Showing 249001 words to 252000 words out of 479911 words

Chapter 84 - K.A.W Complete Hausa Novel

01 Jan 2025

6185

so bin bayan sumayya, amma sai ta fasa, Sumayya ta faɗi maganganu masu muhimmanci, da yakamata ta tsaya ta ji menene, amma sumayya ba ta fushi, idan kuma tayi tana da wahalar sha'ani, dan haka bata bi bayanta ba ta koma wurin barrister Habib da wannan matan.

***
Ƙarfe biyar Al'amin ya koma maɓoyarsu, bayan su Walid suna ta fama da shi, ya ce a sallame shi, sun ce sai ya gama warwarewa, shi kuma ya san akwai hatsari zamansa a asibitin, suna fita salla ya fice daga ɗakin, ya bar Asibitin.

Sai dai yana shiga ɗakinsa, ya tarar da wata baƙar rigar, irin wadda aka ajiye masa da safe a asibiti, ya ɗaga ta ya juya, irin waccan ce sak.

Ita ma a take ya yayyagata, ya watsar, ringing ɗin waya ya ji a ɗakin, ya duba ya ga wata ƙaramar waya keypad, wata lamba ce ke kiran wayar.

Ya ɗaga ya saka a kunnensa.

"Al'amin Viper, ka daina jayayya da ƙaddararka, bin wannan ƙaddarar itakaɗaice mafitar da ta rage maka, ka karɓi kayan da muka baka, ka dawo gida Viper" aka katse kiran, ya bi lambar, amma aka ce lambar dose not exist. Yayi jifa da wayar ya ja da baya ya tsaya yana huci.

Ayshercool
08081012143

60
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724

Ya cigaba da zazzare ido, yana kallon ɗakin, ya ɗauki wayar da ya watsar, ya sake haɗata, ya kuma kiran lambar, amma a sai ace masa lambar dose not exist.

Ya fita waje, ya zagaye gidan yana dube-dube amma bai ga kowa ba, ya koma cikin gidan ya ɗauki wayar da rigar da ya yayyaga, ya shiga banɗaki, ya watsa su a masai ya fito.

***
Nabila kuwa bayan tafiyar sumayya, ofishin Barrister Habib ta koma, suka sake gaisawa da matan nan, ya ce "Ina sumayyan?"

"Ta tafi gida ne, na ce gani me yake tafe da su ne?"

Ya kalle su sannan ya kalli Nabila ya ce, maganarki da ki ka yi, su sumayya T ladan suka saka a radio, a kan Barrister Naja'atu Bunkure, shi ne ya sanya suka zo, su sanar miki da wasu abubuwa da zai taimaka miki".

Nabila ta ce "Masha Allah, bari na aika baba masinja, ya sayo musu ruwa da lemo, naga azahar ta wuce, kafin nan nima nayi salla"

Ya ce "To babu laifi"

Tayi salla ta dawo, suka zauna da matan, ɗayat ta fara bata labarin abun da ya faru "Ni 'ya ce da ni, mun rabu da mahaifinta, tana wurin babanta, yayi mata auren dole, take ta guje-guje saboda ba ta san mijin. Ake ta fama har tayi yinƙurin kashe kanta, magana har gidajen rediyo, ta turo wakilanta, suka tafi da mu can office ɗin ta, ta ce aure ba dole bane ba, dan haka dole a kashe auren nan. Da fari na so ayi sulhu yarinya ta koma ɗakinta, tun da bama tare da ubanta.
Na din ga yi mata nasiha, a kan tayi haƙuri, tun da babanta yana ta tsine-tsine a kan ta bujire masa, ta haƙura ta yarda, amma matar nan ta ce sai an kashe auren, zata kai ni ƙara hukumar kare hakkin ɗan Adam, ta ɗauke mini 'ya, ta tafi da ita, sai da aka yi sati biyu sannan ta dawo mini da ita ga babanta da mijinta suka ƙara matsa mini lamba, bayan ta dawo da ita, yarinya ta ƙara tuburewa ba ta san zancen aure ba.
Tamkar an canza mini ita, idonta ya buɗe, har mijin 'yar tawa ta saka aka kama aka rufe, aka kashe auren nan. Yanzu maganar da nake yi miki, shekru uku kenan, yarinyar nan ta ce aure wani abu ne al'ada da muke takurawa kanmu a kai, addini bai wajabta mana ba, haka take rayuwarta, sai ta shafe kwanaki ba ta gida, tana yawonta. Babanta ya sallama mini ita, bayan ya gama tsine mana daga ni har ita. Har a cikin unguwa ta cigaba da yi wa sauran ƙasayenta mummunar huɗubar adawa da aure, wai ana tauye musu hakki, kuma wallahi Naja bunkure ce ta mayar mini da 'ya haka,tana fakewa ne kawai da taimako, tana zaluntar mutane".

Ɗayar ta ce "Nima kusan hakan ne, wani yaro ɗan masu kuɗi, ya lalata mini yarinya daga aikenta gidan, jami'an tsaro suka ƙi kama yaron, uban ɗan ya ce in dai arziki yana rana, zai kare ɗan sa, ba wanda ya isa ya kama shi ya hukunta. ni kuma jin shirye-shirye da ake yi a kanta, na taimakon marasa galihu, ya sanya nima na je neman ta taimaka mini. Da farko abu kamar gaske zata taimaka mini, ƙarshe abun ya juye, aka nemi a mayar da case ɗin wai sharri muka yi wa yaron.
Wallahi ƙarshe yarinyata fiya-fiya ta sha ban sani ba, yar shekara goma sha huɗu ta mutu. Wallahi matar nan azzaluma ce, bamu da wurin da zamu je, mu nemi hakkinmu sai wurin Allah, haryanzu idan zance yayi zance a kan tayar da maganar abun da ya faru da yarinyata, wanda hakan ba ƙaramin tsaye mini yake yi ba" tayi maganar tana kuka mai ban tausayi.

Nabila ta tashi ta rungume matar, tana rarrashinta ta ce "Ki yi haƙuri dan Allah, ki kwantar da hankalinki, Allah ya jiƙanta, kuma in sha Allah da ikon Allah sai mun kai matar nan ƙasa, zan yi iya yi na, in bankaɗo duk wani mugun abu da ta aikata muku, kuma sai ta girbi abun da ta shuka, ku yi haƙuri. Yanzu duk zaku bani adress ɗin ku, zan bi cases ɗin ɗaya bayan ɗaya, na tabattar da abun da ya faru kafin na san abun yi"

Jikin Nabila yayi sanyi sosai da sosai, da jin abubuwan da Bunkure take aikatawa, tamkar ba 'ya mace musulma ba, da matan ke iƙrarin ciwon ƴa mace, na 'ya mace ne.

Har kuɗin mota ta basu, bayan tafiyarsu ta kalli barrister Habib ta ce "Yaya habib, ka ji wani yahudanci? Ina laifin ta tsaya a kan iya kashe auren an yi wa 'yar auren dole?"

"Ke ce baki san wacece ita ba sai yanzu, wannan wata ɓoyayyiyar aƙidarta ce, na bawa mata damar ƙin zaman aure da lasisin karuwanci. Tana saye yaran da kuɗi, da abun duniya wurin cusa musu wannan mummunan ra'ayin, da koyar da su daidaiton jinsi tsakanin su da maza".

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, amma duk da haka Alhamdilillah, na samu hints a kan yadda zan bankaɗo asirin matar nan, and one more thing kuma" ya kalleta ya na jiran me zata ce.

"Maganar da muka yi da kai kwanakin baya, a kan case ɗin Aminu Viper"

"Ina jinki"

"Naja'atu Bunkure tana cikin tawagar lauyoyin da suka tsaya kai da fata a kan shari'ar da aka yi masa. Kuma ka san ita ungulu ce ba ta jewar banza, dan haka akwai manufa a cikin shiga shari'ar da tayi. Viper ba ɗan siyasa bane ba, kuma ba shahararren mai kuɗi bane ba, balle ace tsaya masa tayi a shari'ar. Dan haka akwai ayar tambaya a kan charges ɗin da aka yi masa na kisan kai.
Take a look at it barrister, an tsare mutum shekara biyar, an yi masa shari'a sau biyar kawai, an kai shi prison an ajiye babu conclusion na shari'ar, is je guilty or innocent? Kwatsam an ce ba a ganshi a prison ba, kuma an cigaba da nemansa, ruwa a jallo, anya akwai gaskiya a lamarin nan kuwa?"

Ya tsura mata har ta gama, yayi murmushi ya ce "Haka kwanyar nan take cike da basira, amma aka ƙarar da ita a wurin iyayi da kwalliya?.
Maganarki gaskiya ce Nabila,  amma ina rabaki da case ɗin Vipern nan, akwai badaƙala sosai a kan case ɗin".

Nabila ta ce "Me da me ka sani a kai?"

"Nothing much, kawai na san dai akwai bita da ƙulli ne a ciki sosai"

Ta jinjina kai ta ce "Haka ne, bari na tafi gida, yau a matuƙar gajiye nake" tayi masa sallama, ta tafi office ta ƙarasa shirinta, ta tafi gida. Ta sake karo da file a office ɗin.

Cikin mamaki ta ɗauka, ta fara buɗewa.

Aka rubuta continuation a ciki.

Cigaban tarihin Naja bunkure ne, bayan rape da aka yi mata, cousin brother ɗin ta, aka rufe case aka ce abu ne na dangi, bayan ta ƙara girma tayi aure, ta sha wahala sosai a hannun mijinta na farko, ya azabtar da ita tamkar baiwarsa, ko haihuwa ba ta yi ba auren ya mutu.
Yayanta ne ya taimaka mata, ya mayar da ita makaranta, tayi candy, ta shiga jami'a, sai dai bayan rasuwar yayanta, aka rasa mai sponsiring ɗin ta, ta cigaba. Mahaifiyata na can wani garin tana aure, babanta kuma ya ce ba ruwansa da ita, tun da taƙi zaman aure.
A lokacin har wurin ɗan majalisar su, ta je neman kuɗin makaranta, lokacin yana tare da Indabo, indabo ya ce zai bata, amma sai dai ayi bani gishiri na baka manda. Ta amince tun daga nan, ta zama tamkar matarsa su watse ya biya mata kuɗin makaranta, babu wani sirri nasa da bata sani ba.

Ta nemi ya aureta, bayan tayi graduation, amma yaƙi, ganin haka ya sanya, ta samu wani suka daidaita ya aureta, sai dai Indabo ya cigaba da bibiyarta.

Ta fara aiki a matsayin lawyer mai zaman kanta, Naja tana da burin yin luxry life sosai, sai dai mijinta yana da rufin asiri amma ba irin wanda take hange ba, Indabo yayi mata alƙawarin haɗa ta da manyan mutane, lokacin ya zama ɗan majalisa, wanda zata din ga samun alkhairi da damarmaki.
Kwaɗayi da buri, ya sanya suka koma ruwa da aurenta, ya din ga kashe mata kuɗi, yana kuma haɗata da manya. A wurinsa ta koyi shaye-shaye. Tsakanin ta da mijinta babu ragayya ko kyautatawa, duk son da yake nuna mata da kulawar da yake bata sam baya gabanta.

Ta fara tashe sosai tana shahara, ana programs da ita a kafafen watsa labarai, ta buɗe ƙungiyar ta ta kanta, bayan joining ɗin ƙungiyoyin yahudawa, masu da'awar daidata jinsi, reshen Nigeria, ta cigaba da yi musu aiki ta ƙarƙashin ƙungiyar ta.

Sai dai a haka take miyagun harƙallarta, na yi wa manyan mutane safarar mata a birnin tarayya, musamman ƙananan yara, da akan yi amfani da su saboda asiri.

Red handed mijinta ya kamata, chats ɗin ta da wani minista, na ƙazanta, yayi kuka, amma ko a jikinta, ta ce idan ba zai iya ba ya rabu da ita. Haka ya saketa, ta samu cikakken gashin kanta.

Ba ta taɓuwa, ko da kuwa tayi laifi, yanzun nan ƙungiyoyin kare hakkin ɗan Adam zasu shiga lamarinta. Ta din ga binne mutane ta hanyar bayyana musu kyawawan ayyukanta, da ɓoye na laifin.

Bayan mutuwar aurenta labari ya bazu, mutane suka din ga tsinewa mijinta, wai ya saki macen kirki, aka yi hira da ita, ta din ga kuka tana yi tsohon mijinta sharri kala-kala.

End the story.... Aka rubuta a ƙarshen page ɗin.

Wani irin gumi, ya din ga tsatstsafowa Nabila, ta ma rasa abun yi, da tunanin da yakamata tayi, ba ta bari ta takura ƙwaƙwalwarta wurin hasaso waye ya kawo mata file ɗin a karo na biyu ba, kawai ta ɗauki jakarta ta fita.

***
Sumayya ce a tsaye tana kuka wiwi, shi kuma ya zuba mata ido, ko ƙiftawa baya yi, sai da tayi mai isarta sannan ya ce "Kukan ya isa haka, meyafaru?"

Ta share hawayenta ta ce "A gaskiya sir, ni na gaji da aikin nan, na samu matsala da ni da Nabila, ni Nabila ba ƙawata ce kawai ba, ƴar uwata ce, ta riga ta yi fushi, ba zata saurare ni ba, ni ban san wanda ya gaya mata ina bibiyarta ba, ga wancan honorable ɗin ya addaba mini, duk motsina sun sani, sai kuma sun tambaye ni, me tayi me take ciki, banda barazana da suke yi mini ba yau ba gobe, ni dai dan girman Allah ka yi wani abu a kai, kar ni ko ita ayi wa wani illa, indabon nan fa ba imani ne da shi ba" ta ƙarasa maganar tana sake fashewa da kuka.

Yayi murmushi ya ce "Haba ƴar jarida, ya da kuka wiwi haka da karaya nan da nan? Da kin sanni, kin san zan taimake ki? Baki san ya aka yi na gane Indabo yana yi miki barazana ba. Har na shigo lamarin ba, dan haka ba zan bari a cutar da ku ba, dukkaninku a kan gaskiya ku ke, sai dai ita naga buyaginta yayi yawa.
Ki yi haƙuri ku daidaita, da haka zan cigaba da yi mata supplying abubuwan da take buƙata a harkar shari'ar nan"

"Sir yanzu fa ka gama cewa buyaginta yayi yawa, sai ce mini munafuka take yi, babu yadda tsakanunmu yanzu"

Ya ce "No, tayi fushi ne kawai, and ki ƙara kiyayewa sosai da sosai, ki daina bari tana gane kina bibiyarta".

Sumayya ta ce "Yanzun ma, wallahi ina kiyayewa, ban san yadda aka yi ba"

Ya din ga rarrashinta, sannan ya saka aka ɗauke ta a mota, aka mayar da ita gida.

***
Nabila da ƙyar ta isa gida, ta watsar da kayan a kan gadonta, ta fara kiran wayar Viper, amma a kashe, ta kira ta Walid amma baya ɗagawa, haka ta haƙura ta shiga banɗaki tayi wanka ta yi alwala ta fito.

Har washegari da safe, Nabila tana neman layin Walid, hankalinta ya ƙara tashi, tayi tunanin ko wani abun ne ya same shi.

Tana saka kayan abinci a motarta, Nasir ya fito.

Ta ce "Yaya ina kwana?"

Ya amsa da "Lafiya ƙalau, wai ina ki ke zuwa da kwanukan abinci kwana biyun nan ne?"

Ta ɗago ta kalleshi ta ce "Ci nake yi mana, wataran ai wuni nake yi bana gida"

Ya ɗage kafaɗa ya ce "Ban sanki da dakon flask ba, saboda haka kin gwammace ki ci biscuit da sauran kayan ciye-ciye"

"Haba yaya, yanzu ba mota ce da ni ba? Kuma zan je in ta cin abinci nikaɗai duk ga mutane ne a wuri?"

Ya girgiza kai ya ce "A'a, amma yanzu ƙarfe bakwai saura kwata, har shida da rabi kin fita, saɓanin da har goma saura sai ki kai a gida"

Ta tsaya sosai ta dube shi ta ce "Yaya me kake nufi ne? Ka daina ɓoye-ɓoye ka fito fili ka sanar mini cewar, tuhumata kake yi, da aikata rashin gaskiya mana"

Yayi murmushi ya ce "Ai ba a tuhuma sai an tabattar da zargi my dear"

"Da ka daina zargin, dan wahalar da kanka kawai zaka yi, ko kuma irin abun naku zaka yi mini na masu kaki" tayi maganar tana murmushi.

Shi ma murmushin ya yi, ya ce "A sauka lafiya"

Ta amsa da Amin ta tafi.

Tana tafe a hanya sai ga kiran wayar Walid, ta ɗaga wayar ta ce "Oga Walid, sai kiranka nake yi a waya, shi wayarsa ba ta shiga, wayarka kuma baka ɗagawa"

Walid ya ce "Bari kawai, kin san halin mutumin naki sai a hankali ai, jiya bayan tafiyarki, ya kafa mitar sai an sallame shi daga Asibiti, da mu da likita muka din ga rarrashin sa, yayi mana banza, mun fita salla ya gudu, baki ga yadda hankalinmu ya tashi ba, na ce musu kawai mu koma gida, dama ya saba irin haka, ko lokacin da ƙanwata take raye, haka take fama da shi, idan aka kwantar da shi, da ɗanyen ciwo haka zai bar asibiti sai dai ta ƙarasa masa dressing a gida ya warke".

Nabila ta ce "Allah sarki, Allah ya yi mata rahama, shi kuma ya bashi juriya. Kana ji na, zan shigo dan ga abinci ma nayi, yayana ya fara saka mini ido ne, dole na canza takuna, zuwa azahar zan bar motata a chamber, zan zo in sha Allah"

Ya ce "To Allah ya kawo ki, dan zuwan naki yana da amfani, yaƙi cin abinci ya ƙi shan magani, yana kwance kawai tun jiya"

"In sha Allah zan zo, ayi masa sannu" ta ajiye wayar tana murmushi, rigimar Viper tana da yawa, idan ba ka da haƙuri ba zaka iya da shi ba.

Har ta fara neman lambar sumayya, sai kuma ta fasa kiranta, dan har ta manta sun yi faɗa. Kawai ta din ga jin ta wani iri, akwai abubuwa da dama da take son gaya wa sumayya, saboda kusancinsu da shaƙuwarsu, ta musamman ce. Sai dai haryanzu tana mamakin dalilin da zai sanya a din ga bibiyarta ta hanyar sumayya, kuma waye yake bibiyar ta ta.

Sai dai ta fara zuwa courts ɗin da take da trials, ta gabatar da shari'oi, sannan ta koma asibitin da aka kai ramma, lokacin da aka yi mata fyaɗe.

Ta nemi a bata copyn report ɗin da aka yi confirming rape case ɗin, aka ce an bawa ƴan sanda. Ta nemi ganin likitan da ya kula da ita, aka ce ya tafi ƙaro karatu, a bata lambarsa nan ma aka cigaba da yi mata yawo da hankali.

Sai da ta gama zagayenta, sannan ta ajiye motar a wani wurin parking, ta karɓi pass, ta tafi wurin su Viper.

Yau a tsakar gida ta tarar da shi, sun shimfiɗa masa tabarma, yana zaune yana ya danna wayarsa, sai dai idanunsa sun ɗan yi wuri wuri ya faɗa, gabansa kuma kwalin sigari ne da lighter.

Tayi sallama duk suka amsa, ya ɗaga kai ya kalleta ya mayar ya sunkuya.

"Ohhh masha Allah, the most handsome man ever saw, kaga yadda ka yi kyau sosai da sosai" ta nemi wuri ta zauna a gabansa ta ce "Manya gatan wasa, fisabilillahi mutum sai ya gudu daga Asibiti ba a sallame shi ba? Idan kuma bai warke ba fa, ni gaskiya ban ji daɗi ba"

Ba ta saka ran zai kulata ba, ta ce "Ina wuninku, ya mai jiki kuma?"

Suka amsa da sauƙi.

Walid ya ce "Ba yadda bamu yi da shi ba, amma sai nemansa muka yi muka rasa"

Tayi dariya ta ce "My, ya kake haka ne, duk muna ta taka, amma kai ko a jikinka. Wannan sigarin ina fatan ba sha aka yi ba, kaga an ce jininka ya hau, kuma kana smoking ba zai sauka da wuri ba, an ce mini baka cin abinci, duk ka rame ai ba zan ji daɗi ba" ta janyo ledar abinci ta ce "Ka yi haƙuri ban kawo abinci da wuri ba, Yaya Nasir ya fara saka mini ido" ta ƙarasa maganar tana miƙa masa plate, da cup ɗin da ta zuba masa kunun alkama.

Ya saka hannu ya karɓa, ya fara ci.

Liti ya ce "Wato mai zamani mune

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login