Showing 180001 words to 183000 words out of 479911 words
zan nemawa kaina mafita"
"A'a yaya, wallahi gara ki kai ƙara hisba a kashe auren, da ki yi zina da aure, ko a sasanta ku ayi masa nasiha".
Ta girgiza kai ta ce "Mama tayi mini asiri, banda wanda matarsa take yi mini. Gaba ɗaya ba na gabansa, duk sai na yi maganinsu, daga nan har chadd ko zan tafi tsirara, su surayya ba zasu auru ba, kuma sai na kashe auren nan, ba zan iya ba. Kar ki damu da sai kin yi mini nasiha, dan ba zan ji ba wallahi. Kin ga bari na hanzarta zan je na karɓo kayan cajina a wurin wanda nake karɓa. Ke ni ko da mastern naki zaki haɗa ni ne, ya din ga bani kayan "
Jauhar ta girgiza kai cikin matsananciyar damuwa ta ce "Ki dai canza tunani yaya hafsa, ni master na yi nasara a kansa, da addu'a da haƙura, abun da yake yi ya kusa zama tarihi, ke ma da zaki yi haƙu......
"Kin ga tafiyata jauhar, ga farfesun kifi nan da doya, ki samu ki ci, sai anjima".
Abun duniya ya ishi jauhar, dan sai da ta zubar da hawaye, ta ɗauki waya ta kira Baba, suka gaisa ya tambayeta ya makaranta ya mijin naki, ta ce "Lafiya ƙalau Baba, dama wani abu ne ya saka na kiraka".
"To waliyiyya, Allah ya sa lafiya"
"Baba dan Allah ka shiga lamarin auren yaya hafsa ka saka baki, kar abun da ba a so ya afku, yanzu ta bar gidan nan ni dai ina jin tsoro, dan Allah baba ka saka baki"
"Waliyiyya kina ji na?"
"Eh baba"
"Duk Wanda ya ce ;zai haɗiyi gatari, sai ka sakar masa ƙota. Babu yadda ban yi ba, idan auren nan ba zai yiwu ba, a raba uwatta taƙi, na zauna da shi mijin, ya ce shi ba ta da cikakkiyar lafiya, kuma ba ta da kunya, uwatta ta tsaya a fuskanci menene matsalar, tun da ta saka son abun duniya a gabanta, amma taƙi. Ta ce wai asiri babar tijjani tayi mata, suna nan suka ta faɗace-faɗace, kuma na san duk hakkinki ne, ni na zubawa sarautar Allah ido".
"A'a baba, dan Allah kar ka ce haka, kada laifinsu ya shafeta, su matanka ne, ita kuma 'yar ka ce, hafsa fa ta cigaba da ta'amalli da miyagun ƙwayoyi baba ka yi wani abu a kai".
Ya girgiza kai ya ce "Jauhar kenan, zan yi ki yi mata addu'a Allah ya shiryeta"
Suka yi sallama ta ajiye wayar cikin matsananciyar damuwa.
Al'amin ya dawo gidan yana mitar kwana biyu lambar guduma ba ta shiga sam, yana ta kiransa a kan idan an yi musu albashi, ya gaya turo da kuɗi a yi wa iyayensa sayayya, ya basu na neman albarka.
Amma shiru lambar ba ta shiga, ya kira P.A ya tambaye shi ya kasa samun sa. P.A ya ce masa suna nan ƙalau yana can yana aikinsa, yana zaton ko wayar ce ta samu matsala. Haka kawai Al'amin ya ji bai amince ba.
Ayshercool
08081012143
44
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
Arewabooks ayshercool7724
Gaba ɗaya ya kasa samun nutsuwa sai da jauhar ta farga ta ce "Master ya ne?"
"Na kasa samun Nura a waya"
Ta ce "Allah sarki, ɗan uwa nagari in sha Allah zaka same shi, maybe ko babu caji ne a wayar"
Ya ce "No, kusan sati fa kenan, na kira P.A ya ce mini suna nan lafiya, wataƙila wayarsa ce ta samu matsala, idan ma haka ne, ai ko wayar wani ya ara ya kira ni, tun da kusan kullum sai na yi waya da shi, na ja masa kunne"
Jauhar ta ce "Haka ne, amma ƙara masa kwana biyu mu gani"
Jiki a sanyaye ya ce "To shikenan"
Al'amin ya hana jauhar duk wani aikin wahala, su halimatu ne ke zuwa ta yi guiding ɗin su, su yi mata snacks ɗin da ake kai wa wurin shayi, sai bead work da take yi tana daga zaune, shi ma faɗa yake yi yana mita.
Iya haƙuri da ɗaga ƙafa ta san yayi mata, dan yau sakata yayi a gaba yana mita, ba dan yana son cikin nan ba, da tuni ya daɗe da bin rariya shi ma.
"Master" ya ɗaga kai ya kalleta, ya haɗe rai.
"Wai laifin me na yi ne?"
"Ni gaskiya na gaji, sai yaushe cikin zai gama ƙwari ne? Nima ai yakamata a duba lamarina"
Murmushi ta yi, yadda yayi kicin-kicin, kamar wani ƙaramin yaro.
"Lamba nawa ake so?" Tayi maganar tana kashe masa ido.
"Na gaji da lamba uku huɗu, lamba ɗaya nake so"
Jauhar ta ce "Baka damu da babyn nan ba ko?"
Ya girgiza kai ya ce "Wallahi na damu da shi, ina son abuna, amma ba shikaɗai yake buƙatar ya rayu ba, kuma ba shikaɗai yake buƙatar ki ba" yayi maganar a marairaice.
Ta ɗan yi shiru tana nazarinsa, da gaskiyar sa, kusan kullum ba ta da lafiya, tana kallo wasu lokutan sai dai yayi zamansa a ɗakinsa, ya busa hayaƙi, dan kar ya takura mata, ko ya karya dokar da aka saka saboda cikin.
"Kin yi shiru fa"
Dariya ta yi ta ce "Subhanallah, master da shagwaɓa, lamari ya ɓaci, to lallaɓani".
"Ai lallaɓakin nake yi"
"Inyee dama ka iya shagwaɓa baka taɓa yi mini ba, yanzu da da safe zan ce ka yi mini mazewa zaka yi kana hararata. To daga yau mayar maka da fankarka zan yi, dama ta fara tsufa".
Al'amin ya ce "Zan yi zuciya fa"
Ta ce "To yi mana idan zaka iya, huta roro waken gizo yaƙi 'ya'ya" tayi maganar tana jan dogon hancinsa.
"A'a ba zan yi ba ma"
Tayi murmushi tare da rungume shi.
Har suka kwanta tana lafiya, sai cikin dare ya farka ya ganta a zaune, ta takure wuri guda.
"Madarata, ya aka yi ne?"
Jauhar ta ce "Bakomai, zafi ne ya dame ni"
"Zafi kuma? Ga fanka na yi?. Ko numfashin ne?"
Ta ce "A'a, lafiya ƙalau nake numfashina"
Ya ce "To ya aka yi na ganki a zaune?"
Tausayinsa ya kamata, har istigfari take yi, ta gaji da ce masa ba ta da lafiya ba yau ba gobe.
"Master ka kwanta dan Allah, na kasa baccin ne"
Cikin damuwa ya ce "Ka kwanta ka yi baccinka"
"A'a ban yadda ba, akwai matsala ne, gaya mini?"
"Marata ce take ciwo"
Cikin tashin hankali ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Allah ya sa ba zubewa zai yi ba, ya salam"
Ta jingina da jikinsa ta ce "Ciwon fa ba mai damu bane ba, ƙullewa tayi, na ji kwanciyar babu daɗi, shiyasa na tashi zaune"
"Ko asibiti zamu je? Wallahi ina son cikin nan zahra, na kwaɗaitu da son ganin abun da zaki haifa mini, tun da muka rasa na farko, nake tunanin ko yaushe zamu kuma samu? Kuma mun samu wannan karon ma, zan yi dalilinsa, mu je asibiti kawai".
Cikin sigar rarrashi ta ce "Master, dan Allah kar ka ɗaga hankalinka, ba ciwo take yi mini ba, ƙullewa tayi ne sosai kuma na duba babu abun da yake fita. Ɗawainiyar da ka ke yi da ni ka da Allah ya gajiyar da kai, Ubangiji Allah ya nuna mini ka daina komai kan Allah ya kawo mana babynmu"
Yayi ajiyar zuciya ya ɗora hannunsa a mararta ya ce "Ba zan taɓa gajiya da duk wani abu da ya jiɓance ki ba, ba alfahari nake yi miki ba, ɗan halak ne ni, kar ki taɓa sakawa ranki zan gaji, da ƙarfin ikon Allah ba zan gaji ba, in sha Allah, ni dai duk abun da ki ka ji na ciwo ki gaya mini dan Allah, ina son kasancewa da ke da iya adadin abun da zaki haifa mini, mu yi rayuwa mai tsayi da daɗi. In sha Allah zan yi iya ƙoƙarina na zama uban kirki ga 'ya'yana, kuma miji abun alfahari gareki"
Haka kurum ta ji jikinta yayi sanyi, da maganganun sa, ji take kamar akwai wani abu mai girma da zai faru da su, sai dai ba ta sani ba, na daɗi ne ko akasin haka.
Ta sake lafewa a jikinsa, tana jin tsananin buƙatuwar son cigaba da kasancewa da shi a cikin rayuwarta, ita wannan kulawar da yake yi mata, tana shafe dukkan sauran abubuwan da yake aikatawa.
Zuwa da safe ta ji ƙwarin jikinta, har ta ce masa zata makaranta, da ƙyar ya amince, saboda tana da test.
Har ta fito ya karɓi jakarta, ya ce shi zai kai ta, kar ta hau ɗan sahu, ayi ta gargada da ita.
Ya duba jakar ya ce "Ina inhaler ki?"
Ta ce "Tana aljihun wandona"
"Meyasa ba zaki saka a jaka ba"
"Zai iya yiwuwa ciwon ya tayar mini, jakar tana nesa da ni, amma a wandona da na laluba zan ji ta"
"Allah ya baki ingantacciyar lafiya, ya rabaki da ciwon nan gaba ɗaya"
Ta ce "Amin bugun zuciyata"
Ya ce "Iyeeee?"
Ta jinjina kai ta ce "Eh mana"
"To bani da kuɗi dai, kayan abinci zan sayo mana, idan kuma na ɗauka na baki shikenan"
Ta tsuke fuska ta ce "Kai ba ayi maka abun arziki, da na yi maka kalamai, sai ka hau ce mini ba ka da kuɗi, me ka ke nufi"
Al'amin ya ce "Ai ke ɗin ce, wasu lokutan haka ki ke yi mini, bana sanin lokacin da ki ke sakawa na zazzage miki aljihuna"
Jauhar ta tura baki ta ce "Wannan kalaman wataran da kuɗi ba zaka ji su daga bakina ba"
Take jikinsa yayi shock ya ce "Ban da irin wannan wasan" idonsa ya nuna ƙarara tsananin fargabar rasata.
Ta basar da zancen, ya kaita makaranta.
Abu kamar wasa, sama da kwanaki biyar, Al'amin bai ji ɗuriyar Nura ba, bai kuma same shi a waya ba, dan haka ya wanke ƙafa ya tafi gidan indabo, kasancewar ba shi da shamaki da gidan, babu mai tambayarsa wurin wa ya zo, ina za shi, kai tsaye ya shige.
Ofishin indabo na gidan ya tafi, kasancewar imdabon yana Abuja, cikin sa'a ya tarar da P.A.
"Mai zamani, ya aka yi ne?"
"Na kasa samun Nura a waya"
"To ai ina zaton wayarsa ta samu matsala ne kamar yadda na gaya maka"
Ya girgiza kai ya ce "Ba zai yiwu ba, shirun yayi yawa. Ba zai yiwu na baku amanar yaro, garin da ba uwar sa babu ubansa na kasa samunsa a waya, kusan sati biyu, na zauna na yi shiru ba, ba zai yiwu ba, dole ka san duk yadda zaka yi ka haɗa ni da shi"
"Amma mai zamani ina nan yana Abuja, a ina zan iya haɗaka da shi?"
Cikin ɗaga murya ya ce "Ka kira indabon, duk yadda zai yi ya haɗani da shi"
P.A ya tsaya yana kallon sa.
"Zaka yi abun da na ce, ko sai na saka maka ƙarfe?"
Ya janyo waya ya kira Indabo, suka gama magana. Ya kalli Al'amin ya ce "mun yi magana da honorable, ya ce in anjima zai aika a duba shi, yanzu suna meeting da shugaban ƙasa".
Yayi ƙwafa ya juya zai fita, Abdul ya kawo kai shi ma ya shigo. Sai dai Abdul ya tsaya yana jiran Al'amin ya bashi hanya, wannan ce haɗuwar su ta biyu, kasancewar ba a ƙasar yake zaune ba, ya fi sanin ɗayan wato Ja'afar.
Ala'amin bai tsaya jira ba, ya yi wa Abdul wata muguwar bangaza da kafaɗarsa, sai da ya dangana da faɗuwa ƙasa.
A fusace ya miƙe zai bi bayansa, P.A da sauri ya tsare shi ya ce "Kul, sai ya yi maka illa, ba mutunci ya cika ba wasu lokutan"
A fusace Abdul ya ce "Mahaukaci ne shi, baka ba ka ga irin bangazar da ya yi mini bane?"
"Yi haƙuri, ai duk abun da ka ga honorable yana bi a sannu, ka san ba ƙarami bane ba, yi haƙuri".
Ya kalli P.A ya ce "Babu ruwana za abun da yake bi a sannu, wallahi muka sake haɗuwa sai na koya masa hankali" ya juya ya fasa yin abun da zai yi.
Har la'asar Al'amin yana kallon wayarsa, yana jiran kiran indabo, ya je wurin shayi, komai yana tafiya dai-dai, ya tafi gida.
Yayi jajjage ya feraye doya, ya dafa ruwa ya zuzzuba a flask, duk ya rage wa jauhar aiki.
Wayarsa ta fara ringing, ya ɗaga ya kara a kunnensa.
Muryar Nura yaji ƙasa-ƙasa ya ce "Yaya"
"Kai Nura wani irin shirme ne zaka kashe waya, ko ta wani ba zaka ara ba ka kirani, ina ta tunanin meyafaru da kai?"
Nura ya ce "Ka yi haƙuri dan Allah"
"Ya ake ciki? Na ji muryarka wani iri?"
Nura ya ja numfashi ya ce "Zazzaɓi ne yake damuna, sun bani hutu ma, an kai ni asibiti an bani magunguna ma"
"Yasalam, kai daga zuwa garin mutane sai rashin lafiya, ko aikin ne da wahala?"
Ya ce "A'a"
"To Allah ya sauwwaƙe, zan cigaba da kiranka, idan ka ga babu hali, kawai ka dawo gida"
Nura ya ce "Godiya nake, Allah ya kiyaye ka ya ƙara tsawon zamaninka"
"Ka huta, ka kula sosai duk yadda ake ciki, ka sanar mini, ina fatan sun sallameka, dan na ga wata ya ƙare"
"Eh an bani kuɗi masu yawa ma, ka bani account number ɗinka, na sako maka abun da na samu, amma a ciki a sayawa Antynmu turimin atamfa dan Allah, da ita da babata a sai musu iri ɗaya"
Al'amin ya ce "A'a, ta gode sosai, amma ba haka za ayi ba, ka ba wa maman abun da zaka bata, ka tallafawa babanka da wani abun ya sai kayan abinci"
Nura ya ce "Shikenan, tun da ka ce haka, amma dan Allah ka saya musu atamfa iri ɗaya da mamanmu, tana sonta sosai "
Al'amin ya ce "Zan duba na ga abun yi, ka kula da shan magani ka ji ko?"
"In sha Allah"
"Good boy, sai anjima" ya kashe wayar, sai ya ji wata irin sa'aida a zuciyarsa jin muryar nura, dan babu irin saƙe-saƙen da bai yi a kansa ba.
Da jauhar ta dawo, aikin gida ƙarashe ne, duk yayi, sai godiya take yi masa tana yi masa addu'a.
Jauhar tun da cikinta ya fara tasawa, da an buga gate, sai ta saka hijjabi tana ɓoyewa, wai kunya take ji.
Yayi ta yi mata dariya, ya ce "Da ki ɓoye, da ki bar shi, ƙarewa haifarsa zaki yi ƙarshen kunya, gara ma ki bar shi kowa ya gani".
Cikin shagwaɓa ta ce "Ni dai ka bari na ɓoye abuna"
Ya ce "Ai sai ki yi ta yi"
Al'amin ya sha mamaki kuɗin da guduma ya turo masa, dubu ɗari da hamsin, wai a bawa babansa dubu ashirin kawai, sauran har da su oga liti da oga walid ya ce duk rarraba musu.
Al'amin ya ce "Wai aikin direban ne aka baka wannan kuɗaɗen har haka?".
"Eh Oga, ka san birnin tarayya ne nan, kuɗi ba wahala suke yi musu ba, ka cigaba da yi mini addu'a, jikina ne babu daɗi"
Al'amin bai matsa da bincike ba, ya ƙyale shi.
Jauhar ta yi mamaki da ya kawo mata atamfa, sai Nura ne ya turo da kuɗi a saya mata iri ɗaya da mamansa.
A lokacin ta ƙara yadda da ƙani ya ɗauki Nura, da wani ne daban ya bata, cewa zai yi ba zata saka ba.
Al'amin da kansa tare da rakiyar su Walid, suka je suka kaiwa mahaifiyar Nura, abun da ya aiko a bata, ta din ga murna tana yi wa Al'amin godiya tare da yi masa addu'ar gamawa da duniya lafiya.
Mai unguwa kuwa raina dubu ashirin ɗin nan yayi, a ganinsa tun da Nura ya tafi Abuja, dubunan ɗaruruwa zai aiko masa, ya fara zargin ko Al'amin ne ya rage kuɗin.
Ɓangaren Abbu kuwa, Abba ɗan wurin rahila, ya haɗa kai da abokai, suka fara yi wa Abbu sata, da ƙaramar sata suke yi masa, wani ya gani ya kawar da kai, wani kuma ma bai san sun yi ba.
Sai dai a wannan karon, satar da suka yi masa ba ƙarama bace ba, dan har ya kai ga reporting wurin Jami'an tsaro, da fari rahila ta ɗauka abun mai sauƙi ne, dan ta na ta yi wa Abbu masifar a kan me zai tayi mata terere da ɗa dan ya ɗauki kuɗi, ai shi mai rufa masa asiri ne yayi masa nasiha, sai dai ta girgiza da ta ji ya saka 'yan sanda sun kama shi.
Tamkar za ta yi hauka, da ƙyar ya saka aka sake shi, ya ce sai dai ya bar masa gida ya koma gidan ubansa, nan ma ta ce sai dai ya zaɓa ko dai ya zauna da ita da yaranta ko kuma idan ya matsa su tafi gaba ɗaya, ya ce ta kwashe yaranta su tafi.
Sai da ta ga ba ta da sauran mafita, sannan ta koma lallaɓa shi, da ƙyar ya saukko.
Juahar tuni ta fara zuwa awo, dan yau shi ya rakata awon ma, a wurin scanning aka nuna masa yadda zuciyar jaririn take bugawa.
Gaba ɗaya ya rikice, bakinsa ya ƙi rufuwa, ya zubawa screen ɗin ido, yana ta washe baki yana murmushin.
Jauhar ta ce "Ni fa na gaji zan tashi"
Ya ce "Ɗan yi haƙuri, bari na ƙara ganinsa mana"
"Ka ga me? Me ake ganewa a nan, ni banda duhu ba na ganin komai"
Al'amin ya kalleta ya ce "Sautin bugun zuciyar ta sa ne nake ji har cikin raina"
Sai da mai scanning ɗin ya yi dariya, aikuwa ta tashi zaune ta ce "Ni na gaji, haka kurum, na fuskantar tun yanzu kafi son ɗan tayin nan, to ka matso ka saukko da ni"
Ya miƙe ya saukko da ita daga kan gadon, ya ce "Ki din ga motsawa a hankali, kar ki takura shi".
Tayi murmushi ta ce "Idan ban tafi da gudu ba, ka ce ba ni ba ce"
Ya ce "Yi haƙuri, ai dole na lallaɓaki" suka je aka gama yi mata awo, suka tafi wani shago na kayan jarirai, suka fara sayayya, kasancewar an ce musu tun a wata shida, kan ciki yayi bakwai ake haɗa kayan haihuwa, saboda haihuwa za ta iya zuwar mata a wata bakwai, sannan ya tanadi kuɗi, dan ba a san ya haihuwar zata zo ba, ko ta haihu da kanta, ko kuma ayi mata tiyata.
Ta zo ta shirya kayan da suka sayo a wani ɓangare na wardrobe ɗin ta, kallon kayan kawai nishaɗi yake sakata.
Washegari da safe, yana falo yana kallon wrestling, ta fito daga ita sai wata rigarsa da ta saka shirt ce, tayi mata yawa nesa ba kusa ba, iya cinyarta ta tsaya, sai kanta tayi kalba guda biyar, ta sake su ta fito tana miƙa tare da hamma.
Ya buɗe mata hannayen sa, yana murmushi, ta ƙarasa ta zauna a kan cinyarsa, ya rungumeta ya ce "Sannu"
"Yauwwa. Ina kwana?"
"Lafiya ƙalau, ya jiki ya