Showing 210001 words to 213000 words out of 249515 words
sai mu yi waya" Usman yace "To in sha Allah, thank you so much Dr" Dr Khalil yayi murmushi yace "You are welcome" Daga haka Dr Khalil ya koma gun Mayraah yace "Ki je ku tafi..." Ko rufe baki bai yi ba Mayraah ta fashe da kuka tace "Wallahi ni dai tsoronsa nake ji, na shiga uku" Dr Khalil ya buda ido yace "Saboda me?" Cikin kuka tace "Zai iya marina na sani, dama yaya Maheer ne" Dr Khalil yayi murmushi yace "Haba dai, ba abinda zai maki" Cikin kuka tace "Wallahi zai iya, me yasa ba Yaya Maheer bane ya zo" Juyawa Dr Khalil yayi ya kalli Usman da ya rungume hannu yana tsaye jikin mota fuskarsa babu yabo babu fallasa, komawa yayi wajensa yana ɗan murmushi yace "Barrister don Allah ayi mata hakuri, tace tsoro take ji zaka bugeta" Usman ya girgiza kai yace "Not at all.... Ka tambayeta ko na taɓa dukanta, she is waisting our time, muna da tafiya a gaba" Dr Khalil yace "To plss ayi hakuri barrister" Sai da Dr Khalil yayi da gaske da Mayraah sannan ta tafi ta shiga motar Usman, amma tana shiga sai ta wani tsuke fuska tana makale da handbag dinta, Usman ya kara yi ma Dr Khalil sallama sannan ya bude driver seat ya shiga ya tada motar, Dr Khalil ma ya nufi motarsa, har suka hau kan hanya bai ce mata ba ita ma bata ce masa ba.
[7/30, 8:07 PM] Khaleesat Haiydar💖: Mayraah na ganin sun kusa Suleja ta kallesa a karo na farko tana fidgeting fingers dinta a hankali tace "Don Allah yaya zan iya dauko jakana?" Ganin bai ce mata komai ba driving dinsa kawai yake, ta kauda kai bata sake cewa komai ba. A hankali Mayraah ta bude idonta daga baccin da ya dauketa ta gansu a cikin garin kaduna, gyara zama tayi da sauru ta tana kallonsa don ya maida mata kujeran baya yanda zata zama comfortable sanda take baccin, shi dai driving dinsa kawai yake pretending kamar bai ma san ta tashi ba, tun daga Abuja har zuwa yanzu da suke kaduna yaki ce mata komai, duk da almost half of the journey ma bacci take, wani hotel taga sun shiga bayan yayi parking ya bude motar ya sauka, babu bata lokaci ita ma ta sauko tana kallonsa ya kulle motarsa ya nufi cikin hotel din, ta wani tura baki ta bi bayansa, executive room ya biya masu, bayan ya amshi makullin dakin suka bar reception din, ita dai bin sa kawai take a baya har zuwa dakin, har cikin ranta take wishing dama Maheer ne, babban parlor ne da bedroom suka yi lodge in... Bayan ya ajiye wayoyinsa da car key ya cire agogonsa ya ajiye kan kujeran parlon Mayraah dai sai bin sa take da kallo tana turo baki, sai a sannan ya daga kai ya kalleta, ta sunkuyar da kai da sauri kamar munafuka, sai kuma ta ga ya nufi kofa har ya fita ya kulle kofar, a hankali ta karasa ta bude kofar bedroom din ta shiga ciki, bayan ta ajiye handbag dinta da wayarta ta koma parlon, sabulun da hotel din suka basu ta dauka ta shiga bandaki tayi wanka sannan dauro alwala ta fito ta koma daki, bayan ta idar da sallah ta rage Ac din dakin ta kwanta duk da yunwan da take ji don ko abincin rana bata ci ba, tana ta kwance taji an bude kofar dakin, kin juyowa tayi sai ma kulle ido da tayi da sauri don bata san me zai ce mata ba, sai taji yace "Fito ki dauki abinci" tana jin haka ta bude ido ta turo baki duk da ba ganinta yake ba sai kuma ta mike zaune tana murza ido tana kallonsa, juyawa yayi ya bar bakin kofar, ta sauka daga kan gado ta bi bayansa, Kallon ledan abincin dake kan table din gabansa tayi, sae taki karasawa ta dauka don ita fa bata yarda da wannan shirun da yayi mata ba, can ganin bai ce mata komai ba a hankali tace "Toh ni don Allah ka ajiye min kasa in dauka" Sae a sannan ya daga kai ya kalleta, tayi narai narai da ido ita ma tana kallonsa, gani take kawai planning din yanda zai wanka mata mari yake, tashi taga yayi ya bar wajen ya koma 3 seater ya zauna, tana tafiya a hankali ta tafi ta dau ledan ta koma daki tana satan kallonsa, shi kuma ya bi ta da kallo. Washegari da asuba Mayraah ta idar da sallah bayan ta gama azkar dinta har ta koma ta kwanta taji yayi knocking kofar dakin, ta mike zauna tana kallon kofar har ya bude, zamowa kasa tayi daga kan gadon murya can kasa tace "Ina kwana yaya" yace "Ban sani ba... dauko stuffs dinki mu tafi" Ta ɗan buda ido tace "Bazan yi wanka ba" Kallon da taga ya mata ya sa ta tashi da sauri ta dau handbag dinta da waya, ya juya ya bar bakin kofar ta bi bayansa tana duba wayarta dake nuna karfe shidda da rabi, check out suka yi daga hotel din bayan ya basu makullin dakin, ta bude front seat din motarsa ta shiga, bayan some minutes of warming up the car suka fita daga hotel din ya kama hanyar kano. Karfe tara suka shigo garin kano, Mayraah na ganin sun kusa gida haka kawai jikinta yayi sanyi, lokaci daya taji ta rasa sukuni, she don't know how everybody will accept her back, bata san ko Ammi will still welcome her back home ba, tunanin hakan yasa hawaye ya cika idonta ba tare da ta sani ba don kawai ji tayi yana sauka fuskarta, rufe fuskarta tayi da hijab dinta tana shessheka, Usman ya kalleta yana ci gaba da tukinsa yace "Ohk in maida ki Abujan kenan?" Cikin kuka tace "Aa" Yace "To me ya faru?" Ta fashe da wani sabon kukan tace "Ban san ko Ammi..." Kasa ci gaba tayi saboda kuka, Usman yayi kasa da murya yace "Ammi missed you, since you left she is not fine" Mayraah ta daga kai ta kallesa hawaye na sauka idonta, bai sake ce mata komai ba har suka shigo anguwan, yana horn bakin gate mai gadi ya bude gate din da sauri, ya shiga ciki yayi parking a garage, Bayan ya kashe motar ya juya ya kalli Mayraah da ta fada duniyar tunani, yace "I hope u will never repeat such mistake again" Ta juya a hankali ta kallesa sai kuma ta gyada kai, a hankali yace "Abba was there for you, i was there for u, so was Doctor but u decided to follow ur heart that lead you astray" Cikin rawan murya tace "I am sorry" bude motar yayi ya sauka, amma ta kasa bude motar ta fito duk jikinta yayi sanyi wasu sabbin hawayen na zuba idonta, zagayowa yayi ya bude mata kofar yana kallonta, sunkuyar da kai tayi ta sauka ya nuna mata entrance din gidan yace "Mu je" Babu musu ta fara tafiya tana share hawayenta gabanta na faduwa, tsoro take kada Ammi taki ce mata komai, she don't think zuciyarta zai iya daukan hakan, yana biye da ita a baya har suka iso entrance din shiga parlor, ta kasa bude kofar ta juya ta kallesa har sai da ya karasa gabanta ya bude kofar bai shiga ba ya juya yana kallonta, muryarta na rawa tace "I am afraid" Yace "U need not to be, everyone misses u badly" Ta gyada masa kai tana goge idonta, yace "Shiga..." Ba musu ta wucesa ta shiga parlon ya bi ta da kallo, Mayraah na shiga parlon tayi ido hudu da Haseenah dake tsaye kofar kitchen tana jiran sabon mai aikin Ammi ta bata irish din da taji tana soyawa wai ita bazata iya girki ba, Sake baki Haseenah tayi tana kallonta, Mayraah ta dauke idonta ta kalli direction din stairs jin kamar ana saukowa, Maheer ne ke saukowa tare da Ammi yana ce mata "Gaskiya Ammi i am only doing this because of you, but it's stressful for me, menene yasa baza a sa ta a mota ita ma ta tafi kadunan ba...." Ido hudu yayi da Mayraah dake kallonsa babu ko kiftawa, ai bata san sanda ta nufesa da gudu ta rungumesa ba ta fashe da kuka, murya can kasa as if bai yarda ita bace yace "Mimi??" Haseenah tayi saurin dauke kai bayan ta saki wayarta dake hannunta ba tare da tasan ma tayi hakan ba, juyawa Usman yayi bayan ya dauke kai ya fita daga parlon, Ammi ta kasa motsawa daga stairs din da take tsaye, hawaye na zuba idon Mayraah ta rufe fuska a kirjinsa tayi karfin halin cewa "I missed you so much yaya" as if whispering yace "Why did u leave just like that Mimi?" Ido hudu tayi da Ammi dake tsaye hawaye a fuskarta ta kasa saukowa downstairs din, Mayraah ta sauke idonta kasa... Zame jikinta tayi daga na Maheer ta daga kai tana kallonsa kamar yanda shi ma yake kallonta babu ko kiftawa, he is just hoping this is not one of his everyday dreams, har sannan hawaye bai daina sauka idon Mayraah ba, kawai tayi gathering courage ta tafi wajen Ammi, Ammi na ganin haka ta fashe da kuka sosai, Mayraah ta rungumeta cikin rawan murya tace "Don Allah kiyi hakuri Ammi, ban san yanda zan yi ba ne..." Haseenah bata san sanda ta fita daga Parlon ba tare da ta amshi irish din da take jira ba ta koma Chalet. Mama Ladi da ta fito daga bangaren Ammi cike da masifa tana cewa "Haka kawai ba dangin iya ba na baba wannan wahala haka, o'o wallahi bazan iya ba don nayi ma kaina fada na daina shiga abinda bai shafeni, ga daki can an bar mata ban san me yasa take biyo mu nan tayi ta mana kazanta tana cutata ba...." Komawa baya Mama Ladi tayi da sauri tana gwalo ido bayan ta hango Mayraah tace "Wacece wannan kuma?" Sai a sannan Mayraah ta sake Ammi ita ma tana kallonta, Mama Ladi ta rike haɓa tana gyada kai tace "Ba shakka!! to ina iyayen naki da suka jefa ki a kwata kina jaririya? Inji dai tare ku ka dawo da su?" Mayraah ta sunkuyar da kanta, Mama Ladi tace "Amma wallahi ke kam da ba don kada Ammi ta kullaceni ba sai ince butulu ce ke me manta alkhairi, haka kawai kika kama hanya kika shiga duniya kika bar mata da hawan jini mu kuma kika bar mu da rashin isasshen bacci kullum cikin tunaninki da alhinin bacewarki, Sannan yanzu ba kunya ba tsoron Allah galau galau kin kwashi kafafuwa kin dawo ke kadai, ni fa duk tunanina tare ai za ku dawo da iyayen naki tunda baki da mutunci kiri kiri kin nuna ai babu abinda kika hada damu, duk abinda muke maki kika rufa ido kika ci mana mutunci, haka nayi kwana biyu a asibiti wajenki ko runtsawa ban yi ba ga yunwa, amma baki gani ba sai da kika zalunce mu kika daga mana hankali, Mamuda ya dawo kamar wani zautattce wani lokacin takalmi wari wari yake sa wa ya fita, duk caji opis din kano babu wanda bai tafi ya kai cigiyarki ba, mu dai Allah ya isa rashin cin abinci da wadatattcen bacci da kika janyo mana" Tuni Ammi ta kama hannun Mayraah suka bar wajen, Mama Ladi ta bi bayansu still. Tun da Mayraah ta shigo parlon Ammi take kallon Badiyyah dake kwance kasa tayi wani bakikirin kamar bata taɓa haske a rayuwarta ba ga wasu uban kuraje da suka cika mata fuska, Mayraah ta zauna kan kujera don Ammi da take son tambaya ko Badiyyar bata da lafiya ne tuni ta fita daga parlon, kasa daurewa Mayraah tayi tana kallon Mama Ladi tace "Mama bata da lafiya ne?" Mama Ladi tace "Wa? Wai Badiyyah? Ai Badiyyah cikin shege tayi in baki labari Mera, cikin shege dai da kika sani" Tsabar shock Mayraah bata san sanda ta mike tsaye ba, Mama Ladi tace "Aa koma ki zauna ba wani batun rikicewa don kema bamu san daga inda kike ba yanzu haka" Mayraah ta dinga kallon Mama Ladi babu ko kiftawa, Mama Ladi na kakkabe kujeran da taga Badiyyah ta zauna dazu tace "Hajja dai in gaya maki ta sallama ma duniya Badiyyah tace ko sunanta aka kira mata bata yafe ba, ta mata Allah ya isa yafi cikin kwando, ko ido suka hada sai ki ga Hajjan ta fara tari kamar zata shide yanzu haka zancen da nake maki Hajja tana can gidan Yahanasu a kaduna, sai kin ga gidan ko kiwon kare baza ayi a gidan nan ba don sai cuta ta kama karen ya mutu a banza, ni dai tun da na rakata ko minti sha biyar banyi cikin ɗan kuturun gidan ba na gudu gidan Mariya tunda dai abinda ya faru ba wai ya shafeni bane kawai zumunci nake dubawa, banda ma na kai zuciya nesa ai da sai dai ki dawo ki ga na canza wani pamilyn, don wannan pamilyn namu dai ba pamilyn nuna ma duniya bane, pamilyn mu ya zama barbadadden pamilyn, Badiyyah ta lalata mana Pamily kawai sai dai muce Allah ya isa, gidan Mariya da na gudu in samu sauki can kuma yanda kika san kasuwar kurmi tunda babban gida ne uwar mijin da uban mijin duk suna ciki da bataliyarsu, wannan karen ya shigo, wancan dokin ya fita haka dai abun ba tsari, ke in takaice maki washegari da asuba nasa aka kaini tasha na hau mota na dawo kano inda na fi wayo, to shine sabida rashin tsoron Allah aka makala ma baiwar Allah Ammi Badiyyar take ta fama yanzu haka, banda ma Mamudan mutumin kirki ne ina zai yarda wannan annobar ta zauna masa gida ta lalata masa tarbiyyar yaransa maza, ai da muna da yan uwa a kauye kyan Badiyyah kawai a turata can har sai ta haihu ta zauna tayi renon shegen a can, to bamu da kowa a kauye, Mamudan ma fa da farko kin amincewa yayi yace a fitar masa da ita daga gidansa, to kin dai san Abban naku da shegen tausayi ga kuma tausayin matarsa da yake, a haka dai daga karshe yace a kyaleta ta zauna amma ko nan da gate baya son ta je kada yan anguwa su sa shi a bakin duniya suce ga me cikin shege a gidansa, kiri kiri Mariya taki tafiya da ita aka bar Ammi da wahala, Allah dai ya isa kawai" Mayraah sai kallon Badiyyah da hawaye ke sauka idonta kawai take, kullum sai tayi kuka kamar ranta zai fita a gidan saboda Mama Ladi, da kyar ma in Mama Ladi bata daura mata depression ba saboda bad mouth dinta, Mama Ladi tace "Don haka kike baya baya da ita, mu ma duk baya baya muke da ita gaskiya, mu a zamaninmu idan mutum yayi cikin shege ma rataye kansa kawai yake ya mutu, ko kuma ya gudu ya bar garin sai bayan shekara hamsin, to ita kinga ai taki yin ko daya" Bude kofar parlon aka yi Ammi ta shigo da breakfast ta kawo ma Mayraah, ko bata bude baki tace komai ba kasan tana cikin farin ciki mara misaltuwa, she looks so happy wanda duk wanda yasanta yasan rabonta da wannan farin cikin an kwana biyu, Usman really took she and Maheer unaware don duk abinda yake yi bai gaya masu ba, Mama Ladi ta bi ta da kallo har ta ajiye tray din hannunta tana kallon Mayraah tace "Taho ki karya daughter" Mama Ladi ta rike haɓa tace "Yanzu tun safe in tashi ko ruwan shayi da ke da shegiyar sabuwar me aikinki baku bani ba sai wannan mata da bamu san daga inda take ba zaki kawo ma tray guda na kumallo jikinki na ɓari? Ni da na kwana gidan baki ban komai ba sai warce bata kwana ba?" Ko kallon Mama Ladi Ammi bata yi ba sai ma daukan tray din da tayi ta wuce dakinta da shi tace "Taho Mimi" Mayraah da duk jikinta yayi sanyi da halin da Badiyyah ke ciki ta share hawayen idonta ta bi bayan Ammi tana tafiya a hankali zuwa bedroom dinta. Ammi da kanta ta hada mata shayin ta debar mata komai sannan ta koma ta zauna tana kallonta, Mayraah ta daga kai tace "Ammi Abba fa?" A hankali Ammi tace "Na kirasa yana hanya" Mayraah ta dau shayin da Ammi ta hada mata ta fara sha, Ammi ta mike ta fita daga dakin zata je kai ma Mama Ladi nata breakfast din, Ammi na fita babu dadewa Maheer ya shigo dakin, Mayraah ta daga kai tana kallonsa har ya iso inda take ya duka yana kallonta, ta sauke idonta tace "In hada maka shayin kai ma?" Ya sauke boyayyen ajiyar zuciya yace "Ki rage min kawai" Tace "Sai mu sha tare..." Zaunawa yayi saman darduman yana facing dinta, bayan ta kurbi shayin hannunta ta mika masa, ya amsa ya kai baki, ita kuma ta fara cin irish din da Ammi ta zuba mata da ketchup da kwai, Ya ajiye cup din shayin bayan ya sha a hankali yace "Me yasa kika tafi Mimi?" Bata yarda ta dago kai ta kallesa ba cikin sanyin murya tace "That's bygone yayana" Ya gyada mata kai kawai still looking at her, bayan few seconds tace "Baza ka ci irish din ba?" Dauka yayi ya fara ci, ta dau cup din shayin ta sha kadan ta ajiye, daga kai tayi suka hada ido, yace "I missed you Mimi" Ta ɗan yi murmushi tace "I missed you more" A haka Ammi ta shigo dakin ta samesu, Ammi na kallonsa tace "Ba ga can naku an kai maku ba?" Mayraah ta kalleta tace "Ammi ni ce nace ya ci" Shi dai murmushi kawai yayi, Ammi ta zauna gefen gado still looking at them.
[7/31, 7:19 PM] Khaleesat Haiydar💖: Mayraah na gama yin breakfast ta shiga yin wanka bandakin Ammi, Maheer kuma ya fita da tray din da suka yi breakfast din