Showing 348001 words to 351000 words out of 479911 words

Chapter 117 - K.A.W Complete Hausa Novel

01 Jan 2025

6105

musamman tsakanin malaman dagacin ƙauyen, da ƴan rigar su jibo, a kan a samu fahimtar juna, su bar Jibo yayi karatu, su ma idan suna buƙata zasu iya kawo wasu yaran, a cigaba da yi musu karatu, amma suka ƙi suka ce ba sa son yahudanci.

Abu sai da jami'an tsaro suka shiga, suka ce sai Jibo yayi karatu, ba tare da an cigaba da tsangwamar sa ba.

Da kyar aka samu masalaha, sai dai can a riga suka ce, sai dai ya bar musu rigar su, babar sa ta din ga kuka tana yi musu magiyar kar su korar mata ɗa.

Idan bai ga dama ba, idan ya tafi sai juma'a yake dawowa, kan ya dawo innarsu ta ɗan tanadar masa busashshiyar fura, man shanu, nono, ta ce ya tafi da su, kar ya ji yunwa, haka kurum ta ji ita dai tana son abin da yake yi. Ta fuskanci ƙalubale sosai da sosai, ana cewa ita take goya masa baya, duk lokacin da ya zo, idan zai tafi sai chubaɗo tayi ta kuka saboda sun shaƙu.

Tana da shekaru huɗu, haka zai zauna da ita, yana koya mata idan baffa ya ƙyalla ido ya ganshi, ya ɗauke chubaɗo yayi ta yi masa masifar kar ya lalata masa yarinya shi dai ya je ya ƙarata.

A haka aka zaɓi ɗalibai har da maitama, aka ce za a kai su makarantar kwana.

Nan ma an sha gwagwarmaya, kan maitama ya tafi.

Chubaɗo na da shekaru shida, Allah ya yi wa mahaifiyar su rasuwa, maitama yana can makaranta. Da ya zo hutu ya sha kuka, ya shiga tashin hankali da kiɗima mai yawan gaske.

Da aka nutsa, suka sake ce masa sai dai ya zaɓa, ko boko ko ya dawo yayi aure, amma ya ce boko, suka ce to ya bar musu riga. Bai damu ba, bai kuma daina zuwan ba.

Baffa ya auri ramata, ta riƙe mairamu hannu bibbiyu kamar ita ta haife ta. Sai dai tun tana ƙarama, take fama da matsalar numfashi, sai dai ko maganar asibiti ba ayi, sai dai ayi ta banka mata hayaƙi, wai iskokai ne, cike da jahilci. Ga kuma matsalar iskokai da take fama da su.

Maitama ya ɗauke ta, ya kaita asibiti babu wanda ya sani, likitoci suka tabattar da athma ce da ita, wanda irin ciwon ne ya kashe mahaifiyar su.

Sai da aka kusa ƙaramin yaƙi a zuriyar, saboda kai mairmu Asibiti da yayi.

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, maitama ya yi degree, ya tafi aikin soja, amma duk sunansa Bayahude a wurin mutanen rigar.

A yanzun ma haka suka ƙyale shi, bayan yi musu barazanar saka yahudawa su ƙwace musu shanu su kore su daga riga.

Har magana yake yi wa mairamu da turanci, kuma tana iya gane wani abun.

Ya fara kashe bakinsu, bayan da ya fara basu 'yar shinkafa kyauta.

Lokacin aurensa da kyar suka je masa walicci, sai dai da suka ga birni sun rikice da yawa, ya so a bashi mairamu amma fafur suka hana shi.

Shekaru suka cigaba da ja, chubaɗo na da shekaru goma sha uku a duniya, tsantsar kyawunta, ya fara baiyyana, samarin ƙauyen sun fara kawo hari, saboda kyakywar gaske ce, sai dai da yawa suna tsoron larurarta ta matsalar numfashi da suke cewa aljanu ce.

Duk lokacin da Maitama ya zo garin, sai ya kawo mata kayan sawa, na kwalliya, wanda babu wata yarinya da ta taɓa amfani da su a rigar. Ya kan bugi cikinta duk wanda ya ji ya nuna yana sonta, sai ya je yayi masa barazanar saka yahudawa su kama shi, su mayar da shi ƙarfe.

Ya kan kawo mata litattafai, ya sayo mata radio, ya gaya mata lokutan da ake gabatar da wasu shirye-shirye a radio na yara.

Watarana da ta zama ranar mabuɗin sada chubaɗo da ƙaddararta, ta bi 'yan matasan matan da suke fita can bakin hanya sayar da nono, domin ta je ta ga motoci, ta fita da shanu, ta fake da haka, dan Baffa baya barinta ta je ko ina.....

Ayshercool
08081012143

84
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

*BRIGHT PENS SECOND BATCH*


Fitar ta yi wa mairamu daɗi sosai da sosai, dan ko kiwo zata fita, ba ta yi hanyar barin garin, balle ta fito bakin hanya.

Suna zazzaune, shanunta na gefe na kiwo, sai nishaɗi take ji, tana ƙissima ta nan hanyar hammanta yake wucewa, idan zai zo riga, ko kuma ya tafi. Yayi mata alƙawarin komai daɗewa zai zo ya ɗauketa daga riga, ya tafi da ita can in da yake, ita ma ta ga gari, amma ba zata ji daɗin tafiya ta bar baffa da dada ba. Gashi rashin jituwar hamman da baffa baya yi mata daɗi, sai dai tana fatan barin rigar, tana son tayi karatu irin na hammanta, babban abin da yake ƙara burgeta da yi mata daɗi, shi ne idan ya zauna yana koyar da ita karatun addini, yana bata tarihin Annabi Sallallahu alaihi Wasallam, da sahabbansa wanda yake matuƙar ratsata da sanya mata nutsuwa da farinciki.
Idan ta tafi birni, wurinsa ta san kullum sai ya bata tarihin Manzon Allah da wasu annabawan. Kuma ta huta da takurar baffa, a kan rashin fitowar manemanta, da an fara magana sai abu ya lalace, ya fara zancen ko iskokai ne suke hana maganar, ya saka ayi ta banka mata hayaƙi, dan an saka hayaƙi kuma sai ta hau suma, hakan ya sanya suke ƙara yadda da hakan. Bayan haka bijirewar jibo na zaman riga da zaɓar boko da barazanar da yake yi, ya ƙara sanya samarin garin nesanta kansu da Chubaɗo.

"Chubaɗo, tunanin me ki ke yi ne?" Firgigita ta farka tana murmushi ta ce "Bakomai, daɗi nake ji, yau gani a bakin hanya, ina ta kallon motoci" sauran yan matasan suka din ga yi mata dariya, dan su suna zuwa, ita ce dai baffa baya barinta zuwa ko ina.

Wani mutum suka hango yana tunkarosu, hannunsa riƙe da galan, gashi matashi a ƙalla zai shekara ashirin da bakwai, a ganinsu babba ne, amma sanye da ƙananan kaya, wanda hakan baƙo ne a wurin su.

Yayi musu sallama suka amsa, ya ce "Yan mata dan Allah ina zan samu ruwa? Motata ta ɗauki zafi, a can baya na bar ta, kuma ina son zan yi salla, ruwan sha ne kawai a mota ta"

Dukkaninsu kowa ya ce "Bai sani ba"' ban da chubaɗo, da tayi ƙuri da ido tana kallon kayansa, hamma yana saka irin kayan, kenan shi ma bayahude ne?.
Ya ja ya tsaya cikin damuwa yana waige-waige, da alama kuma a gajiye yake.

Kamar daga sama cikin siriryar muryarta ta ce "Na sani, amma ruwan  rafi ne, kuma a ɗan ciki ne" tayi maganar tana nuna masa hanya, yanayin hausar ya tabattar masa da cikakkiyar bafulatana ce, duk yan matan babu mai mayafi, suna sanye da kayan saƙi da ɗan kwali.

Duk suka waiwaya suna kallon chubaɗo.

Ya ce "Yauwwa yar albarka, nuna mini wurin"

Cikin harshen fulatanci, suke gargaɗin ta a kan meyasa zata bi kaɗo, daga ganin sa yau.

Ta ce "A tarihin Annabi da hamma yake bata, Annabi yana taimakon mutane, kuma babu kyau wulaƙanta mutane" ta wuce gaba ya fara bin ta a baya.

Tayi gaba ba tare da ta ce masa uffan ba, tana ta kaɗa 'yar sandarta, tana cilla ƙafarta cikin nishaɗi.

Ya ce "Ba a kusa ba, na gaji" ta tsaya ta waiwaya ta ce "To kawo abun ka zauna ka jirani, sai na ɗebo maka".

Ya ce "A'a mu je" suka cigaba da tafiya, sun yi tafiya sosai, sannan suka ƙarasa rafin, ya durƙusa yayi alwala, ya ɗebi ruwa a galan ɗin da ya zo da shi.

Yana satar kallonta, gaba ɗaya ba ta da wata damuwa, tana ta wasa da layar da take wuyanta ta sauko har kan ƙirjinta, hannu ɗaya kuma tana wasa da sandarta.

Ya gama suka nufi komawa, ya ce "Ya sunanki ne?"

"Mairamu"

Ya ce "Masha Allah, sunana Bashir, ina yawan wucewa ta hanyar nan, ba taɓa zaton akwai mutane ba, ko daga wani wurin ku ke zuwa?"

Ta ce "A'a rigarmu na can ciki"

Ya ce "Masha Allah, mu je na sai nonon na sha, idan zan wuce na din ga tsayawa mu gaisa, ba zan manta da taimakon da ki ka yi mini ba"

"Ba ni nake sayar da nonon ba, ni rako su kawai nayi, shanuna nake kiwo"

"Au har kiwon shanu ki ke yi? Lallai ke jaruma ce" suka yi maganar lokacin da suka dawo in da ya tarar da su, ya sa nono mai yawa sosai, ya basu kuɗin.

Ya ce "Mairamu, sai na sake dawowa, ni ɗan garin azaren jihar Bauchi ne, ta nan nake wucewa, sai mu din ga gaisawa na gode sosai Allah ya saka da alkhairi" ta amsa da amin.

Suka koma gida, sai da aka gaya wa ramata mariƙiyar chubaɗo, ta bi wani kaɗo ta raka shi rafi, ramata tun daga ranar ta hanata bin su.

Bashir ya daɗe yana wucewa, idan ya tambaye su ina mairamu, sai su ce masa an hanata zuwa. Ya ce idan sun je su gaishe ta.

Sukan gaya mata, sai da ta ce musu to, amma bata ɗauki hakan da muhimmanci ba.

Maitama ya sake zuwa rigarsu, sun fafata da baffa sosai, a kan ya bashi mairamu, amma ya hana shi, ya ce shi aure zai yi wa yarsa, ba za a kaita cikin kafurai ba.

Ga surutu ya fara yawa a kan rashin aurar da chubaɗo duk da irin kyau da Allah ya bata.

Maitama ya kawo mata ƙatuwar radio da carsets, na wa'azi da tarihin manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam, ya koya mata yadda ake amfani da ita.

Da daddare ƙawayenta da maƙwabtansu, zuwa suke su taru ta kunna musu, suyi ta saurara, idan wannan ya ƙare a saka wancan.

Wani zuwa maitama ya zo da matarsa da ya aura, har da yara biyu da ta haifa, a wannan karon suka fara zuwa garin tare.

Duk da haushin maitama da suke ji, sun karrama matarsa da yaransa sosai da sosai, sai dai a fili ta nuna ƙyamarta ga rigar, da nuna ita ba zata iya zama ba.

Mairamu kamar ta haɗiye yaran nan, tayi ta ɗaukar ƙaramar tana goyawa, tamkar ta haɗiye su, da kyar suka yi sati ɗaya.

Watanni shida suka shuɗe, mairamu ta sake bin ayari, zuwa bakin hanya wadda ta tasamma zama ƙaramar kasuwa.

Ana ta hada-hada, kawai ta yanke jiki ta faɗi, numfashi ya sarƙeta, ya zamana ko motsi bata iya yi.

Gaba ɗaya hankalinsu ya tashi, suka rasa yadda za su yi da ita, kamar an yi masa wahayi, sai ga motar Bashir, ya zo wucewa ya tsaya zai sayi nono ya wuce, ya hange su sun yi cincirindo a wuri ɗaya.

Ya sauka ya fita, yana zuwa ya tarar da chubaɗo a baje a ƙasa ko motsi bata yi.

Cikin tashin hankali yake tambayarsu, meyafaru da ita? Suka gaya masa faɗuwa tayi.

Saroro suka yi, ganin ya taɓa ta, ba ta motsa ba, sai wani irin numfashi mai sauti daga ƙirji da take yi.

"A garin nan kuna da Asibiti ne?" Suka ce "A'a, sai dai wurin mai magani"

Bai yi sanya ba, ya ɗauki mairamu, ya sakata a motarsa, ya ce wasu daga cikin su su bishi, su tafi kaita Asibiti.

Hama ce ta ce masa "A'a mufa rigarmu ba a zuwa asibiti" duk aka rasa mai bin sa, kawai ya shige motar ya ja ya tafi da ita.

Cikin tashin hankali, suka kwashi kayansu, suka koma riga.

A lokacin maitama yana gari, ai kuwa cikin kiɗimewa, aka yi ayari suka taho bakin hanya, amma babu Bashir babu alamarsa.

Ramata kuwa tuni ta fara kuka tana salati, tana Allah ya rufa mata asiri ya sanya a ga mairamu, ba ita ta haifeta ba, amma akwai soyayya da shaƙuwa a tsakanin su.

Sai dai suka dawo bakin hanya, amma babu Bashir babu chubaɗo, sosai Baffa ya din ga yi wa ramata faɗa, ta din ga kuka kuwa.

Maitama ya ce su bari zai je asibitocin hanya ya duba, in dai da gaske kamar yadda sauran suka faɗa, asibiti ya ce zai kaita, to zai ganota.

Baffa ya ce lallai sai dai su tafi tare, suka rankaya suka din ga duddubawa, ƙarshe a wani asibiti a nan jalingo suka gano mairamu.

Maitama ya fara yi wa mutumin masifa, a kan dan meyasa zai ɗauke ta ya tafi da ita.

Bashir ya ce "Ku yi haƙuri dan Allah, na san na ɗaga muku hankali, cikin yaran an rasa wanda zai biyo ni, na tarar da su da ita a gefen hanya, ba ta numfashi shiyasa kawai na ɗauke ta zuwa asibiti, in da muka fara zuwa suka turo mu nan"

Baffa ya din ga faɗan shi baya zuwa asibiti, bai yadda da wannan abun ba, a ɗaukko masa 'yar sa ya tafi da ita.

Maitama ya ce "A'a ba za ayi haka ba".

Chubaɗo ta galabaita sosai da sosai, baffa ya cigaba da mitar, sai an bashi 'yar sa, za a kashe masa 'ya duk an ɗaura mata wasu kwanuka a fuskarta.

Likitoci suka ce, ba zasu bayar da chubaɗo ba, ba ta warware ba, aka din ga kai ruwa rana da baffa, da kyar aka lallaɓa shi, ya ce yar sa ba zata kwana a wurin ba.

Yamma sosai, Maitama yana son mayar da baffa gida, amma ba zai yiwu ya bar mairamu a asibiti ba, da mutumin da bai sani ba, ga lokacin babu waya.

Ya lallaɓa baffa, ya kai shi tasha ya ce komai dare zai dawo masa da mairamu gida.

Sai dai ya ga Bashir ba shi da niyyar tafiya, ya ce "Abokina mun gode da taimakon da kayi mana, zaka iya tafiya fa"

Bashir ya ce "Ba zan iya tafiya na bar ta a halin nan ba, zan yi ta wasi-wasi ne. Dan ban manta alkhairin da tayi mini ba watanni baya" ya bashi labari.

Nan hira ta ɓarke, yake bawa maitama labari, cewa shi coustom ne, ƙarshen wata yake komawa Bauchi hutu, yanzun ma gida zai tafi ya tsaya sayen nono, ya tarar da chubaɗo babu lafiya.

Har yake bashi labarin, ainihi shi ɗan kasuwa ne, ya fi son harkar kasuwancin sa, amma aka turasasa masa wannan aikin, duk a takure yake.

Shi ma maitama yake bashi labarin shi soja ne, nan da nan suka saba, suka din ga hira, kasancewar jikin da ɗan sauƙi.

Yake gaya masa burinsa a kan mairamu tayi karatu, amma baffansu baya so, soyake lallai sai ya aurar da ita, ga shi bata da cikakkiyar lafiya.

Suka kwana tare ta farfaɗo sosai aka bata magani, maitama ya ce ya samu dama, tafiya zai yi da mairamu can garin da yake aiki, a Benue state.

Haka aka yi, asubar fari suka hau motar Bashir, ya je tasha in da ake hawa motar garinsu, ya bayar da saƙo a gaya wa Baffa, Bashir ya rage musu hanya, maitama yayi ta yi masa godiya sannan suka rabu.

A hanya ya sake jaddadawa mairamu, zai tafi da ita gidansa da yake zaune, taji daɗin hakan, sai dai ta wani fannin ta ji kewar gida, yadda aka rabota da garin babu ko sallama.

A cikin barrack gidan sa yake, matarsa kawai sai ganinsa tayi da mairamu, dan hatta kayan sakawa a hanya ya saya mata.

Bayan ya huta take tambayarsa, lafiya ta ganshi da ita, ya sanar mata ta dawo nan da zama, nan ta ce bata yarda ba, shi kuma ya ce to ta koma gidansu, shi zai rayu da ƙanwarsa.

Ta ɗauki gaba da fushi da shi, shi kuwa ko a jikinsa, chubaɗo bagidajiya ce a birni, ba ta iya komai ba, ta din ga ganin abubuwa kamar ba a duniya ake ba, maitama da kansa ya din ga koya mata abubuwa.

Baffa ya rikice kamar yayi hauka, bayan samun saƙon maitama, na ya tafi da mairamu.

Mairamu daga ita sai maitama, sai yaran gidan take mu'amala da su, hatta amfani da kayan wanka komai shi ya koya mata.

Satinta uku a garin, babu alamar musulmai a in da suke, duk sati maitama yake kaita ganin likita, saboda matsalar ta. kwatsam sai ga Bashir. Abun ya basu mamaki nesa ba kusa ba, wai duba mairamu ya zo.

Nisan tafiyar kawai maitama ya din ga hangowa, suka karɓe shi, suka karrama shi sosai da sosai, ya din ga murnar ganin mairamu ta samu lafiya. Sai da ya kwana a garin sannan ya koma.

Sai dai bayan wata guda ya sake dawowa, a lokacin maitama ya saka mairamu a makarantar boko, karatun addini kuma, yana koya mata a gida.

Duk wani aikin gida, mairamu tana yi wa matar hammanta, amma sam bata gani, kawai ta tsaneta.

A wannan karon, maitama ya rutsa Bashir, a kan ya gaya masa dalilin zuwan da yake yi, bai yi ƙwauron baki ba, ya sanar masa son mairamu yake yi.

"Kana mutumin birni, tayaya zaka auri bafulatanar daji, yarinya ƙarama?"

Ya ce masa shi babu komai zai iya yana son ta a haka, sai dai da magana ta yi magana, ya sanar masa yana da mata biyu.

Maitama ya ce yayi haƙuri, ba zai iya aura masa mairamu ba, duk da matashi ne, ko talatin bai yi ba, amma yana da abin hannunsa, ya ce yarinya ce yar ƙauye mara wayo wahala kawai zata sha.

Sai dai mairamu, bai gaya mata yana son ta ba, amma maitama ya lura da yadda take murna idan ya zo.

Sai dai hakan bai hana shi, sake niƙo gari ya zo Benue ba, saboda mairamu. Maitama ya sake jadda masa, ba zai bashi mairamu ba, ya ce shi in dai zai zo ya ganta shikenan, haka ya cigaba da sintiri.

Wani zuwa da yayi, ya bata wasiƙa lokacin da ya zo, ta zauna ta karanta ta kasa, saboda manyan turanci ne, ta kai wa hammanta ta ce ya karanta ya fassara mata, ita ba ta san me aka rubuta ba.

"Kalaman soyayya ne" ya bata amsa. Sai tayi shiru tana mamakin wace irin soyayya kuma?.

Tana kewar baffa da kuma dada, amma tana jin tsoron gaya wa hamma yayi fushi.

Sai da ta shafe watanni biyar, sannan maitama ya je riga, aikuwa ya sha takaici, dan ƙiris ya rage baffa yayi masa baki, ya ce ya dawo masa da 'ya ya aurar da ita, kar ta lalace.

Maitama ya ga idan ya dawo da ita, ba zata cigaba da samun kulawa ba, saboda yadda suka jahilci zamani da cigaban da ya zo da shi.

Ya ce "To yanzu akwai mijin da zaka aura mata ɗin?"

"A'a amma zan samo mata"

"Ni ina da wanda zan

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login