Showing 216001 words to 219000 words out of 479911 words
yi masa amsa kuwwa.
Falon indabo ya nufa, ya na zuwa ya hau shi da faɗa, "Wane irin rashin mutunci ne zai sanya ka ƙi ɗaga waya tun jiya? Har na fara tunanin wani abun ne ya same ka? Kana can mashaya kana iskancin naka daka saba ko? Wallahi ka nutsu ba za ka lalata mini siyasa da shirina a banza a wofi ba, saboda shashancinka da rashin sanin ciwon kai ba, dole ka san abun da ka ke ciki ka shiga hankalinka"
Zama yayi ya haɗe rai, yaƙi magana, har Indabo yayi masifarsa ya gama, sai da ya gama haki, sannan ya ce "Jiya Naja'atu ta zo mini hankali a tashe, yarinyar da ka yi wa fyaɗe, mutumin da aka ce shi yayi, wata lawyer za ta tsaya masa, ta je har office ɗin Naja'atu neman in da aka tsaya a case ɗin. Ina tsoron ranar da abokan adawa za su ɗagomu, ko su bankaɗo miyagun laifukan da ka ke aikatawa. Yanzu ina ka kai yarinyar yaya aka yi da ita?"
"Ban sani ba, wace yarinyar nake magana a kai? Yarinyar da ka yi wa lalatar nake yi maka magana".
"Amm...m...wai ita rahama?"
"Kai ka sani, ina tambayar ka kana tambayata?"
Abdul ya ce "Ba Naja ce ta je ba, zata ba su kuɗi a rufe zancen ba?"
"Zan kife ka da mari wallahi, uban najar, ba ta je ba suka ƙi karɓar kuɗin, suka ce sai an karɓar musu hakkinsu ba? Ka ce mini zaka kashe yarinyar yaya ka yi da ita? Sannna yaya ka yi da uwar yarinyar, muddin case ɗin ya cigaba aka samu sani leakage mun kaɗe, zan iya asarar wannan wahalar ta wa, takarar ma ba zaka samu ba".
Abdul ya dubi Indabo ya ce "Amma daddy ka riƙe muƙamai da dama a garin nan da ƙasar nan, kai yakamata ace ka zama governor nan ba ma deputy governor ba da ka ke ƙoƙarin ɗora ni a kai ba, ni da ka bar ni da sabgar siyasar nan takura mini za ayi na kasa sukuni yadda nake so".
Indabo ya jinjina kai ya ce "Taɓɗijan, bilki anya ni na haifi yaron nan kuwa? Kina jin abun da yake faɗa?"
Ta sha kunu ta ce "Wace irin magana ce wannan ka ke yi?"
"Ki na jin abun da yake gaya mini, Abdul siyasa lissafi ce, idan ya ƙwace maka, babu wata fomular da zata yi maka solving duk wani hardship da zaka shiga. Na gama da jihar nan, sonake ka riƙa mini, sama nake tunani tawagarmu mu ƙarasa mamaye ƙasar nan, komai a lissafe nake yin sa".
Abdul ya yi ajiyar zuciya ya ce "Yarinyar ta mutu ai, babarta ce take nan"
"Ka tabattar?"
Abdul ya jinjina kai. Indabo ya ce "Dole aje a nemo babarta, ita ma a kawar da ita, kar su ɓata mana aiki"
Cikin tashin hankali ya ce "Ita ma wai kashetan za ayi?"
Indabo ya ce "To me za ayi idan ba a kasheta ba? Sai asirinmu ya tonu kuma, sannan azo a fara neman mafita?.
And na ɗaga komawata Abuja, sai Allah ya kaimu weekends, kai kuma zaka tafi jibi in Allah ya kaimu, akwai meeting da shugabannin jam'iyya na ƙasa da na jiha, sannan akwai meeting na musamman da deligates, dan dai a samu ayi nasara. Sai ka je ka yi shiri ka bar ni da sauran"
Gaba ɗaya jikin Abdul ya yi sanyi, ya tsare mahaifinsa da ido.
"Menene kuma ka tsaya kana kallona? Kafin ƙarshen watan nan kuma za a kai kuɗin aurenka, gidan party chairman kai da 'yar sa".
Abdul ya murza goshinsa, saboda yadda kansa yake sara masa, gaba ɗaya ya rasa abun yi.
***
A nutse sumayya take kallon Nabila ta ce "Arfa, idanunki sun nuna akwai damuwa, meyake damunki ne kamar ma fa kuka ki ka yi" kamar Sumayya ta soso mata wurin da yake yi mata ƙaiƙayi, kawai ta saka mata kuka.
Sumayya ta ce "Matsalata da ke kenan, shagwaɓa arfa" ta share hawayenta tana zumɓura baki.
Sumayya ta yi murmushi ta ce "Ƙila fa ba wani abin kirki ne ya saki kukan ba, ina jinki ko duk Najar ce, yaya ku ka yi da ita?"
Nabila ta ce "Wannan ai azzalumar mace ce" nan ta gaya wa Sumayya yadda suka yi.
Sumayya ta jinjina kai ta ce "To hakan ne ya saki kuka?" Nabila ta girgiza kai ta ce "Ke na gaji ne, kaina ya ɗauki caji, kin ga rashin mutuncin da barrister Kabir ma yayi mini duk saboda ita, ni kamar na karaya ma, amma wallahi ba zan janye ba"
Sumayya ta yi dariya ta ce "Manya gatan wasa, karaya ba taki ba ce ba, akwai ƙalubale sosai a duk wata nasara da ake son cimma, dan haka ki yi haƙuri ki cigaba da addu'a, In sha Allah sai kin cika burinki a kan Naja'atu".
"Wallahi sumy da kamar na karaya, amma ba zan karayan ba in sha Allah, sai na cika burina"
"Yauwwa mutuniyar Viper" da sauri Nabila ta kalleta ta ce "Me ki ka ce?"
"Mutuniyar Viper mana, ko shi yanzu kin ɗaga masa ƙafa, kin haƙura da nemansa kin koma kan fansarki ta naja'atu bunkure?"
Nabila ta ƙurawa fuskar Sumayya ido ta ce "Al'amin mai dogon zamani" tayi maganar tana murmushi.
Sumayya ta ce "Ban gane ba"
"Kawai shaƙar da yayi mini nake tunawa ne, na kusa sheƙawa".
"Amma haryanzu ba ki sanarwa DSP ba, yakamata ki tamakawa aikinsa fa"
Nabila ta ce "Taɓ haka kurum ya gaya wa Abba, ya saka Abba ya harbe ni da bindiga har lahira, na je wurin ɗan daba, ba dani ba bari na tafi gida, marata ma ciwo take"
Nabila ta tashi, sumayya ma ta tashi za ta rakata, a reception suka haɗu da P.A, gaban sumayya ya faɗi, ya din ga bin su da kallo, ita da Nabila.
"Malam ka kalli gabanka mana, ji jaraba zai saka na faɗi" Nabila ta yi maganar cikin ɗaga murya tana kallon P.A
Sumayya ta ce "Na shiga uku, haba Arfa, babba ki ke yi wa haka?"
"To waye ya ce ya kalle ni?"
P.A ya ce "Yi haƙuri, wallahi kallon sani nake yi miki ne, kina yi mini kama da wata da na sani"
Nabila ta kwaɓe baki, yayin da jikin sumayya ya hau rawa.
Ya ce "Sumayya wurinki na zo fa" gaba ɗaya sumayya ta rikice, dan kar P.A yayi wani abun da zai sanya Nabila gane wani abun, dan sharp brain ce da ita sosai.
Nabila ta ce "Bar rakiyar kawai, ni na tafi sai mun yi waya, kuma ki daina ccacanza lambobi kina kirana, kamar wata mara gaskiya ko 'yar 419, idan na kira layinki ba zaki ɗaga ba, sai ki yi ta canza lamba" gaban sumayya ya faɗi, mussaman kallon da P.A yayi mata.
Cikin yaƙe Sumayya ta ce "Layina ne yake bani matslaa, sai mun yi waya".
P.A ya tasa ta a gaba, zuwa news room, in da take aiki, ya rufe ƙofa ya kalleta ya ce "Wato canza lamba ki ke yi ki yi waya da ita ko?".
Sumayya ta ce "Ban san me zaku iya yi mata ba, dole sai na tantance abun zan din ga gaya muku a kanta".
"Haka muka yi da ke? Kin zaɓi ki salwantar da rayuwarta kenan?"
"Ba zan salwantar da rayuwarta ba, kuma babu abun da zai same ta sai wanda Allah ya ƙaddara mata, ku bani a hankali ai ina sanar muku da duk wani abu da take aikatawa kamar yadda ku ka buƙata. Menene na biyo ni nan kuma, ka yi mini magana a gabanta sai ta gane".
P.A ya ce "Ta gane me? Muddin ki ka bari ta gane, sai ta zama gawa, an sanar mini ta zo ne, kuma na san muddin ta zo, wani muhimmin abun ne ya kawo ta. Me yake faruwa? Dan kar ki yi zaton ke kaɗai ki ke yi mana aiki, duk motsinki kema ana saka mana ido a kai".
Sumayya ta yi ajiyar zuciya ta ce "Zauna mu yi magana".
Nabila kuwa bayan ta fito harabar radiyon, still motar nan ta sake gani, wadda aka taɓa bin ta da ita, ta ganta a law firm ɗin su, yanzu ma gata a gidan rediyon su Sumayya, kuma lambar motar ce ta sake tabattar mata da motar ce dai.
Wani guntun murmushi ta yi ta ce "Bari dai na ga ƙwal uwar daka".
***
Ramma ba ta sake ganin Abdul ba sai can dare, ba ta yi zaton zai kulata ba ma, ta ɗauka fushin da yayi ne ya hana shi dawowa, dan har ta fara bacci, ta ji motsinsa a bedroom ɗin. Ta buɗe ido ta kalleshi, ta ga bai kulata ba. "Kayi dare da yawa yau" ya waiwaya ya kalleta ya ce "Idonki biyu?"
"A'a motsinka ne ya tashe ni"
"Barin gidan nan zamu yi, gobe in Allah ya kaimu" cikin rashin fahimta ta ce "Saboda me?"
"Wani dalili kawai, zan yi tafiya ne na sati ɗaya"
"Kuma ka tafi ka bar ni nikaɗai?"
Ya ce "Eh babu abun da zai same ki, can zamu koma gaba ɗaya, bana son a gano ki a nan".
Ta taɓe baki ta ce "Kana nufin dai haka zan cigaba da zama kenan?"
"A'a ina tunani a kan zaman mu"
Tayi shiru, ta gyara kwanciyar ta, ta cigaba da baccinta.
Juya tayi, ta ganshi a zaune, yana hana haɗa ƙwayoyi, ya ɓalle wannan ya ɓalli waccan. Matsawa ta yi ta ƙwace ta ce "Ba zaka sha wannan ƙwayoyin ka mayar da ni jakarka ba, ba zai yiwu ba, wallahi ko na bar maka ɗakin" a sanyaye ya ce "Ba wanda ki ke tunani bane ba, damuwace ta ɗan yi mini yawa, bacci nake son na yi" ta saka hannu ta kwashe packets ɗin ta ce "Kai kamar ba likita ba, anya ma ba likitan bogi bane ba, haryanzu ina tantama babu likitan kirki da zai yi abun da ka ke yi".
"Ke ba zaki gane ba ne, ki bani kawai idan ba haka ba, baccin ba zai yiwu ba".
"Aikuwa sai dai kar ka yi" ta watsa su bayan gadon, ta gyara kwanciyar ta.
***
Nabila tana zaune, tana kaɗa ƙafa tana cin gugguru, ta na zancen zuci, ta kalli wayarta da take silent, sai haske take yi, ta saka hannu ta ɗauka, ta saka a kunnenta.
"Hello barka da dare"
A hankali ta ce "Yauwwa"
"Ya gida aiki?"
"Alhamdilillah"
"Na ce ina da ƙorafi, a taimaka mini an ce na je office, na je sau biyu ba kya nan"
Ta yamutsa fuska ta ce "Wake magana ne?"
Ya ce "Ni ne"
"To kai wa?"
"Bawan Allah, ni ne na kira ki rannan. Wataƙila ina da magana mai muhimmanci da ke".
Nabila ta yi guntun tsaki ta ce "Da maganar mai muhimmanci har haka, da ba a waya zaka tsaya kana zagaye-zagaye ba". Ta katsewayar, tana cigaba da ɓata fuska.
Lambar Viper ta kira, ta na jiran ya ɗaga, har ta sare da zai ɗaga, ta ji ya ɗaga wayar.
Tayi gyaran murya ta ce "Ka na ji na? Na san ma kana ji, ba magana zaka yi ba. An ce baka taɓa mata, amma ni kullum burinka ka kashe ni, ka yi ta shaƙe ni, ko cikakkiyar lafiya ba ni da ita, idan ka yi haƙuri ka ba a hankali zan yi maka bayanin komai, amma ka fiye zafin zuciya haryanzu maƙogwarona kamar an shaƙeni da ƙarfe nake ji" ta yi maganar har da kukan kissa.
Yayi shiru yana sauraren ta.
"Ba zan yi zuciya na daina zuwa ba, har sai ka gaya mini sauran labarin nan, na ji ina 'yar madara take, ina son saninta, akwai abubuwan koyi da yawa a rayuwar ta. Zan sake dawowa in sha Allah, amma ka rage zafin rai dan Allah, mu yi magana ta fahimta"
Nasir ne ya shigo ɗakin unexpected, ta ɗaga kai ta kalleshi, ya ƙura mata ido.
Ba ta canza daga yadda take ba, ta ce "Sai anjima, zamu yi magana" ta katse kiran ta kalli Nasir ta ce "Yaya shigowa ba excuse?"
"Da wa ki ke waya?" Ta gyaɗa kai ta ce "Wani ne"
"Wani wa?"
"Is confidential"
Ya ƙura mata ido ya ce "Confidential as how?"
"Haba Yaya, client ɗina ne fa"
"Amma ki ke wannan kashe muryar?"
Ta ce "Ikon Allah, to ai he's not just a client, ammm" ba ta ƙarasa ba ya juya ya fice, ta yi ajiyar ta ce "Ohh ni Nabila, yaya ai sai dai ka yi haƙuri"
Walid ne ya shigo ɗakin, dawowarsa kenan, ya tarar da Viper, a ɗakinsa, yana goge wuƙarsa sweazland. Ɗan mama kuma na zaune a gefensa.
Zaro ido ya yi ya ce "Me zan gani haka? Viper waye ya ɗaukko wannan wuƙar, ya kawo maka?" Al'amin yayi shiru yana jujjuyata a hannunsa.
Ya kalli ɗan mama da yake sunkuyar da kai, aikuwa a fusace ya saka ƙafa ya daki ɗan mama ya ce "Amma an yi shegen yaro, wallahi baka da mutunci ɗan mama, uban wa ye ya ce ka ɗaukko masa wuƙar nan?"
Ɗan mama ya ce "To wai ya zan yi dan Allah? Cewa yayi sai na ɗaukko masa, kuma Oga liti ne ya ɗaukko ya bani, wai operation za su fita gobe, Madaki yana cikin gari"
Walid ya din ga ɗurawa Ɗan mama ashariya, ya juya ya nufi Viper, Amma Viper ya miƙe tsaye, ya fito da harshen sa waje ya mayar.
Walid ya nuna kansa ya ce "Ni zaka sakawa ƙarfe?"
"Ƙwarai, muddin ka yi ƙoƙarin dakatar da ni, wallahi jininka za ta sha, ai na gaya maka ka nesanta yarinyar da ni, muddin ina ganinta ba ni da wata nutsuwa, dan haka ba ka da ikon, dakatar da ni".
Walid cikin ɓacin rai ya ce "Hanyar da muke ƙoƙarin bi, ba mai ɓullewa ba ce, ka yi haƙuri"
"Shhhh" ya yi maganar tsare Walid da ido.
"Dalla matsa, ni zaka yi wa barazana, ka je ka yi duk abun da ka ga dama, na daina shiga harka, tafiya zan yi ku ƙarata da kai da su litin, mu gani idan hanyar za ta fishshe ku"
Suna cikin faɗa liti ya shigo, suka ya tarar da su, liti ya ce "Kai walid, ba zaka hanamu abun da muke so ba, ka hanamu motsawa, wancan banzan madakin, yana ta rashin mutunci a gari, wallahi sai mun ɗauki fansa" Walid ya fice ya bar musu gidan cikin matsanancin ɓacin rai.
***
Abdul ne da ramma suke tafe a mota, tana ta kallon hanya, ya yi locking ɗin motar, ga glass ɗin ta tint ne.
"Wai tafiyar nan ba zata ƙare ba, ni fa na gaji".
"Eh, cinikinki zan je na yi na sayar" ta harare shi, ta cigaba da kallon titi.
Wata unguwa suka yi, babu gidaje da yawa a wurin, sai tsilla-tsilla, kuma manya manyan gidaje ne, na alfarma a rukunin.
A ƙofar wani ƙaton gida ya tsaya, aka buɗe masa gate, ya shiga, wasu irin manyan karnuka na ta kai komo a harabar gidan, ya zagaya yayi parking, ya cire lock ɗin motar, ta buɗe ta fita.
Shi ma ya fito, ya buɗe boot, ya ciro akwatuna, ya ce "Mu je"
"Yanzu da ka mayar da ni gida, gara ka sake kawo ni nan?"
Yayi gaba ya ce "Idan karnuka suka cinyeki, kya taho" ta bi bayansa tana rarraba ido, gida mai kyau na alfarma.
Saman bene suka hau, ya kaita wani katafaren bedroom, ya ce "A nan zaki zauna, zuwa lokacin da zan dawo, kafin nan na samo mafita, zaki iya shiga ko ina, an ajiye duk abun da ki ke buƙata, sai dai ko haraba ba zaki fita ba. Zan ajiye miki waya duk abun da ake ciki, ki kirani ko idan kina buƙatar wani abu, wayar lambata kawai zaki iya kira".
"Wai dan Allah nikaɗai zaka bari a gidan nan, ni tsoro nake ji wallahi"
"Ki yi haƙuri mana, ba zan daɗe ba, na ɗan lokaci ne, zaki yi missing ɗi na ko?" Yayi maganar yana kissing ɗin goshinta. Kuka take yi sosai, ya rungumeta yana rarrashin ta.
***
Yau ma kaca-kaca Walid ya yi da su Viper, Liti yana supporting ɗin Viper a kan iya wuya, kawai su afka su ɗauki fansa.
Duk yadda walid ya so fahimtar da su, suka ƙi fahimta.
Nabila ta fara gane kan hanyar zuwa gidan su Viper, kanta baya kullewa kamar da.
Babu tsammani ta yi karo da Walid, ta ja ta tsaya, ta zata zai yi mata masifa, ta ce "Ina wuni?"
"Lafiya ƙalau"
"Amm yana ina?"
Ya nuna mata dutsen da yake can gaba, ya ce "Yana can, amma ki daina wahalar da kanki, taurin Al'amin yayi yawa, an ɗaukko masa wuƙarsa, zai je ya yi gaba da gaba da madaki yau, ki ƙyale shi kawai"
Ta girgiza kai ta ce "A'a, zan jarraba sa'ata" tayi gaba ta nufi in da dutsen yake, ba ta ƙarasa ba ta hango shi, a zaune a gefen bishiya, cikin inuwa yana ɗan kaɗa ƙafa, ya na shan sigari.
Ta ƙarasa ta zauna a kusa da shi ta ce "Barka da rana" bai amsa ba, ta saka hannunta, ta zare sauran karan tabar hannunsa ta ce "Ayi mini uzuri, ba na son hayaƙi, mara zuciya na sake dawowa. Dan Allah kar ka shaƙe ni, magana zamu yi ta fahimtar juna"
Ya ɗaga kai ya kalleta, ya yinƙura ya miƙe, ita ma ta tashi ta tsaya a gaban sa, ka saurare ni ko sau ɗaya ne, zafin zuciya da gaggawa shi ya sanya ka rasa da yawan mutane masu muhimmanci a rayuwarka".
Sweazland ya saka mata a wuyanta, ya ce "Gargaɗi na ƙarshe, ki rabu da ni, ki fita daga rayuwata".
Ta kalli yadda wuƙar ke ƙyalli a saitin wuyanta ta ce "Sai na ji ƙarshen labarinka, na ji wa ka kashe? Kuma ina jauhar da abun da yake cikinta?"
Ya kalleta ita ma cikin ƙwarin gwiwa ta cigaba da kallonsa, duk da ƙasan zuciyarta a tsorace take.
"Ki daina kallona a haka, meyasa ki ke son ki zama raunina ne?" yayi maganar muryarsa na rawa.
Ayshercool
08081012143
53
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
Arewabooks ayshercool7724
"Meyasa zan zama rauninka ne? Wallahi ba cutar da kai zan yi ba, ba na nufin yin hakan. Idan niyyata kenan a baya yanzu na canza tunani, dan Allah ka fahimce ni".
Ya sauke numfashi ya ce "Me ki ke buƙata?"
Ta ce "To dan girman Allah mu zauna, sai mu yi magana, ba dan ni ba"
Ya koma ya nemi wuri ya zauna, ta yi ajiyar zuciya, tare da ƙara jinjinawa Jauhar.
Ita ma ta zauna, ya ce "Ina jinki"
"Kamar yadda na gaya maka da farko, na yi nadamar abun da nayi, wallahi ba ni da niyyar cutar da kai ko kaɗan.
Dan Allah ka yi haƙuri, a