Showing 165001 words to 168000 words out of 249515 words

Chapter 56 - Mayraah Hausa Novel Complete

20 Nov 2024

1557

Tare suka koma office din Dr Khalil Ahmad ya kwanta. Wajen uku da minti arba'in ya tashi daga baccin da yayi, bai ga Dr Khalil a office din ba, ya fita yana rike da makullin motarsa, sai da ya fara zuwa ward din da aka kwantar da Mayraah, kwance ya sameta idonta biyu, har ya karaso ya tsaya kusa da gadon bata ce masa komai ba, yace "Jikin da sauki?" Ta gyada masa kai, yace "Allah ya kara afuwa" Tace "Ameen, Pls ina Dr din?" Ahmad yace "U need anything?" Ta girgiza masa kai tace "Kawai ka kira min shi pls" Yace "Ohk, i will.... Kun yi magana da yan uwan naki?" Mayraah ta sauke idonta kasa, can tace "Ni iyayena ba garin nan suke ba suna Bauchi, admission na samu a nan" Yace "Ok.. ke student ce?" Ta gyada masa kai tace "This is my first time in Abuja, na samu admission a University ne, to kafin in samu hostel shine nayi lodging hotel din" Ahmad yace "Kin samu hostel din ne yanzu?" Still ta gyada masa kai tace "Ana kan processing din mun ne" Yace "Zuwa yaushe?" Tace "Nima ban sani ba, amma idan aka gama zan bar hotel din" Yace "Na gane, shikenan ni zan tafi Allah ya kara lafiya...." Tana kallonsa tace "Ameen, thank you" Yace "I will be checking out of the hotel idan na koma, so take care of ur self, Allah ya bada sa'an karatu" Tace "Ameen, Nagode" Daga haka ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita, har parking space Dr Khalil ya raka abokin nasa yace "To yanzu sai yaushe kuma in ka tafi?" Ahmad yace "May be nan da 5 weeks bikin Humaira" Dr Khalil yace "Ohh haka ne fa, To Allah ya tsare" Ahmad yace "Ameen" Daga haka ya bude motarsa ya shiga, Dr Khalil ya koma cikin asibitin ya tafi ward din da Mayraah take, ya karasa kusa da gadon yace "Ya jikin yanzu?" Tace "Na ji sauki" sai kuma tayi kasa da murya tace "Pls is there anywhere i can get sanitary..... " Sai kuma tayi shiru" Yace "Ohk, give me a minute" Daga haka ya juya ya fita. Da safe breakfast lafiyayye aka kawo ma Mayraah kamar yanda ake ma sauran patients din asibitin, har ta mance rabon ta zauna tayi breakfast din kirki, sosai kuma ta ci abincin, tana gamawa ta koma ta kwanta, bayan sallan asuba Dr Khalil ya shigo ward din yana kallonta yace "Ko dai ba garin nan iyayenki suke ba? Naga har yanzu baki ce za ki kira su ba" Ta gyada masa kai tace "Ni student ce, na samu admission ne a University" Dr Khalil yace "Oh ok, amma ai ya kamata su san baki da lafiya ko" Ta girgiza kai da sauri tace "Aa bana son in daga masu hankali, jiya fa na zo garin" Yace "Really?" Ta gyada masa kai, yace "Daga ina?" Ta ɗan yi shiru sai kuma tace "Bauchi" Ya ɗan buda ido yace "That's far" Kamar warce ta tuna abu kuma tayi saurin cewa "But my aunty is in Suleja with her husband" Dr Khalil yace "Ohk sun san kin taho Abuja kenan" A hankali tace "Sai nayi settling a hostel zan je wajensu" yace "Ohk that's good, ni zan tafi gida kin ga night duty nayi, zaki kira aunt din taki ne ta taho yanzu?" Mayraah tace "Ni fa na samu sauki, dama idan aka min allurai shikenan sai in ci gaba da shan magani kawai, i am feeling much better now" Yace "Kina nufin a sallameki kenan?" Ta gyada masa kai, yace "Are you sure?" Nan ma ta gyada masa kai yace "Ok then, are u still going back to the hotel?" Tace "Yes" Yace "Toh let me get u discharged sai in ajiye ki hotel din before heading home" Tace "To Nagode" Tare Mayraah suka fito reception da Dr Khalil, duk nurses din sai sallama suke masa da fara'a kana ganin haka kasan he is a free man, a haka har suka fito haraban asibitin, Mayraah dai sai kallon girman asibitin take because it is so beautiful and big, ambulances kusan biyar ne cikin compound din asibitin, sai da ta ga ya shiga motarsa sannan ita ma ta shiga, bayan sun bar asibitin yace "Ya sunan hotel din?" Shiru tayi tana son tuna sunan hotel din, yace "Ko kin manta?" A hankali tace "I can't remember" driving dinsa ya ci gaba da yi har suka iso hotel din yayi parking yana kallonta, duk da tayi mamakin yanda yasan hotel din haka dai tace masa "Nagode" yace "You are welcome Maryam" ta juya ta kallesa tace "Mayraah" yace "Sorry about that" bude motar tayi zata sauka yace "Anytime u are sick, you can come to the hospital ki ce kina neman Dr Khalil" Ta gyada masa kai tace "Thank you so much" yace "You are welcome" Daga haka ta sauka daga motar ta shiga cikin hotel din, tana shiga receptionist din da ta bata makullin dakinta tace "Wannan mutumin da ya kai ki hospital jiya ya biya maki kudin daki na sati daya" Mayraah ta dinga kallonta babu ko kiftawa, can a hankali tace "Toh Nagode" Daga haka ta wuce sama zuwa dakinta. Yanda Ammi taga rana haka ta ga dare, gaba daya ta rasa me ke mata dadi a rayuwar, gashi bata ji alamar Abba a gidan balle matar da ya auro, a yanda ta fahimta ma kamar ita kadae ce a gidan, da safe wajen karfe tara tana zaune kan darduman don tun dawowarta jiya bata shiga daki ba sai dai ta shiga bandaki ta dawo ta zauna kan darduman, ta daga kanta da ke mata azaban ciwo jin an bude kofa, Usman ne ya shigo Maheer na biye da shi, Ammi ta sunkuyar da kanta, Maheer ya zauna yana kallonta yayi kasa da murya yace "Ina kwana" Ammi ta kasa amsa masa wasu sabbin hawayen suka cika idonta, Usman ya zauna kan kujera shi ma yana kallonta a hankali yace "Ina kwana" Kawai ta fashe masu da kuka sosai, Maheer ya rufe ido ya bude cike da karfin hali yace "Don Allah ki bar kukan nan haka Ammi, addu'a kawai shine mafita, pls u are stressing ur health" Ammi ta katse sa hopelessly tace "Ta yaya zan bar kuka Maheer? I failed as a mother, I failed u all, i failed Mayraah, I wished i neva witness a day like this, gwara ace bana duniyar da wannan..." Kukan da take yasa ta kasa ci gaba, Usman na kallonta yayi kasa da murya yace "U didn't fail Ammi, mu kan mu shaida ne kan son da kika yi ma Mayraah, we are not in the position to question God akan abinda ya faru, dama haka Allah ya riga ya tsara babu dubaran da zai canza hakan, ki kwantar da hankalinki, in sha Allah Mayraah will be back home safe and sound, babu abinda zae sameta" Ammi dai kuka kawai take, Maheer ya mike yace "Let me get you tea" Daga haka ya fita daga parlon don yasan tun jiya bata ci komai ba, Usman ya ci gaba da kwantar mata da hankalinta don abun sai yayi masu yawa kuma idan Ammi ta kwanta ba lafiya, it's better su dinga lallabata suna kwantar mata da hankali. Da yammacin ranan Maheer na zaune wani eatry da goran ruwa a gabansa, ya fi awa daya zaune eatry din, ya kalli agogon wrist dinsa for d countless time dai dai sanda Musharraf ya shigo eatry din, Musharraf na hango Maheer ya nufi inda yake zaune, ya basa hannu suka gaisa sannan ya zauna kujeran dake facing dinsa, Maheer yace "Sorry nace mu hadu nan Dr ban san ko na shiga hakkin ayyukan ka ba, i am so sorry for the inconvenience this might have cause you" Musharraf yace "Never mind, i am all ears" Maheer na kallonsa calmly yace "Dr nasan Mayraah tana wajen ka, babu inda zata je da ya wuce wajen ka, don babu wanda ta sani sai kai, and tayi hakan sau uku kenan if i am not mistaken, but if i may ask pls idan kanwarka ce Mayraah zaka ji dadin wani saurayi ya dinga bata shelter ko yana hosting dinta saboda wani issue ya faru a gidansu?" Kallonsa kawai Musharraf yake, can yace "Ban gane abinda kake nufi ba" Maheer yace "Mayraah is missing since yesterday kuma babu inda zata je tun jiya har zuwa yau da ya wuce gun ka, you know her whereabout don haka kaji tsoron Allah, abinda baza ka so ayi ma kanwarka ba kar kayi ma kanwar wasu, at the first place ma in taje wajenka me ya kamata ace kayi as a responsible guy? That aside pls kai ba musulmi bane? Ta yaya ma zaka ci gaba da relationship da yarinyar da iyayenka suka ce baza ka aura ba in dai ba wata manufar gareka a zuciya game da ita ba? Meye amfanin relationship din da kai kasan will neva lead to marriage tsakaninku tunda iyayen ka sunce baza ka auri mara asali ba? Why not go ur way and leave the innocent girl alone pls?" Mikewa Musharraf yayi ya buga table din gabansu yace "You are talking bullshit, da nasan kirana kayi ka bata min lokaci baza ka gan ni a nan ba Malam" Daga haka ya juya ya bar wajen a fusace, Maheer ya bi sa da kallo har ya fice daga eatry din. Musharraf na shiga motarsa maganganun Maheer suka dinga masa yawo a kai zuciyarsa na bugawa, Mayraah bata gida tun jiya? To ina ta tafi? Since yesterday yake ta kiran wayarta switch off, har he was planning on coming to their house to check on her today, sosai kalman Mayraah bata gida tun jiya da Maheer ya fada yayi distablizing dinsa, da kyar ya iya jan motar ya bar parking space din eatry din yana tunanin to ina ta tafi, sosai yaji hankalinsa ya tashi, Maheer na fitowa eatry din ya kira Abba yace "Abba mun hadu da shi, ya ki saurarana, wanda hakan ke nuni da truly suna tare da Mayraah...." Abba da ke ta jiran kiran Maheer tun dazu yace "Turo min numbersa, i will get him arrested immediately, his parent were the root of every problem occuring now, i wil surely get him arrested a yau din nan har sai ya fito min da daughter na...." Maheer ya tura ma Abba number Musharraf, babu bata lokaci Abba yayi making few calls nan da nan aka fara tracking Musharraf.....
[7/16, 8:10 PM] Khaleesat Haiydar💖: Musharraf na dakinsa bayan la'asar Maminsa tayi knocking, yasan ita ce but saboda damuwar da ya cika zuciyarsa ya ki tashi ya bude kofar, may be idan taji shiru zata yi tunanin bacci yake ta wuce kawai, continuously yaji take knocking din kofar, hakan ya sa ya ajiye wayar hannunsa da yake ta dialing number Mayraah amma switch off, ya mike ya nufi kofar ya bude yana kallonta bai dai ce komai ba, daga sama har kasa take kallonsa tace "Me kake yi a ciki nake knocking baka responding Musharraf?" Ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya yace "Kawai na kwanta ne Mami, i want to get some rest" Mami ya dinga kallonsa, ganin damuwar dake fuskarta yace "Is anything wrong Mami?" Ta karasa cikin dakin ya bi bayanta yace "Mami wani abu ya faru ne" Mami ta juya tana kallonsa cike da damuwa tace "I should be asking u that Musharraf, tell me what are you hiding from me? menene ke faruwa?" Musharraf ya shafa kansa yace "Me ke faruwa kamar me fa Mami, kin ga anyi wani abu ne?" Mami tace "You are not saying the truth, tell me kai da waye ku ke da matsala? Menene kake boye min?" Ya ɗan buda ido yace "Matsala kuma? I don't have issue with anyone" Mami tayi shiru still looking at him kafin tace "Then me yasa police officers suka zo gidan nan nemanka yanzu?" Kallonta ya dinga yi cike da mamaki yace "Police officers kuma? I don't understand" Mami tayi kasa da murya sounding so disturbed tace "Kar ka boye min komai don Allah son, me yake faruwa?" Musharraf yace "Wallahi Mami ban sani ba..." Bai sake cewa komai ba ya fice daga dakin Mami ta bi bayansa tana kiransa bai tsaya ba har ya sauka downstairs, ya nufi kofar parlor ya bude, wasu mutane uku ya gani tsaye dai dai bakin kofar parlon, daya daga cikinsu yace "Musharraf Abdallah??" Musharraf yace "Yes, how may i help you?" ID card dinsa ya ciro don dukkansu ba uniform bane a jikinsu, Ɗan sanda na nuna ma Musharraf ID card din yace "You are under arrest" Juyawa Musharraf yayi ya kalli Mami dake tsaye bayansa, trying all possible best to calm her down yace "U need not to worry pls Mami, it's not something serious, zan bi su mu je" Mami da hankalinta yayi mugun tashi bata ko kallesa ba balle ta sauraresa tana kallon officers din tace "Pls wani division din ne?" Wani officer ya gaya mata, ta juya ta koma sama da sauri don dauko makullin motarta da gyale, Musharraf ya bi yan sandan har kofar gida zuwa gun motarsu, babu wanda zai ce yan sanda ne don motar ma me kyau ce suka zo da shi, nan suka kama hanyar station tare da Musharraf. Maheer na zaune asibitin da aka kwantar da Haseenah wajen karfe biyar na yammacin ranan, she is responding to treatment don har ta fara iya cin abinci a hankali, amma fa tana jin jiki don fuskarta ya kumbura suntum saboda azaban bugun da kanta ya sha, tun da abun ya faru shi dai bai ga mahaifiyarta ta zo asibitin duba ta ba, danginta ne kullum ke sintirin asibitin su kawo mata wannan su kawo mata wancan, kuma ko sun zo basa ce ma Maheer komai, ko Aunties dinta idan ya gaishesu basa amsawa fuska a murtuke suke wucesa shi kam ko a jikinsa don duk ya kagu a sallameta a asibitin shi ma ya sallameta zuwa gidansu don har ransa yasan bazai iya zama inuwa daya da Haseenah ba kuma, shi mamakin ma yanda aka yi har ya auri Haseenah yake kamar wanda aka yi ma rufa ido, ko da yake baka sanin halin mutum ai sai ka zauna da shi dama, he regret knowing her har suka kai ga aure, yana zaune haraban hospital din yayi nisa tunanin da yake don shi har a sannan gani yake Mayraah na gun Musharraf, infact bai ma yarda bata wajensa ba, few minutes ago Abba ya kirasa ya sanar masa anyi arresting Musharraf, so kawai yana jiran Abba ya sake kiransa yace masa Musharraf yayi admitting Mayraah na wajensa, yana wannan tunanin kiran Abba ya shigo wayarsa, da sauri ya daga, Abba yace "Akwai wanda ke tare da matar taka a asibitin ne ka taho Miller road ka sameni yanzu?" Maheer yace "Miller road, Ina kenan a nan Abba?" Abba yace "I will send you the full address" Maheer yace "To" Shi fa duk tunaninsa Abba baya kano da bai gansa a gida ba, though ya dai lura kamar Hajiya Amina ma bata can gida amma he was thinking tare Abba ya tafi da ita, mikewa yayi don Aunties din Haseenah na ciki tare da Haseenar ya shiga motarsa ya bar hospital din, address da Abba ya tura masa ya bi har dai daga karshe ya ga kansa a wani hadadden layi na manyan masu kudi, don duk gidajen wajen hadaddu ne na karshe, yayi parking a number gidan da Abba yace yayi parking yana kallon gidan wondering whose house Abba yace ya zo, bude gate din gidan aka yi bayan ya kira Abba ya sanar masa ya iso kofar gidan, ganin haka ya shiga ciki yayi parking, a compound ya tarar da Abba tsaye waiting for him to come in, ya sauko daga motar Abba yayi leading dinsa har zuwa babban parlon gidan shi dai Maheer na ta mamaki yana bin gidan da kallo, Maheer na shiga lafiyayyen parlon ya zauna yana kallon Abba yace "Abba whose house is this?" Abba yace "Gidana ne" Da mamaki Maheer yace "Gidanka kuma Abba? Gidanka?" Maimakon Abba ya basa amsa sai cewa yayi "Yanzu kawun nan matar ka suka bar nan, her paternal and maternal Uncles" Nan da nan mood din Maheer ya canza, Abba yace "Sun zo sun bada hakuri akan abinda ya faru...." Maheer ya girgiza kai trying his possible best to be calm yace "Abba gaskiya bazan iya ci gaba da zama da ita ba....." Abba yace "Maganar banza ma kake kenan, ni zaka mayar karamin mutum? Meye dalilin da baza ka ci gaba da zama da ita ba, anyi abinda yafi haka ma an koma an ci gaba da zama balle wannan abun da ya faru duk kwamacalar mata ne da haukan mata" Maheer ya kalli Abba cike da damuwa yace "Abba wai kaga abinda sisters din mahaifiyarta suka yi ma...." Abba ya dakatar da shi yace "Bana son jin komai, dama su mata ai abinda yafi haka ma za su aikata don haka babu ruwana da wannan batun, har mahaifiyar yarinyar yanzu sai da ta kira suka bani waya tace ayi hakuri, ta kuma ce za ta zo har gida ta bada hakuri sannan ita ma kakar taku zata je ta bata hakuri, kaga wannan na nuni da iyayen nata ma ba kananun mutane bane ai, balle ko da basu zo bada hakuri ba ban ga dalilin da zaka saketa ba, ita da ma aka ji ma mummunan rauni take asibiti..." Maheer ya dake yace "Amma Abba...." Abba ya dakatar da shi again yace "Maheer bana son gardama, a lokacin da aka ce maka ka dauke Mayraah daga gidanka ai baka yi gardama ba, sai nine ka raina? Wato ni ban isa in gaya maka ba" Maheer bai sake cewa komai ba ya jinginar da kansa da kujera yana jin zuciyarsa ba dadi, shi duk zatonsa a kan Mayraah Abba ke kiransa, ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login