Showing 237001 words to 240000 words out of 479911 words
wa rayuwarka, shari'a ta kasa tsaya maka ya sanya ka zama haka. A labarinka da oga walid ya bani, da tun a lokacin da aka kashe yayanka, hukuma tayi abun da ta dace, da duk ba a zo wannan gaɓar ba.
Muna iya jure rashin makusantanmu ne, saboda ƙarfin imani, da tuna wanda ya bamu ne ya karɓi abunsa, amma idan wani ya zama sila, na rasa mutane masu muhimmanci a rayuwarmu, wannan imani na yarda da ƙaddara ya kan yi rawa a zukatanmu, mu kasa yadda da wanda ya bamu ne ya karɓa. Kai ba ɗan ta'adda bane ba mai babban suna, cin hanci a doka da shari'a su ne suka mayar da kai duk abun da ka zama a yau. Ba kowace zuciya ce zata jure tana kallon wanda ya cutar da ita yana rayuwa cikin kwanciyar hankali, alhalin ita an bar mata tabo mara warkewa ta jure ba.
Ban ce zan kai 'yar madara ba, amma na fuskanci giɓin da ka rasa nima akwai makamancin sa a rayuwata, da yake ci mini tuwo a ƙwarya yake damuna, ina ɓuya in yi kuka wasu lokutan na ji na tsani komai, kamar na kashe kaina na huta.
Jin labarinka ya sanya, na fuskanci me ka ke ji a zuciyarka. Har abada duk tsanani ba zan sake kuskuren kallonka a matsayin ɗan ta'adda ba, kuma zan tabattar wa da duniya haka, da izinin Allah. Sai an gyara fannin shari'a an murƙushe rashawa da bambancin hukunci tsakanin ɗan talaka da mai kuɗi, mai ƙarami da babban uban gida, idan ana son rage yawan 'yan ta'adda" tun da ta fara magana, yake kallonta, duk da tana yi tana zubar da hawaye, hakan ya tabattar masa da akwai wani pain a zuciyarta ita ma.
Ya juya ya cigaba da danna computer, ta kifa kanta tana goge hawaye. Ta kwantar da kanta a kan teburin, tana danna wayarta.
Ta ɗaga idonta ta kalli, yadda yake ta sarrafa computer, bata san me yake yi ba.
Yanzun ma hotonsa take ɗauka tana murmushi, kamar ba yanzu ta gama kuka ba.
"Master" yayi mata shiru.
Ta sake cewa "Maciji" tai maganar tana dariya.
"Viper, maciji mai hatsarin gaske, yau ka fito daga raminka, ka zo wurina, sarana ka zo yi ne?" Still bai kulata ba.
Ta tashi sosai ta ce "Da ni 'yar sugar da yar madara, wacce ta fi kyau ne? Kodayake na san ma ita zaka zaɓa, kafi sonta, amma dai kyakykyawa ce? Sannan fara ce ko baƙa? Doguwa ce ko gajeriya, ina son in ganta ka nuna mini hotonta, ko ba zaka bani haɗa ni da ita ba?". Sai da ya dafe goshinsa, Nabila bata gajiya da surutu, Jauhar akwai lokutan da ba ta kula shi da hira, idan ba ya cikin mood, shi wannan surutun nata ba zai bari su daidaita ba.
Ya fizge wayar hannunta, yana dubawa yana danna computer.
"Wai hacking ɗin wani zaka yi ne? Ni baka yi mini bayanin me ka ke yi ba, sonake ma mu yi magana, amma ka ƙi kulani, sai aiki kake yi kai kaɗai".
Ya tashi tsaye ya ce "Zan yi salla"
Ta nuna masa toilet, ya shiga yayi alwala, ya fito yayi sallar azahar, sanann ya kalleta ya ce "Tashi mu tafi"
Ta tashi tsaye ta ce "Ina?"
"In ƙarasa miki labarina, amma bisa sharaɗin da na gindaya miki da farko, babu gudu babu ja da baya, duk tsanani da wahala" ta jinjina masa kai.
Ya ɗauki facemask ɗin sa ya saka, ya sanya baƙin glass ɗin sa ya yi gaba.
Dama yau hijjabi mai niƙab ta sako, dan haka ta saka niƙabin, ta bishi.
Cikin ikon Allah, chamber babu kowa, duk lawyoyin sun tafi kotuna, sai massenger da mai gadi.
Suka fito, ta ce "To ina zamu je? Ba zai yiwu ka ƙarasa mini a nan ba?"
"I have to test you more, before i completely trust you" daga haka ya tarar musu napep, ya gaya masa in da za su je.
Suna tafe tana ta addu'a, Ubangiji Allah ya kare su, ya tsare duk in da za su je, Allah kar ya sanya ya cutar da ita, ko wani ya kama su.
Kasancewar rana ce sosai, layin shiru babu kowa, suka tsaya a ƙofar wani gate, ya ciro mukulli a aljihunsa ya saka ya buɗe, ya ce ta shiga. Ta shiga sannan shi ma ya shiga ya rufe ƙofa.
Ta tsaya tana kallon gidan, ya jingina da gate ɗin ya tafi tunani.
"Waye yake mini kokowa da ƙofa zai karya mini gate?"
"Ɓarawo ne ya zo sace matar gidan" tayi dariya ta ce "Da alama ɓarawon nan, bai san gidan wa ya zo ba ko? Ka bari mijina ya zo ya same ka" tayi maganar tana fitowa daga falon, fuskarta ɗauke da murmushi da tsohon cikinta.
"Wai da ke muka haɗa kuɗi muka sai rigar nan ne? Ki din ga ɗaukar mini kaya kina sawa"
Ta tura baki ta ce "Kai da kaya mallakar wuya ne, da kayan da mai kayan duk mallakin 'yar madara ne" tai maganar tana sakar masa murmushi.
Nabila ta ce "Ya naga ka tsaya, ina ne nan?".
Yayi firgita ya dawo daga tunanin da ya tafi.
Ya tunkari ƙofar falon, zuciyarsa na bugawa da sauri da sauri, ya saka mukulli ya buɗe.
Falo ne sosai, komai neat sai dai yayi ƙura sosai.
Ta tsaya tana ƙarewa falon kallo, taji wani abu ya kama zuciyarta.
"Viper, nan ne gidanka da 'yar madara tana ina? Kuma baka tsoron azo a kama mu?"
Bai ce mata komai ba yama wuce ya shiga bedroom ɗin, ya tsaya yana ƙarewa ɗakin kallo, komai ya din ga dawo masa, tamkar mai mafarki.
Tana tsaye, ya fito da wani riyo a hannunsa ya zo gabanta ya ajiye, yayi kneel down a gaban riyon, ya buɗe ya shiga fesawa kayan turaren florie. Ya din ga ɗago kayan, na jarirai ne, komai na haihuwa yana ciki intact, hatta zannuwa zamzam, bagaruwa, pad pampers komai akwai a ciki.
Duk wanda ya ɗago sai ya fesa masa turaren ya ajiye, muryarsa na rawa ya ce "Ɗaya daga cikin ƙamshi mafi soyuwa a wurin jauhar kenan".
Gaba ɗaya zuciyar Nabila ta tsinke, gabanta ya tsananta faɗuwa, ta ɗauki kayan, ita ma ta kai hancinta.
"Yanzu tana ina? Ina kuma jaririn naga kayansa na jariranta haryanzu?"
Ya ɗaga kai, yana kallon in da Nabila take zaune, ya ga jauhar kwance a wurin, cikin jini, tana ɗago masa hannun tana la'ila ha illa la, ya Allah.
Daga nan bai sake sanin in da kansa yake ba, sai ji yayi an watsa masa ruwa mai tsananin zafi, da ratsa fata a jikinsa.
Ya yinƙura zai tashi a gigice, amma yaji shi a ɗaɗɗaure, tamkar huhun goro.
Ya buɗe idanunsa da ƙyar cikin matsananciyar galabaita, amma ya kasa magana, haka zalika wuyansa ya kasa tsayawa.
"Idan ya watstsake, ku cigaba da tuhumarsa, har sai ya amsa laifin da bakinsa"
"Ok sir"
Suka cigaba da kwara masa ruwa mai zafi, amma sai dai ya zabura ya ƙanƙame jikinsa, amma babu baki.
Suka kwance shi daga mugun ɗaurin da suka yi masa, sai dai ana gama kwance shi, ya faɗo ƙasa jikinsa a sake.
Ɗaya daga cikin su ya ce "Haryanzu bai gama dawowa hayyacinsa ba, ku ƙyale shi tukuna"
Indabo sai kaiwa yake yi, yana komowa a falonsa,ya rasa me ma yakamata yayi, gefensa ga P.A ga kuma madaki a zaune.
"Wallahi kayi mini hauka madaki, ni ban san zaka yi mini sakarcin ba. Bambancinka da Aminu kenan, abun da aka saka shi yake yi, idan ka ga ya canza, to ya hango abun da ya fi naka ne, yanzu idan ya farka ya tona mana asiri ya kenan?"
P.A ya ce "Honorable, ka kwantar da hankalinka C.P yana hanyar zuwa nan, zamu ji mai zai ce mana"
Madaki ya ce "Honorable, da ka san hatsarin da yake tattare da yaron nan, da baka ce haka ba, mugun shu'umi ne. Hodar nan da guba na haɗata, kisa take yi har lahira, nayi mamaki da aka ce bai mutu ba, ba laifina bane ba, nayi iya ƙoƙarina".
CP ne yayi sallama, ya shigo falon, suka amsa tare da mayar da hankalinsu kansa, ya miƙa wa Indabo hannu suka gaisa. Cikin zaƙuwa indabo ya ce "Yaya ake ciki C.P?"
"Eh to, maganar gaskiya fa ya farfaɗo, kuma yana daf da watstsakewa a ko wane lokaci. Abun da muka yi guda ɗaya ne, a report ɗinmu, mun shigar da cewa ya sha kayan maye ne, ya bugu ya halakka matarsa".
Indabo yayi shiru sannan ya ce "Kai naji daɗi, amma kamar hanyar ba tayi ba sosai, idan ya buɗe bakinsa, zai iya faɗar gaskiya fa"
C.P ya ce ba zamu bari haka ta faru ba, lokacin da muka je gidan, mun goge duk wani abu da zai nuna hujjar wani ne ya shiga ya aikata laifin ba shi ba. Sannan mun ajiye miyagun ƙwayoyi har da hodar iblis, da sunan mun kama su a gidan. Idan za a fara sharia dole a samo ƙwararrun lauyoyi, kuma a yi wa alƙalin kyakykyawan gani, ni dai daga ɓangarena komai zai tafi dai-dai da yardar Allah. Tun da dama ya riga ya shahara kowa ya san ɗan daba ne"
Indabo ya yi ajiyar zuciya ya ce "Haka ne, na gode sosai da sosai C.P, zaka ga saƙo da yardar Allah, kuma zan cika alkawarin da nayi, muddin komai ya tafi cikin nasara, amma C.P ba zai yiwu ku yi masa wani abu, ku kashe shi ba kawai?"
Ya ce "No, muddin wani abu ya same shi, mu kuma zamu zama abun arziki, saboda sanarwar da kakinmu ya fitar mun tabattar da yana hannunmu cikin ƙoshin lafiya"
"Shikenan babu laifi, na gode sosai da sosai" ya sallami C.P ya tafi, ya ce "Aikin Naja'atu ya zo, P.A kira wo mini ita".
***
"Ka yi magana ka amsa laifinka, ka sauƙaƙa mana kai ma ka sauƙaƙawa kanka, idan ba haka ba mu zamu bi hanyoyin da zasu sama mana sauƙi"
Al'amin ya ɗago da kyar, saboda a cikin mayen da yake, suka yi dukan tsiya, tamkar sun samu jaki, jikinsa ya ƙara mutuwa, kowace gaɓa ta jikinsa ban da ciwo, babu abun da take yi.
"Ka amsa, ka ce ka sha kayan maye ka kashe matarka"
Gefen bakinsa duk jini, sun tuɓe shi, daga shi sai vest da gajeren wando, ya sake ɗaga idonsa, karo na farko yayi magana ya ce "Ina jauhar?"
"Ban sani ba, ni kake tambaya ina juahar? Bayan ka kasheta?" Tsaki yayi, ya taƙarƙare ya yinƙura ya tashi tsaye, suka saka kokara suka daki ƙafafuwansa, ya hantsila ya faɗi a wurin.
Duk abun nan da ake yi, da jibgar da yake ci, shi kawai mafarki yake yi, jira yake yi ya farka, dan ba ya son baccinsa ya cigaba da nisa, zai kai Jauhar asibiti da wuri.
A haka aka shafe kwanaki bakwai, amma Al'amin, yaƙi sakawa ransa cewa gaske ne ba mafarki ba.
Kwanaki bakwan nan, babu wanda ya zo in da yake, ba wai dan ba a samu masu zuwan ba, an hana kowa ganinsa.
Liti da walid, da sauran jama'arsa babu irin sintirin da ba su yi ba, amma aka hana su ganin sa.
Mutuwar jauhar, ta karaɗe kowane gidan jarida, unguwanni zuwa gidaje.
Abbu yayi kuka tamkar zai yi hauka, yayi dana sanin kasancewar sa mahaifin Al'amin.
Gidansu jauhar kuwa, ba su san sun yi rashi ba, sai da aka tabbatar da mutuwar jauhar, kowa kuka da zubar da hawaye.
Abbu yana kuka, ya sanya gwiwoyinsa a ƙasa, yana roƙon Baba ya yafe masa, da ya san Al'amin zai kashe masa 'ya, ba zai yarda a aura masa ita ba.
Baba ya girgiza kai ya ce "Alhaji Ibrahim, ni wallahi haryanzu ban ji na yadda Al'amin zai kashe mini 'ya. Akwai abun da ya faru ni ban yadda shi ya kashe mini jauhar ba"
Abbu ya ce "Wace hujja kake nema ko shaida bayan wannan? Ni na haifi Al'amin, kuma kowa ya san yana ta'amalli da miyagun ƙwayoyi"
Cikin kuka mama ta ce "Yaron nan ya cuce mu, bai yi mana adalci ba, haihuwar ɗa irin jauhar a gidan nan, daga kanta an gama, ba ayi ba, kuma ba za ayi ba"
Hafsa ta girgiza kai ta ce "Baba nima ina bayan maganarka, ƴan kwanakin nan, ina zuwa gidanta sosai da sosai, ina haɗuwa da shi, ita take bani labarin galabar da ta ci a kansa, da bani misalai daban-daban da aurenta. Son da yake nuna mata a gabana ba ya jin kunyata ko nauyina, suna matuƙar ƙaunar junansu. Har take gaya mini na tayata da addu'a, yanzu sigari ce kawai damuwarta da shi, har sai da na ji raina ya biya, da irin kalar soyayyar da suke yi wa junansu, dan haka gaskiya ban yadda mai zamani zai kashe jauhar ba, mutumin da idan zata fita baya nan, yake sawa ana bibiyarta dan kar wani ya kawo mata farmaki, mugwayen karnuka ya ajiye a layinsu, suna gadinta lokacin da yayi tafiya, duk dan kar a taɓa ta, gaskiya ban yadda ba".
Anty ma tana kuka ta ce "Babu abun da mai shaye-shaye ba zai iya aikatawa ba, dan haka ba abun mamaki bane dan an ce ya kasheta, Allah sarki jauhar wannan wane irin mummunan ƙarshe ki ka yi?"
A fusace Saifu yana kuka ya ce "Kar ki sake aibata mana gawar jauhar, wallahi ba ta yi mummunan ƙarshe ba, ta bi Allah, ta yi wa iyaye biyayya, ta yi biyayyar aure, idan ana nuna ɗan aljanna a duniya to jauhar ce, koma wane irin mutum ne shi, ai ku kuka yi bita da ƙullin da ta aure shi, kuma wallahi Allah ba zai bar kowane azzalumi ba, ita ta mutu ta huta". Haka aka din ga musayar yawu, har sai da Baba ya tsawatar tukuna.
Da taimakon Naja'atu Bunkure, suka haɗa kai da lawyoyin gwamnati, Indabo ya cika su da kuɗi, har da alƙalin kansa. Domin tsayawa tsayin daka wurin tattara shaidu da hujjoji.
Haka zalika ta fito ta bayyanawa duniya cewa, zata tsaya tsayin daka, har sai ta ga abun da ya ture wa buzu naɗi, sai an bi wa jauhar hakkinta, na kisan gilla da viper ya yi wa jauhar, mussaman dama ya riga yayi suna a harkar sha da fataucin miyagun ƙwayoyi da kuma harkar daba.
Ranar fara shari'a, haka aka zo da mai zamani a cikin sarƙa, yana ɗingisa ƙafa, saboda azabar da ya sha a hannun 'yan sanda, a kan ya amsa cewa shi ya kashe jauhar.
Aka fara gabatar da shari'a, wani lawyer ya gabatar da kansa a matsayin wanda zai kare Al'amin, bai taɓa ganinsa ba, sai ranar a cikin kotun.
Aka gabatar da charges ɗin da ake yi wa Al'amin.
Ɓangaren tawagar lauyoyin gwamanti, da su Naja bunkure, suka din ga gabatar da shaidun bogi, suka kawo ƙwayoyin da suka samu a gidan Al'amin, tare da kawo bayanan likita, na cewa dukanta aka yi har ta kai ga rasa ranta, da abun da yake cikinta.
Abun bai tsaya a nan ba, sai da aka kawo malam lawan, bayan shaƙa masa wasu muhimman kuɗaɗe, ya zo ya bayar da shaidar Al'amin ya saba dukan jauhar, idan ya je ya sha ya bugu, haka za su yi ta jiyo ihunta yana dukanta, a ranar ma sun ji kukanta, sai dai ba su yi zaton zai kasheta ba.
Muryar Liti ce ta dawo da Al'amin hayyacinsa, dan duk surutan da ake yi, bai san me ake cewa ba.
"Ƙarya kake yi dan ubanka, Viper ba ya dukan yar madara, ba ita ba kowace mace ma baya duka, a matsayin ku na maƙota idan yana dukanta, meyasa baku kai wa yan sanda ba, ƙarya kake maƙiyin Allah la'ananne, Viper ba zai taɓa cutar da matarsa ba, ba shi ya kasheta ba" jami'an tsaro suka yi waje da liti.
Sai dai wani irin ihu da Viper yayi, sai da wasu suka fara gudu, ya daki katakon gabansa da ƙafarsa ya ce "Ƙarya ne, jauhar tana nan a raye, gobe zata haihu, matata bata mutu ba"
Da ƙyar aka danne shi, Alƙali ya aika shi gidan prison, tare da ɗage shari'ar.
Haka ya cigaba da buge-buge, tamkar zai jefar da motar gidan yarin, sai da suka sumar da shi, sannan suka samu nutsuwa.
Tun daga wannan ihun, bai sake magana ba, ba cin abinci, sai dai zai yi salla kawai.
Har aka yi zama na biyu a kotu, bai ce uffan ba, duk wasu hujjoji Bunkure ce ta samar da su, lawyern gwamanti gabatarwa kawai yake yi.
Sai dai juyin duniya, ya yi magana, yaƙi yi.
Bunkure ta je gaban Al'amin ta tsaya ta ce "Amsa ɗaya kawai kotu take buƙata daga bakinka, kai ka kashe matarka jauhar?"
Ya ƙura mata rinannun idanunsa, ta din ga yi masa wani irin kallo, mai cike da rainin wayo.
Ya jinjina mata kai alamar eh.
A nan suka buƙaci a ƙarƙare shari'ar, ba tare da wata huɓɓasa ba, lawyern Al'amin, ya ce ya yarda da duk abubuwan da masu gabatar da ƙara suka gabatar. Daga haka aka sake ɗaga shari'ar zuwa wata guda.
Wata gudan da sai da ya shafe shekaru biyar a prison, ba a cigaba da shari'ar ba, ba kuma a sallame shi ba.
Kullum burinsa shi ne ya farka daga mafarkin nan da yake yi, shi dai ya san matarsa na raye, ba ya cin abinci baya iya bacci, ya koma tamkar mahaukaci.
Sai dai lokaci zuwa lokaci yana yi musu ihu, da kiran matarsa, ya kan kira sunan madaki da Indabo.
Lokaci lokaci, ya kan ga aiken abinci, hakan ya sanya ya ƙara sakankancewa jauhar ce ke yi masa aike, bai sake ganin wani yazo wurinsa ba, tsawon shekaru biyar ɗin nan.
Rana tsaka aka ce masa ya fita ya tafi gida an sallame shi.
A ƙofar prison ɗin ya tsaya, yana tuna lokacin da ta zo tafiya da shi, lokacin da aka rufe shi, aka ce an kama shi da cocaine.
Bai tsaya ko ina ba, sai unguwarsu, da ƙafa ya taka ya tafi, amma ya tarar da gate ɗin a rufe.
Sai yayi tunanin ta koma gida ne, dan haka sai ya fara tafiya gidansu, dan tabattar wa.
Gidansu ya fara zuwa, rahila da yaranta, gaba ɗaya suka dare, suka gudu ɗaki tana ihu ta ce "Ka fita ka kore shi, gashi can an sako shi, Allah wadaran yan siyasa, sun sako masifa da annoba, wanda bai san halacci ba".
Abbu ya fito ya kalli Al'amin, ya koma kamar wani mahaukaci, a gigice ya nufo Abbu ya ce "Abbu, ina jauhar? Ta haihu ne? Ina abun da ta haifa?"
Abbu ya ja da baya ya ce "Kar ka matso kusa da ni, Jauhar tana