Showing 294001 words to 297000 words out of 479911 words
yana nazari.
Ya zauna a kusa da shi ya ce "Sannu da hutawa"
"Yauwwa sannu da zuwa"
"Yauwwa, tunanin me ka ke yi ne?"
Viper bai ba shi amsa ba ya ce "Meye labari?"
"Labari, yan unguwar su madaki, sun addaba wa yan unguwarmu, naji ɗan mama ya ce zai shiga unguwar, sai kuma na je maɓoyar madaki, na tarar baya nan, ko dai ya tafi wani wurin bamu sani ba?"
Viper ya ɗan kaɗa kai ya ce "Kar ka damu na san in da yake"
Cikin mamaki ya ce "Ka san in da yake kamar yaya?"
"Kamar yadda na ce" ya faɗa a taƙaice.
Shiru ya wanzu na wani ɗan lokaci, Viper ya ce "Jibi yarinyar nan zata shiga kotu, ta kuma ce a kwankin nan zata fara shari'ata, i need to assist her, a haka ma rayuwarta na cikin hatsari, muddin ta shiga case ɗin nan matsaloli zasu ninku fiye da baya, akwai buƙatar na taimaka mata sosai"
Walid ya ce "Haka ne, Allah ya tabattar mana da alkhairi, ya bamu dukkanin nasara, ka yi yanci mai zamani, ka daina wannan zaman ɓuyan"
Viper ya dafa kafaɗar Walid ya ce "Mai laya"
"Na kiyayi mai zamani"
"Mu huta wannan zaman ɓuyan zaka ce, idan Allah ya bamu nasara, in ga kun tsaya da ƙafafuwan ku, na aurar da kai, da wancan sarkin faɗan"
Walid ya ce "A'a, ka yi yanci, muga farincikinka da walwalarka sun dawo dai, mu dai mu cigaba da gurgura rayuwa"
Viper ya girgiza kai ya ce "Aure yana da daɗi mussaman idan ku ka yi dace kamar yadda na yi. Ni na taɓa yi na more shi, kuma yakamata ku yi, idan na bari ku ka ƙarar da rayuwarku a kan hidimata kawai ban yi wa kaina adalci ba muhsin"
Walid ya ce "Taɓ anya na taɓa jin ka kira ni da ainihin sunana kuwa?"
Viper ya yi murmushi ya ce "Ka tuna mini da watarana, da 'yar madara ta sakani a gaba, ta ce sai na gaya mata ainihin sunayenmu, na ce mata ni Muhammad Al'amin, kai Muhsin, liti Abdullahi. Ta rafka salati, ta ce kalli yadda duk kuka mayar da sunayenku wani iri, har ma ɗan gara yaya walid, duk da shi ma wataran mai laya kake ce masa, gaskiya ku canza hali, sunayenku masu daɗi, amma duk kun canzawa kanku suna. Na ce ;Sunan waye yafi daɗi, tayi murmushi ta ce na mijina, na ce yauwwa ke ma sunanki mai daɗi an saka miki wani iyayi daban. Muhsin ku yi aure akwai alfanu a cikin aure, haryanzu na kasa manta rayuwar cikin aure, na san abu ne da ba zai bar ƙwaƙwalwata ba. Ina son naga kun samu cigaba a rayuwar ku, ba zan yi alfahari da ku ƙarar da rayuwarku a kaina ba"
Walid ya kalli Viper ya ce "Al'amin, ko mai muka yi maka a rayuwa ka cancanta, ai duk ɗan halak baya manta alkhairi, idan kai ka manta ni ba zan manta ɗawainiyar da ka yi da ni da mahaifiyata ba, haka zalika mutuntawar da matarka tayi mana"
"Muhsin, mahaifiyar ka, mahaifiyata ce, ka daina saka wannan a lissafi"
Walid ya ce "Na daina, amma dai sai mun fara aurar da kai tukuna, farincikin ka da walwalarka su dawo, sannan mu san abun yi mu ma"
Viper ya girgiza kai ya ce "Bani da ra'ayin kuma yin aure a rayuwata, wancan ma tsautsayi da ƙaddara ne ya saka aka yi shi"
Walid ya yi murmushi ya miƙe ya ce "Wannan kuma, ƙaddarar tausayi da soyayya zai saka a ayi shi" har Walid ya yi gaba, Viper ya miƙe da sauri ya ce "Ina ba zai yiwu ba, jauhar ce kawai a zuciyata" kawai walid ya ɗaga masa hannu ba tare da ya waiwaya ba ya yi gaba yana dariya.
***
Salim ya kalli Abdul da ya shigo a gajiye, ya zauna ya ajiye labcourt ɗin sa a gajiye.
"Yaya ne mutumina, na ganka a wahale"
"Aiki na sha yau ɗin nan, na je asibiti ya kai huɗu, na duba wanda na yi wa tiyata, sannan na yi wa wasu aikin sai godiyar Allah"
Salim ya yi murmushi ya ce "Sannu, ko in ɗaukko maka abar ne, ina da ita a mota?"
Abdul ya girgiza kai ya ce "Rahama ta san warin giya, faɗa zamu yi da ita"
Salim ya ce "Wow, to ko abinci zamu je ka ci?"
Nan ma ya girgiza kai ya ce "Ina da special cook a gida, yarinyar nan dar ce" yayi maganar yana kashingiɗa.
Salim ya kwashe da dariya ya ce "Allah mutumina, ta saduda kenan?"
Abdul ya yi murmushi.
"Ina jinka, bani labari"
"Salim, kai ka san komai, tun da ka tafi fa babu labarin mahaifiyar yarinyar nan, gashi ta matsa mini na mayar da ita gida, ni ba mayar da itan ne ya dame ni ba, na fara yi wa daddy bayani ko zai fahimce ni, ya hau ni da faɗa da zagi, kuma wai lallai sai na kai masa ita, sai an kaita kotu ta bayar da shaida, ni fa na yanke shawarar zan ɗauke ta mu ƙara gaba, har takarar ma bana so. Wallahi Salim ban taɓa dana sanin aikata wani abu a rayuwata ba, irin yi wa rahama fyaɗe ba, kuma ban taɓa jin so da ƙaunar wani abu a raina ba, kamar yadda nake jin son ta, ya mamaye zuciyata ba, Salim wallahi ba zan iya rabuwa da rahama ba, ba wai ina sonta da jikinta ko wani abu ba, ita ɗin nake so"
Salim ya ce "Ƙarya ne malam, mun san komai fa"
Abdul ya yi murmushi ya ce "Ita ta sani ai, ba zan yi maka ƙarya ba"
Salim ya ce "Kar ka damu, na fahimta maganar ka ɗauketa kayi gaba bai taso ba fa, ka zauna ka yi wa daddy cikakken bayani"
"Salim na san waye mahaifina ciki da bai, muddin na fito da rahama, zai iya salwantar da rayuwarta, ita kanta mahaifiyarta ina tantama a kan bashi ne ya ɗauke ta ba, ni kuwa a kan rahama sai dai ayi duk wadda za ayi"
Salim ya waro ido ya ce "Da iyayen naka? Abdul yaushe ka koma haka ne? A cikinmu duk rashin nan da kai da Saif kun fi mu mutunta iyaye ma da jin maganar su mussaman kai, meyasa ka ke son canzawa saboda mace?"
"Kamar yadda take yawan faɗa, na riga na ɓata rayuwarta, dan haka ba zan bari a sake tagayyara rayuwarta ba, ina son rahama irin son da nake son na ƙarasa rayuwata da ita, idan Daddy ya cigaba da matsawa, ba zan yi wancan auren ba"
Ya girgiza kai ya ce "Ba za ayi haka ba, ka je ka fara maganar da mahaifiyar ka, ko zata fahimceka"
Ya ce "Taɓ ayi sha'ani kawai, zan je zanji kiran da yake yi mini amma in fito da rahama dai, gaskiya ban ji zan iya ba"
"Amma fa Abdul mun tafka shirme a gaban uwar yarinyar nan, anya zata yafe maka kuwa? Ga tsiyar da ka je ka kuma yi daga baya"
Abdul ya numfasa ya ce "Sharrin giya ne, da gigin arziki da nake ji da shi, nake jin kamar zan iya taka na ƙasa da ni, ni komai zata yi, mini tayi mini amma ban da raba ni da yarinyar nan".
Salim ya ce "Lallai ka faɗa da yawa mutumina"
"Rahama, akwai haƙuri, duk da ina cin zagi a wurinta da tsinuwa, amma da ta ganni cikin rashin lafiya, ko damuwa hankalinta yake tashi, ita take dafa abincin da zan ci, yau har da yi mini guga. Nifa yarinyar da aka ce za a haɗa ni da ita, gaba ɗaya bata yi mini ba buɗaɗɗen ido ne da ita, gara a bar ni da rahaman dai, na san koma menene ni ne sila"
Salim ya jinjina kai.
***
Nabila ce a tsaye a gaban court, tana ƙoƙarin fara gabatarwa da mai shari'a appeal ɗin su, ta kalli barrister Habib, ya jinjina mata kai alamar bata ƙwarin gwiwa, ta tsaya ta gabatar da kanta cikin harshen turanci, tare da fara karantowa kotu koken su.
Na kotun ta yi duba da rubutaccen jawabin da suka gabatar, a kan hukuncin da kotun farko ta yi, bisa ga wasu kurakurai da suke ganin an tafka a wurin yin shari'ar, na rashin bayyanar wadda abun ya faru da ita a gaban kotu, da rashin gabatar da medical report ta hannun ɗan sandan da kuma likitan da ya tabattar da yin laifin ba.
Hakazalika a hujjojin da suka gabatar a kotun farko, akwai sautin murya, na mahaifiyar ramma tana koken a kawo mata agaji, domin kuwa wanda ya yi mata fyaɗe ya dawo ya ɗauke ta, idan kuwa haka ne, wanda ake zargi ba shi ne ya aikata wannan laifin ba, sannan kuma wanda ake zargin ya amsa laifin ne, a sakamakon barazana da aka yi masa, da haka take roƙon kotun ta bibiyi shari'ar da kotun baya tayi, ta tabattar da adalci"
Ta miƙa file ɗin aka miƙa gaban mai shari'a.
Suna tafe a mota tare da barrister Habib ta ce "Yaya, gaba ɗaya jikina a sanyaye yake, gani nake wannan karon ma, ba zan yi nasara ba"
"Bana son saurin karaya dan Allah, kin manta wadda ki ke ƙoƙarin tunkara ta fi wadda ki ke yi yanzu? Kuma yanzu hankalin mutane da yawa ya dawo kanki, ba common mutanen gari ba, har da ma'aikatan shari'a"
"Idan Allah ya sa na yi nasara, akwai gagarumin tonin silili fa" tayi maganar tana murmushi.
Barrister Habib ya kalleta ya ce "Na me fa?"
"Zaka gani kai dai, ya batun case ɗin Viper, samo mini copyn shari'ar da na ce?"
"Ai na gaya miki ba aiki ne mai sauƙi ba, ina nan ina ƙoƙartawa, yanzu idan aka san ina ƙoƙarin samo file ɗin ma, rayuwata na cikin hatsari"
Ta jinjina kai ta ce "Haka ne, Allah ya ba da sa'a"
***
"Inadabo, wallahi akwai matsala muddin Abdul bai kawo yarinyar nan ba, tun da ya ce maka tana wurin sa ya fito da ita mana"
"Naja duk wani ƙoƙari ina yi, bai taɓa bujirewa umarnina ba sai a wannan karon, yama daina zuwa in da nake gaba ɗaya, bana samun wayoyinsa"
"Ka san kuwa me nasararta a appeal ɗin nan yake nufi? Yarinyar nan fa ba zata zuba mana ido ba, dole ka yi ƙoƙari fa a kai"
"Kar ki damu, zan ga alƙalin da kaina"
Bunkure ta girgiza kai ta ce "Ƙoƙarin ka ba a kan alƙali kawai zai tsaya ba, har da wannan yarinyar, dan ni na yi iya yi na"
Inadabo ya katse kiran, ba tare da ya sake yin magana ba.
****
Babu tsammani, indabo ya shiga falon mai ɗakinsa, ya tarar da ita tana yi wa Abdul faɗa. Yayi turus, sannan cikin tsananin ƙuluwa ya ce "Ai dama na sani, ke ki ke goya masa baya, yake rashin mutunci"
"A'a nima fa yanzu na ganshi, nake tambayarsa ba'asin ina ya shiga, kar ma ka ɗora mini wannan zargin"
"Wato Abdul ban isa da kai ba kenan ko? Nayi maka magana sai ka ɗauke ƙafarka gaba ɗaya daga gidan ka daina zuwa, ina yarinyar take?"
Abdul ya yi shiru ya ƙi magana.
"Ka gaya mini in da take, tun ban tattaka ka ba, yau an yi appeal ɗin shari'ar yarinyar, kuma muddin aka wanke mutumin nan, babu lallai ka tsira ba tare da asirinka ya tonu ba".
Abdul ya ce "In dai hakan yana nufin na cigaba da rayuwa da ita, shikenan ni ba komai asirin nawa ya tonu, dan Allah Daddy ka yi haƙuri, wallahi ba zan iya fito da rahama gaban duniya ba, ban san iya abun da zaka yi mata ba, kuma bana fatan abun da zai ƙarasa zubar da mutuncinta, dan kuwa fito da ita gaban kotu kamar cigaba da yayata abun da ya faru da ita ne"
Tamkar shashasha indabo ya tsaya yana kallon Abdul, babu kunya babu tsoron Allah Abdul yake gaya masa wannan maganganun.
Ya numfasa ya ce "Babu laifi, ni na san matakin da yakamata na ɗauka".
***
Nabila ta shiga office ɗin ta, ta zauna ta janyo drower zata ɗauki biro, ta ga file, ta ɗaukko file ɗin ta buɗe, kawai taga copyn shari'ar Viper ne a ciki, sai da ta razana ta ja da baya, tana waige-waige.
A razane ta ɗauki waya, ta kira barrister Habib, ya ɗaga ya ce "Hello Nabila"
"Barrister ka samo file ɗin nan ne?"
"A'a, ina ta ƙoƙari dai a kai, ki yi haƙuri"
"Barrister, file ɗin na gani a office ɗina"
Ya ce "Wane file ɗin?"
"Na shari'ar Viper"
"Iyee, waye ya baki?"
"Nima ban sani ba, a office ɗina na tarar kamar yadda aka ajiye mini na Bunkure"
"Kar ki gaya wa kowa, gani nan zuwa"
Ta ajiye wayar tana sake dudduba file ɗin.
Ji ta yi an buɗe ƙofar office ɗin ta razana da sauri tana ɓoye file ɗin, ya rufe ƙofar office ɗin, ya ƙaraso.
Ta ce "Yau ma kai ne da kanka?"
Ya ce "Eh, ko in koma ne?"
"A'a, bisimillah zauna"
Ya samu wuri ya zauna, kamar yadda a wancan karon, tayi masa hidima, haka ma a wannan karon, ta haɗa masa tea, ta bashi abincinta da ta zo da shi, ta bashi" wannan karon babu gardama ya karɓa ya ci.
Ta ciro file ɗin ta ajiye masa ta ce "Yau da safe aka kawo mini shi, ban san kuma wanda ya kawo ba"
Ya karɓa ya bubbuɗe, yana dubawa.
"An fitar da sanarwar cigaba da nemanka jiya, wai yaranka sun je sun yi faɗan daba, jami'an tsaro na ta cigaba da yayata nemanka"
Ya girgiza kai ya ce "Ni ma na ji, sai dai ni bani da masaniyar hakan, na samu labarin faɗa tsakanin yan unguwarmu da yan unguwar su madaki, ban san ma me ake ciki ba"
"Zan je kotu, na nemi kotu ta hana kama ka, kafin na ɗauki mataki na gaba"
Viper ya jinjina kai yana kora shayin hannunsa.
Ya ce "Bani system ɗin ki"
Ta ɗaukko, ta bashi ya ciro tab ɗin sa, ya ɗan jima yana danne-danne, yayin da ita kuma take satar kallonsa kamar yau ta fara ganinsa.
Kamar kar ya tafi ta daina ganinsa, wani irin shauƙi da farinciki ya din ga ratsa zuciyarta.
"Ki shirya, zamu je ki ga shaidar da nake da shi, idan da abun da ki ke buƙatar sani"
Ta ce "To shikenan, ka sanya lokaci sai mu je, sai kuma mu yi ta addu'a".
Ya ɗan daddana tab ɗin hannunsa ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Barka da wannan lokaci, kana magana da mai zamani ne.
Babu buƙatar yin doguwar magana, na san zuwa yanzu ka san labarin haɗuwata da ɗanka, zuwa yanzu na san duk wani motsinsa, duk in da yake zuwa na sani, amma ba wannan ba, akwai buƙatar ka bibiyi case ɗin ɗanka da ka ke musayar sa da ni, a lokacin da yake Nigeria yake aikata laifuka, ina da babban albishir gareka, Mexico na shirin miƙawa amurka shi, ya fuskanci shari'a, kuma ina mai sanar da kai kisan kai ne hukuncin abun da ya aikata.
Na san zaka yi mamakin yadda aka yi aka kama Jafar, akwai buƙatar mu haɗu fuska da fuska nayi maka bayani" ya katse wayar, tare da tashi tsaye ya ce "Ka zan bar wurin nan"
Ita ma ta miƙe ta ce "Amma....
"Amma me?"
Sai ta tsaya tana kallonsa "Ina son mu yi magana ne, ina da tambayoyi"
"Ba yanzu ba, am not safe here"
Ta ce "To muje, na raka ka gate nima fita zan yi" ta tattaro file ɗin, da jakarta suka fito.
Tun kafin su ƙaraso, ya zuba masa ido, duk da fuskar Viper sanye yake da facemask, amma hakan bai hana shi gane ko waye ba.
Suna ƙarasowa yayi murmushi ya ce "Barrister, wurinki na zo, ina Abuja aka ce mini kin samu accident, sai dai na samu labarin da sauƙi jikin, duk da haka na ce bari na zo na ganki, kuma na ganki da baƙo. Assalamu alaikum" yayi maganar yana miƙawa Viper hannu.
(Ayi mini afuwa ji na shiru, bani da lafiya ne)
Ayshercool
08081012143
71
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
Arewabooks ayshercool7724
Viper ya tsaya ƙyam yana kallon Alhaji mu'azzam da ya miƙo masa hannu.
A rikice Nabila ta ce "Amm eh, ai na ma warware na ji sauƙi, ka shiga, ka jira ni a office ɗina, yanzu zan dawo"
Viper ya kalli Nabila ya ce "Koma ciki" sai ta tsaya tana rarraba ido, tana kallonsa tana kallon Alhaji mu'azzam wada.
Wani irin kallo Viper ya yi mata, da ya tilasta mata barin wurin, tana waiwayawa.
Viper ya saka hannunsa a hannun Alhaji mu'azzam, ya sauke facemask ɗin sa yana kallon cikin idonsa.
"Dama ana ganinka, ka yi wa hukuma wuyar kamawa? Ya aka yi na ganka tare da yarinyar da nake so, kuma nake fatan na aura?"
Viper ya tsananta riƙon da ya yi wa hannun Alhaji mu'azzam ya ce "Ka gaya mata wani abu ne?"
"Kamar me fa?"
"Ka san abun da nake nufi" yayi maganar yana ƙara tsare shi da ido.
Alhaji mu'azzam ya ce "Kana tsoron wani abu ne?"
"Ba maganar tsoro bane ne ko akasin haka, gargaɗi ne nake yi maka, idan baka furta ba kar ka fara, nike da alhakin kai ƙarshen wannan lamarin, idan ka yi wani yinƙuri da zai kawo tangarɗa ga abun da nake tsarawa, ka san abun da zan iya aikatawa".
Alhaji mu'azzam ya yi murmushi ya ce "Da fari jauhar, na bar maka ita, a wannan karon kuma Nabila, kar ka zama mai......
"Jauhar ta wa ce, haka zalika Nabila, muddin zan cigaba da ganin fuskar jauhar a cikin ta Nabila ta haramta a gareka, ba kai ba kowane mahaluki ma" ya fizge hannunsa daga na Alhaji mu'azzam ya mayar da facemask ɗin sa ya bar wurin.
Nabila kuwa kai komo ga din ga yi a office ɗin ta, cike da fargaba da tsoro.
Kankarofi ya turo ƙofar office ɗin Nabila ya shigo, ta tsaya tana kallonsa yayi mata murmushi ya ƙarasa ya ce "Madam ya na ganki a tsaye ne?"
Murmushin ƙarfin hali ta yi ta ce "Bisimillah zauna mana"
Ya zauna ya ce "Ashe tsautsayi ne ya kuma afkuwa haka, ya ƙarfin jikin?"
Ta ce "Jiki da sauƙi Alhamdilillah"
"Amma dai babu wani mummunan rauni ko?"
Ta ce "Eh, gocewar ƙashi na samu a hannuna, amma Alhamdilillah da sauƙi"
"To Alhamdilillah, na ji daɗi ƙwarai, ya shari'a kuma?"
Tayi murmushi ta ce "Mu na ta fama, sai fatan Ubangiji Allah ya iya mana"
"Allah ya yi jagora, kin ga kamata yayi ace har gida na je dubiya, daga nan na miƙa buƙata ta ga Abba, ayi komai a kan lokaci, kin ga babban mutum ne ni, amma soyayya ta saka