Showing 315001 words to 318000 words out of 479911 words

Chapter 106 - K.A.W Complete Hausa Novel

01 Jan 2025

6058

da ido.

Sumayya ta kalli agogo, lokaci ya cika, ta na tsaka da sallama da masu saurare, Nabila ta tashi ta fice, tana kammalawa, ta tashi ta bi Nabila, amma tuni ta ja motarta ta bar wurin.

Ta koma tana sauke numfashi, kiran kankarofi ta gani, ta ɗaga wayar suka gaisa, ya ce "T ladan, meyasa ki ka yi wa Nabila wannan tambayar a tsakiyar program?"

"Sir nayi ne, dan tun yanzu ta kare kanta a wurin mutane, kafin abu ya bayyana su yi mata kallon, maciya amana mai fuska biyu "

"Sumayya waye ya gaya miki ana iya wa ɗan adam ne? Ba a taɓa iya wa mutum, dan haka ki kiyaye gaba, yayi wuri ki fallasa abun haka gaba ɗaya, amma babu laifi, baki yi kaifi ba, hakan zai ƙara mata ƙaimi"

Sumayya ta ce "Ok sir, na gode" ta ajiye wayar ta yi shiru, ita a zahiri tayi hakan ne, ko Allah zai sanya Nabila ta ji nauyin dubban al'ummar da suke goyon bayanta, ta sassauta koma ta haƙura da batun Vipern nan, amma ba ta ga alamar hakan a tattare da ita ba.

Abbu kuwa a zabure ya miƙe tsaye, jin program ɗin da yayi, shi ba wani ma'abocin jin radio bane ba, yau kawai ya kunna yana saurare, ya ji shirin ya ƙayatar da shi, haka zalika muryar barrister, kamar sananniya ce a gare shi.
Sai dai jin sun yi maganar Viper, ya sanya ya tashi a kiɗime, tare da ɗaukar radion ya fito tsakar gida.

Rahila ta ce "Ya dai na ganka a firgice haka?"

"Wani shiri na gama saurara, wata lauya ta shigar da koken kotu ta hana kama Aminu, ko gidan radiyon zan je, wataƙila su sun san in da yake"

Ta kwaɓe baki ta ce "Ina rabaka da sabgar yaron nan, idan sun san in da yake me zaka yi masa? Salon ka sanya kanka a masifa, wanda ake nema ruwa a jallo da laifin kisan kai? Ka ganshi ka yi masa me? Guduwa fa yayi daga gidan yari"

Ya ƙura mata ido, kawai ya girgiza kai, ya kashe radion ya fice.

****

Nabila tana driving, wani abu ya tsaye mata a maƙogwaronta, kukan ma gaba ɗaya ta kasa saboda baƙin ciki da ɓacin rai.

Katafaren gate ɗin aka buɗe mata, ta shiga da motarta, tayi parking, ta sauka ta nufi cikin gidan.

A falo ta tarar da mahaifiyar ramma, tana ganin Nabila, ta tashi da fara'arta, tana yi mata sannu da zuwa.

Nabila ta zauna cikin yaƙe, suka gaisa, kamar kullum yau ma mahaifiyar ramma, kallon Nabila take yi, kamar ta haɗiyeta, ita dai ban da an yi mata gargaɗi, da tuni ta faɗi abun da yake ranta, dan ta tantance abun da take tunani, sai dai an gargaɗeta a kan aikata hakan, dan haka ta ja bakinta ta tsuke.

"Mama ina fatan dai babu wata matsala ko? Ki cigaba da haƙuri, in sha Allah an kusa dawo miki da ramma, kuma hujjoji nake son kammala tattarawa, na gano ainihin mai laifin, za a gabatar da shi a gaban kotu, idan da wani abu ki gaya mini"

Ta girgiza kai ta ce "Ba wani abu, ina ta godiya Ubangiji Allah ya baki nasara, na gode sosai da sosai da ke da Alhajin da ya taimake ni, ina godiya Allah ya biya ku, ya ƙara miki zaman lafiya da mijinki"

Nabila ta ce "Ai ba mijina bane mama"

"A'a ba Alhajin ba, Aminu"

Cikin mamaki Nabila ta ce "Aminu kuma? Nifa ban taɓa aure ba, ba ni da aure" tayi maganar tana murmushi.

Babar ramma ta ɓoye mamakinta, kar kwaɓarta tayi ruwa ta ce "Au, ai na zata kina da aure ne, Allah ya kawo miki nagari, ya baki mai sonki da gaskiya, Allah ya tsaya miki, kamar yadda ki ke ta ƙoƙari a kanmu"

Nabila ta ce "Amin mama, dan Allah a cigaba da yi mana addu'a, addu'aeku, ita ce ke tasiri a rayuwarmu"

Maman ramma ta ce "In sha Allah, addu'a yanzu aka fara"

Nabila ta ce "Na gode sosai" ta tashi ta nufi hanyar fita, babar ramma ta bi ta da ido, dan ranar farko da ta fara ganin Nabila, ban da an gaya mata kafin ta zo, an yi mata bayani, da babu abun da zai hanata kurma ihu, ta ce taga gawa.

Tana driving sannu a hankali, ta tsaya ta sai abun da zata ci a gida, dan ba sabgar su take shiga ba.

A harabar gidan, ta wuce Nasir, ya zuba mata ido, duk ta bi ta rame, saboda ta saka jaraba a ranta, ko kallonsa ba ta yi ba ta wuce. Duk sai ya damu da ramar da ya ga tayi, amma yana nan a kan bakansa sai ya kama Viper, ko zata mutu dan haushi.

"Ga agolancin ga yawon ta zubar, ga ta'addanci, gashi an gandame an riƙa a gida babu aure, abun bai yi miki yawa ba kuwa Nabila" Sauda tayi maganar tana dariya.

Ta sake cewa "
An baki damar ki gusa ki bamu wuri, saboda baƙin naci, kin liƙe mana a gida, tun da ba zaki tafi ba, ki iya kanki, muna son ubanmu, ba zaki kashe mana da baƙin cikin ki a banza ba"

Nabila ta tsaya cak, tare da murnar Sauda ta takale ta, ko banza ta rage zafi idan ta yaɓa mata magana.

"Ke da ki ke son uban naki, sai gashi kin gagara zaman aure, kin ƙi karatu balle hankalinsa ya kwanta. Ai sauda zaki yi mini gorin aure ne, a lokacin da ke ki ka iya zama a gidan naki mijin. Kuma karki manta da ni agola ce mai 'yanci, a dalilina igiya biyu aka sauke wa babarki ta aure, idan ku ka cigaba da matsa mini, ragowar ɗayan ma sai na tsinketa, sai ku ji daɗin zawarci tare ga uwa ga 'ya. Yawon ta zubar kuma, ina da abun bayar wa yayi mini rana, kema idan ki na so ki bayar nonsense"

Sauda ta tashi a ƙufule, Nabila ta ce "Kin san dai ba dakuwa zan yi ba, dama koma wa ki ka yi ki ka zauna"

Sauran wanda suke wurin, suka tuntsure da dariya, dan yadda Sauda ke zuba mulki da rashin mutunci a gidan nan, Nabila ce kawai maganinta.

****
Cikin mamaki Abdul ya ɗago ya kalli indabo, saboda marin da ya kwaɗa masa.

"Ina na kai mini kuɗi Abdul?"

Abdul ya yi shiru yaƙi magana.

"Ka gaya mini in da ka kai mini kuɗi, kafin na tattaka ka a wurin nan? Yarinya da ka fito da ita, da kar ka fito da ita, matsalarka ce, ba zaka kashe ni da ɓacin rai ba, sai na samo wani wanda ba zai watsa mini ƙasa a ido ba, ina ka kai mini kuɗi?"

Mahaifiyar Abdul ta ce "Abdul wai ba magana ake yi maka ba? Ina kuɗin da ya zuba a account ɗin ka, da sunan campaign kuma ya muka yi da kai a kan yarinyar nan?"

Abdul ya numfasa ya ce "Na yi wa 'yan garin su rahama gyaran makarantu da hanyoyi, na yi musu boreholes, sai kuma registration da nayi mata na karatu bar zuwa jami'a" ya faɗa kai tsaye.

Salallami suka hau yi, da tafa hannu.

Indabo ya ce "Abdul, kuɗin ka kwasa ka ƙarar a kan garin yar matsiyata da karuwa?"

Ya girgiza kai ya ce "Daddy ba karuwa ba ce ba, koma menene ni ne mai laifi, fyaɗe nayi mata, nayi hakan ne, dan na goge laifina"

A fusace Indabo ya rufe shi da duka, ga ƙiba ga hawan jini yana fama, a take ya hau haki, da kyar P.A ya janye shi daga jikinsa.

"Ƙarya ma kake yi, ka fito mini da kuɗina, sai na yi seazing ɗin asibitocinka, da duk wata kadara daka mallaka, da wadda na mallaka maka, ni zaka tonawa asiri, wallahi baka isa ba, kuma zan saka a nemo mini yarinyar ko ina ka kai ta, zan yi maganinka daga kai har ita".

"Dan Allah daddy kar ka cutar mini da ita, ba tayi laifin komai ba, ni zaka hukunta"

Ashariya ya din ga zabgawa Abdul, yama rasa me zai yi, kuɗin da suka yi sama da faɗi da su, domin campaign bisa ga yarjejeniyar idan an yi nasara zasu mayar da kuɗin da uwar riba, ga balli na neman tashi, dama kuɗin mutane ne na wasu hukumomi a ƙasa, ga balli na neman tashi, kuma Abdul ya yi masa hauka.

P. A ya ce "Kayi haƙuri, kar ka je wani abun ya sameka, ka rabu da shi, zamu san abun yi, mu fara kashe case ɗin can na gaban kotu tukuna".

"Na fara tunanin anya Abdul ɗa na ne? Ƙiriƙiri ya zaɓi mace a kaina, ni zai tozarta?"

P.A ya ce "Jarabta ce da kuma ƙuruciya ke damunsa"

"A shekara talatin da shidan ne ƙuruciya?" P.A ya din ga bashi haƙuri yana lalaɓa shi, Abdul kuwa tunu yayi ficewarsa.



*****

Madaki na zaune a cikin ɗaki, ya din ga jin hayaniya, da iface-iface ana sara suka a ƙofar gidan da yake.

Wani daga yaran sa ya shigo da kyar, ya ce "Madaki, yan ƙofa ne fa suka zo gidan nan, muna ta fama da su, sai ƙoƙari suke lallai sai sun shigo gidan nan, su sareka"

Madaki ya tashi ya ƙwalalo ido, sai dai kan yayi magana, sun faɗo gidan, sun kai su bakwai, suka zo ka hau shi da sara da suka, wasu na waje na faɗa da yaran madaki.

Duk da akwai ƙarfin zuciya, yana ta ƙoƙarin kare kansa, amma sai yaji jikinsa kamar an canza masa wani, duk yayi wani iri babu ƙwari, suka din ga saransa, ƙarshe suka janyo shi daga cikin gidan, suka din ga jan sa a ƙasa tamkar abun banza, duk da iya ƙoƙarin da yaransa suka yi, su ƙwace shi, amma abu ya ci tura, tsofaffin yaran Viper, da yan unguwar su, da ya din ga shiga yana addabawa ya hana su sukuni, su suka yi gangankon ɗaukko shi, suka yi masa laga-laga, suka din ga yawo da shi, lungu da saƙo, daga ƙarshe da ƙyar jami'an tsaro suka kawo masa ɗauki, suka tarwatsa matasan, suka ɗauke shi a galabaice, dan ba su zaci yana raye ba, suka kai shi Asibiti.

*****
"My Abdul" ta yi maganar tana murmushi, cikin hanzari ya ɗago, dan bai zaci daga bakin ramma maganar ta fito ba.

"Meyafaru ne? Gaba ɗaya na ganka a cikin tashin hankali?"

"Rahama abubuwa sun ƙara cakuɗe mini, barin ƙasar nan zamu yi"

Cikin mamaki ta ce "Mu bar ƙasar nan, mu je ina?"

"Rahama abubuwa ba zasu tafi yadda na tsara ba, zamu bar Nigeria"

"Ban gane ba, uwata fa?"

Abdul ya ce "Zan saka a kawo miki ita, yanzu visa za ayi miki, amma sai na fara barin garin nan da ke"

"Abdul, ni fa gani nake wannan guje-gujen, duk ba zasu kaimu ba, kayi haƙuri ka yi abun da mahaifinka ya buƙata mana"

Ya kalleta ya ce "Na kai ki kotu ki gaya wa duniya, ni ne nayi miki fyaɗe? Ba wannan ne ya dame ni ba, abun da zai biyo bayan shaidar da zaki bayar shi ne abun jin, dan haka ki nutsu kiyi abun da na ce kawai"

Murmushi ta yi masa da ita kaɗai ta san ma'anarsa, ta wuce shi ta tafi kitchen.

****
Daga Naja'atu har Indabo fuskokinsu ɗauke da damuwa, Bunkure tayi ƙwafa ta ce "Gaba ɗaya hankalina a tashe yake, lallai gaskiyar hausawa, ɗan hakin da ka raina, shi ne yake tsole maka ido, yarinyar nan dai ta dage sai ta ga bayana, idan asirina ya tonu, ban san wane irin kallo zan yi wa al'umma ba. Abdul duk shi ya janyo wannan abun.

P.A ya ce "Duk ku kwantar da hankalinku, babu wani abu da zai faru, kamar yadda ka yi umarni, dattijon nan zai shiga silent, yanzu uwar yarinyar ta rage, ita muke binciken in da take, kuma ita ma zamu ganota in sha Allah, Abdul ma muna daf da gano, wurin da ya ɓoye yarinyar nan"

Indabo ya girgiza kai ya ce "Ban san in da Abdul ya koyi wannan baƙin taurin kan ba, magana ta fito fili, an ce a binciki ministocin da muka ƙulla harƙallar kuɗaɗen nan da su, na san kuma dole sai sunana ya fito, wai ya kwashe kuɗin nan, ya yi wa yan ƙauye ayyukan raya ƙasa, na rasa uban abun da ya samu a jikin yarinyar talaka mara galihu, ya nace mata take abun da ta ga dama har haka"

Bunkure ta sauke numfashi ta ce "P.A ya batun barrister Nabila?"

"Kamar yadda na gaya muku, sponsiring ɗin ta ake yi, na gwada sakawa a kamo mini ita, amma hakan ya gagara akwai jami'an da suke bin ta, wanda ba san suwaye ba, kuma da alama ita kanta ba ta san suna bin ta ba"

Indabo ya ce "Kar ku ja da nisa, kankarofi ne, babbar buƙatar sa ya ga ya kai ni ƙasa, ya rama abun da nayi masa, kuma yayi kaɗan".

*****
Nabila na zaune a ɗakinta, tunanin ma ta rasa wanne yakamata ta yi, kawai ta ga Nasir ya shigo ɗakin, ba ta ko motsa ba, balle ya sanya ran za ta kula shi.

"Nabila"

Ta ɗaga ido ta kalleshi. "Da gaske ke ki ka nemi a hana kama Aminu Viper"

"Eh" ta faɗa a nutse.

"Nawa aikin ki ke burin ɓatawa kenan, me nayi miki haka ne?"

Ta kalleshi ta ce "Ba kai nake fatan ɓatawa aiki ba, duk wani mara gaskiya sai na ɓata masa aiki. Gaba ɗaya ka canza i miss my old DSP, the only person that understand me" tayi maganar tana tashi ta bar shi a ɗakin.

Tana office ɗin ta, tana son zuwa duba jikin malam garba, tana son zuwa wurin 'yan sanda, tana son ganin Viper, ga kuma maganar Abba da ta tsaye mata, da ya ce taje ta nemi ubanta, ta bar masa gida.
Kenan Abba ya goyi bayan ɗan sa, shi ma a wannan karon ya nuna mata, gurbin ido ba ido bane ba.

Turo ƙofar office ɗin aka yi, ta tashi zaune sosai daga kashingiɗar da tayi, tana tunanin ina ta taɓa ganin baƙon nata.

Ya samu wuri ya zauna, suka gaisa, ya ce "Baki gane ni ba ko?"

Ta jinjina kai ta ce "Gaskiya dai"

"Haka ne, magana na zo mu yi da ke mai muhimmanci"

Nabila ta ce "Ok, ina jinka"

"Saƙo ne daga wurin distinguish Ma'aruf Indabo, na zo mu yi magana mu fuskanci juna da ke"

Nabila ta yamutsa fuska tana kallonsa.

"Muna yi miki tayin ki fanshi kanki da kanki ne, kan abun da ba a so ya afku"

"Ɗan yi sauri, ina da wurin zuwa"

P.A ya ce "Maganar da na zo da ita, ta fi abun da zaki je yi muhimmanci, muna son ki janye shari'ar nan ta batun fyaɗe nan, case ne tsakanin ki da Bunkure, kuma ko yanzu kin cika burinki a kanta, akwai maƙudan kuɗaɗe muddin ki ka aikata abun da na ce"

Nabila ta ce "Malam na yi maka kama da shashasha ne? Da Bunkure nake case ɗina, meye nasa a ciki? Bibiyar rayuwata da ya saka aka din ga yi, da ƙoƙarin kashe ni, duk bai ishe ku ba, shi ne zaka zo mini da maganar bunkure? Wallahi idan kaga na bar case ɗin nan, to an hukunta ainihin mai laifin ne, kuma muddin wani abu ya same ni, kai ko mutuwa nayi, ina da manya manyan hujjoji a kan sa, da suke a hannun wakilai ne, akwai wanda za su ɗora, in sha Allah sai na bayar da misali a Nigeria, an fara hukunta masu riƙe da madafun iko, da iyalansu, ba wai doka a kan talaka kawai ba, everyone is equal before the law"

"Haka ki ka ce?"

"Hala kurma ne kai?"

Ya ce "To bari mu gani, yaro bai san wuta ba sai ya taka"

"Na santa farin sani, tun da na ɗaukko ƘARFEN CIKIN WUTA, da ya gagari hannaye da yawa"

P.A ya kalleta ya ce "Me ki ke nufi?"

"Zaka fahimta nan ba da jimawa ba"

Yana fita tayi tsaki, ta ɗauki jakarta ta fita, a nan ta bar motarta, ta hau abun hawa ta tafi gidan Viper.

Yana tsakar gida, daga shi sai ɗan mama a gidan, suna hira.

Sun daɗe suna kallon juna, sannan ta ƙarasa ciki, ta samu wuri ta zauna ba tare da ta ce masa uffan ba.

Ya samu abu ya zauna, ya ce "Ya ake ciki, meye labari?"

"Ko ka neme ni, kwana biyu ina cikin damuwa da tashin hankali, amma ko a jikinka"

Ya tsuke fuska ya ce "Menene?"

"Vi"

Ya Kalle ta, tare da ɗage girarsa ɗaya.

"Ka dubi girman zatin Allah, ka tausaya mini, ina ga ciwon zuciya na daf da kamani, kowa ya ja da baya ya juya mini baya, Abba ya yayyaga hotunan nan ya watsa mini, ya ce naje na nemi ubana na bar masa gida, daga shi har yan gidanmu, babu wanda yake kula ni. Gashi a  tsakiyar program sumayya ta hau yi mini tambaya a kanka, yanzu ta ko ina mutane sai attacking ɗina suke yi a media, saboda case ɗinka, client ɗina malam garba wai ya yanke jiki ya faɗi na je na duba shi, na tarar wai ya samu stroke, yanzu P.A ɗin Indabo ya bar office ɗina da tashi barazanar, kuma haryanzu ka ƙi gaya mini dalilin da ya sanya Indabo yake bibiyata. Na rasa ya zan yi me zan yi ne? Kamar na gaza, ba wanda zan je na samu duk na gaya wa damuwata, dan Allah Viper ka gaya mini wacece ta jikin hoton nan, ina jin kamar ina da alaƙa da ita, tun da ni dai na san ba ni bace ba, dan Allah idan akwai wani abu da ka sani ka gaya mini, atleast na rage wata damuwar".

"Na gaya miki ban san komai ba, 'yan gidanku zaki tambaya"

"Na gaya maka ba zasu gaya mini komai ba, so kake sai na mutu ban san babana ba, idan kana da yadda zaka yi ka taimake ni dan Allah, ko hakan ne alfarmar da ya rage da zaka yi mini a rayuwa" tayi maganar tana haɗa hannayenta biyu cikin sigar magiya.

"Ana kiranki a waya"

"Ni ba ta waya nake yi ba, ka taimaka mini dan Allah"

"Ki ɗaga wayarki " yayi maganar yana kallon ta.

Ta ɗaukko wayar, ta ga lambar barrister Habib ce, ta ɗaga wayar ta ce "Hello"

"Na duba office ba kya nan, Allah ya yi wa malam garba rasuwa yanzun nan" miƙewa ta yi tsaye, ta saki wayar, ta tashi za ta nufi hanyar fita, jikinta yana rawa.

Cikin zafin nama, Viper ya tashi ya riƙe ta, gaba ɗaya ta gigice, ta ce "Sun kashe shi, wallahi kashe

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login