Showing 51001 words to 54000 words out of 249515 words

Chapter 18 - Mayraah Hausa Novel Complete

20 Nov 2024

1514

taji tsanarsa ko kuma haushinsa sai taji kamar an kara mata wutan sonsa ne a zuciyarta, ita kanta bata san yanda aka yi sonsa yayi mata yawa haka a zuciyarta ba, a da ta san tana sonsa amma ba kamar yanda take jinsa har cikin ranta yanzu ba, kwanciya tayi nan corridor ta takure waje daya duk da sanyin tiles din, a haka bata san sanda bacci ya dauketa ba, cikin bacci ta ji warm hand din mutum a fuskarta dama a ɗar ɗar baccin ya dauketa, hakan ya sa ta farka a tsorace ta mike zaune tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" a gabanta ta gansa a duke yana kallonta, ta dinga komawa baya a tsorace duk jikinta na rawa, hannu ya nuna mata alamar tayi calm down, ita dai har ta manne da bango bata bari sun hada ido ba, cikin sanyin murya yace "I am sorry Mayraah" Sai a sannan ta daga kai tana kallonsa, ya sunkuyar da kai yace "For good 6 years ban sha alcohol ba Mayraah believe me, that was my foregone habit, na daina tun bayan da na dawo daga America, i don't know what came over me yesterday, i felt i was loosing my mind" Kasa ci gaba yayi, ita dai kallonsa kawai take, bayan few seconds ya dago yana kallonta da idanunsa da suka kada yace "Damuwa yayi min yawa, ban san halin da zan shiga idan na rasa ki ba" A hankali Mayraah tace "Ur foregone habit?" Ya dinga kallonta kafin yace "Kin gansu da yawa a fridge ko? Billah na frnds dina ne ba nawa ba, ba ga dakunansu kin gani a kulle ba, we do spend our weekends together here, ni ne ma nakan dade ban zo nan ba, wllh nasu ne ba nawa ba" Mayraah dai tayi shiru bata ce komai ba, yace "Tashi mu shiga ciki ki kwanta" Sosai gabanta ya fadi amma bata nuna hakan ba, ta dake tace "Ina zaka kai ni daga nan kuma?" Yayi kasa da murya yace "Abuja, za mu je can a daura mana aure, daga can zamu fita kasar..." Mayraah ta sunkuyar da kanta tace "Ohk, but promise me baza ka taɓa ni ba har gari ya waye" Ya dinga kallonta babu ko kiftawa, can yayi kasa da murya yace "Idan na taɓa ki ma ai ni zan aure ki ba wani ba" Taji gabanta ya fadi amma ko da wasa bata nuna hakan a fuskarta ba tace "Then babu inda zan bi ka a daura mana aure idan har baza ka bari sai bayan an daura auren ba zaka zo kusa da ni, ko ka mance addininka ne?" Yayi kasa da murya yace "Yi hakuri Wife, i promise ko finger dinki bazan taɓa ba" Yana fadin haka ta mike ta nufi Bedroom din ya bi ta da kallo wani sonta na fizgarsa, saman gado ya ga ta kwanta duk da fa karfin hali kawai take don ita bata ma gama tabbatar da mayen ya sake sa ba, ya mike ya shiga dakin shi ma, pillow ya dauka ya ajiye a kasa ya kwanta, ta sauke wani boyayyen ajiyar zuciya, a hankali yace "Can i take off the light?" Tace "No" Yace "Ohk" Juya masa baya tayi ita kanta tana mamakin courage din nan nata, sai dai fa har kusan karfe uku bata yi bacci ba sbda fargaba, kamar yanda shi ma yake ta juye juye bai yi baccin ba, Wajen karfe hudu ta juya ta kallesa taga alamar bacci ya daukesa, she needs to get the key of this house kafin ya tashi, ta sidado ta sauka daga kan gadon tana kallonsa, zaro ido tayi ganin makullin ya ajiye a gefensa, ta fara tiptoeing zuwa side din nasa trying her best not to make any noise, can dai ta tsaya tana tunanin ko dai ta kashe wutan dakin sai tayi stretching ta saman gado ta dauko, don yanzu tana zagawa da kyar idan bazai tashi ba tunda bata san ko yana da nauyin bacci ba ko bai da, hakan tayi daga karshe ta kashe wutan dakin ta hau saman gado ta koma side dinsa sannan tayi stretch din kanta ta dauko makullin, bata ankaraba kawai sai gani tayi ta rikito kansa, tsabar gigicewa tayi saurin jefa makullin saman gado tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Duk don kar yaji sound din makullin, shi ko ya mike zauna holding on to her yace "Baby are you okay?" Bakinta na rawa tace "I had a bad dream" ya mike zai kunna wutan dakin ta riko kafarsa da sauri tace "Noo, i switched it off, kar ka kuna plss, bana son hasken" Ya koma ya rikota yace "But are you okay?" Ta hadiye wani abu da kyar tace "Sure, i am fine, zan kwanta nan amma stick to our deal pls" a hankali yace "Ohk" Ta kwanta nan side dinsa gabanta na mugun faduwa, don tasan yana kunna wuta dole zai ga makullin da ta jefar kan gado, yace "In dauko maki duvet din ne?" Tayi saurin cewa "No thank you, kawai ka matsa can ka kwanta" A hankali yace "Okay" Tana jin ya matsa nesa da ita ya kwanta, ta sauke wani boyayyen ajiyar zuciya, har aka kira asuba daga shi har ita babu wanda yayi bacci, fargabanta kar ya kunna wutan dakin in zai je alwala, ai ko tana ganin ya mike tace "Pls kar ka kunna min wutan" He was surprise don yayi zaton bacci take, a hankali yace "Ohk dear" Tana ganinsa ya kunna na bandaki sannan ya shiga, ta sauke wani ajiyar zuciya yana kulle kofar bandakin ta mike da sauri ta kunna wutan dakin ta dau makullin sannan ta dau Hijab dinta da ya linke mata tun jiya da daddare ta saka, da sauri ta fita zuwa parlor, kan centre table taga cash da bata san ko nawa bane, ta dau 5k a ciki jikinta na rawa ta nufi kofa ta bude da mukullin ta fita, har wani ɓari jikinta yake ta nufi gate din gidan ta dinga gwaggwada bunch din makullin hannunta har ta samu na gate din ta bude a hankali, sannan ta fita, kulle gate din tayi ta waje sannan ta jefa makullin making sure bai yi hanging a barbed wire ba har sai da taji faduwarsa a kasan compound, sauri sauri gudu gudu take tafiya tana waigen bayanta, can dai ta ga ta fito babban titi ga motoci sai wucewa suke, haka ta dinga sauri har ta fara ganin masu adaidaita sahu ta tsayar da wani ta shiga, yace "Ina za ki Hajiya?" Tace "Tasha" Yace "Toh" sai da taga sun yi nisa sannan tace "Don Allah ya ma sunan garin nan" Juyawa yayi ya kalleta, sai kuma yace "Amma dai ke bakuwa ce ko?" Tace "Eh" Yace "Ai naga alama, to Zaria ne nan" Ta buda ido sosai wato Zaria ma ya kawota, Mai adaidaita sahu na ajiyeta a tasha ta samu motar kano ta hau, nan da nan motar ya cika suka yi set off zuwa kano, sai a sannan ta sauke wani ajiyar zuciya hankalinta ya dawo jikinta, assuming bata yi duk wannan dubarun da tayi ba tasan Dr Musharraf bazai bar ta haka ba, kafin karfe bakwai da minti talatin sai ga su a cikin garin kano.....

Babu wanda ya rintsa a gidan Abba daren ranan nan, ga Ammi jini ya hau sosai, don she is under medication a gida har da karin ruwa, zuwa sannan duk kowa yasan an fasa auren Mayraah sannan Mayraah ba er gidan Abba da Ammi bace, wajen karfe takwas da rabi jama'a duk sunyi cirko cirko a parlor har da baƙin da suka zo daga nesa da wasu makotansu Ammi, kowa dai duk jiki a sanyaye, duk da ba bacci Ammi take ba amma idonta a rufe suke ita kadai tasan abinda take ji a wannan lokacin, gani take kamar shikenan bazata sake ganin Mayraah ba har abada, Mama Ladi ta fyace majina cikin rawan murya tace "Ni wllh nasan annamimiyar da ta hada wannan bam din aka shiga wannan rudanin a gidan nan...." Hajja dake zaune tayi tagumi a parlon ta juya tana kallon Mama ladi, rai bace Hajja tace "Amma dai nace maki ki iya bakin ki Ladi, wannan wace irin rayuwa ce baki da aiki sai hada hutsuma cikin jama'a? Tun cikin dare kin ishemu kinsan wanene kinsan wanene, to ke a garin kano kike da zaki hakikance kinsan wanene, haba don Allah ki bari mu ji da daya mana, wannan fa ba karamin magana bane kuma kina ji Mamuda yace sai yayi Shari'a da koma wanene yayi mana haka" Mama Ladi ta mike tace "Tun jiya zan yi magana kike hanani magana Hajja, to wallahi ni dai da iyayenmu suka haifeni kema kinsan ba munafuka bace ni, kuma babu ruwana da harkan munafurci, a cikin ku akwai warce nace ma Badiyya taje wajena har tayi kwanaki biyar?" Duk kowa yayi shiru yana kallon Mama Ladi har Hajja don kam bata gaya ma kowa ba, cike da mamaki Aunty Mariya tace "Taje yin me a wajenki Mama Ladi?" Mama Ladi tace "Wallahi ina zaman zamana sai ga shegiyar yarinyar nan Badiyya kamar an jefota karaye, yarinya ta zo ta giggilla min karya wai ana nuna banbanci tsakaninta da Mera don an ga bata da uwa bata da uba, duk kowa ya tsaneta har saurayin da ke nemanta da aure ance ya hakura ya nemi Mera kuma har ya hakura gashi an saka ranansa da Mera, sannan sau dari idan Mariya zata kira sai dai tace a ba Mera baza tace a ba Badiyya waya ba, ni ko da zuciya ta debeni nace wacece Mera? meran da bamu hada komai da ita ba babu dangin iya ba na baba ko dai ita Ammin da Hajjan sun mance ne, nan ko na kwashe duk yanda aka samo Mera na gaya ma Badiyya da zuciya daya ba da zuciya biyu ba, ban san da er iska munafuka nayi tadi ba" Mama Ladi na kai wa nan ta fashe da kuka tace "To yanzu zan fasa kwan nan a gaban kowa, wllh wllh Badiyya ce ta lalata maganar auren nan daga dai na bata labarin wacece Mera da zuciya daya" Ammi ta bude ido ta mike zaune tana kallon Mama Ladi babu ko kiftawa, ita kanta Hajja kasa kwakkwaran motsi tayi tana kallon Mama Ladi, Aunty Mariya ta fashe da matsanancin kuka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, me yasa kika mana haka Mama Ladi?" Bude kofar parlon aka yi Mayraah ta shigo, tsaye tayi bakin kofar tana bin kowa da kallo kamar yanda duk aka yi still a parlon ana kallonta da shock, Mayraah ta nufi Ammi da gudu hankalinta tashe ganin drip a hannunta tace "Ammi... saboda ni ne?" Mama Ladi ta rushe da kuka tace "To da saboda waye? Banda mun sa ma kanmu salama ai har mu da sai kin ganmu da karin ruwan a hannu, Dama nace masu babu inda zaki je dole ki dawo garemu ko da bamu hada komai da ke ba, ko don halaccin da muka maki ai kya dawo, To idan ba jiya ba ke kin taɓa sanin cewar ba Ammi da Mamuda bane suka haifeki? Ko a bakin wanin mu kin taɓa ji? Kinga ai basu taɓa nuna maki banbanci tsakaninki da ainahin yaran da suka haifa a cikinsu ba, kuma soyayyar da suke maki yasa suka boye ma duniya ba su ne asalin iyayenki na gaskiya ba mu ma kuma muka ja bakinmu muka yi shiru muka taya su rufa wannan asirin banda yanzu da asirin ya tonu, amma gata kam ai babu irin wanda baki samu ba a wajensu Mera, da yawa wa enda ke gun iyayensu na asali ma basu samu gatanki ba wllh, ko su Maheer da suka haifa basu samu haka ba magana ta gaskiya, to don me baza kiyi la'akari da wannan ba zaki gudu ki bar mu cikin tashin hankali ki tauye mana baccinmu jiya, yanda muka ga rana haka fa muka ga dare, kuma da kika kama hanya kika gudu ina zaki je? Ke da baki da dangin uwa balle na uba" Mayraah da ko karasawa gun Ammin bata yi ba ta tsaya tana sauraron abinda Mama Ladi ke gaya mata babu ko kiftawa, lokaci daya ta dinga ganin parlon na juya mata ta dinga kallon Mama Ladi da ta dawo mata double double a ido, Ammi ta kasa daurewa ta hade kanta da kujera tana kuka sosai tana jin zuciyarta na mata zafi, Aunty Mariya ma kukan take don su duk tunaninsu Mayraah tasan asalin me ke faruwa daga bakin Musharraf, dalilin da yasa ta bar gida kenan jiya, Mama Ladi ta sharce majina tace "A nan bakin wani masallaci a cikin garin Yola aka yasar da ke ko cibiyarki bai fadi ba, a lokacin Mamuda na fama da baƙin talauci ya fito zai share masallaci ya jido ruwa kafin a fara fitowa sallan asuba ya ganki cikin yakunannen tsumma uwarki ta wurgar da ke ta kara gaba" Tsawa Hajja ta daka ma Mama Ladi ta mike tana huci tace "Ke mahaukaciyar wace gari ce Ladi?? maza dauko rubabben akwatinki ki kama hanya ki koma karaye tun raina bai gama baci ba...." Ko rufe baki Hajja bata yi ba suka ga Mayraah ta sulale nan kasa, dai dai shigowar Usman parlon yayi saurin karasawa inda ta fadi, tsabar rikicewa Ammi mance drip din hannunta tayi ta mike tayi kan Mayraah a guje, sauran mutanen parlon ma duk suka nufi Mayraah suna salati, Mama Ladi dai sai gwaggwale ido take a inda take tsaye.....




Still on todays discount for the book Mayraah, pay 300 Naira into
👇🏻
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

Ur evidence via 07087865788

To be included to group, discount ends today by 12am. Subscribe and read happily.
Thank you.
[6/11, 5:49 PM] Khaleesat Haiydar💖: Maheer na zaune kan kujeran dake kusa da gadon dake dakin asibitin ya jinginar da kansa da kujeran idonsa a lumshe, Usman na tsaye jikin window din dakin yana danna wayarsa, lkci lkci yake daga kai ya kalli saman patient bed din da Mayraah ke kwance, she is being unconscious tun safe sai wajen karfe daya da wani abu ta farka, tana farkawa kuma babu bata lokaci aka mata wani allura shine har yanzu take bacci and this is almost 4pm, motsi yaga tana yi, ya saka wayarsa a aljihu ya nufeta, ya duka a bit closer to her yana kallonta, bude ido tayi a hankali, tana hada ido da shi ta fara kokarin tashi zaune, Usman ya rike hannunta yace "Do not injure ur self, akwai drip a hannunki" Bude ido Maheer yayi da sauri, lkci daya ya mike tsaye holding on to her yace "Are you okay Lil sis?" Mayraah dai sai kalle kallen dakin asibitin take, Maheer ya fahimci she is trying to recall things, ya maidata ta kwanta yace "Lay still, you will be fine in sha Allah Mimi" Bin su Mayraah ta shiga yi da kallo kamar ranan ta fara ganinsu, bayan kanta da yayi mata nauyi har kirjinta ma ji tayi yana mata wani azababben ciwo, dafe kirjin tayi tana son magana amma ta kasa, Maheer dake rike da ita har sannan yace "Kina jin ciwo a nan ne?" Kai kawai ta gyada masa hawaye na sauka idonta, yasan dole zata ji haka cause she had a terrible panic attack that triggered her Asthma, tun daga gida yayi kokarin reviving dinta har suka taho asibitin aka kwantar da ita giving her the necessary treatment, ya jinginar da pillow din kan gadon da bango sannan ya sa tayi resting a jiki yace "U will feel relieved in sha Allah" Usman ya koma inda yake ya tsaya yana kallonsu, Maheer ya bude flask din da Aunty Mariya ta kawo masu da kayan shayi don ko minti talatin bata yi da barin asibitin ba, yayi making din mata shayi ɗan kadan a cup yayi diluting da bottle water sannan ya mika mata a hankali yace "Ki daure ki sha ko kadan ne sai a maki allura for the chest ache" Bata ce masa komai ba don tayi nisa tunanin da ta tafi, ya zauna gefen gadon yana kallonta, sai da yayi gathering courage kafin a hankali yace "Mimi" ta dawo duniyar tunanin da ta tafi tana kallonsa, yace "Amshi shayin ki sha even if it's just a little" Sauke idonta tayi kasa without responding to him, wayarsa ne ya fara ring a aljihunsa ya ciro ganin Abba ne ke kiransa ya daga ya kai kunne, ya gyada kai yace "Eh ta tashi" Yana fadin haka ya kalli Mayraah yana mika mata wayar yace "Za ki yi magana da Abba" Girgiza masa kai kawai tayi ba tare da ta kallesa ba, ya maida wayar kunnensa a hankali yace "Zan kira ka Abba" Ajiye wayar yayi bayan Abba ya katse yana kallonta, ko bata ce komai ba kasan she is in pain, ya ajiye cup din shayin ya juya ya fita daga ward din don kiran likitan da ya amsheta to make some suggestions on more injections da za ayi mata ko zata samu relief gaba daya, Shi dai Usman na tsaye ya rungume hannayensa yana ta kallonta, ta daga kai ta kallesa suka hada ido, sai kuma ta sunkuyar da kanta hawayen dake makale idonta ya sakko fuskarta, jinginar da kai yayi da bango not knowing what to even say to her, he wish he could take away her pain and grief, Maheer na dawowa tare da likitan wayarsa ya fara ring ya ciro a aljihunsa ya ga Haseenah ce, ta kirasa yafi sau arba'in yau, tun da garin Allah ya waye take kira ko daya bai daga ba a kiran sai ma silencing din wayar da yayi ya bar sa a aljihu, ya bar likitan ya shiga ward din shi kuma ya tsaya daga corridor yayi picking din call din nata, babu ko sallama a fusace ta fara cewa "Yanzu Maheer fisabilillahi yau daurin auren namu guda tun da garin Allah ya waye ko message dinka ban gani a wayata ba balle

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login