Showing 228001 words to 231000 words out of 249515 words
ya zaga ya shiga driver seat, hawaye kawai Mayraah take tana kallon Badiyyah dake kuka kamar ranta zai fita, Maheer ya ja motarsa ya bar kofar gidan.
[8/4, 8:39 PM] Khaleesat Haiydar💖: Sai kusan karfe hudu Mayraah suka iso kano daga kaduna, Mayraah ta kalli Maheer tace "Alhamdulillah for journey mercies" Kai kawai ya gyada mata, tace "What should I cook for u idan muka isa gida, kaga kai baka ci abinci ba, ni kuma ka siya min a Zaria" Ya ɗan kalleta yace "Baki gaji ba?" Er dariya tayi tace "Bayan ba ni ce ke driving din ba, i slept all through fa" Ba don yayi missing girkinta ba da bazai bari tayi girkin ba but he is craving her cooking, jin yayi shiru yana driving dinsa tace "Ko baka so?" Yace "Gani nake za kiyi stressing kanki after this long journey, kamata yayi muna komawa gida yanzu kiyi wanka kiyi sallan Asr ki kwanta ki huta" Mayraah ta ɗan yi murmushi bata ce masa komai ba, ya juya ya kalleta jin tayi shiru, sai kuma ya maida dubansa kan titi yace "Ko ba haka ba Mimi?" Tayi wani murmushin tace "Naga kamar u are avoiding me this days, baka son muna magana da yawa, i don't know! u are just being unusual, we weren't like this before" Maheer ya buda ido sosai, babu abinda ya fado masa rai sai lokacin da ita ma ta dinga kokarin avoiding dinsa 3 months back after finding out they are not blood, yasan she is talking about kafin su san matsayinsu ne, yana murmushi yace "Avoiding my lil sis? Kema kin san hakan bazai yiwu ba..." Tace "Then if u are not avoiding me kana da damuwa ne da baka son ka gaya min?" Ya ɗan kalleta yayi murmushi yace "You caught me" Tace "I definitely know there is something, yaya na fa san ka nasan halin ka, i know there is something bothering you, amma shine kake boye min whereas before baka boye min komai" A hankali yace "I will tell u Lil sis, but yanzu ina bukatar in huta na gaji" Tace "Tohm shikenan, and again yaya me yasa baza ka dau transfer ba kai ma ka koma Abuja, naga kuna da Branch a can ai" Maheer yace "Kin manta daga Abujan na nemi transfer na dawo kano, it will be a bit hard to get another transfer back to Abuja" A hankali tace "Try yaya, we will miss u idan muka tafi ba tare da kai ba, kaga shi Ya Usman dama yafi aiki a Abuja and kaduna, nasan he is going back to Abuja too" Maheer yayi murmushi yace "I will try" The rest of the journey was silent har suka iso gida, bayan yayi parking tace "Idan nayi sallah zan maka girkin" Yace "Toh Nagode Mimi" Tayi murmushi ta bude motar ta sauka ta nufi cikin gidan. Mayraah na shiga parlon Ammi ta tadda Mama Ladi kwance ta lullube da bargo, Mayraah ta karasa kusa da ita ta duka tana kallonta da mamaki tace "Baki da lafiya ne Mama?" Mama Ladi tayi kasa da murya tace "Ae tun asuba da na tashi naji kafafuwana sun kasa daukata nasan da matsala, to ilai kuwa gashi" Mayraah tace "Ayya, to Allah ya sauwake, kin sha magani?" Mama Ladi tace "Wa zai bani er nan? Ai yanda kika gan ni a nan tun dazu a haka nake" Mayraah tace "To zuwa anjima sai in fita in amso maki maganin idan nayi sallah" Daga haka Mayraah ta mike ta karasa dakin Ammi, kaya ta sameta tana ta hadawa a akwatuna, Ammi tace "Ya hanya Mimi?" Mayraah tace "Alhamdulillah, ina yini Ammi" Ammi tace "Lafiya lau, ina yayan naki?" Mayraah tace "Kamar ya shiga gida" Ammi tace "Toh kiyi sallah ga abinci can na maku ki duba kitchen" Mayraah tace "Toh Ammi" Ta juya ta nufi kofa Ammi tace "Ki fito da kayanki gaba daya daga press din dakin ki ajiye kan gado, zan jera maki a akwati, amma sai kin ci abinci in kinyi sallah" Mayraah tace "Toh Ammi" Daga haka ta fita daga dakin, tana komawa dakinta tayi wanka sannan ta dauro alwala, bayan ta idar da sallah ta sauka downstairs ta shiga kitchen, duba abinda Ammi ta girka masu tayi, sai kuma ta fita ta koma ta dauko wayarta ta dawo parlon ta zauna tayi dialing number Maheer, yana fara ring Maheer dake kwance ya mike zaune ya daga yace "Mimi" Tace "Yaya me kake son ka ci?" Yace "Koma me kika girka zan ci" Tace "Ohk" Daga haka ta katse wayar, Haseenah dake kitchen din dake Chalet zata zubo masa abinci duk da tasan ba ci zai yi ba, tana jin wayar da yayi da Mayraah ta ɗan yi wani murmushi ta mayar da abincinta cikin warmer ta fito daga kitchen din ta wuce daki, dama girkin da Ammin tayi ne taje kitchen ta debo ba wai ita ta girka ba, Mayraah na kitchen tana ma Maheer girkin da tasan ya fi so wajen karfe biyar da wani abu aka bude kofar kitchen din ta juya, suna hada ido tace "Ina yini Yaya" Yace "Lafiya lau" Karasawa cikin kitchen din yayi yace "Babu abincin ne?" Tace "Aa akwai, Ya Maheer nake ma girki" Ya gyada kai ya dau plate zai debi abinci tace "Ko zaka ci wannan da nake yi" Yace "Aa akwai me shi ae" Tayi dariya tace "Ai zan iya tsam maka kaɗan a ciki" Bai sake kallonta ba ya debi abincin da zai diba ya fita daga kitchen, Ammi na shigowa kitchen zata hada ma Mama Ladi shayi tace "Mimi baki son abincin ne?" Mayraah ta kalleta tace "Aa Ammi yaya nake girka ma favorite dinsa" Ammi tace "Tohh ai shikenan nawa bai yi dadi ba kenan" Dariya Mayraah tayi tace "Aa ko ɗanɗanawa bai yi ba fa Ammi, kawai favorite dinsa nake masa saboda nasan ya gaji" Murmushi kawai Ammi tayi, ta hada shayin da ya shigo da ita ta fita daga kitchen din, Mayraah na gamawa ta fito parlor ta dau wayarta tana kallon Usman dake zaune kan kujera yana kallo a laptop, Maheer ta kira ta sanar masa ta gama, a hankali yace "Ki kawo min nan Chalet Mimi" Ta ɗan buda ido tace "Chalet kuma? Aa yaya kawai ka daure ka zo ka amsa" Yace "Na gaji ne" Ta ɗan yi shiru, sai kuma yace "Ki bar shi kitchen din idan na shigo zan dauka" Tace "Bari in kawo maka yaya" Daga haka ta ajiye wayar ta nufi kitchen, Usman ya bi ta da kallo, daukan abincin tayi ta dawo parlor tace "Yaya kace baza ka ci ba ko?" Yace "Eh" Kofa ta nufa ta fita zuwa Chalet, tana knocking kofar yace "Come in" Ta bude ta shiga sannan ta karasa inda yake kwance, tun da Haseenah ta ji yayi waya da Mayraah ta kawo masa abinci ta sake fitowa Parlon ta zauna, Mayraah bata yarda ta kalli direction dinta ba balle har hakan yasa sai ta gaisheta, she pretends bata ma san tana wajen ba a zaune, tana ajiye masa abincin tace "Ga abincin yaya" Yace "Thank you Mimi" Tayi murmushi ta mike ta nufi kofa ta fita, Haseenah ta bi ta da ido. Ko da Mayraah ta koma sama ta tarar Ammi na ta hada mata kayanta cikin set din akwatunanta, Mayraah tace "Ammi ki bari in karasa" Ammi tace "Aa bar shi ai na kusa gamawa kije kiyi alwala kawai, it's almost Magrib" Bandaki Mayraah ta shiga don yin alwala.... Da daddare Ammi na dakinta tare da Mayraah, Mama Ladi kuma na kwance har sannan cikin bargo Maheer ya shigo parlon, ya zauna ya gaida Mama Ladi ta gyada masa kai kawai, yace "Mama ba lafiya ne?" Mama Ladi tace "Ai tunda na tashi da asuba na ji jikina na rawa nasan da magana, to ilai ga ni nan rai a hannun Allah" Maheer yace "Subhanallah, to kin sha magani?" Mama Ladi tace "Mera ta samo min wani gantalalle na hadiya dazu, amma ba sauki" Maheer yace "Zuwa karfe sha daya kafin kiyi bacci sai ki kara sha, in sha Allah za ki ji sauki" Daga haka ya mike ya karasa Bedroom din Ammi yayi sallama, sai da ta amsa ya shiga, Ammi tace "Ya gajiyan hanya?" Ya zauna yace "Alhamdulillah, ina wuni" tace "Lafiya lau" Wayarsa ya mika mata yace "Aunty Mariya zata maki magana" Sai da gaban Ammi ya fadi, tun barin su kano da safe ta kashe wayarta har yanzu ta ki kunnawa, dazu ma sai wayar Usman ta amsa ta kira Abba, Ammi ta amshi wayar, yace "Ki kirata" Daga haka ya mike ya fita daga dakin, Ammi tayi dialing number Aunty Mariya yana fara ring Aunty Mariya ta daga, Ammi tayi mata sallama, Aunty Mariya ta amsa ta gaisheta sai kuma ta ja wani dogon numfashi tace "Ammi Hajja fa tana gidana yanzu haka" shiru Ammi tayi don tasan kwanan zancen dama, Aunty Mariya tace "Yanzu fisabilillahi ina take son Badiyyah ta tafi? Ta dai san ba zaman kanmu muke ba balle ace lallai mu rike Badiyyah a wannan halin da take ciki, wata dayan da tayi gidanki ma abun a jinjina ma Alhaji ne wllhi, Sanda muke kokarin saita Badiyyah ba duk ita ke tabarbara komai ba take goyon bayanta akan duk wasu mugayen halayyan da take, saboda me kuma yanzu har da ita a gudun Badiyyah? Ai in kowa ya guji Badiyyah to banda Hajja tunda ita ce root din duk abinda ya samu Badiyyah" Ammi ta sauke ajiyar zuciya tace "Ban san me zance ba Mariya, bana son magana shi yasa ma kika ji wayata a kashe, i am tired wllhi" Aunty Mariya tace "To kuwa wallahi Baaba Yahanasu bazata yarda a makala mata Badiyyah ba tana fama da kanta tunda ga Hajjan har ta bar gidan ta dawo nan, ina me tabbatar maki in dai Baaba Yahanasu ce gobe zata kamo hannun Badiyyah ta kawo ta gidan nan ba wai karamin aikinta bane, kuma Ammi kece babba ke ya kamata ki gaya ma Hajja bata da wani Hujjan gudun Badiyyah don ita ce silar duk abinda ya sameta, wallahi ita ce sila, da ta bar mu mun mata tarbiyan da ya kamata da duk haka bai faru ba amma tayi kane kane kan lamarin Badiyyah tana ga kamar ba sonta muke ba, ta dauki kalman maraici ta hure kunnen yarinyar da shi yarinya tayi ta iskancin da ta ga dama babu me ce mata don me, kuma yanzu tace bata da makiyiya sama da Badiyyah, ai bazai yiwu bane, a gabanta ya kamata Badiyyah tayi jinya ba a wani waje ba" Ammi tace "Rufa min asiri, kema zaki iya gaya mata hakan Mariya ba kince tana gidanki ba, sai ki buda mata komai babu boye boye" Aunty Mariya tace "Wai kin ma ji maganganun da ta dinga yi ne ma kuwa, cewa tayi fa mun tura Badiyyah gidan Yahanasu ta karasa ta, idan bamu yi hankali ba wallahi Nijar zata shiga gun er uwarta, wai Bilkisu ce er uwarta yau, ni gaskiya ina ga zan kira kawu Rabi'u in sanar masa duk abinda ke faruwa, kawai Hajja tayi hakuri ta rungumi kaddararsu ita da Badiyyah ta dauketa su koma kaduna su ci gaba da zamansu har Allah ya sauketa" Ammi tace "Kirasa ki sanar masa...." Aunty Mariya tayi mata sallama ta katse wayarta. Washegari Mayraah ta shirya da wuri zata shiga school ta amso statement of result dinta, flight din nasu na karfe hudun yamma ne, so bata san how long zata gama clearance before collecting the result statement ba shi yasa ma ta shirya da wuri, tana shiga parlon Ammi ta tadda Usman zaune yana kallon Mama Ladi dake hadiyan paracetamol, ta karasa ta duka gaban Mama Ladi tace "Ina kwana Mama?" Mama Ladi tace "Ke ban cika son magana ba fa" Mayraah tace "To Allah ya sauwake" Kallon Usman dake kallonta tayi tace "Ina kwana?" Yace "Ina za ki je?" Tace "Zan shiga School inyi clearance ne sai in amshi statement of result, ko zaka yi dropping dina yaya?" Ya mike yace "Mu je" Tace "Toh bari in gaya ma Ammi" Daga haka ta shiga dakin Ammi shi kuma ya fita daga parlon, Usman na dropping dinta a school din yace "Ki kirani idan kin gama" Tace "Toh" Daga haka ya bar school din, sai kusan karfe sha biyu Mayraah ta amshi result din nata sannan ta kirasa, bai wani bata lokaci ba ya shigo school din ya dauketa suka koma gida. Maheer na zaune parlor wajen karfe biyu yana jiran Ammi da ta kirasa sai ga ta ta sauko downstairs, ta zauna tana kallonsa tace "Maheer ya zan yi da wancan tsohuwar?" Maheer ya ɗan yi dariya yace "Wai har yanzu tana kwancen ne?" Ammi tace "Wallahi sai kara lullubewa take fa" Maheer yace "Kar ki damu ku dai ku shirya nan da karfe uku sai in kai ku airport din nasan yanda zan yi da ita" Ammi tace "Toh shikenan" Daga haka ta mike ta wuce sama, karfe biyu da rabi Maheer ya shigo bangaren Ammi, har sannan Mama Ladi na kwance cikin bargo, Maheer na kallonta yace "Sannu Mama" Ta gyada masa kai kawai, yace "Ko za mu koma can bangaren ne Kinga za su tafi airport ne yanzu" Mama Ladi ta ki kulasa, yace "In kuma kin fi son nan din to...." A mugun fusace tace "Kai dalla rabu da ni inji da cutar dake damuna, ko don ba kai ne ke jin jiki ba?" Maheer yace "Shine nace ma Ammi da naga ta dage a tafi Abuja dake nace mata baxa ki iya ba kina jin jiki, zaman jirgi sai me lafiya..." Mama Ladi na kallonsa tace "Ni muka yi haka da kai Mashir?" Maheer yace "Toh ai basa barin mara lafiya ya hau jirgi shine dama matsalar" Mama Ladi ta mike zaune tace "Ciwon kan ne ma kawai ya saka ni gaba amma ni kaina nasan jikina da sauki bana jin komai wallahi" Maheer yace "Sai dai in zan tafi mu je tare, tun da kin ga sati daya ake dauka kafin mutum ya samu kujeran jirgi don ba kullum jirgin ke tashi ba, wannan ma sai da Abba yayi sati biyu yana bi sannan ya samar masu kujeran" Mama Ladi ta koma ta kwanta, Mikewa yayi ya shiga dakin Ammi dake sauraronsu, yayi murmushi yana kallon Ammi yace "Bari in fita da akwatunan" Ammi dai bata ce komai ba tana mamakin Mama Ladi yanzu kawai sai ta kara kwasan jiki ta bi su Abuja, ina laifin ma ta bari sai bayan kwana biyu haka da komawarsu in ma zuwa zata yi, ai sai abun ya zama rashin hankali kuma, tun bikin Maheer fa take gidan, har Maheer ya kai akwatunan mota Mama Ladi na kwance ta maida bargon gefe daya, Ammi ta fito daga dakinta don karfe ukun ya kusa ta zauna tana kallon Mama Ladi tace "Toh Mama za mu tafi, idan ya so in Maheer zai je sai ku taho tare tunda kujera biyu kawai Abbansu ya samu...." Mama Ladi tace "Ai shikenan, banda ma jikina ya matsa min ai tun a shekaranjiyar nayi niyyar tafiya karaye, to kana naka ne Allah na nasa, ban yi zaton zan kai har yau a gidan nan ba" Ammi tace "Haka ne kam, sai kun zo din dai, bari in je kar mu rasa jirgin" Mama Ladi bata kara tankata ba har ta fita daga Parlon, Maheer ya kai su airport din tare da Mayraah, bayan sun shiga departure ya koma gida.... Karfe biyar suka sauka airport din Abuja, sabon Driver da Abba ya dauka ne yaje airport din daukosu. Ammi bata taɓa zaton irin gidan da Abba ya siya ba kenan a Abuja, she never expect it, mansion ne na gani na fada a anguwa me kyau, kai kana ganin gidan kasan account yayi bala'in girgiza, ga masu gadi biyu da ya saka a gidan da driver daya, har da me watering flowers da sharan babban compound din, abu daya ne babu a gidan wato swimming pool cause it won't be of any use to them, tsabar farin ciki sai da Ammi tayi hawaye bayan ta shiga part dinta it was something she never saw coming, Bedroom din Mayraah yayi biyun wanda ta bari a kano, bandakin ma was very big, dakuna sun wadata sosai a gidan, tun daga sama har downstairs, wajen karfe shidda Abba ya shigo gidan don yana Abujan, Ammi na zaune Bedroom dinta ta ma kasa yin komai sai kallon Mayraah dake jera mata kayanta a press take, Abba na shigowa dakin yana kallon Ammi yace "Me ya samu wayarki ne" cikin sanyin murya Ammi tace "Ban cire a flight mode ba" Mayraah ta gaida Abba, Abba yace "Kema na kira baki daga ba" Mayraah tace "Yana cikin handbag dina" Abba yace "Ohk" Mayraah na murmushi tace "Abba the house is so beautiful Allah ya sanya alkhairi, Allah ya kara maka budi da daukaka, Allah ya sa kafi haka" Abba ya dafa kanta yana murmushi yace "Ameen my Baby gal, hope u are prepared for ur interview tomorrow?" A hankali Mayraah ta gyada masa kai, yace "To maa sha Allah, i know u can do it, congratulations in advance daughter" Tana murmushi ta fita ta bar masu dakin, nan da nan hawaye ya cika idonta, tana komawa nata dakin ta fashe da kuka sosai, she knows she can never pay them in anyway, bata ta taɓa iya biyan duk abinda suka mata a rayuwar nan ba, even if she will how is she going to repay all this? with what will she repay? because of the genuine love they have for her they still have to relocate back to Abuja for the sake of her new work, Bayan Mayraah ta fita dakin Abba ya kalli Ammi da ta kasa dago kanta yace "Gidan ya maki ko a canza yan mata?"
[8/5, 9:15 PM] Khaleesat Haiydar💖: Washegari karfe bakwai na safe Mayraah ta tashi ta sauka downstairs zuwa kitchen