Showing 114001 words to 117000 words out of 249515 words
da toothpaste and brush yayi, sannan ya ajiye takalmanta a kasa kusa da gadon ya juya ya fita daga ward din, sai da aka kira sallah Usman ya fita shi ma. Da safe karfe bakwai da rabi aka yi discharging din Mayraah daga asibitin, suna isa parking space da brothers din nata taga ko wannensu da motarsa a nan, tsaye tayi gefe daya not knowing motar wanda zata shiga cikin su, Usman dai ya bude motarsa ya shiga ya tada ya bar su tsaye wajen yayi wucewar sa from the hospital, Mayraah ta bi motarsa da kallo sannan ta bude motar Maheer a hankali ta shiga ta zauna. Kusan a tare suka isa gida sai dai Usman ya riga su shiga cikin gidan, Maheer na gaba tana biye da shi suka shiga gidan, zaune suka tadda Usman a parlorn downstairs tare da Mama Ladi dake cusa lafcecen kwai cikin biredi tana dannewa, ga cup din shayinta a gefe tana cewa "Wallahi yanzu haka wai suna asibiti, ko wani asibiti ne oho, wa ya sani ko gantalinta zata je mota ya kade ta, tun karfe hudun asuba Ammi ta bar gidan nan har yanzu babu ita babu alamarta inji Saliba me aikinku, ni dai nace sai na ci na koshi kafin inje ko ina babu ruwana da lalacewa inje yunwa yayi min lahani ayi min hisabi da yan hanjin cikina ranan gobe kiyama" Shigowan Maheer da Mayraah yasa ta daga kai tace "Yauwa Mashir wai me ke faruwa haka ne? Saliba tace min Ammi tun asuba ta bar gidan nan" Maheer ya karasa ya zauna kan kujera yace "Sabira dai ko, ina kwana..." Mayraah dai tafiya take a hankali ita ma tana kallon Mama Ladi, Mama Ladi ta yagi kwai da bread ta kai baki tana cewa "Ni jiya da wuri nayi bacci bayan na ci abinci ban san kan komai ba wllhi, ita Salibar ke gaya min an kai Badiyyah asibiti" Bata rufe baki ba Ammi ta shigo parlon rike da basket din flask da kayan shayi, Maheer da Usman suka juya suna kallonta haka ma Mayraah da ta nufeta zata amshi basket din hannunta tace "Sannu da zuwa Ammi" Ammi bata ce mata komai ba kuma bata bata basket din hannunta ba ta wuceta ta karasa cikin parlon tana kallon Maheer da Usman tace "Ina jiranku a sama...." Daga haka ta ajiye kayan hannunta ta wuce sama, duk suka bi ta da kallo, har Mayraah da ke tsaye inda Ammi ta bar ta, Mama Ladi na kora bread dinta da shayi tace "Ko kudi za a harhada na trintment din Badiyyar tunda dai duk mun san dangin ubanta matsiyata ne, tun tana karamarta Ammi ke mata komai sai Mamuda da Hajja da ni, sai kuma ku da ku ka kawo karfi yanzu, ku dai je ku ji, iyaka ku bada dubu daddaya ta rabaku da kowa lafiya tunda ba wani ya aiketa ba...." Usman ya fara mikewa ya wuce sama, Maheer ya tashi ya bi bayansa shi ma, Mayraah dai ta kasa karasawa cikin parlon ta zauna, Mama Ladi ta mike ta dau shayinta da bread tace "To ya ma za a bar ni a nan sai kace wata bare..." Sai kuma ta kalli Mayraah tace "Zo ki dau min shayin nan mu tafi sama kar garin hawa benen nan in barar in shiga uku ance milo ya kare, duk an wani watse a bar mu kamar mun ci mutum" Mayraah da gaba daya jikinta yayi sanyi ta rasa dalilin hakan, ta karasa gun Mama Ladi ta dau mata shayin suka wuce sama a tare. Usman na shiga parlon Ammi ya ga Haseenah zaune kan kujera da hijab dinta har kasa sae counter din carbi a hannunta, duk da yayi mamakin ganinta ya gaisheta a takaice ya shiga dakin Ammi, Maheer ya shigo Parlon few seconds later, he was very very surprise to see Haseenah sitted in Ammi's parlor, ya dinga kallonta, suna hada ido ta kauda kanta ta wani daure fuska tana daddanna counter din hannunta, lkci daya yaji wani mugun ɓaci rai ya zo masa, but ya dai yi calming kansa down bai ce mata komai ba ya wuce dakin Ammi, tsaye ya ga Ammi bakin window duk tana jiran su, kallo daya Usman yayi mata bai ma karasa can cikin dakin ba ya tsaya daga gefen kofa cause her facial expression isn't giving, Maheer ne yayi karfin halin karasawa ciki yana kallonta shi ma, daga shi har Usman babu wanda ya iya bude baki ya gaisheta don basu ma ga fuskar yin haka ba, Mama Ladi ta shigo parlon Ammi Mayraah na biye da ita, buda baki tayi ta koma baya da sauri ganin Haseenah, cike da mamaki tace "Ke kuma daga ina matar nan? Ko dai ba da ke aka tafi jiya ba?? Ni fa na raka ku har mota, garin yaya haka na ganki a nan?" Haseenah dai ta sunkuyar da kanta tace "Ina kwana Mama" Mama Ladi ta nufi dakin Ammi tace "Yau ni naga ikon Allah" Mayraah bata bari sun hada ido da Haseenah ba ta ajiye Shayin hannunta a kasa sannan ta zauna kan carpet din parlon, tun da Haseenah tayi mata wani matsiyacin kallo ta kyabe baki ta kauda kai tana girgiza kafa.... Maheer yayi gathering courage yana kallon Ammi yace "Ina kwana Ammi" A fusace Ammi tace "Ban kwana ba, nace ban kwana ba..." Kallonta kawai Maheer yake yayi shiru, Ammi na nunasa cikin bacin rai tace "Before going into my main point ina son ka maida matar ka immediately first..." Maheer ya sunkuyar da kansa, Ammi ta masa tsawa tace "Are you deaf, ko baka ji na ne?" Ya dago kai a hankali yace "I have done that" Mama Ladi da ta shigo dakin ta buda baki tace "Wai me yake faruwa ne kike daga murya haka? Me ke faruwa ni Ladiyo? Wace matar za a mayar?" Ammi bata ko kalleta ba tana kallon Maheer tana gyada kai tace "Sai yanzu na fahimci inda Hajja ta dosa all this while, sai yanzu na gane abinda take son ta fahimtar da ni na kasa ganewa, i now fully understand Mimi is nothing but a nuisance in our midst now, she is beginning to cause nothing but chaos in this family, kai ka saki matarka da ko sati uku ba kuyi da aure ba duk a saboda ita, shi kuma ɗan uwanka ya sake komawa for the second time yayi ma Badiyyah dukan tsiya duk a kanta ba tare da yayi binciken abinda ya faru ba, a saboda yarinyar nan har yau mahaifiyata bata ɗaga wayata, ko naje inda take babu maganar arziki tsakanina da ita all because of Mimi, is that how she wants to pay us by destroying us? Toh all this is going to end now" Cikin daga murya Ammi tace "Maheer from today henceforth she is not staying in ur house any more, bazata sake zama a gidanka ba nace...." Maheer couldn't believe this is really coming out from Ammi's mouth, ji yayi kansa ya wani sara masa yana kallonta cike da karfin hali yace "Where will she stay then?" A takaice Ammi tace "I don't know, and I don't care Maheer, idan ma kai da Usman za ku dawo hankalinku ku dawo, baku hada komai da ita ba, i repeat babu abinda ku ka hada da ita in any way, she is not ur blood, and because of her bazan zuba ido zumunci ya lalace ba, Ita Badiyyar da ku ka mayar makiyiyarku ita ce dolen ku duk inda za a je kuwa, ita ce er uwarku ta jini, sannan baza ka taɓa hada matar da kake aure da ita ba, matar ita ce dolen ka ba ita ba" Usman ya dinga kallon Ammi da mamaki babu ko kiftawa, jin maganganun nata yake kamar a mafarki, Mama Ladi dai sai zazzare ido take duk da turanci yafi yawa a maganganun amma sarai ta fahimci komai, salati ta saki tayi zaman dirshan a kasa tana girgiza kai tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una, Hajaru yau kece kike wannan munanan kalaman akan Mera? Me suka baki kika sha a asibitin Hajaru, yau mun shiga uku mun lalace, ina ake son Marainiyar ta sa kanta taji dadi kenan?" Kawai sai ta fashe da kuka wiwi, Maheer dake ta kallon Ammi ganin zata fita ta bar masu dakin, a hankali yace "Ohk then, tunda kince babu abinda muka hada da ita, sannan ita din ba jininmu bace yanzu na yarda kuma na amince da hakan, as at before i was still doubting that, don bamu ji kin gaya mana hakan da bakin ki ba duk abubuwan da suka faru, it was hard for us to assimilate Mimi isn't our blood all this while, but after saying this today naji na yarda da hakan har cikin raina, saboda haka ni zan auri Mimi in samar mata gidan da zata zauna to bring an end to all this...." Juyawa Ammi tayi da sauri tana kallonsa kamar yanda Usman ma ya daga kai yana kallonsa, Ammi na kallonsa da kyau tayi wani murmushi tace "Ba da yawuna ba, in kuma gaban kanka zaka yi i assure u baxa ka taɓa ganin dai dai ba..." Juyawa Usman yayi ya fice daga dakin kamar zai tashi sama, Mayraah na zaune parlor kanta a kasa duk tana jin abubuwan da ake yi a dakin, banda murmushi babu abinda Haseenah take tana kallon Mayraah kasa kasa dom everything was clear kamar a gabansu ake yi, Mama Ladi dake rusa kuka ta mike tana kallon Maheer tace "Kawai ta hado kayanta mu tafi karaye Mashir, dama ka taɓa ganin inda barewa tayi gudu ɗan ta yayi rarrafe??" Bata jira amsarsa ba ta fice daga dakin ta koma parlor tana kallon Mayraah tace "Tashi maza ki tattaro kayanki" Sai a sannan Mayraah ta daga kai tana kallon Mama Ladi da manyan idanuwanta, cikin daga murya Mama Ladi tace "Baza ki tashi ba sai kin ga tana watsar maki da kayanki titi" Mayraah ta mike tsaye, Mama Ladi tace "Fita mu je, ai naga akwai sauran kayanki a gidan nan tattaro su gaba daya kawai ki zuba a akwatina" bin bayan Mama Ladi Mayraah tayi suka fita daga parlon zuwa dakinta, Mama Ladi ta bude inda sauran kayan Mayraah suke ta dinga kwasowa tana zubawa a akwatinta, ita dai Mayraah na tsaye tana kallonta kamar statue, Maheer ya shigo dakin looking so weakened and confused, Mama Ladi ta dago bayan ta gama cusa kayan a akwatin tana kallon Mayraah tace "Shikenan abinda zaki bukata kin wani tsaya kamar gunki kina kallona, ko baki ji abinda ke faruwa a gidan bane" Mayraah dai ta kasa cewa komai sai kallonta take, it seems like it's taking her too long to absorb the reality of what is happening, Maheer na kallon Mama Ladi a hankali yace "Tana da jarabawan da zata yi Mama" Yana fadin haka ya karasa ya kama hannun Mayraah suka fita daga dakin kawai, ita dai bin sa kawai take har suka sauka downstairs, Balcony ya fita da ita ya sa ta zauna, shi ma ya zauna ya rike kansa da yayi masa nauyi, gaba daya tunaninsa ya tsaya cak ganin abubuwan yake kamar a mafarki ya rasa wani tunanin zai yi, ita dai Mayraah kallonsa kawai take, can ya dago ya kalleta ganin yanda take kallonsa ya kama hannunta yace "Mimi" sauke idonta tayi ta amsa, yaji wani tausayinta har cikin ransa, seeing her dry eyes ne ya kara daga masa hankali don yasan taji duk furucin Ammi tunda kofar dakin a bude yake ya kuma san ita din me saurin kuka ce amma ynxu bbu ko digon hawayen a idonta.... Haseenah bata taɓa shiga farin ciki irin na yau ba ko aurenta da Maheer bata ji irin wnn mugun farin cikin ba, gaba daya ta kasa tsaye ta kasa zaune a part din Ammi don murna, babu kowa sai ita kadai a part din, aka bude kofar Parlon juyawa tayi da sauri ganin Abba ta sauko kasa tana sinne kai tace "Ina kwana Abba" a takaice ya amsa ya nufi dakin Ammi ya bude yaga babu kowa a ciki, fitowa yayi daga part din ya sauko downstairs ya tadda Ammi zaune a parlon fuskarta a murtuke, Abba na nunata da yatsa cikin bacin rai yace "Ke Hajarah, naga kamar baku san kawaici ba daga ke har mutanen ki, all this while ina ta bin ku a yanda ku ke so don kawai a zauna lafiya, to kun kai ni bango kuma yanzu i am not going to tolerate this nonsense any more, babu wanda ya isa ya gaya min yanda zanyi ko yanda bazan yi ba a gidana, it's my house not anybody's...." Ammi ta dakatar da shi tace "Ohh zagina da iyayena zaka yi akan Mayraah? No tell me zagina da iyayena zaka yi? Naga dai ba wani ya bani shawaran ince zan raini yarinyar nan har zuwa yau ba ko, ba kuma wani ya tursasa ni in riketa ba, sannan kai har kana da bakin magana yanzu? ka mance dauki ba dadin da muka yi da kai a kanta tana jaririya?" Abba yace "Duk wannan ke ta shafa, kuma baki isa saboda ke ko wani naki Mayraah taki zaman gidan nan ba, she remains in this house tunda ba gidan wani bane gidana ne, take it or leave it Hajarah babu inda Mayraah zata je...." Cikin tsawa Abba ya kare maganar, mikewa Ammi tayi tana wani murmushi tana kallonsa tace "Ohh i see, sai ka zabi ko ni ko ita, kuma tunda har aka billo min ta haka wllh wllh bazan ci gaba da zama da ita ba ko me zai faru kuwa, ai da can naga ba wani ya sa na zauna da ita ba, ynzun ma babu wanda zae sa ni in zauna da ita, don haka daga kai har 'ya yan naka da suka kai maka karata sai ku hadu ku zauna da Mayraah, su kuma su nemi wata uwar ba ni ba wllh" Daga haka ta juya fuuu ta wuce sama, Mama Ladi da ta sako da sauri jin hayaniya yayi yawa ta fashe da kuka tana kallon Abba bayan Ammi ta wuce sama tace "Kawai ka korata gida gun uwarta dake zugata su je can su karata Mamuda, ni dai ka gan ni nan babu ruwana bana goyon bayan rashin gaskiya tunda uwata ta haifeni wallahi" Abba da ransa yayi mugun baci ya juya kawai ya bar parlon, Maheer na jin duk yanda Abba suka yi da Ammi, likewise Mayraah dake gefensa, he never saw this coming, bai taɓa tunanin things will turn out this way ba, yasan Usman ne ya je ya samu Abba a part dinsa, ya kalli Mayraah dake ta kallon gate babu ko kiftawa, kawai ya jawota jikinsa, gathering every courage yace "Komai zai wuce Mimi" ta daga kai ta kallesa, sai a sannan ya ga hawaye a idonta, ya rungumeta lkci daya idanunsa suka kada shi ma, yana jin hawayenta na sauka jikinsa, cikin rawan murya yaji tace "Ina zan je yaya?"
_If you are reading this book without payment u owe me 500 till forever_
MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
*Wato idan kina neman turaruka masu musulmin kamshi, irin turaren nan da komin bacin rai dole ya narke yabi ruwa🫠 kiji kamar kinyi bargo da gajimare. Toh ki nemi Scentmania_by_sana by sana 07065525409 kawai kice ta baki 'The Empress combo'. Irin turaren dake sa maigida ya nemi shiri cikin gaggawa. In kinason kiyi activating din inner gimbiyarki👸🏽instantly wannan combo din shi ya dace dake.*
[7/3, 9:26 PM] Khaleesat Haiydar💖: Maheer was speechless and so weak, ya ma rasa me zai ce mata, lumshe ido yayi yana jin kukan nata har ransa, sai dai bai hanata kukan ba cause he want her to feel relieve ko yaya ne, sun fi minti goma zaune a wajen, ya dago kanta yana kallonta a hankali yace "Kiyi hakuri Mimi, komai zai wuce, u still remain our lil sis, we still remain together, babu inda za ki je, i know Ammi is not okay, bata san ta fadi duk maganganun nan ba" Kai kawai ta gyada masa hawaye na sauka idonta tana kallonsa, ya sa hannu ya share mata hawayen cikin sanyin murya yace "I assure you, that's not Ammi" ita dai kawai ta gyada masa kai, ya dagata suka tashi a wajen suka koma ciki, babu kowa Parlon ya wuce sama da ita zuwa dakinta, Mama Ladi na zaune tana tura bread dinta da kwai da sauri ga akwatinta a kusa da ita, tana ganin Maheer tace "Ina gama karyawa ka kai ni tasha Mashir, bazan iya ci gaba da zama ina kallon rashin imanin nan dake wakana ba, zan je ina da wani Malami a karaye, shi yake bani kaikayi koma kan mashekiya da dai itatuwan tsari, shi sa ka gan ni fess da ni da lafiyata, duk wanda yayi min mugun abu kansa yake komawa wllhi, to zan je in sanar masa abinda ke faruwa sannan ya taimaka yaga me ya samu er uwata Hajja, wa ya jefeta take abubuwa haka? don in na bar ta a haka wallahi wuta Allah zai ajiyeta, gwara in je tun wuri in nemo mata taimako, kai kana jin maganganun Ammi kasan zugota aka yi ba yin kanta ba, yaushe har bakinta ya bude zata yi wannan tabargazan, Aa wllh zugota aka yi kuma ba kowa zai zugota ba sai Hajja da tsinanniyar jikarta wanda sai ta kusa ajalinta, ke Hajja tsofe tsofe dake baza ki koma ga Allah ba sai kawai tayi ta hada bamm ke da jikarki Badiyya?? Ai ko zanje ko nawa ne in bada in ceto ta daga shiga wuta, ai ba kyau ace ina aljanna ita tana wuta, er uwata ce uwar mu daya ubanmu daya" Maheer dai bai ce ma Mama Ladi komai ba ya zaunar da Mayraah gefen gado yana kallonta cikin sanyin murya yace "Ki jira ni a nan" Ta gyada masa kai tana kallonsa ya juya ya