Showing 171001 words to 174000 words out of 249515 words

Chapter 58 - Mayraah Hausa Novel Complete

20 Nov 2024

1549

murmushi tace "Kar ka damu, don Allah ina zan samu sim card in siya?" Yace "Ai ina siyarwa" Ta ɗan yi shiru don tasan su suke ma layin register da kansu, can dai tace "Toh bani daya" bayan ya cire kudin ya mayar mata da Atm card dinga sannan ya dauko sabon layi ya mika mata ta amsa tace "Nawa ne?" Yace "Aa ki bar sa, ai ba tsada" tace "Toh nagode, sannan don Allah a can garin ana samun gado ko da ba babba ba?" Yace "Gado? Ko dai katifa irin ta yan makaranta?" Ta gyada kai tace "Shi" yace "Gaskiya can zai yi tsada, kyau a siya daga nan a kai can din kawai" Mayraah tace "Toh, zan tafi yanzu, ka bani numberka anjima idan na saka layin zan kira ka inji yanda ake ciki" Yace "Toh Hajiya" Ya rubuta mata number ta amsa sannan tayi masa sallama ta bar shagon, sai da ta fara biyawa wani karamin eatry ta siya snack sannan ta koma hotel din da take. Mayraah na gama cin meatpie din ta dau magungunanta ta tasha sannan ta kwanta tayi bacci. Bata tashi ba sai can kusan yamma, dauko wayarta tayi ta saka sabon sim card din taga layin ya hau, sai dab da magrib ta kira me pos din, bayan sun gaisa yace mata an biya kudin gidan, tace "To shikenan nagode" Yace "Ko gobe kika ce zaki tare in dai da abubuwan da zaki zuba a gidan ba matsala don sabon waje ne ba wani kwaskwarima da za ayi masa" Mayraah tace "Toh ba damuwa, goben zan zo in sha Allah" yace "To Allah ya kai mu"
Maheer na zaune parlon Ammi da ya siyo ma abinci bayan magrib yana jiran yaga ta fara ci, har da magunguna ya kawo mata don dazu da safe tace masa bata jin dadi, a maganin ya hado mata har da na cin abinci da kuma wanda zai sa ta dinga samun isasshen bacci don kana ganinta kasan bata bacci, ga wani rama da tayi tun ma tana gidan Hajja, ganin har an kira isha Ammi bata da alamar fara cin abincin gabanta yayi kasa da murya yace "Ammi ki ci ko kadan ne ki sha magani pls, nasan fa tun safe babu wani abu da kika ci" Ammi ta kallesa cikin sanyin murya tace "Amma Maheer ina kake tunanin Mayraah zata har kwana uku yau, ba fa wanda ta sani Maheer, ba kuma inda ta sani, ko dai gidan radio da social media za a bada cigiyarta?" Maheer ya sauke boyayyen ajiyar zuciya ya kwantar da murya yace "Duk inda ma take tana cikin koshin lafiya in sha Allah Ammi, kuma addu'a kawai za mu ci gaba da yi har Allah ya karkato da hankalinta ta dawo gida, babu abinda zai sameta da izinin Allah, Mayraah ba ɓata tayi ba balle mu yi cigiyarta she just decided to leave, yanzu ko anyi cigiyar ma kamar muna kara tona ma kan mu asiri ne, ya mace ce ita ana saka cigiyar kowa da perspective din da zai kalli abun, gwara kawai mu ci gaba da addu'a kawai Ammi" Ammi ta share hawayen da ya sakko idonta bata ce masa komai ba, bude kofar parlon aka yi Mama Ladi ta shigo da plate cike da taliya da cup din shayi a hannun ta, Maheer ya daga kai ya kalleta yana nuna mata nata abincin da ya siya mata yace "Baza ki ci wannan din ba Mama?" Mama Ladi tace "Inji wa?? Ai sai can cikin dare idan na farka in sha Allah, taliya ce leda daya na dafa don tun da na sauka wallahi ban samu na ci komai ba, sai wani gantalallen biredi da ruwan shayi da na samu a kitchen Usuman ya bari" Daga haka ta zauna ta fara cin taliyar, Maheer ya ji dadin dawowan Mama Ladi don gidan babu kowa sai Ammi sai Usman da yake kwana gidan shi ma saboda Ammin, amma da safe kuma yake fita aiki, har Maheer ya fara deciding kiran Mama Ladin sai ga ta kamar an jefota dazu da rana lokacin ya dawo duba Ammi.... Maheer yayi nisa tunanin da yake sai kawai ganin Mama Ladi yayi a gabansa tayi kasa da murya tace "Ka sameni a palo Mashir" Maheer ya bi ta da kallo sannan ya kalli Ammi da har sannan taki cin abincin gabanta, ya mike ya bi bayan Mama Ladi suka sauka downstairs, kujera Mama Ladi ta nuna masa tace "Zauna ina zuwa" Ya zauna ya ga ta nufi kitchen sai ga ta ta fito da abun kwasan shara ta ajiye masa tana kallonsa, da mamaki yace "Wannan fa?" Mama Ladi ta wani kyabe baki tana murmushi tace "To a karkashin gadon uwarka na gani an makala sa yana ta reto, kasan ina sauka dazu ko zaunawa ban yi ba na fara kwaleman dakin duk na kwalkwale ko ina, to dai ga tsiyar da na gani karkashin gadon Ammi tana ta rayuwa kai in gaya maka Mashir, ni dai da naga duk a birkice take damuwa ya mata yawa ko nuna mata abun ban yi ba ma har yanzu, kuma wallahi dama ance surkarta ta ajiye asiri a dakinta...." Maheer dake ta kallonta ya katseta yace "Wa yace haka?" Mama Ladi tayi kasa da murya tace "Gun bawan Allahn da naje neman taimako mana, kai baka ga abubuwan dake ta faruwa babu kan gado ba, ai mutum bai ga ta zama ba Mashir, har auren nan da Ubanka yayi wallahi an gaya min...." Maheer ya girgiza kai yace "Wajen boka kenan kike zuwa" Mama Ladi ta zauna kan kujera a gigice tace "Auzubillahi, don Allah ka rufa min asiri kar ka sa ni a bakin duniya Mashir, wani irin boka kuma? Ashe haka kake ban sani ba?" Maheer yace "Yanzu ke har yanzu baki hakura da zuwa gun mutanen nan da ke cinye maki kudi suna maki karya ba Mama? babu fa wanda ya isa ya maka abu sai Allahn da ya halicceka, in mutum ya sa wannan a rai to babu ta yanda za ayi masa mugun abu, ke kawai baki da aiki sai zuwa gun makaryatan banza marasu tsoron Allah" Mama Ladi ta saki baki tana kallonsa, a fusace tace "Kar ka sake gaya min maganar banza Mashir, kai wawa ne baka san komai ba baka san me duniya ke ciki ba, kuma laifina ne don wannan zancen ma ba da kai ya kamata in yi ba don kai ba sa'ar magana ta bace, tsinanniyar matar nan taka dai ita ta saka wannan mugun abu a dakin Ammi, shi yasa duk abubuwa suka cakude haka" Maheer ya kai hannu zai dau layan ta janye parkern da sauri tace "Rufa mana asiri, ni nasan inda zan kai sa, ni kaina bazan bari hannuna ya taɓa ba" Can dai yace "To meye manufar layan da aka sa kasan gadon kenan?" Mama Ladi tayi kasa da murya tace "A rabata da Mera ta tsaneta taji bata sonta kwata kwata, sannan kuma a tarwatsa mata gidanta ta dawo bora, kaga kuma yanzu tsakani da Allah wanne ne bai faru ba? Rabata da Meran ko tarwatsa gidan? Wai ma ina Mamuda don na tambayi Ammin tace min bata sani ba dazu" Maheer ya sauke ajiyar zuciya yace "Ya koma can wani gidan da ya gina da matar" Mama Ladi ta gwalo ido ta daura hannu a ka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, wani gidan da ya gina? Amma ga dukkan alama matar ma matsiyaciya ce shaidaniya, zuwa kawai tayi ta mallakesa ta rabasa da Ammin, kai shegu dai sun yi yawa wallahi a duniya, yanzu ka gaya ma Ammin suna wani gida da katuwar matar?" a hankali yace "Ban gaya mata ba" a hankali Mama Ladi tace "To ka ja bakinka kayi shiru kar hankalinta ya sake tashi don naga ɓatan Mera ya gigitata gaskiya, kar ka kuskura ka gaya mata" Wayarta ta kunce a ɗan kyalle da ta cusa cikin hulan kanta ta mika masa tace "Kira min Mamudan" Maheer ya dinga kallonta, a fusace tace "Kira min shi mana" Amsan wayar yayi, yayi mata dialing number Abba sannan ya mika mata, ta amsa ta kai kunne, yana fara ring Abba ya daga, da karfi tace "Mama Ladi ce Mamuda..." Gaisheta Abba yayi, tace "Don Allah ina son ganinka yau na shigo garin" Yace "Toh sannu da zuwa Mama, zuwa gobe kenan idan Allah ya kai mu" Mama Ladi ta girgiza kai da sauri tace "Wani gobe? A yau nake son ganin ka Mamuda" Yace "Toh zan sa Maheer ya kawo ki inda nake" Mama Ladi tace "O'o ba ruwana gaskiya kawai ka shigo mota ka taho ina nan gidanka yanzu haka gani ni kadai zaune a parlor ba kowa" Abba ya dan yi shiru, sai kuma yace "To gani nan zuwa" tace "Yauwa ina jiranka" Daga haka ta katse wayar tana kallon Maheer tace "Ai kaga ni ba er banza bace da zan je in samesa a wani sabon gida bayan yayi watsin ruwan tsarki da 'ya ta" Shi dai Maheer bai ce komai ba. Maheer na barin gidan da minti arba'in Abba ya shigo wajen karfe tara da rabi kenan, Har sannan Mama Ladi na zaune parlon tana jiransa bayan ta gama cin abincin da Maheer ya kawo mata daxu, Abba na shigowa ya gaisheta da ladabi sannan ya zauna kan kujera yace "Ya hanya Mama?" A hankali Mama Ladi tace "Kai yanzu Mamuda so kake ranan gobe kiyama ka tashi da shanyayyen ɓarin jiki? So kake duk mu tafi aljanna kai kana wuta? Auren da har yanzu bamu gama na'am da shi ba a zuciyarmu shine har ka fara rashin adalci a cikinsa Mamuda? Ita Ammin ka gama cin moriyarta ta zama bola kenan yanzu kake nufi?" Sai kuma ta fashe da kuka tace "Ko me Ammi zata maka a duniya bata cancanci walakanci daga gareka ba Mamuda, balle baiwar Allahn bata taɓa maka komai ba sai biyayya da girmamaka tun kana talakan ka, sai yanzu don kaga ka rasa yanda zaka yi da kudi sai ka canza hali ka kasa hakuri da ɗan kuskuren da ta maka? Ko ka mance ɗan adam ajizi ne? Ammi ta taɓa maka wani gagarumin laifi duk zaman ku tare tsakaninka da Allah?" Abba yace "Yanzu tace maki na mata wani abu ne Mama?" A fusace Mama Ladi tace "Kayi mata mana, sai ta fada sannan za a san ka mata? don me za ka dau bazawarar da ka aura sama ta ka, ka kai ta sabon gida ku tare a can Ita kuma ku bar ta a nan?" Abba yace "Ai ni ban san tana gidan nan ba ma" Mama Ladi tace "Kai dai kaji tsoron Allah kaji tsoron kamun Allah Mamuda, wallahi kaji tsoron Allah ina gaya maka" Abba yace "Yanzu tun da nasan tana gidan duk ranan kwananta zan shigo gidan in kwana a bangarena" Mama Ladi tayi kasa da murya tace "Haba Mamuda, don Allah kayi hakuri.... wallahi ni kaina nasan Ammi tayi kuskure nasan bata kyauta ba amma duk sharrin shaidan ne, kai shaida ne mutuniyar kirki ce Ammi, babu sa wa babu hanawa, kar ka yi mata mummunan hukunci saboda wnn ɗan kadɗarar ya fada mata, wallahi kaddararta ce wannan, amma kai kanka kasan duk bamu fi ta son Mera ba, kayi hakuri ka dubi halin da take ciki ka ja ta jiki ka maida komai ba komai ba har Allah ya dawo mana da gantalalliyar yarinyar nan da ta tafi inda bamu sani ba dama kuma ta saba shiga duniya da er matsala ta faru, Wallahi Ammi na cikin mawuyancin hali yanzu a kan batar yarinyar nan, da wanne kake so ta ji, ga kishiya ka dankara mata Mamuda?" Abba dai yayi shiru bai ce komai ba, Cikin lallami Mama Ladi tace "Nasan ka da hakuri da kauda kai Mamuda, kayi hakuri yanzu ka tafi sama ka duba halin da take ciki sai ka ga ta samu nutsuwa a ranta, babu bawan da ke wuce kaddararsa wllhi, babu tsimi fa babu dubara sai wannan abu ya faru Mamuda" Abba yace "Shikenan Mama, zan duba ta" Mama Ladi tace "Yauwa ko kai fa ɗan albarka, ai haka ake son babba ya gaya ma yaro magana ya ji, ni wallahi ka gama min komai wannan mutunta ni da kake yi" Mama Ladi tace "Yanzu sai ka tashi ka tafi sama ka dubata, ni kuma zan je kitchen in nemi abinda zan ci kar yunwa ta kasheni" Mikewa Abba yayi ya wuce sama zuwa bangaren Ammi.
[7/17, 10:07 PM] Khaleesat Haiydar💖: Washegari da safe Mayraah ta sake komawa gun me pos din a tasha, kamar jiya ma yau Nose mask ta saka don gaba daya a tsorace take da Abujan gani take kawai zata yi jamming wanda ta sani, wajen karfe goma da rabi ta isa shagon nasa, bayan sun gaisa yace "To yanzu zan bar yaron shagona ya jire min shagon sai mu kama hanyar sulejan ki ga gidan Hajiya...." Mayraah tace "Toh shikenan, nagode" Mayraah bata yi tunanin haka Sulejan ke da tafiya daga cikin Abuja ba, don har bayan minti arba'in bata ga sun isa ba, though is not as if she cares about the distance tunda babu abinda ma zata dinga shigowa garin Abujan tayi, at last dai suka iso garin Suleja ya tare masu adaidaita sahu suka tafi anguwan da yace mata gidan yake, anguwar dai ba laifi amma duk yawancin gidajen unguwan na average class ne har ma da lower class, suna isa gidan da aka kama mata bayan ya shiga da ita ko ina tare da wani agent sun nuna mata suka fito compound din gidan yace "Toh ya kika ga gidan ya maki kuwa Hajiya?" Mayraah da bata da choice kawai tace "Eh yayi" Agent din ya bata makullin gidan da reciept din payment ta saka a handbag dinta, bayan ya tafi Mutumin da ya kawota yace "Kin ga ai anguwan bata da hayaniya ko? Ga shi kuma a cike yake da jama'a" Mayraah tace "Haka ne, yayi kam" Yace "Kuma gidan kin ga sabo ne dal bai da matsala" Mayraah tace "Eh duk na gani, amma kasan abinda zai faru? Don Allah idan baza ka damu ba ina son in baka list din wasu abubuwa ka taimaka min ko a kasuwan garin nan ne ka siyo min, gobe nake son zan dawo gidan gaba daya" Yace "Toh babu matsala kamar me da me kenan kike bukata" Nan Mayraah ta zayyane masa duk abubuwan da zai siyo mata a kasuwa na bukatar gida har da kayan abinci, ta mika masa Atm card dinta yace "Aa Hajiya, da dai kawai ki min transfer" Tace "Kar ka damu, bana iya transfer ne shi yasa" Yace "Toh amma fa mantuwa gareni, kyau kawai muje kasuwan tare Hajiya" Ta ɗan yi shiru tana nazari, sai kuma tace "Toh shkkn mu tafi" Tricycle suka samu zuwa kasuwan. kafin yamma Mayraah ta siyi duk wasu abubuwan da tasan zata bukata a gidan tare da mutumin da yace mata sunansa Aminu, har gas da few kitchen utensils sai da ta siya, da labule da aka dinka masu sharp sharp a kasuwar suka siya da karafen labulen, wajen karfe biyar da rabi tana kallon Aminu bayan ya gama saka mata labulen karshe tace "Gaskiya Nagode sosai, Allah ya saka da alkhairi" Yace "Ameen Hajiya, amma yanzu abinda zai faru ya kamata ki ɗan shiga makotanki ku gaisa su sanki ki ce masu ke daliba ce, yau kika dawo unguwan, kinsan yanzu yan sa ido sun yi yawa a duniyar kar su yi zaton ko zaman kanki kike a nan bayan basu san karatu ya kawo ki garin ba" Mayraah dai tayi shiru tana kallonsa, a hankali tace "Haka ne, zan shiga in sha Allah amma sai gobe idan na dawo nan din gaba daya, yanzu na gaji ina son mu koma Abuja ne in hutu sannan in harhada kayana na can" Yace "To ba laifi Hajiya, in dai da wani abu da kike bukata ko na aike koma na menene kawai ki buga wayata, in kin dawo nan din gaba daya har iyayena zan hada ki da su da matana duk da dai gaskiya anguwansu da nisa daga wannan anguwan, sai a dinga zumunci" Mayraah na murmushi tace "Toh shkkn, in na dawo din duk sanda kake da lokaci ko kuma in ka shigo garin sai ka hadani da su" Yace "In sha Allahu kuwa, Allah kuma ya baki sa'an abinda kika zo nema" A hankali Mayraah tace "Ameen nagode" Sai kusan shidda da wani abu suka shiga garin Abuja, Mayraah tayi tayi da shi ya tsaya ta ciri kudi a wajen wani me pos ta basa yace mata wllhi wanda ta basa ma ya isa saboda Allah yayi mata, taji dadin hakan har ranta, she really appreciate him, ta samu adaidaita sahu da ya maida ta hotel don duk ta gaji. The next day Mayraah tayi check out daga hotel din ko kwanakin da aka biya mata bai cika ba ta koma sulejan wajen karfe sha daya na safe, zaunawa tayi a gefen gadon dakin tana bin ko ina da kallo, tun barin ta gida sai yau kawai taji tunanin yayyinta ya cika zuciyarta, ita kanta tasan tana kewansu, this made her feel so down tun safe take jin ranta babu dadi, lokaci daya ta ba kanta courage ta shiga kitchen ta dafa Indomie wanda har ta mance rabon da ta ci Indomie, kamar yanda Aminu yace mata gidan kam da wuta don har suka gama abubuwan da suke yi jiya ba a dauke wuta ba yanzu ma gashi da ta zo ta tarar da wuta, ta jona wayarta a caji sannan ta saka hijab ta fito zata yi yanda Aminu yace mata, karamin gidan dake gefen nata ta fara kwankwasa gate din aka bude, matar gidan na kallonta daga sama har kasa tace "Sannu da zuwa" Mayraah tace "Ina kwana" Matar ta amsa still tana kallonta irin ban sanki din nan ba, Mayraah tace "Ni neigbor dinki ce, jiya na dawo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login