Showing 129001 words to 132000 words out of 249515 words

Chapter 44 - Mayraah Hausa Novel Complete

20 Nov 2024

1529

i want to be sure with what she is doing first, sai gashi Malama ta kama ta, tun fara exams din nake mata kallon mara gaskiya shi yasa ban bar wajen da na tsaya ba" Still lecturer din bai yarda ba sai da ya bude booklet din Mayraah ya duba abinda tayi da wanda ke cikin takardan yaga babu hadi, sannan ya dauke mal-practice form din daga kan table dinta, Kuka kawai Badiyyah take don gaba daya an zagayeta sai ta cika Mal-practice form amma taki yarda ta cika, can dai ta daidaici kofa ta kwasa a guje kamar barauniya ta bar class din, Lecturer din da ta kamata ta dau pen ta cike mata form din don har ID card dinta na kan table ta bar shi, kowa a class din jikinsa yayi mugun sanyi da abinda ya faru, Mayraah ta ji gaba daya komai yayi Vaporizing daga kanta tsabar tashin hankali, har sannan jikinta bai daina rawa ba, Lecturers din suka ci gaba da invigilating dinsu bayan an cike ma Badiyyah mal-practice form kamar babu abinda ya faru, ba Mayraah kadai ba a lot of student sun kasa ci gaba da rubutun exams din barin kawayen Badiyyah, shkkn fa 5 years dinta ya tafi a banza kenan, don in dai aka bude sealed envelope din mal-practice form to magana ta kare kuma, Daga karshe Mayraah ta mike kawai don bata san kuma me zata rubuta ba ta tafi tayi submitting tayi sign out ta fita daga class din, har ta isa gida bata daina hawayen da take ba, don tasan da ba don wannan Coursemate din nasu dake bayanta da Security woman din nan ba Lecturers din nan ko me zata ce baza su taɓa sauraronta ba don marasu mutunci aka hada a class din dama, tana isa hostel ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya... Badiyyah na isa gidan Maheer bata ko kalli Haseenah da cousin dinta Ramlah dake zaune Parlon ba ta shige dakinta jikinta na rawa, ko handbag dinta bata dauko a exam hall din ba, don ma Allah ya rufa mata asiri yau bata kulle dakin nata da makulli ba tunda ba wani abun da zata boye a dakin, turamen atamfar da ga sato cikin akwatin lefen Haseenah dama har ta kai ma tailor dinta ya dinka mata, zaunawa tayi gefen gado tana share zufar da ke ƙeto mata har sannan gabanta bai daina faduwa ba, can ta kwanta ta lullube da bargo ta rufe idonta don har wani mugun sanyi take ji, ko tuna abinda ya faru bata son yi, gani take tunda har ta gudu bata cike form din ba to shikenan ta tsira, kuma fa Malamin nan yace lafiya zata gama exams har ma tayi passing duk courses din, to ya haka? Ya aka yi aka kamata bayan sai da yace baza a kamata ba ko da textbook zata shiga Hall din, taga dai kwanciyar nan baxae kara mata komai ba ta mike ta fito parlor, kilan in ta gaya ma Haseenah abinda ya faru zata fi samun sauki a ranta har a samo mata solution, Haseenah na ganin fitowarta tayi shiru, haka ma cousin sis dinta Ramlah, Badiyyah ta zauna gefen kujera har sannan gabanta na faduwa ta marairaice tace "Haseenah an kama ni da expo a school" Haseenah ta dafe kirjinta ta juya da sauri ta gwalo ido tana kallonta tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, final exam din?? Garin yaya haka ya faru Badiyyah, ba kin ce min Musharraf din na baki Area of concentration ba?" Badiyyah ta fashe da matsanancin kukan tashin hankali tace "Wallahi an kama ni yau Haseenah" Haseenah ta gyara zama tace "Musharraf din na hall din kuma?" Cikin kuka Badiyyah tace "He is not among our invigilators today, Haseenah don Allah ki rufa min asiri ki gaya min ya zan yi? 5 years fa Haseenah" Haseenah tace "kai Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, ga shi makarantar nan naku basu da mutunci har Allah Allah suke su kama mutum da mal-practice don a basu buhun shinkafa da man gyada, yanzu form din suka ciro a envelope suka baki?" Badiyyah ta silalo kasa tana rusa kuka tace "Don Allah ki taimakeni Haseenah, wallahi ji nake kamar zan mutu, ban taɓa shiga tashin hankali irin yau ba, ki gaya min yanda zan yi don girman Allah Haseenah" Ramlah dake sauraronsu ita ma cike da mamaki ta gyada kai tace "Tabdi, ae in dai jami'a ce to kinyi asaran shekaru 5 din nan wllh, babu wani abinda za a iya yi in dai dumu dumu aka kama ki" Haseenah tace "Gashi she is almost 33 yanzu fa Ramlah balle a sa ran zata fara daga farko, sau uku ana koranta a University fa, wannan duk mun sa rai zata yi graduating da muka ga ta kai level 500, duk fa mate dinta masters garemu yanzu" Badiyyah ta marairaice tana kuka tace "Ni dae ko Malamin nan naki zan kira in gaya masa abinda ke faruwa ko da abinda zai iya yi min" Haseenah ta zaro ido tace "Wani malami na? Ni kin taɓa ganin nayi harka da Malami Badiyyah? Ai bana harka da malamai, ban taɓa ba wallahi, to albishirinki dama don naga kwana biyu kina wani daɗɗaga min kai a gidan nan ne yasa na fita harkanki na kyale ki, wallahi kawata ta kirani tace ince maki ki fita sabgar malamin nan da ta hadaki ɗa shi ashe mayaudari ne ba malami bane, ya damfari jama'a ya gudu da kudadensu ya bar Zaria...." Badiyyah tace "Mutumin da yayi min aiki na kuma ga aikin yayi ne za ace ma mayaudari? Kinsan yanda muka fara zama close da Dr Musharraf kuwa yanzu duk sbda aikin da Malamin nan yayi min? To ke abinda baki sani ba last week da nace zan je Bichi da na samu intervals after our 4th paper a school, to Zaria naje wajen Malamin don ma ki ji in gaya maki" Sosai gaban Haseenah ya fadi, a ranta tace shikenan ta banu ta lalace, ynxu Badiyyah taje har gun malaminta kenan a Zaria, Badiyyah ta wani kyabe baki tace "Kuma kallonki kawai nake xaki wani ce min malamin kawarki ne bayan ashe malamin ki ne da shi kike harka, to har hotonki na nuna masa kuma yace min ae ke loyal costumer dinsa ce, yace min kun fi shekara bakwai tare yana maki aiki" Haseenah ji tayi kamar kasa ya bude ta shige tsabar yanda ta gigice har hakan bai boyu ba a fuskarta sai zare ido take, Ramlah dae ta kyabe baki tana kallon Haseenah irin maganinta kenan, Badiyya tace "To ni duk ba wannan ne a gabana ba, bari kawai inje in kirasa kar lokaci ya kure in shiga uku, don in har aka kore ni a makaranta komai zai iya faruwa da ni wllh, har fa Dr Musharraf yace min zai min hanyar samun aiki a babban asibiti as a Qualified Nurse, kafin nan ni kuma nasan duk yanda na bi muka yi aure, kuma yace min fa har kasan waje za a iya daukata aiki" Tana fadin haka ta fashe da kuka ta mike ta wuce daki ta kulle kofa, Haseenah ta daura hannu a ka tana kallon Ramlah tace "Na shiga uku na lalace Ramlah, ban san iyakan me Malam Dauda ya gaya mata ba akan alakata da shi, na shiga uku na lalace" Ramlah na hararanta tace "Ba dai ke bakinki bai tsayawa waje daya ba komai sae kin yi surutu, maganinki kenan wallahi"




*If you are reading this book without payment u owe me 500 till forever*



MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

Ur evidence via 07087865788
[7/8, 1:41 PM] Khaleesat Haiydar💖: Bayan Magrib Mayraah ta fito kofar gida ta dalilin kiran da Maheer yayi mata, har a sannan bata gama recovering daga shock din abinda Badiyyah tayi mata dazu a school ba, gaba daya a sanyaye ta yini ranan, ɗan shayin da take iya sha ma idan ta dawo daga exams yau duk bata sha ba, haka nan ta wuni sai dai ta sha ruwa, ta zauna inda ta saba zama duk sanda yayyin nata suka zo, Maheer dai sai kallonta yake, cikin sanyin murya tace "Ina yini?" Maimakon ya amsa sai cewa yayi "What is it again Mimi? You look disturbed" Cike da damuwa yayi tambayar, nan da nan hawaye ya kawo idonta, for almost 4 weeks now bai ga hawayenta ba duk da a sati hudun nan bai fi sau biyar ya zo wajenta ba, hankalinsa ya tashi ganin hawayen nata, yayi facing dinta a rikice yana tambayarta me ya faru, cikin rawan murya tace "They caught Sis Badiyyah with Mal-practice in exam hall today, shine da taga haka sai ta jefa min takardan da take expo din" Bai san sanda ya mike tsaye ba yana kallonta babu ko kiftawa, ta fashe da kuka tana goge hawayenta da hijab din jikinta, Da wani expression yace "Ta wurga maki takardan? Ta wurga maki as in how? And what happened afterward?" Ta daga kai ta kallesa a hankali tace "A security lady saw when she did that, da kuma Coursemate dina dake bayana, duk sun ga sanda tayi haka sai suka gaya ma lecturers din" Maheer ya sauke ajiyar zuciya ya koma ya zauna, bayan few seconds yace "Amma kin gama exams din Mimi?" Tayi shiru tana kallonsa, yace "Ko baki gama ba?" Cikin sanyin murya tace "I did what i can remember, amma fa yaya an cika mata Mal-practice form don ta bar ID card dinta ta gudu daga hall din, is there nothing they can do about that so that baza a koreta ba? Kasan expulsion ne fa idan an kama mutum yaya" Maheer ya mata wani kallo yace "To ke ina ruwanki in an koreta din? Da bata samu tayi implicating dinki ba shine kika samu bakin magana? What if babu wanda ya ga sanda tayi hakan kin zata ke ma baza a sa ki cike form din ba a kore ku tare? ni dama tun farko nace school is never for Badiyyah, ban san me yasa aka dage sai tayi karatu ba, going to school was neva her calling, kilan yanzu da aka koreta for the 4th time kowa zai hakura da cewar sai tayi karatu a fara nema mata wanda za a lallaba ya aureta" Ita dai Mayraah bata ce komai ba, yace "Nasan baki ci abinci ba" Ta daga kai ta kallesa, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya, ya mike yace "Mu je in siya maki abun da za ki ci" Tace "Ai Ummi bata dakin tana school, the door is open" Yace "Ba ta baki spare key din dakin ba, just close it, mu je mu dawo yanzu...." Mayraah ta mike ta wuce ciki ta kulle kofar sannan ta fito, zaune ta samesa cikin mota yana jiranta, ta karasa ta bude front seat ta shiga motar, har suka bar area din Maheer na jinjina abinda Badiyyah tayi a ransa, shi bai taɓa ganin shaidaniya in human form kamar Badiyyah ba she can go to any extent don yi shaidanci kanta tsaye, ya girgiza kai cike da takaici, can ya juya ya kalli Mayraah da tayi shiru tana tunani ita ma, yace "Wato tana ganin an kamata sai ta fita da gudu daga hall din?" Mayraah bata sanda tayi murmushi ba bayan ta tuna yanda Badiyyah ta gudu daga hall din, Maheer har ya mance rabon da ya ga murmushinta, lokaci daya jikinsa yayi sanyi, he wish she will continue smiling like this forever, Mayraah ta kasa controlling kanta ta fashe da dariya tana kallonsa tace "Yaya u need to see how she jumped and ran out of the hall, Kuma fa first day da muka fara exam din wannan Dr Musharraf din ya kamata da waya tana satan amsa amma yayi covering dinta ya amshe wayar without anyone noticing" Maheer dake sauraronta yace "Akan wani dalili yayi covering dinta? He saw her with expo kuma yayi covering dinta wani irin lecturer ne shi?" Mayraah dai tayi shiru, Maheer yace "Toh ke me yasa ma ku ka zauna waje daya da ita at the first place?" Mayraah ta kallesa tace "Kawai tun first day da muka fara exam din naga ta zauna gefena, shine kullum take zama side dina" Maheer ya girgiza kai yace "Sai taje ta gaya ma wa enda suka dage sai tayi karatu abinda ta aikata on her final paper, it's better she go and learn tailoring in dai ba a samu wanda zai aureta ba yanzu" Mayraah tace "Ai kai ma zata gaya maka abinda ya faru yau" Yace "Saboda me zata gaya min?" Ta ɗan yi shiru, sai kuma tace "Ba ka maida ta gidanka ba yanzu, kaga kai zata fara gaya ma kafin kowa ma" Juyawa yayi ya kalleta da sauri, lokaci daya ya maida idonsa kan titi cike da mamakin yanda tayi tasan Badiyyah na gidansa, bayan some seconds yace "Wa ya gaya maki tana gida na?" Mayraah ta ɗan yi murmushin karfin hali tace "To ai ba wani abu bane don tana gidanka tun da yar uwarka ce, she is ur blood" Maheer bai ce mata komai ba cause he don't want to talk about that again, yayi parking inda yake son siya mata abincin sannan ya juya ya kalleta, a hankali yace "Mu je" Ta girgiza kai tace "I will wait here Yaya" yace "Saboda me?" Ta jinginar da kanta jikin kujeran motar tace "I am tired" ya gyada mata kai yace "To me zan siya maki?" Tace "Anything" Bude motar yayi ya sauka, ya wuce ciki ta bi sa da kallo babu ko kiftawa, ignoring din maganarta na karshe da yayi ya mata ciwo sosai, shirun da yayi mata ya nuna Yes Badiyyah blood dinsa ce. Karfe tara saura Maheer ya ajiye Mayraah a hostel, ta bude motar ta sauka rike da ledan abincin da ya siya mata, a hankali tace "Sae da safe" ya gyada mata kai yana kallonta don tun da suka baro wajen siyan abinci ta zama so silent, zata juya ta wuce ciki yace "Wait Mimi" juyowa tayi ta kallesa, yayi kasa da murya yace "How about ur project?" Tace "Na gama, on Monday zan yi submitting" yace "Ohk, kar ki kashe wayarki zan kira ki anjima" ta gyada masa kai sannan ta juya ta shiga ciki ya ja motar ya kama hanyar gida... Maheer na isa gida ya tadda Badiyyah kadai zaune a parlor, har ya shigo tsakiyar parlon bata sani ba don tayi nisa cikin tunanin da take, ta saka wancan ta warware wannan duk nan neman solution take ma chakwakiyar da ta jefa kanta yau, she just can't imagine ace yau da gaske an koreta a school, tare suke zaune da Haseenah a parlorn, amma Haseenah na jin shigowar motar Maheer ta ruga dakinta da gudu wai zata je tayi wanka don tun safe bata yi wankan ba, Maheer ya gyara tsayuwarsa yana kallon Badiyyah ganin alamar bata san yana tsaye kanta ba yace "How was ur exams?" Firgit ta dawo daga duniyar tunanin da ta tafi, ta juya da sauri tana kallonsa, ta ɗan sosa kai tana murmushin yake tace "Sannu da dawowa yaya" Yace "Sannu, ya exams din?" A hankali tace "Alhamdulillah" yace "Shikenan kun gama kenan ko?" Ta gyada masa kai ba tare da ta bari sun hada ido ba, kana ganin yanda take muzurai kasan bata da gaskiya, yace "To Maa sha Allah, Allah Ubangiji ya baku sa'a, ya baku cleared pass gaba daya" Badiyyah dai taki cewa komai sai sosa kai take, dakinsa ya wuce, yana shiga ya kulle kofa.... Badiyyah ta mike ta wuce nata dakin ta shiga ta kulle ta zauna kasa ta fara shesshekan kuka ta daura hannu a ka, tun dazu ta kasa cin komai tsabar tashin hankali ko ruwa ta kasa sha, bata taɓa shiga damuwa irin na yau ba, ga Haseenah is not helping matters at all don duk shawaran da Badiyyah ta kawo a matsayin mafita sai Haseenah ta kyabe baki ta gwale shawaran tana girgiza kai tace ai fa nace maki ko da uban wa kike yawo kin riga kin koru a makarantar nan kawai, wannan kalman ke kara rikita Badiyyah ya sa tashin hankalinta ya ninku, gashi har yanzu bata samu Malam Dauda a waya ba balle ta gaya masa abinda ke faruwa, ta kirasa har ta gaji da kiransa, wayarta ne ya fara ring ta dauka da sauri taga Malam Dauda da take ta kira ne ya biyo ta yanzu, hannunta na rawa ta daga kiran ta kai kunne ta fashe da matsanancin kuka ta hau gaya masa abinda ya faru, daga karshe tace "Kuma Malam kai fa kace min ko da katon littafi na shiga babu wanda zai kamani, gashi da yan kananun takarda na shiga aka kamani" Sai da suka yi minti goma sha biyar suna waya daga karshe ta ajiye wayar bayan sun yi sallama, nan kuma ta fara tunanin inda zata samu dubu arba'in din nan da yace ta bada ayi aiki, ita dae ta shiga uku, ko dubu ashirin babu a account dinta yanzu haka, gashi yace tana turowa cikin daren nan zai fara aikin rufe bakin duk lecturers din dake nan sanda abun ya faru, hakan zae sa a kasa koran nata, zumbur ta mike ta fice daga dakin tayi hanyar dakin Maheer, ta tsaya jikin kofar dakin tana tunanin abinda zata ce masa, can dai ta kwankwasa kofar a hankali, dae dae nan Haseenah ta fito daga dakinta sanye da kayan bacci ta baxa uban turare a jiki, tana ganin Badiyyah ta hade rai ta tsaya tana kallonta daga sama har kasa, Badiyyah dai ko kallon inda take bata yi ba ta sake kwankwasa kofar dakin, bude kofar Maheer yayi ya kalleta sannan ya kalli Haseenah dake tsaye ta wani murtuke fuska, ya maida dubansa kan Badiyyah yace "Ya aka yi Badiyyah?" Badiyyah ta dawo gefensa ta langwabar da kai ta marairaice murya tace "Yaya dama don Allah akwai wani abu da nake son siya ne, kuma bani da kudi wllh"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login