Nurses ɗin, babu wanda ya nuna ƙyamar sa a gareta.

Aka shirya yaran tsaf, ita ma aka shiryata, ya basu wuri, nurses ɗin suka ƙarasa taimaka mata, ta shirya, aka yi mata allurai aka fito da ita.

Aka wuce da ita postnatal room, ana miƙo wa Viper yaran, amma bai bi ta kansu ba, ya nufi in da aka shiga da Nabila.

"Abla" ya kira sunanta.

Ta ɗago idanunta da suka yi jawur saboda wahala, ga bacci tana ji.

Rungumeta ya yi yana shafa kanta ya ce "Sannu my love, Ubangiji Allah ya yi miki albarka, ya dauwwamar da farinciki a rayuwar aurenmu"

Cikin shagwaɓa ta ce "Vi na sha wahala"

"Na sani sweetheart, na gani, sannu Abla. Alhamdilillah ala kulli halin. Na gode, na gode my world" yayi maganar yana sumbatar goshinta.
Hannunsa ta riƙe ita ma ta ce "Ni na gode da kasancewa tare da ni, ba tare da ƙosawa thank you very much" ya riƙe hannun nata sosai ya ce "Lokacin Jauhar na raye, ta din ga ce mini tsoro take ji, tana son na kasance da ita lokacin haihuwa. Allah bai amince ba, ban kasance da ita ba, amma na cika alƙawarin da na yi mata a kanki"

Nabila ta yi murmushi ta ce "Na yi mata addu'a sosai da sosai, Allah ya jiƙan 'yar madararmu"

"Amin my love"

Abdul ne ya shigo da jariran a hannunsa ya ce "Wai ba kwa san yaran ne? Ana ta rawar ƙafa a baka su, amma ka ƙi kallonsu, ga su nan an yi musu rigakafi, BCG da HB kafin mutane su fara zuwa ɗaukar su"

Viper ya yi murmushi ya ce "Sun wahalar mini da mata, shiyasa na ɗan yi fushi, amma tun da tana nan ƙalau, barakallahu fihum" yayi maganar yana karɓar su, cikin wani irin maɗaukakin farinciki mara misaltuwa.

Abdul ya ce  "Wannan boss ɗin da kai yake kama, fuskarka ce wannan" Viper ya yi dariya.

Su Major ne su ka shigo, shi ma sai da ya fara nufar gadon Nabila, ya tabattar tana lafiya.

Kan ka ce kwabo, Asibiti ya ɗinke da mutane, 'yan barkar Nabila.

Da liti ya zo duk jikinsa a sanyaye, ya din ga jerawa Nabila sannu, halin da ya ganta a ciki ɗazu, ya ƙara sanya masa tausayin mata.

Ya ja gefe aka miƙo masa jarirai.

Bai san lokacin da ya ce "Kan uba, kumbo, Viper wannan fuskar ai taka ce, ka ga jariri yadda ya haɗe fuska kamar zai kai duka. Allah ya baki juriyar tarbiyya, wannan zai yi taurin kai kamar babansa"

Ba wanda bai yi dariya ba, macen ce take ta tsotsar hannunta, tana buɗe idanunta tana lumshe su a hankali.

"Allah ya raya mana ke 'yar madara, Allah ya sa ki ɗaukko halin mai sunanki"

Viper ya ce "Har ka saka mata suna?"

"Eh gaskiya, na saka mata suna fatima zahra, 'yar madara"

Viper ya yi murmushi ya ce "Babanki ya saka miki suna, Allah ya raya ki bisa tafarkin addinin musulunci"

Bayan awanni shida aka sallami Nabila, gida ma da suka tafi, ana ta zuwa barka.

Washegari hafsa su ka zo Kano da Hafsa, Hafsa kamar a bar mata jariran nan.

Alhaji mu'azzam ya ce "Wannan dai na san 'yar madara ce, shi kuma ogan fa ya sunansa".

"Takwara na yi muku kai da Abbu, Ibrahim ace masa mu'azzam ko Khalil"

Ita kanta Nabila ba ta zaci haka zai yi ba, ta ɗauka sunan Nura yayan ramma zai saka"

Alhaji mu'azzam bai taɓa zaton Viper zai yi masa kara haka ba.

"Masha Allah, amma na gode sosai da sosai, idan ina da rabo nima Allah ya bani ɗa namiji, Allah ya

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login