Showing 225001 words to 228000 words out of 249515 words
bayan ta ci kukanta ta gode Allah tace "Toh ma sai kace wata gantalalliyar tsohuwa mara makabuli ina ni ina bin ku wani Habuja, sai kace ban san me nake ba da zan kwashi kafa in bi ku kamar a garin gaɓa gaɓa, ai da wayo na kuma ni ba mahaukaciya bace nasan me nake, amma abinda yayi min ciwo har na zubda hawaye dalilin da zai sa Mamuda yace in dauki Badiyyah mu tafi karaye, a dubi girman Allah a gaya min me na hada da Badiyyah da Mamuda zai ce min haka? To wannan cin mutuncin da yayi min shi ya min ciwo har nake ta kuka amma ba wani abu ba" Ammi dai dake zaune parlon ta sauke ajiyar zuciya bata ce komai ba, Mama Ladi tace "Kuma a gaskiya ni ba a taɓa ci mun mutunci irin yau ba ma tunda uwata ta haifeni, wai in tafi da Badiyyah karaye ashe ma ni na mata cikin, to wallahi ki ja masa kunne ya fita harkata ya bar hada ni da Badiyyah, babu abinda na hada da ita haduwar bariki rabuwar bariki, kakarta ce fa yayata amma ko a lahira ni bazan ga Badiyyah ba, in zuciyata ta debeni sai in iya ja masu Allah ya isa daga Mamudan har shegiyar Badiyyan da yake hada ni da" Daga haka tayi kwanciyarta tana matsar wasu sababbin kwallan tace "Dama da asussuba Mashir ya zo ya kai ni tasha, maganina ma kenan da nayi ta zama nan kamar wata mara galihu" Ammi tace "Kiyi hakuri Mama Ladi duk bai kai...." A fusace Mama Ladi ta mike zaune tace "Rufe min baki, ke da kika ji yana cewa in koma karaye baki da bakin magana ne? Ni na cancanci Mamuda yayi watsi da ni? Da ba don ni ba ai gidansa fanko ya so komawa amma ɗan Adam me mance alkhairi, kullum fa sai an bugo min waya daga karaye ana tambayar Baaba ladi yaushe za ki dawo, da gata na kaca kaca a can, to kafin ku tattara ku koma Habujan ni gobe da Asuba zan bar gidan, kuma ki mayar masa da shegen kudinsa da ya bani bana bukata, ban rasa komai ba a karaye wallahi" Daga haka ta sake komawa ta kwanta tana matsar sabbin kwalla, Mikewa Ammi tayi ta shiga bedroom dinta don for almost an hour Mama Ladi ke ta mita da koke koke ita dai hakuri kawai take bata, wajen karfe sha daya da rabi ta sake fitowa parlon rike da wayarta ta ga Mama Ladi kwance ido biyu, Mama Ladi da bata wuce karfe tara da rabi da ta ci ta koshi take bacci, Ammi dai bata ce mata komai ba ta fita daga parlon ta sauka downstairs, Maheer ta ganin kwance kan 3 seater idonsa rufe, Ammi ta karasa kusa da shi ta taɓasa tace "Maheer" Bude ido yayi, ya mike zaune tace "Baka tafi ka kwanta ba kake bacci a nan" Ya kalli agogo sannan ya mike zaune, Ammi ta zauna daga side dinsa tana kallonsa tace "Ka ci abincin ma kuwa?" Yace "Na ci" Sai kuma ya mike yayi mata sai da safe ya nufi kofa ta bi sa da ido har ya fita, Number Aunty Mariya ta fara dialing sanin mijinta baya gari, yana fara ring kuwa ta daga, tace "Baki yi bacci ba Ammi" Ammi tace "Ban yi ba" Aunty Mariya tace "To ya gidan? Ya su Mayraah?" Ammi tace "Alhamdulillahi" Shiru Aunty Mariya tayi tana sauraren dalilin kiran Ammi don tasan tunda ta kirata by this time akwai magana ne, Ammi ta sauke ajiyar zuciya ta sanar ma Aunty Mariya abinda ake ciki, Aunty Mariya tayi farin ciki da samun aikin Mayraah da kuma garin Abuja da za su koma, she was so happy, tace "To yanzu Ammi ya za ayi da Mama Ladi?" Ammi tace "Mama Ladi? Badiyyah dai.... tambaya za kiyi ya za ayi da Badiyyah tunda ita Mama Ladi tana da inda za ta, Shi kuma yace babu inda za aje masa da Badiyyah, i am confuse ban san ya zan yi ba kuma" Aunty Mariya tayi shiru, can ta sauke ajiyar zuciya tace "Amma dai Ammi shawaran da aka yanke tun farko shine a kai ta Bichi...." Ammi tace "To bari kiji tunda na kirasu na sanar masu abinda ke faruwa buden bakin shi yayan baban nata wai sun kwana biyu su basa Bichin sunyi tafiya, ita kuwa autarsu baban nata ita ma da na kirata bayan kwana biyu ce min tayi tana wajen mijinta a portharcourt yaranta ma na gun kakarsu, Kinga ai sun hada baki kenan, ni kuma gaskiya ban wani ga laifinsu ba, babu wanda zai karbi Badiyyah ko waye ma haka zai yi, ko don na bar zancen ban gaya maku ba? ita kanta Mama Ladi bata san yanda muka yi da yan Bichin ba ai har yau, to yanzu ga abinda Mai gidan yace i don't want to have any issues with him, don da farko cewa ma yayi Mama Ladi ta koma karaye da ita shine ta dinga rusa kuka wai an cuceta an hadata da Badiyyah" Aunty Mariya tace "Kinsan me zai faru Ammi, ai Hajjan yanzu jikinta da sauki don ko jiya naje gidan Baaba Yahanasun dubata don haka kawai ki tattara Badiyyar ki sa ta a mota ta koma can wajensu ai ta san gidan, kuma ba sai kin gaya ma kowa ba kawai su ganta, idan ya so ki kashe wayarki kawai, ni dai Hajja bazata fara cewa Badiyyah ta zo wajena ba tunda tasan yanda yanayin gidan nan yake, in kuma kince ba haka ba to ni kam ban san yanda za ayi ba kuma" Ammi tayi shiru tana nazari, Aunty Mariya tace "That is the only way out fa, infact don ma mun samu Abbansu Maheer din ne amma wallahi ba ko wani namiji ne zai yi tolerating haka ba, ko mai gidana nasan bazai fara yarda Badiyyah ta zauna gidana ba, dama Mama Ladin ce dai dai tafiya da ita karaye ni ko nasan ko daura ma Mama Ladi Badiyyah aka yi a kafa sai ta kunceta" a hankali Ammi tace "To shikenan, zan sa Maheer ya kai ta tasha gobe ya saka ta a motar Kadunan tunda babu wani mafita bayan wannan" Aunty Mariya tace "Shine kawai magana, yanzu yaushe za ku koma Abujan?" Ammi tace "Ya ce jibi..." Aunty Mariya tace "Kai maa sha Allah, wallahi nayi murna sosai Ammi Allah ya sanya alkhairi, dama duk mahakurci bazai taba taɓewa ba, sannan Ammi ina ta son zan maki magana akan matar Maheer, yanzu shikenan ana nufin haka zai ci gaba da zama da ita? Wato ta ci bulus duk abubuwan nan da suka faru uwa uba ga bin bokaye da malamai, asiri har a dakinki?" Ammi tace "Mariya, the girl is pregnant" Sai da Aunty Mariya ta mike zaune daga kwancen da take, tace "Pregnant kuma Ammi?" Ammi ta sauke ajiyar zuciya tace "Har wata uku kuwa, shi dai yace bai san da shi ba, shine Abban nasu yace a jira ta haihu ayi DNA, wannan dalilin yasa muka hanasa sakinta tukunna, yanzu ma nasan kawai suna zaune under same roof ne babu yanda zai yi tunda kinsan baya ketare maganata amma ba da son ransa suke waje daya ba, ai ko da ɗan sa ne ni bazan yi supporting ya ci gaba da zama da ita ba wallahi, for now dai we just have to be patient a jira ta haihu ayi DNA din, kinji dalilin da yasa take gidan nan har yanzu" Aunty Mariya jikinta yayi sanyi, a ranta kuwa har ta fara addu'a Allah sa Maheer have nothing to do with the baby, Allah ya rabasa hada zuri'a da irin Haseenah, can dai tace "Amma Ammi an tabbatar kuwa, anje anyi scan ko kawai da baki ta fadi? Yarinyar nan fa makira ce babu abinda bazata iya aikatawa ba wllhi, sai ta iya forging cikin ma ko a asibiti" Ammi tace "Kin manta shi likita ne Mariya? Anyi scan, ai shine nace maki har wata uku with few days" Aunty Mariya ta tabe baki tace "Ai shikenan, amma what if the DNA result comes out negative after still keeping her for 7 months Ammi?" Ammi tace "Ta cuci kanta ba mu ba" Aunty Mariya ta girgiza kai tace "Allah Ubangiji ya shirya mana zuri'a" Ammi tace "Ameen, sai da safe" Sallama suka yi Ammi ta katse wayar ta wuce sama zuwa part dinta, har a sannan Mama Ladi bata yi bacci ba, Ammi ta kalli agogo da mamaki tace "Baki yi bacci ba Mama Ladi?" Banza Mama Ladi ta mata, Ammi ta karasa cikin bedroom dinta. Washegari da sassafe Ammi ta kira Maheer ta sanar masa yanda suka yi da Aunty Mariya kan cewar ya dau Badiyyah ya kai ta tasha, shi dai yayi shiru yana kallonta, tace "Ko ya ka ga Maheer?" Maheer yace "To ya za ayi dama, tunda relatives din babanta na denying dinta and they are not to be blamed, kawai hakan shine mafita" Ammi tace "Dama nima ban yi blaming dinsu ba" Maheer bai sake cewa komai ba, Ammi tayi kasa da murya tace "Da zaka taimaka ma tunda yau Saturday da kayi dropping dinta a kadunan saboda situation dinta" Maheer yace "Ai yau din ma ina zuwa aiki Ammi, kawai dai ina dawowa da wuri ne" Ammi tayi shiru, sai kuma tace "Toh shikenan" Yace "In ba dai Barrister za ki ma magana ba tunda yana nan" Ammi ta rike haɓa tace "Wani Barrister din?" Maheer yace "Usman mana, shi da ya maida zuwa kaduna kamar zuwa cikin gari" Ammi ta taɓe baki tayi murmushi kawai bata ce komai ba, Maheer ya mike yace "Ko ni sai inje in masa magana yanzu" Ammi tace "Ka dai san dama ba Badiyyah bace, amma ko me zaka ce masa in dai Badiyyah ce bazai je ba" Usman ne ya sauko downstairs zai je kitchen ya hado shayi, Ammi ta bi sa da kallo, ya karaso ya gaisheta ta amsa, ya kalli Maheer yace "Bonjour" Maheer ya daga kai ya kallesa yace "Morning" Zai tafi kitchen Ammi tace "Usman zaka je kaduna ne yau?" Ya juyo ya kalleta yace "Eh" Tace "Kamar yaushe?" Yace "Zuwa karfe goma in sha Allah" Ammi tayi kasa da murya tace "Dama wai taimakawa zaka yi ka ajiye Badiyyah a gidan Baaba Yahanasu" Kallonta Usman ya tsaya yi, can yace "Duk da dai ban tabbatar da tafiyar ba tukunna" Ammi ta ɗan kalli Maheer da yayi murmushi kawai, Ammi tace "Toh shikenan" Juyawa Usman yayi ya shiga kitchen, Maheer yace "Zan dau excuse wajen aiki sai in ajiyeta in sha Allah" A hankali Ammi tace "Allah maka albarka, sai ku je da Mayraah to keep u company, kafin yamma kun dawo in sha Allah, amma sai kun fita da wuri" Karfe tara Maheer ya shirya ya yafi bangaren Ammi, tuni Ammi ta kira Mayraah ta sanar mata tafiyar da za su yi Kaduna, jikin Mayraah yayi sanyi don tausayin Badiyyah take har cikin ranta, Ammi ta sa taje ta hada mata kayanta duk a akwati, Mayraah na hada kayan Badiyyah dake ta bin ta da kallo tace "Me yasa kike hada kayan Mayraah?" Mayraah ta kasa kallonta, har sai da Badiyyah ta sake mata tambayar, ba tare da Mayraah ta kalleta ba tace "Za mu je kaduna ne?" Badiyyah ta mike zaune da kyar tace "Kaduna kuma? Wajen wa a kaduna?" Mayraah tace "Nima ban sani ba, Ya Maheer ne zai kai mu" Shiru Badiyyah tayi amma haka nan taji hankalinta ya tashi sosai, cikin karfin hali tace "Har da Ammi?" Mayraah ta girgiza kai tace "Aa" Daga haka ta mike ta fita daga dakin, tana share hawayen da ya makale idonta ta kulle kofar ta jingina jiki, Usman ne ya fito daga dakinsa ta juya ta kallesa sai kuma ta sunkuyar da kai, har ya karaso inda take tsaye bai daina kallonta ba, jin bai ce komai ba ta daga kai ta kallesa, a hankali tace "Ina kwana?" Yace "Why are you crying?" kamar jira take ta fashe da kuka, ya bi wajen da kallo sannan ya matso kusa da ita ya kamo hannunta da mamaki yace "What happened?" Cikin rawan murya tace "They are taking Badiyyah to kaduna, Yaya idan taje can babu wanda zai kula da ita and she needs care in this her condition, this is her destiny we are not suppose to neglect her..." Usman yace "Is that why u are crying?" Ta gyada masa kai, yace "Did anyone help u carry ur own destiny with you? I mean... did anyone partner with u in all what u went through this pass months?" Mayraah ta dinga kallonsa hawaye na sauka idonta, yace "So she should carry her cross alone" Yana fadin haka ya kai fingers dinsa yana share mata hawayen fuskarta, Mayraah couldn't stop looking at him, she doesn't even understand if she is surprise or Shock at his action, kuma bai fasa kallon kwayar idonta ba while wiping away her tears. Ammi ce ta fito daga part dinta, tunda ta kallesu sau daya daga nesa bata sake kallon direction din ba, Mayraah ta matsa daga kusa da shi da sauri, har dai Ammi ta karaso tace "Kin gama hada kayan ne Mayraah?" Mayraah ta gyada kai tace "Na gama" Ammi ta kalli Usman da ya juya zai sauka downstairs tace "Kai kayi breakfast din ne?" Ba tare da ya juyo ba yace "Na yi" Ammi ta maida dubanta kan Mayraah tace "Shiga ki fito da akwatin ki kai motar yayanku, yana waje yana jiranku" Mayraah ta bude kofar dakin ta shiga, Ammi kuma ta koma part dinta, Mayraah na sauka downstairs da akwatin Usman yace "where are you taking it to?" Tace "Motar ya Maheer, Ammi tace shi zai kai mu" Usman ya gyada kai without saying anything, tana jan akwatin ta fita compound, Maheer na jingine jikin motarsa ya hango Mayraah, ya nufeta ya amshi akwatin, tace "Yaya ina kwana?" Yace "Lafiya lau, how was ur night?" Tace "Alhamdulillah" tare suka karasa gun motarsa ya bude booth ya saka akwatin yace "Ina take?" A hankali Mayraah tace "She is inside" Daga haka ta juya ta koma cikin gidan, duk Haseenah na lekosu ta window with so many thoughts running her mind, can ta ɗan yi murmushi ta juya ta bar bakin windan. Ammi ta shiga dakin da Badiyyah take, ta sameta zaune kana ganinta kaga tashin hankali a fuskarta, a takaice Ammi tace "Maheer zai kai ki Kaduna, za muyi tafiya da Abba, kinga babu kowa gidan, Mama Ladi kuma zata tafi karaye, mai aikin zata tafi garinsu, Mayraah ta samu aiki a Abuja she will be traveling too" Badiyyah ta fashe da matsanancin kuka tace "Ammi ko ni kadai ce don Allah a bar ni zan zauna wallahi, don Allah ku rufa min asiri" Ammi tace "Kulle gidan za ayi, haka zaki hakura ki tafi kadunan sai sanda Allah yayi mana dawowa gaba daya" Tana kuka sosai tace "Ammi wajen wa a Kaduna?" Ammi tace "In an je za ki gani, ki dauko hijabinki ki fito lokaci na wucewa" Daga haka Ammi ta bar dakin, Badiyyah ta tashi tana kuka sosai ta dau hijab ta saka ta fito, dubu ashirin Ammi ta bata ta amsa tana kuka har suka sauko downstairs, har sannan Usman na zaune Ammi ta raka Badiyyah bakin kofar parlon, Mayraah ta dinga kallonta cike da tausayi har ta karaso parking space ta bude mata mota ta shiga ta kulle sannan ta tafi front seat don Maheer na cikin motar a zaune, babu bata lokaci suka bar gidan. Hira Mayraah take ta yi ma Maheer dake sauraronta bayan sun dau hanya, Badiyyah dake zaune a baya tayi nisa cikin tunanin da take gaba daya bata ma cikin hayyacinta bata san me suke cewa ba duniya ta mata zafi, after an hour drive Mayraah ta sauke ajiyar zuciya tana kallon Maheer tace "Ni kadai nake ta labarina" Yace "No, ina jin ki mana Mimi, what were you even saying?" Ƙin cewa komai tayi ta hade rai tana kallon titin gabansu, ya ɗan yi murmushi yace "So now sai monday zaki amshi statement of result dinki kafin ku tafi Abuja? Since u will be going for interview on Tuesday...." Mayraah ta gyada masa kai kawai, yana murmushi yace "C'mon Mimi, i am sorry" Ta ɗan turo baki, yace "Baxa ki hakura ba" Tace "Na hakura but yaya ni tsoron interview din nake, MD din bashi da mutunci kwata kwata wallahi, yana da anger issues, sannan he is rude and arrogant, infact he is so loud for my liking komai masifa da jaraba" Maheer na gyada kai yace "Duk shi kadai?" Mayraah tace "Wallahi, just my few days in that hospital the experience was horrible, har bana son tunawa, wllh he is rude Yaya" Maheer na gyada kai yace "I trust you idan ya maki interview din ma you will only leave him with mouth agape, did u know that ur intelligence is extra ordinary lil sis? I am always amazed with ur intelligence, you graduated with first class, nursing science, ai shima sai yayi mamakin result dinki wallahi, shi kansa ba lallai yayi graduating da first class ba idan nursing science yayi...." Mayraah dai sai murmushi take saboda ƙodatan da yayan nata yake, kafin su isa kaduna Badiyya tayi amai yafi a kirga, suna isa kofar gidan Yahanasu Badiyyah ta fashe da kuka a galabaice, Maheer dai ya sauka ya fiddo mata akwatinta ya kira almajiri, jikin Mayraah yayi sanyi ta kasa sauka daga cikin motar, nan da nan hawaye ya cika idonta, Maheer ya bude ma Badiyyah bayan motar yana kallonta yace "Sauko" Saukowa tayi tana kuka sosai tace "Yaya don girman Allah ku taimakeni ku rufa min asiri, bani da kowa...." Maheer ya katseta yace "Ba Ammi tace maki tafiya za su yi ba, in kin shiga ciki sai ki gaya masu, duk sanda ta dawo sai ki koma kanon ai" Daga haka ya kulle motarsa