Showing 237001 words to 240000 words out of 249515 words
kallesa yace "Incase what?" Dr Khalil na murmushi yace "Incase Watarana mana" Mayraah na komawa dakinta ta dau wayarta taga miss calls din Maheer, murmushi tayi har zata kirasa sai kuma ta tuna za su yi magana da Ya Usman kamar yanda yace mata dazu, ta ajiye wayar with the intention of calling him back idan ta dawo, sannan ta sauka downstairs ko hijab dinta bata cire ba ta nufi dakin da ta gansa ciki daxu.
[8/7, 8:39 PM] Khaleesat Haiydar💖: Mayraah na isa kofar dakin tayi knocking, after a while ya bude kofar, shi in dai aka masa knocking baya bada izinin shigowa sai dai ya tafi da kansa ya bude kofar don bai fiye son ana shigo masa daki ba, she is already used to that, tana ganin ya bude kofar ta bi gefensa ta shiga ciki ya bi ta da kallo sai kuma ya kulle kofar ya karasa ciki yace "But i said later in the night" Mayraah ta zaro ido tace "To yanzu yaushe ne yaya? Everywhere is dark already" Zaunawa yayi yana ci gaba da abinda yake yi a laptop yace "Ai ba ayi isha ba" Ta turo baki tace "Yaya ni dai i am eager in ji maganar me zaka min, is it about my dressing dazu?" Ya kalleta yace "Ai Ammi tace dressing din ya maki kyau" Murmushi tayi tace "In dai shine ni dai kayi hakuri, nace maka bazan kara ba" Yace "Ba shi bane" Tayi shiru tana kallonsa, ya kashe laptop din ya ajiye yace "I just want to know what ur next plan is.... 2 years back kinyi saukan Al-qur'ani, this year kin yu graduating from university, immediately after graduation kin samu aiki, so what do u have in mind next?" Ta ɗan yi murmushi ta sunkuyar da kai tace "Kamar me fa yaya?" Yace "Ko iyakar burinki kenan a rayuwa?" Ta daga kai a hankali ta kallesa, she wish zai gane yanda ta zama desperate ta hadu da nata relatives din ko da guda daya ne, bata son ta zama an ingrate shi yasa take kauda tunanin nan ko da yaushe a ranta bata basa mafaka ba balle ya dameta, amma God knows in this few months har cikin zuciyarta tana son sanin ko da mutum daya ne a jininta, sauke idonta tayi bata ce masa komai ba, a hankali yace "Kinyi shiru" Tayi gathering courage tace "Duk wani abun Alkhairi will always be among my wish everyday Yaya, ba ni kadai ba kowa ma ina masa fatan abun alkhairi ya same sa kullum" Yace "Mayraah" Ta daga kai ta kallesa yace "So in ur wish there is nothing like marriage?" Ta ɗan buda ido, sai kuma tayi murmushi ta sunkuyar da kanta tace "Ai lokaci ne yaya, idan Allah ya kawo lokacin za ayi" Yace "Tell me the truth, is there anything between u and that Dr? I mean Dr Khalil" Mayraah ta zaro ido tace "Not at all wallahi, shi da yake da mata da yaransa biyu" Usman yace "Ohk ba a auren me mata?" Tayi dariya tace "Aa nima ban sani ba" Yace "Baza ki iya auren mai mata ba kenan?" Ta sunkuyar da kai tace "Ni dai ba ruwana" Yace "Abokina me mata ya ga hotonki yace yana so yanzu baza ki iya aurensa ba kenan?" Ta daga kai ta kallesa, sai kuma ta turo baki bata ce komai ba, yace "Am serious" Shiru tayi tana kallon sa, ya sauke idonsa yace "Wasa nake bai da mata, he is single, a Barrister too, are u interested? maganar da za mu yi kenan dama" Nan da nan jikinta yayi sanyi don Musharraf ne ya fado mata, Shi dai Usman kallonta kawai yake examining her reaction at the same time, bayan few seconds tace "Yaya i don't think i will love again...." Hawaye ya cika idonta ta fara gogewa da sauri, shi dai yayi shiru yana kallonta, can yace "Mayraah" ta daga kai ta kallesa tana share idonta, yace "Why won't u love again" Ta fashe da kuka tace "I don't want to remember the pass, ko ma waye zai aureni yanzu dole sae ya fara sanin ko ni wacece, after that no parent will want their blood to marry me" Yana kallonta a hankali yace "Har Ammi da Abba?" Daga kai tayi ta kallesa as if trying to apprehend what he meant by so saying, Bai bata wannan space din ba yayi saurin cewa "Forget that pass u are talking about and concentrate on the future Mayraah" Ita dai bata ce komai ba sae kallonsa take, yace "So i will want you to give this guy a chance" Nan ma dai bata ce komai ba, yace "Banda kula kowa kuma" Tayi murmushin karfin hali bata dai ce komai ba, yace "Promise me that" Ta kallesa kamar yasan abinda ke running a mind dinta yace "Kin dai san bazan yi abinda zai cuceki ba ko?" Ta sauke idonta, yace "So now make that promise baza ki kula wasu ba" Ta gyada masa kai tace "In sha Allah" Yace "You can leave" Mikewa tayi ta nufi kofa ta fita wasu hawayen na taruwa idonta ta koma dakinta. Wajen karfe tara bayan tayi wanka ta kira Maheer, Haseenah dake parlon ta mike jin wayarsa dake ajiye kan kujera na ring, shi kuma yana kitchen yana hada shayi, kallon screen din wayar ta dinga yi taga an sa Mimi with love emoji, ta dinga kallon wayar babu kyaftawa har ya fito daga kitchen, ta juya ta shige daki, ko kallon inda ta bi bai yi ba ya dau wayarsa bayan yayi picking Mayraah ta gaishesa, ya zauna yace "Ina kika shiga?" Tace "Kai dai zan tambaya, bayan tun dazu nake ta kiran wayarka" Yayi murmushi yace "Wayar na silent kika kira dazu, ya kike?" Tace "Alhamdulillah, ya aiki" Yace "Cool, kin je interview din yau?" Tace "Na je" Yace "No issues?" Kai ta gyada masa kamar yana ganinta, sai kuma tace "Ka fara processing transfer din naka yaya?" Yace "Not yet" ta ɗan hade rai tace "Do it soon pls, ko baka missing dinmu" Yace "I will try Mimi, ina missing dinku mana, ina Ammi?" Tace "She is in her room, Mama Ladi ta tafi ne?" Er dariya yayi yace "Jiya na kai ta har karayen wai bazata iya zaman motar haya ba" Mayraah tayi murmushi tace "Ayya, yanzu yaya idan ina son magana da sis Badiyyah ta ina zan sameta?" Maheer yace "I don't really know" Tace "I tried calling her lines severally amma duk a kashe" Yace "May be ta kashe wayar ne" Mayraah tayi shiru, shi ma haka, bayan few seconds tace "Pls try and request for the transfer kaji yaya" Yace "I will do so starting from tomorrow in sha Allah Mimi" Tana murmushi tace "Yauwa yayana, i want to go to bed now" a hankali yace "Alright Dear, sleep tight" Tace "Bye" Daga haka ya katse wayar, ya ajiye ya jinginar da kansa da kujera ya lumshe ido, tun da suka koma Abuja sai dai ya sha tea ko coffee, idan ya fita kuma ya biya restaurant ya ci abinci, kana ganinsa kasan he is not himself, a da yayi niyyar ko zai nemi transfer din sai zuwa nan da wata biyu ko uku, amma yanzu kam yaji bazai iya ba, damuwa yayi masa yawa, ganin daga shi sai Haseenah na kara saka masa damuwar nan, don haka dole ma ya nemi transfer din nan ko ta yaya ne ya koma wajen family dinsa soon. Ranan Sunday da yamma Mayraah ta gama shiryawa ta fito daga dakinta zuwa parlon Ammi, Ammi dake zaune tana kallon TV ta kalleta tace "Ko dai mu bari zuwa gobe ko da daddare ne in kin dawo aiki mu je daughter?" Mayraah ta zauna gefenta tace "Aa Ammi mu je yau pls kin ga fa na riga nayi girkin, nasan goben a gajiye zan dawo" Ammi tace "Toh shikenan, mu je kawai..." Mikewa tayi ta shiga daki ta dauko gyalenta da jaka, sannan suka sauko downstairs, sai da Mayraah ta fara shiga kitchen ta dau warmer din tuwo da miyar ganyen da tayi ta kai mota, driver na compound yana jiran fitowarsu, Mayraah ta sanar masa inda zai kai su sannan ta bude ma Ammi back seat ta jira har ta karaso ta shiga ta kulle motar sannan ta tafi front seat ta zauna, tafiyar kusan minti talatin da biyar suka yi suka iso gidan, Drivern yayi parking bakin gate, Mayraah ta sauka ta dauko warmers din biyu, Ammi ma ta sauko daga motar ta sanar masa jiransu zai yi sannan suka shiga cikin gidan, Karime ce ta bude masu kofar parlon tana ganin Mayraah ta rungumeta cike da farin cikin ganinta tace "Sannunku da zuwa... Ku shigo" Mayraah na murmushi suka shiga parlon da Ammi, ta ajiye warmers din hannunta, bayan Karime sun gaisa da Ammi ta mike tace "Bari in yi ma Hajiyar magana tana daki" Ba a dau lokaci ba sai ga ta tare da Ummi, shigowa parlon Ummi tayi da fara'arta tana masu sannu da zuwa, Mayraah ta koma kusa da inda Ummi ta zauna ta gaisheta, Ummi ta amsa da fara'a tace "Kwana biyu ko leko mu kin ki yi Ilham, shine ranan Khalil ke ce min ai mamanki sun dawo Abujan ma gaba daya, ina jin ko kwana biyar ba ayi ba da ya gaya min haka" Mayraah na murmushi tace "Ai naje kano nayi sati biyu ne shi yasa Ummi" Ummi tace "Maa sha Allah, Maman taki ce wannan ko" Ammi dai murmushi kawai take, Mayraah ta gyada kai tace "Ita ce" Suka kara gaisawa da Ammi, Ammi ta mata godiyan rikon Mayraah da tayi, Ummi tace "Kai haba babu komai, ai yi ma kai ne" Mayraah tace "Inna na daki?" Ummi tace "Tana ciki, ku shiga ku gaisa" Mayraah tace "Nayi mata girki ne" Ummi tace "Ai ko kin kyauta wallahi, Allah maki albarka" Mayraah ta mike tana kallon Ammi tace "Ammi mu je ku gaisa da Inna" Mikewa Ammi tayi ta bi bayan Mayraah zuwa dakin inna, karime ta dau warmers din ta bi su a baya zata kai dakin, Sosai inna tayi farin cikin ganin Mayraah bayan sun gaisa da Ammi tace "Kai amma wannan er taki er albarka ce warce bata mance alkhairi, na dade ban ga yarinya me hankali kamar ta ba, ki ji fa har da girki ta min abun sha'awa, yaushe ma na samu haka a gidan nan, doya ce fa yanka hudu suka hadani da shi dazu kamar a fursin wallahi" Ammi dai murmushi kawai take tana kallon Inna, su da suka yi niyyar barin gidan da wuri sai da inna ta ja Ammi da zance, su ne har kusan karfe shidda a gidan, Ummi ma tuni ta shigo dakin Inna ta zauna suna hiran gaba daya, magana daya biyu sai innan ta Gwale Ummi, Ummi dai ko bin ta kanta bata yi, a haka dai Ammi ta samu suka lallaba suka bar gidan inna na cewa tana nan zuwa zata sa Khalil ya kai ta, bayan sun kama hanya Mayraah na kallon Ammi tace "Kamar Mama Ladi ko Ammi" Dariya Ammi tayi tace "Wannan ai ta so ta fi mama Ladi, gaskiya Ummin na hakuri da ita..." Mayraah tace "Ai kam Ummi ba ruwanta bata biyeta" Washegari ko da Mayraah taje aiki su Khalil basu dawo Lagos ba wai sai Tuesday, hankalinta kwance tayi aikinta a asibitin babu wanda ya takura ta, a ranta ta dinga fatan da ma kar su dawo da MD din nan, a rikesa a branch dinsu na can Lagos din ace an masa transfer. Da daddare Mayraah na shirin kwanciya kiran Maheer ya shigo wayarta, dauka tayi ta zauna gefen gado sannan ta daga, bayan sun gaisa, a hankali tace "Was it successful yaya?" Yace "Nop Mimi, wai sai nan da wata uku" Lokaci daya jikin Mayraah yayi sanyi, for kusan 4 days yake ta kokarin ganin ya samu transfer din zuwa Abuja, har Abba sai da yayi intervening a issue din, duk hope dinta yau idan ya kirata zai ce an maidosa Abuja, jin bata ce komai ba yayi kasa da murya yace "Kin yi shiru" a hankali tace "To me zan ce?" Yayi murmushi yace "Ki ce min congratulations" Ta buda ido tace "Wai anyi Transferring dinka?" Yace "Yes Mimi" Ba karamin farin ciki Mayraah tayi ba, har sallan dare sai da tayi a yan kwanakin nan duk don ya samu transfer din sai gashi kuma ya samu, yace "But Abba ne fa yasan yanda ya bi aka yi Transferring dina, it won't have been possible idan ba don shi ba" Mayraah tace "Maa sha Allah, congratulations yayana i am so happy with this news, yanzu yaushe zaka yi resuming aiki a nan?" Yace "Sai monday next week, but in sha Allah zuwa friday zan dawo Abujan" Tace "Toh Allah ya kai mu yayana" Tana son tambayarsa ko da Haseenahn za su taho amma dai tayi shiru bata yi tambayar ba, yace "Bari in kira Ammi in gaya mata, i told u first before her" Mayraah na murmushi tace "To yaya, bye" Maheer na kiran Ammi bayan ita ma tayi farin ciki tace "To yanzu ya za kayi da yarinyar nan?" Yace "Kawai ta tafi gidansu" Ammi tace "Aa babu wannan zancen Maheer, babu yanda muka iya haka zaka taho da ita nan, the chalet here is almost 2 times bigger than the one u are inside now, hakuri za kayi ku taho tare" Maheer yayi shiru don bai yi expecting Ammi zata ce haka ba, Cikin kwantar da murya tace "I understand you dear, amma kayi hakuri na ɗan lokaci ne, bazan taɓa goyon bayan ka ci gaba da zama da Haseenah ba yanzun ma kai ma kasan akwai dalili ne" Shi dai bai ce komai ba, don gaba daya mood dinsa har ya baci. Ranan Wednesday Mayraah na shiga asibiti da safe bayan ta dubo wata patient a wani ward tana dawowa reception sai ga Dr Khalil ya shigo, tana hango wanda suka shigo tare kawai tayi saurin juya masu baya pretending bata gansu ba, da haka ta nufi wani ward da sauri ta shige ciki kamar zata je dubo wani patient, duk MD na kallonta, nurse din wajen ta gaishesu da ladabi, har MD din ya fara tafiya toward step sai kuma ya dawo ya cire glasses dinsa yana kallon nurse din da kyau yace "Anyi cleaning office dina yau?" Nurse din ta mike da ladabi tace "Yes sir, ai kullum sai cleaner din ya yi cleaning office din sannan ya maida ma secretary spare key... He does that every day ko baka nan" Yace "Fine, i need my library shelf carefully dusted and cleaned to my satisfaction today, Da muka shigo ai kamar ba ke kadai bace a nan" Ta gyada kai da sauri tace "Eh ni da nurse Ilham ce, amma ta shiga ward 3 zata dubo patient" Yace "Good, look for her ki gaya mata abinda nace don ita zata yi aikin ba wani ba, or you just tell her to meet me in my office immediately" Nurse din tace "Okay sir" shi dai Dr Khalil na tsaye yana kallon MD da mamaki, Nurse din ta tafi da sauri inda Mayraah ta shiga don kai mata sakon MD, Dr Khalil ya bi bayan MD da ya nufi step yace "Dama nurse ta taɓa maka gyaran office Dr? We have more than enough cleaners in here" MD yace "Za a fara yau, kai baka ga duk ka sa yarinyar nan ta gama raina mu ba, wato tafi karfin ta tsaya ta gaishemu shine zata shige ward, to zata yi gyaran every nook and cranny na office dina yau kuwa, next time ma idan tayi repeating haka abinda zan yi mata kenan, silly girl" murmushi kawai Dr Khalil yake yana biye da shi a baya. Mayraah ta dinga kallon nurse din da ta kawo mata sakon MD tace "In same sa a office kuma? Allura fa zan ma patient din nan idan ta gama cin abinci" Nurse din tace "I will handle that, kawai ki tafi ya ce yana jiran ki" Mayraah ta fita daga ward din ta taɓe baki ta wuce sama, jiya da baya nan asibitin so conducive wallahi. Knocking din office din nasa tayi tana hade rai, har sai da ta kwankwasa sau uku sannan taji yace a shigo, ta bude kofar ta shiga, gaban table dinsa ta tafi ta tsaya bata bari ta kallesa ba tace "Good morning sir" Bai amsa gaisuwar ba ya nuna mata direction da shelf din Libraryn nasa yake yace "Take out all those textbooks and articles, dust and clean, finish with that first...." Mayraah ta dinga kallonsa taki cewa komai, ya daga kai ya kalleta yace "What are you still waiting for?" Juyawa tayi ta nufi shelf din da ya nuna mata fuskarta a daure, ya bi ta da ido, tana isa nan ta fara sauke textbooks din daya bayan daya tana ajiyesu kasa, sai da ta sauke many of the textbooks ta fara jin kamar dust a hancinta, still dai ta ci gaba da fiddo su, tana ajiye na hannunta taji tari ya taho mata, da sauri ta rufe hancinta da hannunta, kamar tayi triggering tarin sbda ƙuran dake hannun nata, ta durkusa nan kasa da sauri within few seconds she began gasping for breath, bai san sanda ya karasa inda take ba ya duka gabanta ya dago kanta da sauri yana kallonta yace "Are you Asthmatic?" Sai kuma ya janyeta daga wajen textbooks din ya zaunar da ita kan office chair dinsa trying to help her with first aid, amma numfashinta sai kokarin daukewa yake, lkci daya duk ya daburce a wajen kamar bai taɓa zama likita ba a rayuwarsa, gashi dai bayan pills da injections har inhaler akwai a show glass din magunguna dake office din but he was just lost ya kasa yi mata komai, dai dai nan Dr Balogun ya shigo office din, da sauri ya nufosu lkci daya