Showing 201001 words to 204000 words out of 479911 words
mini, ɗan yar matar gidan ne yayi abun ba shi ba ne ba, shi asibiti kawai suka kaita, da shi da ɗaya mai aikin da wani mai yi musu hidima a gidan, definitely duk case ɗin ne but i want to confirm"
Sumayya ta numfasa ta ce "Ban ƙi ta taki ba, amma ki bi a hankali, kin ga a kan case ɗin, sai da Murtala ya kusa rasa aikinsa, ke daga ji kin san case ɗin babba ne"
"Sumayya tsoron da muke ji, da ja da baya shi ke saka wasu ma suke Fuskantar irin matsalolin, idan na gama bincike na, i will raise the case, hatta 'yan sandan nan da abun da suka yi mini, duk sai na yaɗa, just support me sumy, Allah zai taimekemu, ke 'yar jarida ce, zaki iya kema".
Sumayya ta ce "Haka ne, amma kar ki kira ni a wayata, zan ki ra ki da wani layin, sai mu haɗu da yaya murtalan" ta yi wa sumayya godiya, tana sake bawa kanta ƙwarin gwiwar lallai za ta tsaya wa wannan dattijon kuma za ta yi nasara.
***
Abdul ne yake kallon ramma, yadda duk take a takure, tana kallon tv, amma hankalinta ba a kan tv yake ba.
"Rahama"
"Na'am" ta amsa tana kallonsa.
"Meyake damunki ne?" Tayi shiru ta sunkuyar da kai.
Ya kwanta a kan cinyarta, ya ɗora ƙafarsa ɗaya kan ɗaya yana danna remote.
Ya tashi ya ce canzo hijjabinki ki zo, ta yinƙura jikinta na rawa, ta sako hijjabi, ta fito.
Ta tarar da shi a tsaye da mukulli a hannunsa yana waya.
Ta ƙaraso jikinta yana tsuma, tunaninta ko gida zai mayar da ita, ya riƙe hannunta, ya buɗe ƙofar falon suka fito.
Da kansa ya sakata a mota, ya rufe sannan ya zagaya ya kunna motar ya fita da ita.
Sai kallon gari take yi, duk da dare ne ko ina da hasken fitila, tun da ya kawota a sume, ba ta sake fita ba, kuma ba ta san a ina take ba.
"Gida zaka mayar da ni?"
Ba tare da ya kalleta ba ya ce "Ai na ce ki daina wannan tunanin ma"
Cinema ya kaita, wai kallon film, bayan tv suka baro a gida, ta din ga waige-waigen yadda za ta yi ta gudu, amma a in da suke zaune, yana rungume da ita, ga wurin duk ƙabilu ne, abun da ta fuskanta, ba iya cinema ne wurin ba, dan daga can wani wuri, kaɗe-kaɗe na tashi.
"Naga ki na ta waige-waige, ba mahaukaci bane ni, da zan kawo ki inda zaki iya guduwa, ko ki yi wa wani magana ba, kowa sabgar gabansa kawai yake yi a wurin nan, gara ma ki nutsu"
Tayi ajiyar zuciya ta ce "Ko bangon duniya zaka kai ni, idan Allah ya yi niyyar fitar da ni ba ka da dabara".
Yayi murmushi kawai, sai da ya gama abun da yake yi, ya ɗauke ta, suka tafi ya kulleta a mota, ya sayo mata abinci, ya mayar da ita in da suke.
***
Nabila kuwa tana ta bin kwatancen da dattijon nan yayi mata, na gidan zulai ɗaya mai aikin da suke aiki tare da ramma, amma ta kasa gane kwatancen, ganin ta gaji, kuma ta hanyar ake bi, a je in da Viper yake, ya sanya ta tare abun hawa, ta sake tafiya.
A wannan karon da ta sauka, google map ɗin ta buɗe, tana duba abubuwan da suke wurin, ba tare da gazawa ba, ta cigaba da yawon bulayin neman gidan, cikin sa'a bayan shafe mintuna talatin tana bulayi, ta hango gidan.
Wata irin ajiyar zuciya ta yi, sannan ta nufi gidan.
Ƙofar gidan a rufe, ta saka hannu ta tura ƙofar, tayi sallama.
Ƙofar ta buɗe, sai dai ba ta ji motsi ko alamar mutum a gidan ba.
Duk da gabanta faɗuwa yake yi, amma haka ta ke ta addu'a ta shiga. Tsakar gidan ko ina shirgi, can bokiti, ga tukunya can kaya sauran sigari tsakar gidan kaca-kaca.
Ta ƙarasa ta leƙa ɗakin, ta hango Viper durƙushe a kan gwiwarsa, yana ƙoƙarin yi wa kansa allura, sai dai hannunsa sai rawa yake yi, gashi ya huda jijiyar, jini ya fara zuba.
Da sauri ta ƙarasa, ta durƙusa, ta gyara masa sirinjin, ta cigaba da zuba masa ruwan allurar.
Rintse idanunsa yayi, jin yadda allurar take ratsa jikinsa.
Babu tsammani, ta zare sirinjin ta ce "Wannan abun da ka ke yi, zai iya shafar ƙwaƙwalwarka fa" ba ta gama maganar ba, ta ji ya faɗo a jikinta, ta faɗi a wurin saboda nauyinsa, ƙoƙarin ture shi take yi, dan ji ta yi tamkar wani ƙaton dutse ne ya faɗo mata.
Ya ɗago idanunsa ya kalleta, ya saka hannu ya shaƙe wuyanta.
Numfashinta ya fara fita sama-sama, ta rirriƙe hannunsa idanunta suka yo waje.
Walid ne ya faɗo ɗakin da gudu, ya fara ƙoƙarin janye Viper daga kanta.
A tunaninsa jikin Viper yayi sakin da zai ture shi kawai, amma ya ji da ƙwarinsa.
A wahale ta ce "Zaka kashe ni fa" a hankali ya saki wuyanta, Walid ya ɗago shi da ƙyar, ya kalli walid, ya kalleta ya sake mayar da idonsa kan Walid da ƙarfin gaske ya ce "Walid"
"Na'am Al'amin"
"Walid matata, matata walid! Ɗa na Walid mata ta" yayi maganar yana wani irin ƙaraji, tare da jan rigar walid da ƙarfin da sai da ta yage.
"Easy maza, easy yi haƙuri"
"Walid zan haukace, walid kaina zai tarwatse, me zan yi ne wai, ka fitar mini da yarinyar nan, ba na son ganinta matata walid" yayi maganar yana girgiza kansa.
Nabila ta tashi da kyar, tana ta haki, ta ce "Zaunar da shi zan yi masa magana dan Allah"
Walid ya ce "Ɗauki jakarki ki tafi, yi sauri"
Kawai Viper ya shammaci Walid, ya buga kansa da ƙarfi a jikin bango, take jini ya fara biyo hancinsa, ya faɗi ya suma a wurin.
Nabila ta ƙwala ihu, saboda sautin da kansa ya bayar, da ya buga kan, Walid ma a rikice ya ɗago shi, amma ko motsi baya yi.
Ayshercool.
08081012143
49
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
Arewabooks ayshercool7724
Cikin matsanancin tashin hankali Nabila ta nufe su, Walid ya rikice, ya rasa me ma yakamata ya yi ya taimakawa Viper.
Cikin azama Nabila, ta ɗaga kan Viper yana kallon sama, ta ciro hular kanta, ta toshe hancinsa da yake zubar da jini, ya zamana ta gefen bakinsa yake numfashi.
Cikin kuka ta kalli walid ta ce "A kai shi asibiti mana, ya bugu da yawa, tun da abun ya kai ga zubar da jini ta hancinsa"
Walid ya ce "Ba za a kai shin ba, uban waye ya ce ki kuma zuwa ai duk ke ki ka ja?"
Cikin rashin fahimta ta ce "Ni kuma? Ni me na yi? Zuwa na yi na bashi haƙuri a kan abun da na yi bisa kuskure, wallahi ban yi masa komai ba, tarar da shi na yi yana yi wa kansa allura jikinsa yana rawa, na karɓa amma wallahi ban yi masa komai ba. Ko duk haushin abun da na yi wa ɗan uwanku ne? Na je station ɗin ai, kuma na yi magana da shi, dan Allah ku yi haƙuri rashin sani ne ya sanya na aikata abun da na yi masa, abun da ake faɗa a gari a kansa daban, ni kuma ban san gaibu ba, amma dan Allah ku yi haƙuri" tayi maganar hawaye wani na bin wani a fuskarta.
Walid ya ce "ya isa haka, tashi ki tafi"
"A haka za a bar shi, ba zaka kai shi asibiti ba?"
"Ta yaya zamu kaishi asibiti ana nemansa a kama shi?"
Fizge-fizge Viper ya fara yi, yana ƙoƙarin tashi, Walid ya daddane shi, cikin ɗaga murya ya ce "Walid"
Ya ce "Na'am Al'amin"
"Liti" walid ya ce "Ya shiga banɗaki".
Viper ya sake cewa "Mai laya"
"Na kiyayi mai zamani, Allah ya ƙara maka lafiya"
"Gobe zamu je asibiti da ƙanwarka 'yar madara, sun ce inducing za su yi mata 'yar madara za ta haihu, ragonta yana ƙauye wurin Hajiya"
Walid ya ce "Masha Allah, Allah raba su lafiya"
"Walid"
"Na'am mai zamani"
"Cikin nan yana ba ta wahala, nima na ƙagu ta haihu, na ga yarona, sunan ƙanina nura zan mayar, idan ta kuma haihuwa na saka sunan Sadik".
Walid ya ce "To Allah ya kawo mana su lafiya da albarka"
Wani irin ihu ya hau yi, yana ƙoƙarin ture Walid, cikin ƙaraji ya ce "Walid matata ɗa na, ba zan iya komai ba, ka riƙe madaki, kar ya illata mini mata, ka riƙe shi walid wai me ka ke yi ne?"
Sosai suke kokowa da Walid, ga hancinsa na cigaba da zubar da jini, ga damuwa da fita hayyaci a dalilin allurar nan.
Walid ya ce "Sai na ci uban ɗan mama idan ya dawo, bai ji me na gaya masa a kan kawo maka kayan maye ba, sai ya saka mun yi babu ka rasa ƙwaƙwalwarka tukuna".
Nabila kuwa iya ƙarfinta take kuka, tsananin tausayinsa ya mamaye zuciyarta, da ƙyar walid ya danne shi, a hankali jikinsa ya saki, ya daina motsi, amma yana motsa idanunsa, a buge yake ya fita hayyacinsa amma ba bacci yake yi ba, abubuwan da suka wuce ne suke dawo masa cikin mayen.
Nabila ta ce "Dan girman Allah ka gaya mini ƙarashen labarin nan, ina jauhar ina abun da yake cikinta?".
Walid ya ce "Kin ga ni ba wannan ne a gabana ba, lafiyar ɗan uwana da taya shi ɗaukar fansa ita na saka a gaba, dan haka ki tashi ki tafi kawai"
Nabila ba ta sake magana ba, ta tashi jiki a sanyaye, ta ɗauki jakarta, har ta kai bakin ƙofa, ta waiwayo ta sake kallonsa, hakan yayi dai-dai da buɗe idanunsa, sun yi jawur gwanin ban tsoro, ya tsura mata ido, a hankali ta juya ta fice.
Cikin maye ya ce "Mai laya"
"Allah ya taimaki mai zamani"
"Ba na son ganin yarinyar nan, zan iya fara kisan kai a kanta".
Walid ya girgiza kai ya ce "Ba ka taɓa yi ba, kuma ba zaka fara a kanta ba" surutan da Viper ya cigaba da yi ne, ya tabattar wa da Walid ba ya cikin hayyacinsa.
***
Ramma ta na zaune, ta na cin farcenta, tana zancen zuci, ta ji Abdul ya kama hannunta.
Sai da ta firgita, kasancewar tayi zurfi a zancen zuci.
Hannunsa riƙe da nail cutter, ya fara cire mata faratan ya ce "Ƙazama kawai, da baki ki ke cin farce" janye hannunta ta yi ta ce "Ni kar ka shafa mini cuta" tayi maganar tana haɗe rai.
"To cuta ta nawa kuma, in dai ina da ita da tuni kin ɗauka ta can wurin. Duk rashin ji na, ina using protection, a kanki ne kawai nake gaba gaɗi, shi ma dan na san am safe na killace ki" tsaki ta yi ta kawar da kanta gefe.
Ya kama hannunta, ya cigaba da yanke mata farcen ta ce "A banza, wallhi ko haɗiyeni zaka yi, ka fito da ni, ba zan yafe maka zaluncin da ka yi mini ba"
Bai kalleta ba ya ce "Dama ban ce ki yafe mini ba ai" ya na cikin yanke mata, ta ga yana ɗan yamutsa fuska, ya gama ya tashi ya koma ɗaki, ta kalli falon komai tsaf solomon yake gyarawa, a ranta ta ce "Dama aure ne da ni, ace nan gidana ne ba wannan ƙazantar ba. Tunanin hakan kawai ya saka idanunta cika da hawaye.
Ta ɗaukko magazines ɗin da ke falon, tana ta kalla, har ta manta da shi a gidan, ta shiga bedroom ɗin, ta tarar shi a kan gado yana murƙususu.
Ta kalleshi ta ce "Menene?"
A wahale ya ce "Kira mini solomon" ta juya ta fita, ta kiro shi.
Ya ɗaga kai ya ce masa ya kawo masa biro da takarda.
Ya kawo masa, yayi rubutu a jiki, ya ce yaje ya sayo masa.
Solomon ya fita cikin sauri, ta kalleshi ta ce "Wai menene?"
Ya ce "Epigastric pain ne"
"Me kenan" ya nuna mata cikin sa.
Ramma ta ce "Sannu Allah ya sa mutuwa zaka yi na huta"
Yayi mata shiru, ya cigaba da juyi, ya dunƙule hannunsa yana dukan gadon a hankali, yana yi yana miƙa alamar yana jin jiki sosai.
Ta tsaya tana kallonsa, gumin da yake yi, ya sake tabattar mata ya fara galabaita.
Yayi mata nuni da hannunsa ta je, ta ce "In zo in yi maka me?"
Girgiza kai ya hau yi, yana kiran "Mummy, rahama cikina am in pain"
"To sannu"
Ta samo jarka da ruwa, ta tofa masa bisimillah ƙafa 19, da suratul fatiha ƙafa 7, ta hau kan gadon ta ce "To tashi ka sha ruwa" ya tashi da ƙyar ya karɓa, ya shanye, yayi jifa da jarkar, ya kwanta a kan cinyarta ya ce "Rahama cikina"
"Allah ne yayi maganinka, a cikin sakans idan ya ga dama, zai rabaka da rayuwarka, ka ga idan mutuwa zaka yi, ga saɓo kana yi, ga zaluncin da ka yi mini, Allah ya sa ka mutu".
Abdul ya ce "Da na mutu shahidi, ciwon ciki ne ya kashe ni, kuma ƙarshe ace ke ki ka kashe ni".
"Ko shahidi ka mutu kan ka shiga aljanna, sai ka shiga .... Sai kuma ta yi shiru. "Allah dai sai ya ƙwatar mini hakkina a wurinka na zalunta ta da ka yi"
Solomon yayi knocking, Abdul ya ce ya shigo, ya shigo da leda a hannunsa, Abdul ya karɓa, ya sakawa kansa butterfly needle, ya saka ramma ta haɗa allurar da aka kawo, ya ce tai masa.
"Ni ba zan iya ba, tsoro nake ji"
"Tsoron me malama, ciwo zai kashe ni"
"To ni taɓa yi na yi?"
Cikin tsawa ya ce sai ta yi, hannunta na rawa, ta zuba allurar a cikin butterfly needle ɗin.
A haka ya nuna mata yadda za ta saƙala masa ruwa, yana yi suna faɗa, ta saka masa ya sa hannu ɗaya ya janyota, ya sake kwanciya a kan cinyarta.
Yadda yake wash wash da kiran sunanta, sai ya ƙular da ita kamar ba namiji ba.
"Ni ka daina kiran sunana tun da ba ni na ɗora maka ba"
"Wash rahama cikina" tsaki ta yi ta ce "Wai shekarunka nawa?"
"36yrs" yayi maganar yana kallonta.
"Amma an yi asarar ƙuruciya, idan ba ka yi wasa ba kana cikin wanda annabi ya ce kun yi asara, ka tafiyar da ƙuruciyarka a shirme da shashanci, a mintuna ashirin ɗin nan da Allah ya ga dama, da yanzu babu kai, me zaka ce wa Allah, ka sha giya ka kwana kana zina da 'yar da ka raba da uwatta, ka canza tunani da halaye, ko Allah ya yi maka rahama".
Ya lumshe idanunsa ya yi shiru, bai ce mata komai ba.
***
Nabila kanta tamkar zai tarwatse ita ma haka take ji, so take ta kamo bakin zaren tallafawa Viper. Babban abun da yake buƙata yanzu rehabilitation ne, a fara nesanta shi da shaye-shaye, sannan a kwantar masa da hankali da ƙoƙarin tirsasa masa karɓar ƙaddararsa ta hanyar da ya dace. Sannan a fuskanci kamo zaren tsaya masa, ya ɗauki fansar abun da aka yi masa ta hanyar doka, ba ta hanyar da yake tunanin ɗauka ba, sai dai alamu sun nuna mata ba zai sarrafu cikin sauƙi ba, balle a samu fahimtar juna da shi, sai dai ta ƙudurce a ranta, duk tsanani da wahalar lamarin, za ta tsaya a kan sa, ko da kuwa sanya rayuwarta cikin hatsari ne, za ta yi domin taimakon Viper.
Sai dai hakan ba zata yiwu ba, sai ta ji ƙarshen labarinsa, amma ta yaya?. Da ta tuna yadda yake kururwa yana kiran matarsa, ɗansa sai ta ji ta karaya, tausayinsa ya ƙara kamata.
Ringing ɗin wayarta ne ya katseta daga tunanin da take yi, ta ga lambar sumayya, ta ɗauki wayar ta kara a kunnenta.
Sumayya ta ce "Na yi wa Uncle murtala kwatancen gidanku, zai zo ya same ki, sai ku yi magana".
Nabila ta ce "Kai sumy, ban da ni ki bari na je na same shi, ni da nake nema?"
Sumayya ta ce "Ya zo ya same ki is more safe, ba wanda zai kawo wani abu, kin san yanzu rayuwa babu tabbas mussman irin aikinmu".
Nabila ta yi murmushi ta ce "Hakane masoyiyya, na gode sosai, saura ɗaya aikin"
"Wanne kenan?"
"Waye indabo?"
"Kin ga ki raba kanki da indabon nan, wai me ki ke nema a kansa ne? Ba dai kin yi masa wulaƙanci kin ƙi gaishe shi ba, menene na bibiyarsa"
Nabila ta yi murmushi ta ce "Ba zaki gane ba, ki taimaka kawai"
"Nabila kamar kina ɓoye mini wani abu fa".
"Ba abun da nake ɓoye miki, mamakinki kawai nake yi, duk kin canza kina abu kamar mara gaskiya kwanan nan sumayya"
Dummm gaban Sumayya ya faɗi ta ce "Ban gane ba"
Nabila ta yi dariya ta ce "Kar ki manta fa ni lawyer ce, idan na so zan gane idan ma baki da gaskiya, don't mind me kawai dai na ga kina ƙoƙarin kawar da maganar indabon nan ne, shiyasa nake tsokanarki, am about to do something big, zan gaya miki menene daga baya"
"Nabila Please, kar ki je ki yi abun da ba shikenan ba, ki raba kanki da duk wani abu da zai sake haɗa ki da Aminu Vipern nan, kar ma a cetare ku ke. Ki bar DSP yayi aikinsa dan Allah"
"Ni ba maganar Viper nake yi miki ba, case ɗin dattijon nan nake magana a kai, amma ki binciko mini maganar indabon nan, ko na binciko da kaina".
Sumayya ta ce "To shikenan na ji zan yi, amma ki san in da zaki din ga zuwa da abun da zaki din ga yi kin ji arfan Abba"
Nabila ta yi murmushi ta ce "Ji sai ka ce wata uwata, to na ji sai anjima" ta kashe wayar tana murmushi, a duniya bayan Abba ba ta tunanin akwai wanda ya kai Sumayya damuwa da ita, da tsoron ta aikata wani abu, da zai janyo mata matsala.
Bayan sallar magariba, Murtala ya kirata a waya, ya sanar mata da ya zo, yana ƙofar gidan su.
Ta saka hijjabi ta fita, suka gaisa ya ce "Sumayya ta ce "Ki na nemana"
"Au ba ta yi maka bayani ba?"
Murtala ya ce "Tayi mini, daga bakinki nake son ji".
"Haka ne, ka ga wani case na samu, na wani dattijo, an yi framing ɗin sa, wai yayi wa wata yarinya 'yar aikin da yake gadi fyaɗe, na je na yi magana da shi, yayi mini bayani, ya ce ba shi bane ba, ɗan yayan matar gidan ne, so abubuwa da yawa are similar to rahoton da ka bayar kwanakin baya, shiyasa na ce bari na neme ka, ka ƙara yi mini bayanin yadda abun yake".
Murtala