Showing 249001 words to 249515 words out of 249515 words

Chapter 84 - Mayraah Hausa Novel Complete

20 Nov 2024

1567

the pain yace "Dysmenorrhea?" Gyada masa kai tayi da sauri, ya mike ya bar wajen, magani ya yafi ya dauko mata da ruwa a glass cup, hannunta na rawa ta amsa ta sha, shi dai yana duke gabanta yana kallonta, don bata daina kukan da take ba, bayan kusan minti goma yace "Tashi ki koma daki..." Ko rufe baki bai yi ba cikin rawan murya tace "Aa wallahi bai daina ba, kilan allura zaka min, dama allura ake min" Daga sama har kasa ya kalleta seeing how confident she still is in between pains, Bai yi niyyar mata alluran ba saboda ta riga da ta sha drugs, but ganin she is still in pain har karfe uku kawai ya hada alluran ya mata, nan parlon ta fara bacci ya tasheta ta wuce daki. Washegari har karfe takwas bata tashi ba, har sai da ceo ta shigo ta tashe ta, bayan ta fito daga wanka ta shirya sannan ta dau wani jacket dinta dake akwati ta sa sannan ta fita parlor, Ceo na kallonta tace "Breakfast yana dinning table" Mayraah ta nufi dinning din ta zauna. Wajen karfe goma na safiyar Mayraah na waje tare da Usman da zuwan sa kenan, yana kallonta yace "Hope you are better now?" Ta gyada masa kai tace "Na ji sauki" yace "Me yasa baki kirani jiyan ba, though the ceo might not gree to that since...." Shiru Usman yayi bayan ya hango MD da ya fito daga cikin gidan, tunda Mayraah ta kallesa sau daya ta dauke kai gabanta na faduwa yake, kallonsa kawai Usman yake kamar yanda shi ma MD ke masa kallon cikin ido, har ya zo ya wucesu leaving his designer perfume scent behind, Usman ya dinga kallon jacket din da ya daura shoulders dinsa, can ya kalli Mayraah da ta juya kai taki kallonsu, a kan gado fa ta ajiye jacket din nasa ashe ya shiga ya dauka, Usman yace "Mayraah" Da sauri ta juya ta kallesa, yace "Wannan ba Jacket din da kika ce min Ceo ta baki bane?" Ta hadiye wani abu da kyar tace "Yaya shi ne, amma ai kilan shi ma ta basa ne ya sa...." Kana jin yanda take maganar kasan karya take, Calmly yace "Mayraah" Shiru tayi tana kallonsa, yace "Whose jacket is that?" Ta sunkuyar da kanta a hankali tace "Na shi ne, a airport ya bani saboda ni ban ciro nawa a akwati ba don ban san haka sanyin yake ba, shine sai ya bani nasa in saka" Kallonta kawai Usman yake, ta daga kai ta kallesa jin yayi shiru, after some seconds yace "To kin yi kokari" Tana ganin ya juya zai bar wajen ta marairaice tace "Yaya don Allah kayi hakuri, wallahi ina tsoron kar ka min fada ne shi yasa nayi maka karya" Yace "Infact karya kike still kice min babu komai tsakaninki da wannan mutumin, saurayin ki ne" Mayraah ta buda baki tana kallonsa da mamaki, juyawa yayi ya bar wajen ta bi sa da kallo, tafi minti uku tsaye wajen daga karshe ta juya a hankali ta fara tafiya zuwa cikin gidan.....

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login