Showing 240001 words to 243000 words out of 249515 words
kuma yake tambayar me ya sameta, yana fahimtar Asthma ne ya fara mata abinda ya kamata a wajen, cikin kankanin lokaci ya dauko pills a show glass ya bude ya dau bottle water dake kan table ya bata, with his help ta hadiyi pill din, they were there for almost 15 mins yana kokarin calming dinta har ta fara sauke numfashi a hankali, MD was just standing like a quack Dr a wajen with no help, Dr Balogun ya dinga mata sannu, bayan some minutes yace "Are you okay now?" Ta daga idanuwanta da suka kada, duk da azaban da kirjinta ke mata ta gyada masa kai, yace "Ok now duk ward din da kika ga babu kowa a nan sama kije ki kwanta, get some rest" Tayi karfin halin mikewa tsaye Dr Balogun ya bata hanya yana mata sannu, tana fara tafiya ta ji kanta na juya mata tayi baya zata fadi, kafin ta kai kasa MD yayi saurin riketa, Dr Balogun yace "Her Bp is low" kwantar da ita MD yayi kan examination bed dake office din nasa, Dr Balogun na kallonsa yace "Akwai coffee powder ayi making mata coffee ta sha?" MD ya dauko Tea cup dinsa yana wankewa sau daya ya kalli cikin cup din keenly, kafin yayi attempting sake komawa ya wanke Dr Balogun ya amshi cup din yace "I will do it..." Cikin mintuna kadan yayi making coffee a cup din ya mika masa yace "I have a patient in my office... I will be back idan na sallamesa yanzu" MD ya amshi Coffee din ya juya yana kallon Mayraah da idonta ke a rufe, Dr Balogun ya fita daga office din da sauri don dama tambaya ya shigo yayi masa....
[8/8, 8:54 PM] Khaleesat Haiydar💖: Mayraah na sauka second floor ta hadu da Dr Khalil ya fito office dinsa da wasu files, yana ganinta ya nufo ta da sauri yace "How are you feeling now?" Ta gyada masa kai a hankali tace "Alhamdulillah, i am better now" yace "Ina za ki je?" Tace "Driver yana jirana a waje" Yace "Did he ask you to go home?" Ta gyada masa kai, yace "Alright, Allah ya kara lafiya" Tace "Ameen, Nagode" Downstairs suka sauka a tare, ta tafi ta dauka handbag dinta tayi ma Nurse Hafsat sallama sannan ta bar asibitin, tana isa gida Ammi dake parlonta suna waya da Aunty Mariya ta kalli agogo sannan tayi ma Aunty Mariya sallama ta mike tana kallonta da mamaki tace "Naga kin dawo da wuri" Mayraah ta kalli agogo dake nuna karfe biyu tace "Bana jin dadi ne" Ammi ta nufeta da sauri tana taɓa jikinta tace "Subhanallah, me ya sameki? Since when?" Mayraah tace "I had an attack daxu da safe" Ammi ta zaunar da ita kan kujera da damuwa tace "Garin yaya?" Mayraah ta sauke ajiyar zuciya tace "Ina jin wajen kamar akwai ƙura ne, ni kuma ban sani ba, amma ai naji sauki yanzu, an bani magani na sha after sometime na dawo normal shi ne har nayi bacci" Ammi tace "Toh Allah ya sauwake, but duk in kika ga wajen da zai iya accommodating dust ki dinga saka nose mask Mimi, ki daina fita babu shi kin ji?" Mayraah tace "In sha Allah Ammi" Ammi tace "Bari in kawo maki abinci, kin yi sallah?" Ta gyada kai tace "Nayi" Ammi ta mike ta fita daga parlon zata je kawo mata abinci, Mayraah ta jinginar da kanta da kujera, bayan wani lokaci wayar Ammi ya fara ring, Mayraah ta mike tana kallon wayar ganin wanda ke kiranta ta karasa inda wayar yake ta dauka sannan tayi picking ta kai kunne, sallama yayi ta amsa, a hankali tace "Good afternoon" Daga daya bangaren yace "Are you okay?" Murmushi tayi tace "Me yasa ka tambaya?" Yace "I sense that from ur voice, baki da lafiya ne?" Tace "Asthma dina ne ya tashi a asibiti" Yace "Subhanallah, how did that happen?" Tace "I am very fine now, naji sauki sosai, yaya hope dai ka gama shiryawa? Kasan friday din ya kusa fa" Yace "Sure, Allah ya kai mu lafiya" Tace "Ameen" Yace "Kin sha magani amma?" Tace "Eh an ban a asibiti" Yace "Toh Allah ya sauke, be careful plss Mimi always go around with ur nose mask to avoid such issues" Tace "To yaya" Yace "Ammi fa?" Tace "Taje kitchen" Yace "Ohk, i will call her back later, go and get some rest Mimi" a hankali tace "Bye" Washegari Wednesday Dr Khalil na office dinsa bayan fitar wata patient MD ya shigo, Dr Khalil ya daga kai yana kallonsa har ya karaso ya zauna yace "I just finish speaking with Ceo, tana son zata yi magana da yarinyar nan, kaga daga common Asthmatic attack jiya shine tayi taking advantage taki zuwa aikin yau, who does that pls, idan nayi magana kace i am not being considerate..." Dr Khalil yace "Sai kace mata bata da lafiya mana..." MD yace "To dama idan ba haka ba me kake son in ce mata, imagine ceo fa, yarinyar da common workshop a lagos bata kai a fara zuwa da ita ba shine take tambayar ko tana da international passport, for what? ni ban ma san yanda zan mata bayani cewar ba a bisa ka'ida aka dauketa aiki a asibitin nan ba, idan ba ayi hankali ba fa sai ceo tace da ita za aje conference din nan" Dr Khalil yace "Nan din ba bakin ciki zaka mata sir? Tun da kaga haka ceo din is gradually becoming fond of her, jininta ya hadu da ita ne, kai ne har yanzu ka ki kwantar da hankali ka lura how lovely the pretty girl is ba" MD yace "And how will dat add any impact to my life? That is not my problem Khalil, yanzu cewa tayi a kira ta a tambayeta ko tana da international passport, and i should feed her back immediately" Kallonsa kawai Dr Khalil yake, MD yace "So now after some minutes i will call and tell her tace bata da international passport..." Dr Khalil ya jawo wayarsa yayi dialing number yana fara ring ya sa a handsfree, ba a dau lokaci ba aka daga, murya can kasa tayi sallama, her voice was so cool and calm, MD ya masa wani kallo ya mike amma sai bai fita ba, Dr Khalil ya amsa gaisuwar da tayi masa yace "Ya jikin?" Tace "Alhamdulillah" Yace "Me yasa baki zo aikin yau ba" Ta ɗan yi shiru, sai kuma a hankali tace "I am still recovering, kuma ni bana son a dinga min masifa anyhow" Dariya ta ba Dr Khalil, MD ko ya gyada kai bayan ya ji me tace, Dr Khalil yace "To wa ke maki masifa Mayraah?" Tace "MDn ku mana, he is always finding fault where there is none, ko gajiya baya yi da fada, energy da yake sakawa a fada da ma a field dinsa yake sakawa da ya fi, kuma gwara ni ranan allura ne kawai na ɗan zama confuse da zan ma yarinya, shi kuwa a whole asthmatic patient a gabansa babu abinda ya iya yi, just going up and down like a student, i nearly thought him to be quack wallahi, ko ni da nake nurse bazan yi haka ba...." Dr Khalil ya cire wayar a handsfree da sauri laughing out loud, kallon wayar MD ya dinga yi babu ko kiftawa, yana ganin Dr Khalil ya cire a handsfree ya fizge ya mayar handsfree din, Mayraah tace "It's not funny fa, na dade ina mamaki da na dawo gida jiya, ko level 4 student a medicine bazai yi abinda yayi ba" Dr Khalil yace "To ai shikenan, a takaice dai kin fi sa sanin aikin likitanci kike nufi kenan?" Without thinking twice tace "Na fi sa composure a aikin, may be because i don't shout and Nag" Dr Khalil na dariya yace "To sai anjima, zan kira ki" Tace "Ohk" MD ya dinga kallon wayar hannunsa, ita kuwa ganin Dr Khalil bai katse ba sai ta katse kiran, MD ya ajiye masa wayar kan Table a takaice yace "Call her back tayi providing International passport dinta gobe" Dr Khalil yace "Aa kai da kace...." MD ya katse sa yace "Instruction din da Ceo ta bani kenan, don haka kayi abinda nace maka" Yana kai wa nan ya fita daga office din, dariya kawai khalil yake don har cikin ransa yaji dadin maganganun da Mayraah tayi a kan kunnensa, shi kansa jiya da Dr Balogun ke basa labari yayi mamaki, MD da ko shure shuren mutuwa mutum yake calmly yake masa abinda ya kamata as a medical Dr amma just common Asthmatic attack da ya sameta jiya ya kasa taɓuka komai ya dawo kamar learner, to in ba rami me ya kawo rami, daukar wayar yayi ya sake kiran Mayraah bayan ta daga yace "Kina da international passport?" Ta ɗan yi shiru, sai kuma tace "Eh" Yace "In za ki shigo gobe sai ki taho da shi" Da mamaki tace "Why?" Yace "Ceo ce ta ce a sanar maki haka" Mayraah was a bit confused, ta ma rasa tunanin da zata yi, to me za ayi da passport din nata, sallama Dr Khalil yayi ya katse wayar. Washegari da taje asibiti har rana MD bai shigo ba, tun da safe ta kai ma Dr Khalil passport din nata, wajen karfe biyu suka shiga theatre za su yi wani aiki da Dr Balogun da Dr Khalil, tana kokarin saka nose mask before putting on her sterilized hand gloves kamar ance ta juya suka yi ido hudu da MD, dauke kai tayi don bata ma san ya shigo ba and she felt unhappy after realizing tare da shi za ayi aikin, yawanci aikinta a Operation theatre bai wuce ta dinga mika Sterilized Instruments ba sai kuma suture, MD zata dinga mika ma Instruments din kamar wancan ranan, tana mika masa abinda ya bukata na farko suka hada ido sai kawai ya fadi daga hannunsa, wata nurse ta dauko wani Sterilized Instrument din da sauri ta kawo masa, sau hudu suna haka da shi, it is either idan zai maido mata sai ya fadi a hannunsa, ko kuma idan ta mika masa zai amsa sai a samu matsala, ita dai she is calm, Dr Khalil ya dawo inda Mayraah take yayi kasa da murya yace "May be u are tired, just go, nurse Sadeeya will continue...." Ta dan kallesa a ranta tace ko dai MD dinku is tired, duk fa sun ga shi ke contaminating Instruments din not her, daga hannunsa suke faduwa ba nata ba, juyawa tayi ta bar wajen, karfe shidda saura driver dinta ya zo ya mayar da ita gida. Ranan friday da yamma Maheer ya iso daga kano via flight, Mayraah was so happy seeing him don ita da driver ne ma suka je airport tarbo su, yana gama gaisawa da Ammi ta kai sa wani daki dake parlor da damuwa tace "Yaya naga ka rame, what's happening?" Yace "Aiki mana, kema nan da kwana kadan zaki ga kin rame ba dai kin fara aikin ba" Mayraah bata yarda ba, ta dinga insisting ya gaya mata what the problem is, Haseenah dai tafi minti ashirin zaune ita kadai a parlorn, Ammi da ke kitchen tana karasa girkin da take ta fito Parlon ganinta ita kadai ta nufi dakin da Mayraah ta kai Maheer, Ammi kanta wasn't happy with how she saw Maheer, tana kallonsu tace "Ka tashi ga chalet din can a bude yake, kun bar ta ita kadai parlor, ya kamata taje ta huta ita ma, Mimi zata kai maku abincin yanzu" Shi gaba daya ya ma mance da wata Haseenah, bayan some minutes ya mike ya fita a dakin. Bayan minti sha biyar Mayraah ta kai masu abincin Chalet, Yana bedroom Haseenah kuma na zaune parlon ta bi ta da ido har ta ajiye abincin sannan ta fita... Ammi na zaune parlonta da Maheer sai Usman dake danna wayarsa, da damuwa tace "Gaskiya ni dai hankalina bai kwanta ba kwata kwata, yaushe ma ta fara aikin ta samu full experience har matar zata ce xa aje conference da ita England? Ina manyan likitoci da Nurses din asibitin, aa gaskiya bazata ba" Maheer ya sauke ajiyar zuciya yace "Kai ya ka gani Barrister?" Sai a sannan Usman ya daga kai ya kallesu yace "It's weird gaskiya, daga fara aiki ko sati biyu bata yi ba a kawo maganar fita waje, irin wannan tafiyar ai da experienced staffs ake zuwa" Maheer yace "Haka ne, nima kuma nayi mamaki" Ammi da hankalinta ya tashi tace "Ni gaskiya aikin ma sai a bari, kuma fa matar ba musulma bace, gwara a samar mata a wani waje kawai ta hakura da wannan" Murmushi kawai Maheer yayi, Ammi tace "Abbanku da na dawowa yau zan gaya masa, aikin ya fita kai na gaba daya wallahi" Mikewa Usman yayi ya fita daga parlon, Ammi ma ta mike tace "Kasan zan yi bakuwa bari in je in ga ko me aikin ta gama abinda na sa ta" Yace "Ohk" Ammi na fita parlon Maheer ya mike ya tafi dakin Mayraah. Kusan karfe uku Hajiya Maimuna mahaifiyar Haseenah ta iso gidan, tun da ta shigo hankalin Haseenah ya ki kwanciya, kawai dai tana zaune parlorn ne tana yaken karfin hali, Ammi ta tarbeta sosai suka gaisa da fara'a, Mayraah ta kawo mata abincin da aka mata, Hajiya Maimuna tace "Kawai na ce ko a gurguje ne in zo in ga gida kafin in koma kano, gida kam Alhamdulillah yayi kyau Allah ya sanya alkhairi, Allah ya sa rai aka yi ma" Ammi tace "Ni da na zata kwana za ki yi Hajiya?" Hajiya Maimuna tace "Ai daga gidan nan airport zan tafi, biki muka shigo tun ran juma'a wallahi, to nayi niyyar zuwa jiya asabar sai Allah bai yi ba sai yanzu" Ammi ta sauke ajiyar zuciya tace "Toh amma ai za ki ci abinci Hajiya" Hajiya Maimuna tace "Wallahi na ci abinci kafin in fito, Alhamdulillah" Ammi tace "Da kika kirani dazu da safe har nake tunanin in kin zo akwai maganganun da za mu yi Hajiya" Sosai gaban Haseenah yayi mugun faduwa jin abinda Ammi tace, Mayraah dai na zaune parlon ita ma, Hajiya Maimuna tace "Flight din na dare ne Hajiya, ko yanzu za mu iya maganar, Allah dai ya sa lafiya" Ammi ta ɗan yi murmushi, sai kuma tace "To gaskiya ba lafiya ba Hajiya" Hajiya Maimuna tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, ina ji Hajiya" Haseenah ta mike zata bar parlon, Ammi tace "Aa ki dawo ki zauna Haseenah" Sunkuyar da kai tayi ta koma ta zauna, Nan Ammi ta fara yi ma Hajiya Maimuna bayanin duk abinda ke faruwa bata boye mata komai ba, Daga karshe Ammi tace "Nasan kin san wasu maganganun nan wasu kuma ba lallai ki sani ba... To kin ji abinda ake ciki Hajiya" Hajiya Maimuna da ta kasa dago kanta sai zufa take bayan few seconds, tace "Amma baki kyauta min ba Hajiya, wallahi baki kyauta min ba, yanzu duk abubuwan nan su faru babu wanda ya sanar min, na kwanaki ma da tayi dambe da kawarta Badiyyah banda ta kira kannena suka je suka yi rashin mutuncin da suka yi babu yawuna wallahi ban sani ba Hajiya, ban san komai ba, yanzu ni Haseenah zata tona ma asiri ta kunyata ni a idon duniya duk zatona tana zaune lafiya gidan mijinta?" Sai kuma ta fashe da kuka ta mike tace "To wallahi Allah ya isa tsakanina dake Haseenah, kin cuceni don sai ace tarbiyar da na maki kenan, bayan Allah na gani nayi iya bakin kokarina ganin na maki tarbiyyar da ya kamata dai dai gwargwado" a fusace ta rufeta da mari ta ko ina tana zaginta, Ammi ta rikota da sauri tace "Aa Hajiya ba sai kin doketa ba, don Allah kiyi hakuri...." Hajiya Maimuna na huci tace "Wallahi dama in ta kashe auren ta nemi gidan wata uwar ba ni ba, kar ta kuskura ta nufo inda nake, da dadi ba dadi haka nayi hakuri a gidan ubanta har mutuwa ta rabamu ban taɓa yaji ba wallahi komin tsanani kuwa, shi kuma Maheer saboda me zai zauna yana hadiye wannan takaicin ya kasa sama ma kansa mafita ya kara aure tunda Allah ya rufa masa asiri, Kishiya kawai zai mata ya tattara ya koma wajen amaryar, kai ni ko yanzu ya saki Haseenah bazan ce masa don me ba don naga kokarinsa ya kuma nuna shi cikakken namiji ne, ina kuma me bashi shawara ya kara aure cikin gaggawa don huce wannan takaicin" Ammi tace "Yanzun ka akan maganar auren ake, don bazan boye maki ba aure xai kara nan ba da jimawa" Hajiya Amina tace "Toh maa sha Allah, Allah Ubangiji ya masa albarka wallahi" Kuka kawai Haseenah take kamar ranta zai fita bayan ta gudu bayan kujera, Hajiya Maimuna ta dau jakarta tana kallon Ammi tace "Duk hukuncin da ku ka ga ya dace ku yanke a kanta ni babu abinda ya sha min kai, ko me ku ka yi dai dai ne wallahi, kuma nayi da na sanin haihuwar Haseenah" Kofa ta nufa tana huci, Ammi ta bi bayanta tana kokarin dakatar da ita Hajiya Maimuna tace Airport zata kawai, a haka ta bar gidan ko minti daya bata kara ba, babu abinda ya tsaya ma Haseenah a rai take kukan da take sai auren da Mumynta tace Maheer ya kara har Ammi na cewa nan ba da dadewa ba zai yi auren, wato nan ba da dadewa ba zai auri Mayraah don karshenta kenan, kuma tayi mafarkin aurensa da Mayraah yafi a kirga a yan kwanakin nan, goge hawayenta tayi ta fita daga Parlon ta ɗan yi murmushi ta nufi chalet. Da daddare Maheer na parlon Ammi bayan ya gama sauraronta yace "Amma dai don Allah Ammi me yasa za ki ma mahaifiyarta wannan maganar, sulhu ma nake nema da ita kenan? Ni fa Ammi na gama zama da Haseenah wllh tllh, duk wannan maganganun da kika yi ma mahaifiyarta ba shi da amfani