Showing 462001 words to 465000 words out of 479911 words
gyara ce da kwalliya, babu borar mace sai wadda ta so.
(0706 971 1327 da kayan likitar mata, bbau ruwanki da matsalar sanyi, ko fargabar amfani da kayan da baki san da yaya aka haɗa su ba, domin tsoron cutar da lafiyarku. Domin ɗaga likkafar taku kimar, ku kasance masu yawan ibada da addu'a, biyayya tare da gyara da ingantattun magunguna na gyara)
Sai da suka kira Sumayya su ka yi video call da ita, domin daga abin da Nabila take missing, har da Sumayya.
Cikin ikon Allah, hutun wata guda Viper ya samu, domin ya ƙarasa jinyarsa, dan haka suka nufo Kano.
Nabila cike da murna ta dawo, sai dai gidan su ya sha uwar ƙura, suna zuwa mayafinta kawai ta ajiye ta hau gyara.
Viper ya taimaka mata da abin da zai iya, ya tsallake ya fice, ya tafi wurin 'yan amanarsa.
Tas Nabila ta ƙalƙale gidan, ta kira sumayya a waya, ta gaya mata ta dawo, ta ce mata za ta zo.
Ta kuma kira Walida a waya, bayan sun gaisa take yi mata maganar liti.
Da fari nuƙu-nuƙu ta fara yi, daga baya kuma ta saki jiki ta yi mata bayanin komai.
A fitar da Viper ya yi, har gidan su ramma ya je, yaji daɗi da mama ta gaya masa ta koma makaranta, amma ta damu da rashin tarewarta, ta gaji da yadda sai dai ya zo ya ɗauketa su na yawo a gari.
Viper ya ce kar ta damu zai yi magana da Abdul ɗin.
Bayan ya koma gida yake gaya wa Nabila, da weekends Walid da liti za su zo, dan tun da aka yi bikinsu, Walid ne kawai ya zo.
Ta ce masa to.
Can gidansu Hafsa kuwa, 'ya'yan mama da Anty Zakiyya ta yi wa asiri, da kyar ta samu suka auru, kullum cikin ciwo suke, dan ɗaya daga cikinsu kamar zata zare, idan ta fara aljanu kamar zata haukace, hakan ya tsananta wutar ƙiyayyar da ke tsakanin su, kuma aka yi rashin sa'a, dukkaninsu babu wadda take jin daɗin zaman aurenta, ɗaya kishiyoyi sun sakota a gaba, sai da aka yi saki biyu a shakera biyu.
Ɗaya kuma dangin miji da maƙwabta, sun hanata sukuni, ga miji ba ya son haihuwa.
Abin duniya ya isheta, ta rasa abin da yake yi mata daɗi, ga Tijjani ya auri wata fitinanniyar yarinya da ba ta da kunya, ba ta ganin mutuncinta ko kaɗan, shi kuma ya zama tamkar soko, sai abin da take so shi yake yi, ba ya ji ba ya gani a kan matar nan, bai ƙi ya ɓata da kowa ba a kanta, ciki har da maman. Dan idan ta yi masa ƙorafi a kan matar, sai ya daina zuwa gaisheta.
Saifu ne dama mai ɗan dama dama, shi ma kuma ba ya ji, ya haɗa kai da yaran masu kuɗi, yana ta rashin ji, duk da ya rage, ga kuɗi yana samu, amma ya fi mayar da hankali a kan shaye-shaye da kashewa 'yan mata kuɗi, sam ba ya yi wa rayuwarsa wani tanadi.
Waɗannan tarin matsalolin ne, suka haɗu suka addabi zuciyar mama, ta kasa sukuni da jin daɗin rayuwar, duk in da ta motsa ɓacin rai da damuwa sun baibiyeta cikin yaranta kowa da halinsa.
Kawai aka wayi gari tana wanka, ta yanke jiki ta faɗi a cikin banɗaki, aka ɗauketa aka kaita Asibiti, a nan aka tabattar da ta samu shanyewar ɓarin jiki.
Ba ta iya yi wa kanta komai sai dai ayi mata, hatta najasa a kwance take yi, kasancewar jinya ba abu ne na ɗan lokaci ba, ya sanya yaran nata suka fara ƙosawa suke bata wahala.
Hakan bai zame wa Zakiyya izina ba, dan a iya cewa ita murna ma tayi, yanzu miji ya zama nata itakaɗai.
****
Liti sai ƙarewa gidan Viper kallo yake yi, an zuba wa Nabila kaya na alfarma, gidan yayi kyau sosai da sosai.
Nabila ta gabatar musu da kayan ciye-ciye, take cewa Walid "Shi ne yau baka kawo mini Shahida ba"
"Ai ita na kawo ta ma, ke fa baki taɓa zuwa gidanmu ba"
Tayi murmushi ta ce "In sha Allah zan zo, ai ina son zuwa ziyara sosai da sosai, dan ba sai na jira Vi ba, shi sabgoginsa da yawa".
Suka hau abinci da ci, Walid yana ta santin abinci, amma liti da ya karkace sai cewa ya yi "Abincin nan ya kusa kamo na 'yar madara daɗi, ita fa miyar 'yar madara sai ka kwana uku kana jin magginta a bakinka"
Walid ya ce "Sannu faisal, ka tsayar da kunnuwa kamar zomo, ka na ta gizo, ka yi wa mutane shiru"
Ta basar ta ce "Vi wai yaushe ɗan mama zai dawo ne?"
Viper ya kalleta ya ce "Sai ya shekara biyu ai, in sha Allah zan je na gano shi"
"Har shekara biyu, bai yi yawa ba?"
"Ni da na yi biyar mutuwa na yi?"
Tayi murmushi ta ce "To ai kai kai ne, shi kuwa abin tausayi"
Yayi murmushi ya ce "Shi ma zai jure ai"
Walid ya ce "Ina fatan Viper ne ya daka sakwarar nan, dan ta yi daɗi ta daku"
Ta ce "Mara lafiya ne zai daka? Haryanzu hannunsa yana yi masa ciwo fa"
Liti ya sake kallon falon ya ce "Ohh Allah sarki yar madara, gidanku na tuna Viper, da ta tare babu ko plasta, aka saka mata kayanta a ciki haka, gashi ta mutu, wata ce take morar arzikinka"
Viper dai bai yi magana ba, Nabila ta tashi ta ce "Bari na shiga daga ciki, ku gaida gida zan ɗan kwanta"
Viper ya kama hannunta, ya yi kissing bayan hannunta, ya ce "Allah ya ƙara zaƙin hannu, abinci ya yi daɗi sosai"
Cikin jin kunya ta ce "Allah ya ƙara buɗi, cefane yayi kyau sosai" ta tafi tana murmushi.
Liti ya ce "Haryanzu ina jin ba daɗi, idan na tuna ba jauhar ce ke more soyayyar nan ba"
"Abdallah" Viper ya kira sunansa yana kallonsa.
Ya kalle shi.
"Ka daina yi wa Nabila abin da ka ke yi mata, son Nabila son Jauhar ne. Wani darasi da na ƙara koya a rayuwata da Jauhar, shi ne dama sau ɗaya take zuwa a rayuwa, ko ka yi amfani da ita ko ta wuce. Na samu dama na saka halaccin da Jauhar ta yi mini da soyayya da kulawa, amma ban yi ƙoƙarin hakan ba, sai a ƙarshen rayuwarmu, kuma mutuwa ta zo ta rabamu. A yanzu wata damar na samu na saka halacci da alkhairi, dan haka a daina kushe mini Abla please"
"Tuba nake maigida an daina in sha Allah"
Ya tashi ya yi musu rakiya, sai da ta jiyo falon shiru, sannan ta fito ta hau gyarawa.
Yayi mamakin bayan dawowarsa, da take masa dan Allah su je su duba mama a asibiti, tun su na Abuja, aka ce mata tana asibiti babu lafiya.
Shi mamakin da take bashi, kamar gaba ɗaya rayuwarta ba ta da riƙo, komai girman laifin da aka yi mata kuwa, da ta gama buyaginta, sai ta saukko.
A daren suka je suka dubata, Nabila har da ba su kuɗi, sai da ta yi kuka, ganin yadda bakin maman ya karkace, sai zubar da yawu yake yi, ga wani irin warin kashi da take yi, duk da da pampers a jikinta, da alama tun safe ba a cire mata ita an canza wata ba.
Da daddare suna kwance, tana jikin Viper, ta ce "Vi"
"Mmm"
"Dan Allah in tambayeka mana, amma kar ka ji haushi Please"
Ya ce "Idan kin san zan ji haushin kar ki yi"
"Am curious"
"Go ahead"
"Na ga ka na da kishi sosai, amma na ga kamar akwai shaƙuwa sosai, tsakanin Jauhar da su yaya Walid"
Murmushi ya yi mai sauti, tare da shafa bayanta ya ce "Haka ne, dan ma Allah ya jiƙan rai Nura baya raye, ta fi shaƙuwa da shi sosai da sosai. A lokacin da ta shigo rayuwata, daga ni har su babu wani mai guiding ɗin rayuwarmu, ba mai saka mu, babu mai hana mu, abin da muke so shi muke yi.
Bayan ta shigo rayuwata, ta fara ƙoƙarin nuna mana mu ma mutane ne.
Tana da kirki da sauƙin hali sosai, a duk lokacin da na shiga matsala, babu wanda yake tsayawa a kaina, sai ita, su kuma su na dafa mata, babu wanda zai saurareta idan ba su ba.
Ko sakakken abinci ta yi, sai ta ajiye musu.
Gashi tana matuƙar girmamasu, saboda ta san dai babu wanda ya damu da mu, sai su ɗin dai.
Saboda ita muka daina askin banza, kamar babarmu, haka za ta zauna ta yi ta mita, bayan na haɗu da Nura kuwa, tun da ta fuskanci matsalarsa shi ma ta rashin kulawar iyaye ne, da ƙarancin shekaru, take tausaya masa.
Ya girmeta, amma shi ne ɗan aikenta, har kasuwa yawon sayo mata kayan shirin dutse shi yake yi mata, ina jin kishin ba bana ji ba, amma na yadda da ita, kuma idan na wulaƙanta su, saboda su daina zuwa in da take, idan na shiga matsala wa zai taimaka mata?.
Ta kai ta kawo, Nura sai ya samo abin sa, bai kalli in da nake ba, sai dai ya zo wurinta.
Idan matsala ce da shi ma, ita zai gaya wa saboda ni masifaffe ne, ta rayu da mu da tausayi ne, da kulawa babu ƙyama da jin cewa bamu da amfani, shiyasa Liti kullum cikin yabonta yake. Ta shiga cikin tashin hankali, ta kaɗu sosai da mutuwar Nura"
Ta sauke numfashi ta ce "Na fahimta, Allah ya yi musu rahama gaba ɗaya"
Ya ce "Amin my sugar girl"
"Bari zan ɗan je na dawo"
Ta kalleshi ta ce "Yanzu kuma? Ƙarfe tara saura fa, haba Vi"
"Ba zan jima ba, ki yi haƙuri yanzun nan zan dawo fa"
Ta ɗaga shi ta ce "To a dawo lafiya, banda rigima" ya sumbaci goshinta yana murmushi ya sauka.
Sai dai ba ta san ina za shi ba, ba ta san lokacin da ya dawo ba, dan sai asuba da ta ji yana tashinta tayi salla.
Gidansa da ya zauna da Jauhar, ya tafi, gidan ya yi ƙura sosai, saboda ya kwana biyu bai zo ba.
Ya haska gidan da fitilar wayarsa, kamar walƙiya ƙwaƙwalwarsa ta tariyo masa wani moment da suka yi.
Ta shigo ta tarar da shi a falo, ta ɗago masa wata jarka ta ce "Master, waye ya sha wannan abin?"
"Ni ne, ba lemo ba ne ba?"
cikin halinta na shagwaɓa ta ce "Master magani ne fa"
"Haba dai, na basir ko shawara? Ni fa in ce, ai na zata lemo ne da, amma bakomai ai tun da maganin basir ne"
Kamar ta yi kuka ta ce "Ni meye haɗina da wani basir dan Allah, kai komai na ajiye sai ka cinye, da wanda na baka da wanda ban baka ba, har nawa da naka duk sai ka haɗa ka cinye" tayi maganar tana hararsa.
Yayi mata shiru, ta gama fushinta, sai da ta manta, sannan ya ce "Ai ki na da kuɗi, a kuma haɗo miki wani mana, ke ki na neman kuɗinki da kyar, su na yi miki wayo, su na karɓar miki kuɗi, suna haɗo abin da baki sani ba su na baki"
Ta kalleshi ta ce "Su wa?"
"Masu ce miki ki sai maganin mana, ai ina jinku, ni da na zata lemo ne ki ka yi ba ki san mini ba, shi ne zan sha rabona sai daga baya na fuskanci menene a ciki, amma bakomai ai ni na sha miki maganin, zai yi miki amfani" banza ta yi masa, ta ƙi kula shi.
Dariya ya yi ya ce "Hajiya magana nake fa"
"Sai dai ka yi kai kaɗai, ba zan kula ka ba"
Murmushi ne ya suɓuce wa Viper, ya din ga jin tamkar ya buɗe idanunsa ya ganta.
Ya jima a gidan, sannan ya fita ya nufi hanyar gida.
Wurin ƙarfe takwas da rabi, Nabila ta fito tana kiransa, dan ta farka baya kan gadon.
Waya ta tarar da shi yana yi.
"Walid jiya kasa bacci na yi, na je gidanmu ne, na daɗe a can sai kusan ɗaya saura na koma gida. Ina ga zan sayar da gidan nan ne, ko kuma a gyara shi a zuba 'yan haya a ciki".
Ƙoƙarin barin wurin ta yi, ya ɗago suka haɗa ido, ya katse wayar ya ce "Ranki ya daɗe, ya aka yi ne? Ko in zo?"
Ta girgiza masa kai ta ce "Dama waya nayi da Abba ne, na fara yi masa maganar su Walida ne, amma na ga kana waya, bari na shiga ciki" ta ƙarasa maganar a gurguje, kamar mai tsoron wani abu, ko mara gaskiya.
Mintuna goma, ya ji ya kasa jurewa, ya tashi ya shiga bedroom, ya tarar da Nabila ta zubo da kaya tana ninkewa.
"Abla" ta ɗago ta kalleshi, ta mayar da kanta ta sunkuyar.
Takawa yayi gabanta, ya karɓe rigar hannunta, ya ce "Kalle ni, menene?" Ta sunkuyar da kai ta ƙi kallonsa.
"Abla am talking to you" kawai hawaye ya fara gangarowa daga cikin idanunta.
"Ya Salam Abla why, kishi ki ke?" Tafukan hannayenta ta saka a kan fuskarta tana kuka mai tsuma zuciya.
Cikin rikicewa ya ce "Ki fahimce ni abla, ki tsaya na yi miki bayani" yayi maganar yana riƙe hannunta.
Girgiza masa kai ta yi, ta ƙwace hannunta ta fice daga ɗakin.
Ya dafe kansa cikin tsananin damuwa ya sake bin bayanta.
**
Indabo kamar yana kan ƙaya haka yake jin zamansa a Nigeria, gani yake komai ma zai iya faruwa.
Da sassafe ya yi sallama da matarsa, bai tsaya ya saurari Abdul ba, ya tafi airport.
Sai dai yana cikin jirgi, wani mutum da facemask ya bashi wata takarda ya tafi, bai san waye ba, kuma mutumin bai yi masa magana ba, bai tsaya ba domin amsa tambayar da Indabo zai yi masa ba.
Ayshercool
08081012143
Bin bayan Nabila yayi yana kiran sunanta, amma ba ta tsaya ba, ya cim mata a ɗaya bedroom ɗin, tana ƙoƙarin rufe ƙofa.
Ya buɗe ƙofar ya tsaya yana kallonta, fuskarta ta koma ja, haka idanunta ma sun yi jawur.
Jiki a sanyaye ya ce "Abla, dan Allah ki tsaya ki saurareni, na yi miki bayani ba yadda ki ke zato ba ne"
Girgiza masa kai ta yi ta ce "No need, ba sai ka yi ba, na riga na fahimta"
"Ba ki fahimta ba abla, kin yi mini gurguwar fahimta, dan Allah ki tsaya ki ji"
Cikin kuka ta ce "Ni ba sai na ji ba, na riga na fahimta, ba zan taɓa samun gurbi a zuciyarka ba, ni ka aureni ne kawai ka din ga kallon hoton jauhar, ba zaka taɓa so ma ba, this is the chance you ask me to give you, shikenan na fahimta"
Diriricewa yayi ya ce "Ba haka bane, baki fahimce ni"
"Ba sai na fahimta ba, your actions show's, da tuntuni ka bar ni na tafi a kan yadda na bar wa zuciyata, na aurenka shi ne sabuwar jarrabawar da zan fuskanta, ka yi mini maganganun da suka sanya na ji na aminta ina da kima a idonka, amma bakomai"
Riƙota yayi yana goge mata hawayen fuskarta ya ce "Ko ba zaki saurare ni ba, ki daina kukan nan dan Allah ba na so" fizgewa ta yi daga jikinsa, ta shige toilet, yana jin yadda ta fashe da kuka mai tsuma zuciya.
Har cikin ransa yake jiyo kukan nata, ya nemi wuri ya zauna jiki a sanyaye, tun yana sanya ran zata fito, har ya haƙura ya tashi ya fita.
****"
"Na san wasiƙata zata iskeka a dai-dai lokacin da yakamata, kafin na jaka da nisa, bari na ɗan ja ka baya, zamanin da kana yaron 'yan siyasa, kun zo garinmu wani sha'ani, aka kai mu wurinku, wai zaku bamu tallafi, aka haɗamu 'yan matasan yara marasa galihu, aka kai wa uban gidanka, ya zaɓi wanda zai lalata, saɓanin cewar da aka yi za a bamu tallafin karatu da sana'a.
Ina cikin waɗanda bai zaɓa ba, dan haka ban san me za ayi musu ba, na shiga damuwa burina ba zai cika ba na karatu, ba a zaɓe ni ba, ba zan samu tallafi ba. Ka yi amfani da wannan damar ka keta mini haddi, da sunan zaka saka ubangidanka ya bani tallafi.
Matan da ka lalata da yawa, na san babu lallai ka tuna, sai dai shi irin wannan mikin, ba ya taɓa goguwa a zuciyar wanda aka illata.
Naja'atu Bunkuren nan dai, da ka lalata da ƙuruciya a garin bunkure lokacin kana yaron ɗan majalissa, ni ɗin ce dai, ƙaddara ta sake haɗa mu, ba tare da ka gane ni ba. Sai dai ba tare da ka sani ba, ka cika alƙawarin da ka yi, na tallafar karatuna, kuma muka ɗora daga in da ka dasa aya.
Ganin ina morarka, ya sanya na haɗiye mummunan ƙudurin fansar da nake da shi a kanka.
Sai dai duk da haka, na yi shirin ko ta kwana ta kowace irin fuska, saboda sanin tsagwaron mugunta da zaluncinka.
Lokaci ya yi da ka ke tunanin, ka ci moriyar ganga ka ya da kwauronta, ina! Idan har ka zauna a gida Nigeria, tonon sililin da zan yi maka ba zaka taɓa sha ba, haka zalika in da zaka ma ba zan bar ka ba, duk in da zaka shiga a faɗin duniya sai na kawo ƙarshenka, dan haka ya rage naka, ko ka dawo Nigeria, ko kuma ka tafi duk in da ka ke so, sai na kawo shafe tarihinka ta hanya mafi muni, zai zama daidai da ɗaukar fansar abin da ka yi mini a baya, aikin da na yi maka tsawon lokaci ma kuma ya zama halacci ga ɗawainiyar da ka yi da ni, na barka lafiya" tamkar zuciyarsa zata faso ƙirjinsa haka take bugawa, sam bai san ta ina yakamata ya fara ba, ya koma Nigeria ko kuma ya ƙarasa Saudiyya?.
Nan ya shiga lissafi, me take tunanin ta ƙulla masa, da har take iƙirarin kawo ƙarshen sa a duk in da ya shiga a faɗin duniya?
Har labarin lalatar da ya taɓa yi da yarinya a garinsu ya taɓa bata, amma ba ta taɓa nuna masa cewar ita ce ba, ashe duk tsawon lokacin nan wani abu ne a ranta game da shi.
Ya rasa abin da yake yi masa daɗi, gaba zai yi ko kuwa baya, duk iya tunaninsa ya rasa wane irin tuggun take shirya masa.
*****
Abbu kuwa ya gabatar wa da maman ramma, abin da Viper ya zo masa da shi, gam da ya aureta, ta ɗan yi shiru sannan ta ce "Alhaji Ibrahim, ni a wannan shekarun nawa, me nake nema da zan sake yin aure?"
Ya girgiza kai ya ce "Ba fa ki yi hamsin ba, kuma auren nan duk in da aka je