Showing 27001 words to 30000 words out of 249515 words

Chapter 10 - Mayraah Hausa Novel Complete

20 Nov 2024

1503

fito birni suka yi kudi babu zato babu tsammani, to ko wacece uwarta a cikin matan parlon oho...."

Mami da sisters dinta suka bi Musharraf da kallo ganin yayi hanyar stairs without even noticing them a parlon, Mami tace "Musharraf" tsayawa yayi sai kuma ya juyo yana kallonsu kafin ya dawo cikin parlon ya gaishesu, duk tunanin Mami ya gano kayan lefen da aka rage ne ganin mood dinsa, har ce ma sisters dinta tayi kada wanda yayi masa maganar duk don a zauna lafiya, Mami tace "Ina ka shiga tun dazu?" Ya shafa kansa a hankali yace "Ina tare da frnds dina" Mami tace "Are you okay?" Ya daga kafada yace "Sure" Tace "Ban ga ka ci abinci ba?" Yace "Na ci" yana fadin haka ya juya ya wuce sama duk suka bi sa da kallo, definitely tasan akwai wani abu gaya mata ne bazai yi ba, Aunty Baby tace "To ko amaryar ta sanar masa babu wasu abubuwa a kayan ne tunda kince a gidansu aka hada kayan?" Aunty Fatima tace "By all odds ta gaya masa" Mami dai bata ce komai ba, don ma in da gaske yarinyar ta gaya masa ae abinda ta gani ta gaya masa. Musharraf na shiga dakinsa ya zauna gefen gado ya rike kansa da yayi masa nauyi, ya dade bai shiga irin wannan damuwar da ya shiga yau ba, he can't even think straight, duk yanda ya so saita tunaninsa hakan yaki yiwuwa, abubuwa iri iri ne ke masa yawo a kai, he is super confuse at this moment, me ke shirin faruwa haka, inda wani abu daban ne ya damesa haka da yayi sharing dinsa da Mami but not this, to me ma zai ce mata, how will she even react to this, tashi yayi ya nufi window ya tsaya staring into space babu ko kiftawa, yafi minti goma tsaye a haka kamar wanda ya tuna abu sai kuma ya juya ya nufi kofa da sauri ya fita daga dakin ya sauka downstairs, har sannan su Mami na parlon, bai kalli inda suke ba ya fita compound, gun security man din gidan ya nufa, Mutumin ya taso da sauri ganinsa, Musharraf yace "Ko da za a sake baka wani sako ka ba Mami or anybody in this house, ka amsa kawai ka ajiye ni ka bani, kaji me nace maka?" Security man din yace "An gama ranka shi dade" Juyawa Musharraf yayi walking slowly ya koma ciki, yana shiga Bedroom dinsa wayarsa na katsewa, ya karasa ya dauka yana duba me kiransa, miss call din Mayraah ya gani, ya dinga kallon screen din sai kuma ya zauna gefen gado yayi dialing numberta, yana fara ring ta daga, tayi masa sallama, ya amsa yace "How are you" Tace "Alhmdlh... yau ma kayi tafiya ne?" Gently yace "No" Shiru tayi na few seconds kafin tace "Are you okay?" Ya lumshe idonsa ya bude yace "Not really" Da damuwa tace "What's wrong?" Yace "I was so stressed today, i don't feel okay, i think i am getting sick" Tace "Kuma baka sha magani ba" Yayi kasa da murya yace "Give me prescription...." Tace "Ohk, i will send u via text message right away" Yace "Thank you" katse wayar tayi cikin few minutes sai ga text ya shigo wayarsa, ya shiga message din da ya ga ta rubuta kamar haka "No Drugs... Just stay relaxed, get enough rest.... I mean, sleep like a baby, and dream of me" Ya maimaita message din yayi sau uku, thinking if it's really coming from her or wani ne ya rubuta mata, ya dai yi murmushi, yayi mata reply kamar haka "Not when u are not by my side" Yana tura mata text din ya ajiye waya ya shiga bandaki feeling a bit relieved.... Ko da ya fito bandaki goge jikinsa yayi da towel ya shirya cikin pajamas dinsa, sannan ya kwanta saman gado ya dau wayarsa, ya ga tayi masa reply kamar haka "Let the count down begin from today...." Dialing numberta yayi har ya gama ringing bata daga ba, ya kuma kiranta still no response, and yasan she will neva respond.
Ranan asabar, Ammi na dakin da ke cikin parlor tare da sister dinta Aunty Mariya, makota ne yan shigowa ganin lefe cike a parlorn babu masaka tsinke, yan uwan Ammi na nesa da na kusa da matan Brothers din Abba sai aminiyar Ammi Hajiya Safiyya su ma duk suna parlon zaune suna monitoring kayan tunda duniya ta dawo babu gaskiya, tun jiya Ammi bata samu sun yi wata maganar kirki da er uwarta ba warce take aure a garin kaduna, sai dai ita Allah bai taɓa bata haihuwa ba, ita ma jiya wajen karfe sha biyu ta iso gidan, kuma bazata koma ba sai bayan biki, dama su hudu Hajja ta haifa, Ammi, sai marigayiya Rukayya warce ta haifi Badiyya, sai kaninsu namiji da Allah yayi ma rasuwa kusan 8 years back ko aure bai yi ba, sannan Aunty Mariya warce ita ce autarsu, Aunty Mariya dake kallon Ammi ta sauke ajiyar zuciya tace "Allah dai ya fishsheta don kam gaskiya ban ga mutunci tattare da dangin mijin nan da zata aura ba, abu babu arziki??" Ammi tace "Shi yasa abun ya dameni.... Ga Mayraah kin ga ba magana take ba, baza ta iya kwatan kanta ba, kar su je suyi ta cutar min da ita" Aunty Mariya tace "In sha Allah hakan ma bazai faru ba Ammi, komai zai zo da sauki, za mu yi ta taya ta da addu'a" Ammi tace "Hatta kayan fa ba iya su kenan ba, Ita Hajiya Safiyya ai ta sani don su suka hada kayan, sun cire abubuwa sosai daga cikin lefen nan" Aunty Mariya ta bude baki tace "Haba dai?" Ammi tace "Akwatunan ma da ta nuna min ya tura mata ta WhatsApp ai ba iyakarsa kenan ba, ke dai Allah ya rufa asiri ya sa gidan zamanta ne" Aunty Mariya tace "Ikon Allah, amma kamar babu dangin Mamarsa gun yan kawo kayan ko?" Ammi tace "To ban sani ba dai" Aunty Mariya tace "Ki kwantar da hankalinki Ammi, in sha Allahu gidan zaman Mayraah ne, babu me cutarta da izinin Allah tunda mijinta na sonta kuma yana da ilimi bazai bari a taka masa mata yana gani ba" Ammi tace "Allah ya sa hakan" Aunty Mariya tace "Kin sanar ma Mama Ladi bikin nan kuwa?" Ammi tace "Na gaya mata tun sanda aka sa rana, da har tace bazata iya zuwa ba kuma daga baya ta kirani wai ai bata san har da na Mahir ba tana nan zuwa" Aunty Mariya tace "Allah dai ya rufa mana asiri kar ta zo ta addabi jama'a ta wargaza mana taro" Ammi tace "Wallahi nima fargaban da nake kenan, da tace bazata zo da farko ba baki ga farin cikin da nayi ba wllh, ban son komai ya hadani da baiwar Allahn nan gaskiya, ni wllh da ta hakura mun yafe zuwanta" Aunty Mariya tace "Hajja za mu yi ma magana kawai su yi taronsu a gidanta don gaskiya abun bazai yi kyau ba idan baiwar Allahn nan ta sauka gidan nan" Ammi tace "To ki gaya ma Hajjan haka" Aunty Mariya tace "In sha Allahu, ai anjima Maheer zai je ya kawota ganin kaya zan mata magana idan ta zo, wai Badiyya fa? ba naji some weeks ago kince ta dawo gidan nan ba" Ammi tace "Uhm Badiyya taki zama wllh Mariya"
Har kusan karfe sha daya na safe Mayraah dake dakinta taki fita ko nan da corridor saboda mutane taga Musharraf bai kirata ba, ta saba during weekend yawanci before 9 yake kiranta, sai da ta ga karfe sha daya har da minti goma sannan tayi deciding ta kirasa, ta dau wayarta dake Caji tayi dialing numbersa, har ya katse bai daga ba, ta dai ci gaba da karatun da take don on Monday suna da test har biyu, tana zaune kan darduma bayan ta idar da sallan azahar Aunty Mariya ta shigo dakin da sallama, Mayraah ta mike ta linke darduman da tayi sallah tana amsa sallaman Aunty Mariya, Aunty Mariya tace "Ki sakko ki debi abinci Hajiyata" Mayraah ta marairaice tace "Aunty mutane sun yi yawa a gidan" Aunty Mariya tace "Babu wasu mutane duk sun tafi sai imu imu, ki fito ki zuba abinci" a hankali Mayraah tace "Toh" Aunty Mariya tace "Ko kuma bari in sa Sabira ta kawo maki kawai" Mayraah ta ɗan yi murmushi tace "Yauwa Aunty Nagode" Juyawa Aunty Mariya tayi ta fita daga dakin Mayraah ta xauna kasan carpet din dakin tana duban agogo dake nuna karfe daya da yan mintuna, har sannan kuma Dr Musharraf bai yi returning call dinta ba, or did he travel today? Ta kasa hakuri ta kara dauka wayar ta sake kiransa nan ma no response, or is he still sick, ajiye wayar tayi nan da nan taji she is disturbed da ta tuna yace mata baya jin dadi jiya, tana ta zaune har Sabira ta shigo mata da abincin ta ajiye mata ta fita, kasa cin abincin tayi, ta ci cokali biyu kawai ta rufe ta mayar gefe, ta mike ta kwanta kan gado, tana ta kwance bayan kusan minti talatin wayarta yayi vibrate ta dau wayar duk tunaninta shi ne sai ta ga Hamida ce, Ta daga bayan sun gaisa Hamida tace "Amarcy za mu zo ganin lefe da su Amina yanzu" a hankali Mayraah tace "Hamida baza ku bari gobe ba?" Hamida tace "Zaki fita ne?" Mayraah tace "Akwai mutane da yawa gidan ne, i won't be comfortable ko kun zo, ku bari idan an rugu zuwa gobe pls" Hamida tace "To Allah Ubangiji ya kai mu, ke har fa na amso anko na wajen tela, sai kin ga dinkin yayi kyau wllh in gaya maki, Amina ma sun amso nasu, saura lace din ne ba a karasa ba" Mayraah tace "Ohk shikenan" Hamida tace "In ji dai sun saka maki kayan fitar biki a akwati ko sai next week zai kawo maki?" Mayraah tace "Yace min an sa, ni kinsan ban ga kayan ba ma har yanzu" Hamida tayi dariya tace "Idan muka zo duk za mu gani tare" Mayraah tace "Allah ya sauwake, ni ce zan ga lefe da ku, ba wani lefen da zan gani" Hamida tayi dariya tace "Ke dai sai mun zo" Daga haka suka yi sallama, Mayraah ta ajiye wayar ta koma ta kwanta. Har tayi bacci ta tashi wajejen karfe uku da rabi Musharraf bai kirata ba, nan taji ta shiga damuwa sosai, bandaki ta shiga tayi wanka tayi alwala sannan ta fito, sai da tayi la'asar bayan lokaci yayi sannan ta sake kiransa, sai da ya kusa katsewa ya daga, Nan da nan ta hade rai kamar yana ganinta tace "Why are u not picking my calls since morning?" Yace "Ba na ce maki bana jin dadi jiya ba" cike da damuwa tace "Har yanzu? Did you go to the hospital?" Yace "Ban je ba" Tace "Toh wani magani ka sha?" Yace "Ban sha ba" Shiru tayi sai kuma tace "Baka da lafiya kuma baza ka sha magani ba?" A hankali yace "Babu maganin" Tace "Mami fa?" Yace "Tana gida" Da mamaki Mayraah tace "Kai kana ina?" Yace "Bana gidan" Ta ɗan yi shiru, sai kuma tace "Why are you answering that way?" Yace "How am i answering Mayraah?" Ta dan buda ido tace "Kana ina yanzu?" Yace "I need rest so i am not at home..." Tace "Nasani, cewa nayi kana ina?" Yace "Nan din da nake ma gida ne...." Tace "Ohk, now tell me how you are feeling" Yayi shiru, hakan yasa tace "Hello" Yace "Ina jin ki" Tace "Kayi shiru" Yace "I should tell u how i am feeling?" Tace "Eh" Yace "Ohk i am not feeling fine Mayraah" Da damuwa sosai tace "Don Allah ka gaya min how you are feeling, idan bazaka gaya min ba kuma ka aika wani da prescription ya siya maka magani ka sha" Yace "Wa zan aika?" Tace "Kai kadai ne a gidan wai?" Yace "Yeah" Tace "Amma me yasa zaka zauna gida ba kowa bayan baka da lafiya?" A hankali yace "U said i should get enough rest Dear, shi yasa na zo nan" Mayraah tace "Ni bance kaje inda babu kowa ba" Yace "Ohk ai ban sani ba" Tace "To yanxu ka ci abinci?" Yace "Wa zai bani?" Ta zaro ido tace "Since morning?" Shiru yayi bai ce komai ba, tace "Can i go out and get u some food now?" Bayan shirun few seconds yace "Ohk, with the drug" Mayraah tace "In sha Allah" Daga haka ta katse wayar. Mikewa Mayraah tayi ta ciro kayanta a press, within few minutes ta shirya ta saka Hijab dinta har kasa sannan ta saka Nikab, ta dau handbag dinta ta duba ciki to make sure her Atm card is inside, ta zura wayarta a ciki sannan ta fita daga dakin, tsaye tayi bakin kofa tana tunanin inda zata ce ma Ammi zata je, gashi ita in dai zata yi ma Ammi karya sai ta kamata don bata iya karyan ba ma, A hankali take tafiya zuwa Bedroom din Ammi gabanta na faduwa, tayi sallama a bakin kofar sai da aka amsa mata sannan ta shiga, Ammi da Aunty Mariya kadai ne a dakin suka daga kai suna kallonta, da mamaki Ammi tace "Ina za ki?" Mayraah tayi karfin halin karasawa kusa da su gabanta na ci gaba da faduwa sosai, ta durkusa kasa tace "Ammi zan je in siyo abu in dawo yanzu" Ammi tace "Me zaki je ki siyo?" Da kyar tace "Wani material na karatun mu" Ammi tace "Karya kike yi Mayraah, gaya min inda za ki dai" Mayraah ta marairaice tana tunanin inda zata ce mata zata, Aunty Mariya tace "Ko dai wajen kawayenki zaki?" Nan da nan idea ya zo ma Mayraah ta sunkuyar da kai tace "Ammi kiyi hakuri, wajen Hamida zan je" Ammi tace "Shine sai kin min karya tukun, kuma tun safe baki ce zaki gidansu Hamida ba sai bayan la'asar kina ganin gari na neman lullubewa da hadari, bayan kuma kinsan unguwansu da nisa sosai daga nan, ki bari kawai gobe idan Allah ya kai mu" Mayraah ta daga kai tana kallon Ammi with pleading eyes tace "Nayi alkawarin bazan dade ba Ammi" Aunty Mariya tace "Kawai ki bar ta Ammi tunda tace bazata dade ba, kilan shirye shiryensu za su yi, kawai dai kar ta wuce karfe biyar a gidan" Ammi tace "Wani karfe biyar, Allah sa zuwa biyar din ta isa gidan, can fa gaban unguwa uku ne, kuma ai ita Hamidan ya kamata ta zo, ba wai ta bi ta gidansu ba" Aunty Mariya tace "Ke dai kiyi hakuri ki barta Ammi, nasan dai Mayraah ba fita take ba idan ba kwanan nan ta canza ba, tunda tace sharp sharp zata je ta dawo kawai ta tafi, Allah ya tsare" Ammi dai tayi shiru, can tace "Amma me yasa baza ki bari gobe ba Mayraah?" Mayraah tace "Ina son inje yau ne don akwai reading material dina da zan amso wajenta ran monday muna da test kuma ban yi karatu ba" Ammi tace "Shikenan, Allah ya tsare, amma kar ki jima Mayraah kinga yamma tayi ga hadari, kina gama abinda zaki yi ki kira Maheer yaje ya dauko ki, kar ki wani ce zaki shigo adaidaita sahu" Mayraah tace "To Ammi nagode" Ammi tace "Kina da cash dai ko?" Mayraah tace "Eh" Ammi tace "Toh sai kin dawo" Mikewa tayi ta ma Aunty Mariya sallama sannan ta nufi kofa duk suka bi ta da kallo.




07087865788 WhatsApp only


*Kiya kiya a zo ayi abinda ya kamata kar aji ni tsit kamar an aiki bawa garinsu, free pages har guda sha biyar nayi maku fa, to a zo a sallameni kar in koma gefe inyi shiru* 🙄
[6/2, 4:59 PM] Khaleesat Haiydar💖: 💖💖 *MAYRAAH*💖💖




By _Khaleesat Haiydar_📚✍🏻




8.....

Mayraah na fita gida ta fara tunanin abincin da zata siya ma Musharraf, sannan a ina ma zata samu abincin har ta siya, tayi deciding ta fara fita daga area dinsu tukunna don ba lallai ta samu eatry da zata siya masa abinci me kyau a nan ba, after leaving the area ta samu wani babban eatry ta siya masa abincin with bottle water da drink sannan ta fito, tana fitowa wayarta dake jakarta ya fara vibrate, ta ciro wayan tana duba me kiranta taga Ya Maheer ne, ta ɗan yi jim, yanzu fa kilan tana dagawa idan ta gaya masa abinda ta gaya ma su Ammi sai ya iya cewa ta koma gida, sarai ta san halinsa, taki daga kiran har ya katse, zata mayar da wayar cikin jaka sai gashi ya sake kira, bayan ta ɗan yi nazarin abinda zata ce masa sai ta daga ta kai kunne tace "Yayana...." Yace "Ina kike haka nake jin noises din vehicle haka?" Mayraah ta ɗan buda ido tace "Gidansu Hamida zan je yaya..." Yace "Hamida? Zaki je ko zaki dawo?" Ta ɗan turo baki tace "Zan je dai" Yace "Are you serious?? Since morning baki je gidansu Hamida ba sai yanzu that everywhere is busy? Almost five o clock now" Mayraah ta marairaice tace "Yaya ba dadewa fa zan yi ba" Yace "I see, yanzu kina ina?" Ta ɗan kalli inda take, sai tayi saurin cewa "Nima dai ban sani ba ina cikin adaidaita sahu amma nasan mun kusa, ina amso reading material dina zan juyo, we are having test on Monday" Yace "Ohk, amma baki ga hadari ba?" Ta kalli sama tace "Ba sosai ba, abinda ya ma fara washewa" Yace "Toh Allah ya tsare" Tace "Ameen, Me zaka gaya min ka kirani?" Yace "Wanted telling u kiyi min stirred fried spagh....." Mayraah tayi murmushi tace "Ai dama nasan girki zaka ce in maka, baka taɓa kirana sai in kana son in ma girki, but don't worry yayana idan na dawo zan maka in sha Allah" Yace "Take care, and do not stay long" Tace "In sha Allah" Daga haka ya katse wayarsa, ta ɗan yi jigum kamar me nazari, to ma dai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login