Showing 99001 words to 102000 words out of 249515 words
Ammi na saka turaren wuta amma wnn kam kamar ba turaren wuta bane don wani irin kamshi kamar na yan bori yake, Maheer ya bi ta da sauri yace "Hope u didn't inhale much?" Ta girgiza masa kai still walking away from the vicinity, parking space din ta nufa, shi dai yana biye da ita, ta zauna kan kujera ya duka yana kallonta yace "Kiyi hakuri ki ɗan zauna nan har ya fita, bata san baki so ba" Mayraah dai bata ce komai ba, ya mike ya koma cikin gidan, yana shiga parlon ya fara kwala ma Haseenah kira, ta fito daga kitchen sanye da wani atamfa tayi daurin ture kaga tsiya ga make up a fuskarta ta nufesa ta rungumesa tana taunar gum tace "Oyoyo Baby, sannu da dawowa my husband" Yana yamutse fuska yace "Wannan hayakin meye kika cika a gidan nan Haseenah?" Ta wara ido tace "Turaren wuta mana" Yace "Aa wannan ba turaren wuta bane gaskiya, kuma ba nace maki Mimi is Asthmatic ba? Because of this she can't come inside now" Haseenah ta hade rai tace "And so what? Saboda Mimi kana nufin bazan sa turare gida na yayi kamshi ba kenan?" Yace "Madam!! Ammi tana sa turaren wuta amma ba me hayaki irin wannan kamar anyi gobara ba, beside wannan wani awful smell yake fitarwa unlike wanda Ammi ke using..." Haseenah ta juya ido tace "Toh ni kalan nawa turaren wutan kenan, take it or leave it Maheer" Tana fadin haka ta bar sa tsaye a wajen ta nufi daki, kasa ce mata komai yayi, can ya juya ya fita ya koma wajen Mayraah....
Mayraah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
[6/28, 1:28 PM] Khaleesat Haiydar💖: Greetings to you Hajiya Bilkis (Mom Fa'iq, Maman Eesha) Allah Ubangiji ya ba Baba lafiya ya tashi kafadunsa, ya sa jinya ya zama kaffara Ameen, Hajiya Faty gogori i greet u too with respect Allah ya raya maki zuri'a ya kara maki kwanciyar hankali da farin ciki... Aunty Amina (Sis Amzaj) ina maki fatan alkhairi, Allah ya albarkaci zuri'a, ya raya min Mara Jiddah in sha baki.... Aunty Nurse (Damsel) kema na gaisheki sosai, Allah ya biya maku bukatunki na Alkhairi, ya cika maki duk burukkanki na rayuwa, Ameeen.
Har aka kira Magrib Maheer na tsaye parking space tare da Mayraah da ke ta danna wayarta, ya dawo kusa da ita yana kallonta yace "Mimi let me check ko ya ragu sai mu shiga ciki" Ta daga kai ta kallesa, ya juya ya nufi parlon gidan, har a sannan da hayakin sai dai ba kamar da farko ba, ya juya ya fito ya koma parking space din yace "I think u will be able to manage, in kin shiga daki sai ki kulle kofa" Mikewa tayi ta fara tafiya, ya bi bayanta har suka koma cikin gidan, she held on to her breathe don bata ma son kamshin koma meye Haseenah ta ƙona a gidan, har wani hawa kai yake, tana shiga daki ta kulle kofar tana sauke numfashi, sai a sannan Maheer ya dawo parlor ya shiga toilet dake nan yayi alwala ya tafi masallaci, ko da ya dawo gidan Haseenah na kwance daki yana kallonta yace "Baki yi sallah ba Haseenah" A takaice tace "Nayi" zaunawa yayi gefenta yana kallonta, a hankali yace "I don't mean to hurt u Haseenah, is just that...." Kamar jira take ta fashe da wani shagwababben kuka tace "Wallahi tun ba aje ko ina ba na gaji Maheer, ta yaya ni da gidana kuma turaren wutan da zan sa inji dadi ace baxan saka ba? Shikenan sai in bar gidana ya fara warin ruma saboda wani dalili can?" Maheer yace "No ba ace baza ki saka turaren wuta ba Haseenah, kawai dai ki dinga sa wa da rana idan babu kowa a gidan, kin ga Mimi tana da Asthma, sannan nima hayakin idan yayi yawa yana damuna sosai, but kiyi hakuri" Ta wani daure fuska tace "Sannan kuma magana ta biyu a gaskiya bazan zauna da gandareriyar yarinya haka a gidan nan ba ace bata taimaka min da komai, inyi wanke wanke inyi gyaran kitchen, in share gida inyi goge goge, in wanke bathroom, sannan inyi girki, to wllh bazai yiwu ba ni ba boyi boyin kowa bace, ai ni ma ba lafiyayyar bace ciwon baya gareni...." Maheer dake ta kallonta yace "Yaushe kika fara girkin, in dai ba yau kika yi ba?" Ta masa wani kallo tace "Ae nayi din ne shi yasa nayi magana" Ya shafa kansa yace "Ohk, amma dai shara Mimi baza ta yi ba saboda condition dinta, so zata dinga maki gyaran kitchen sannan ta maki goge goge, har da girki in kina so" Haseenah tace "Sai kuma ta wanke duk bandakin gidan" Shi dai bai ce komai ba, Haseenah ta mike tace "Mu je inyi serving maka abinci, i cooked ur favorite" Yace "Let me take a shower first" Daga haka ya mike ya shiga bandaki ta bi sa ciki. A tare suka fito parlon bayan isha tana makale jikinsa, zuwa sannan ta canza kayan jikinta zuwa na bacci, dai dai nan Mayraah ta fito daga kitchen rike da cup din shayi, Maheer ya hau tura Haseenah da sauri daga jikinsa amma sai ta wani sake makalesa kamar za su dawo daya, Mayraah dai bata sake kallon inda suke ba ta nufi dakinta, Maheer da abun bai masa dadi ba yace "C'mon Haseenah, meye haka kike yi kina ganin yarinya??" Sai a sannan Haseenah ta sakesa tace "Wallahi babu wanda ya isa ya hanani cin amarcina yanda ya kamata, wannan ce yarinya?" Tana fadin haka ta manna masa kiss tace "Bari in kawo maka abinci Baby" Zaunawa yayi kan kujera yana shafa kansa yana kallon hanyar dakin Mayraah, sai ga Haseenah ta dawo parlon ta ajiye warmers din abincin ta fara serving dinsu a plate daya, sai bayan da ta gama zuba masu yace "Mimi ta zuba abincin ne?" Da sauri Haseenah tace "Ehh naga ta diba" which is a lie, saukowa Maheer yayi kan carpet, ya dau spoon, ita ma ta dauka suka fara cin abincin a tare, ba za dai ace abincin bai yi ba amma sai yaji it can never be compared with that of Mayraah, shi har yau ya kasa samun abincin da yayi masa dai dai da na Mayraah be it restaurant or home, hakan yasa yaji gaba daya abincin Haseenah bai masa dadi ba a baki, Haseenah tace "Ya ka ji abincin Dear?" Ya kalleta yana gyada kai yace "It's so good, it's delicious, ban san you are a good cook ba haka" Ta fara wani blushing tace "Anything for my hubby" Yace "Amma fa sai yanzu na kara fahimtar ki da kika ce aiki yayi maki yawa wifee, duk ke kadai kika yi girkin nan ga kuma gyaran gida?" Ta marairaice tace "Wallahi kuwa Dear ni kadai raina babu mataimaki" Yace "Kinsan me zai faru, tunda Mimi bata shara why not kawai ki bar mata girkin ita ta dinga yi tunda naga ta ɗan iya, U can't be stressing ur self this much...." Haseenah na girgiza kai tace "Aa ni zan dinga yi ma mijina girki, haka na taso na gani a gidanmu, saboda me zan bar wata tayi ma mijina girkin da zai ci gani da lafiyata" Maheer bai kuma cewa komai ba ya ci gaba da tuttura abincin, bai ci ya kai spoon shidda ba ya ajiye cokalin yace "Kinsan da daddare bana cin abinci da yawa, i prefer tea" Ta hade rai tace "Baby ko dai abincin bai maka bane?" Ya zaro ido yace "Wannan abincin? Ai ko a babban restaurant sai haka wife, mata nawa ne yanzu ko Indomie basu iya dafa shi yayi kyau ba" Ta marairaice tace "To naga baka ci da yawa ba" Yana shafa cikinsa yace "I'm full, kinsan it's not healthy mutum ya ci abinci da yawa da daddare" Ita dai ta ɓata rai tana jujjuya spoon din hannunta, da sauri ya kawo wani labari duk don ta mance da batun abincin, daga karshe kuma ya bar ta da bashi labarin ya jingina da kujera yana sauraronta inattentively don duk hankalinsa na kan Mayraah, kawai bai san matsalarta shi yasa ya kasa tashi ya je dakin Mayraah din, ita kuwa sai labari take basa wanda duk bai ma san abinda take cewa ba kallonta kawai yake, wayarsa dake kan kujera ne ya fara ring, ya dauka yana duba screen din ya ga Usman ne ke kiransa, picking call din yayi ya kai kunne, bayan ya gama sauraron Usman yace "Me yasa baza ka shigo ba kai?" daga other side Usman yace "Sauri nake, kawai ta zo ta amsa ba sai na shigo ba" Maheer bai kuma cewa komai ba ya katse wayar, mikewa yayi Haseenah ta bi sa da kallo ganin dakin Mayraah ya nufa ta kyabe baki tare da jan tsaki kasa kasa, yana shiga dakin ya sameta zaune gaban madubi daure da towel tana shafe shafenta alamar fitowarta kenan daga wanka, tun da suka hada ido ta sunkuyar da kai ta kasa dagowa, she don't know why she felt soo ashame today, unlike before da bata jin komai, shi kansa sai ya zama uncomfortable ya ɗan fara kame kame yace "Usman yana jiranki a waje zaki amsa sako" Yana fadin haka ya juya ya fita, Mayraah ta dinga mamakin wani sako Ya Usman zai bata da daddaren nan, ta dai mike ta dau kayan baccinta ta saka sannan ta daura hijab har kasa a kan kayan ta fito parlor, tunda ta fito Maheer dake zaune shi kadai a parlon ke kallonta babu ko kiftawa, Tana karasowa tsakar parlon yace "Kina amsa ki shigo gida, do not exceed 2 minutes" Tace "Toh" Daga haka ta fita waje. Tana isa gun motar Usman ta bude front seat tana kallonsa tace "Yaya ina yini" Yace "Lafiya" Ganin ta tsaya bata shigo ba yace "A waje zan baki sakon? Or should i come down to give u?" Bata ce komai ba ta shiga motar ta rufe, ta juya tana kallonsa, ya dauko warmer dake cikin leda a bayan motar ya mika mata, ta amsa yace "Ammi tace a kawo maki" Mayraah bata san sanda ta wara ido ba tana murmushi tace "Nagode sosai, yaya wajen Maleeha zaka je ne?" Ya juya ya kalleta lkci daya ya hade rai yace "Ke yaushe na fara wasa da ke ne?" A hankali tace "Toh naga u look cute" shiru yayi yana kallonta, Tana murmushi tace "Idan can zaka je sai in raka ka" kamar warce ta tuna abu ta zaro ido tace "Lahh, Ya Maheer yace kar in wuce 2 minutes fa" Usman dake kallonta yace "Aiki ya baki a gidan da yace kar ki wuce 2 minutes?" Mayraah dai tayi murmushi kawai bata ce komai ba, Danna wayarsa ya fara yi a motar, ita dai sai kallonsa take, can bayan wasu mintuna yace "What did u need?" Tace "Kamar me?" Yace "Baki bukatar komai?" Tace "Ohk, cream, ya kusa karewa" Yace "Just that?" Shiru tayi tana tunani, can tace "Eh shikenan" Bai sake ce mata komai ba ya ci gaba da danna wayarsa, after another few minutes ba tare da ya dago ba yace yace "When is ur exams?" Tace "Saura 3 weeks" Mayraah dai kallonsa kawai take, can kuma yace "Are you comfortable staying in the house?" Tayi shiru, sai a sannan ya daga kai ya kalleta ya ajiye wayar hannunsa, ta sunkuyar da kanta tace "Yes" Yace "Ke" Ta kallesa yace "Gaskiya za ki gaya min, are you comfortable?" Tace "To ai ba a gidan nake wuni ba, ina zuwa school" Yace "If there is anything you let me know" Ta gyada masa kai, ya dau wani leda a bayan mota ya mika mata ta amsa, ko bata duba ba ta gane shawarma ne, tana kallonsa tace "Thank you" ya ciro Atm card dinsa da bai fiye amfani da bank din ba sosai amma kuma yana saka kudi ya mika mata yace "If u need anything, u can withdraw, will forward the pin to you via sms" Ta amsa still tana kallonsa tace "Thank you" yace "You can leave" bude motar tayi ta sauka tace "Sai da safe" Ya ja motarsa ya bar wajen, tana shiga compound taga Maheer tsaye a balcony, ta karasa tana tafiya a hankali, da ido ya bi ta har ta shiga parlor ta wuce dakinta... Mayraah ta linke Hijab dinta sannan ta zauna ta bude warmer din da Ammi ta bada a kawo mata, pepper soup din kaza ne da yaji kayan hadi, nan da nan aroma din ya cika dakin, tashi tayi ta saka hijab dinta ta nufi kofa, ta bude a hankali ta fita, zaune ta ga Maheer a parlor shi kadai, ta karasa kitchen ba tare da ta kallesa ba, ya bi ta da kallo, plate da spoon ta dauka zata koma daki nan ma ya bi ta da ido, Mayraah ta debar masa rabin pepper soup din ta kai masa parlon, yana kallon plate din yace "Shi ya siya maki?" Tace "Aa Ammi ce ta bashi ya kawo min" Amsa yayi yace "Ni da Haseenah?" Mayraah bata san sanda ta amshe plate din daga hannunsa ba tayi juyawarta ta koma daki ta rufe kofa, ya bi ta da kallon mamaki, bayan few seconds ya mike ya bi bayanta, Mayraah na kokarin juye naman cikin food warmer din ya shigo dakin, kallo daya tayi masa ta ci gaba da abinda take, ya ɗan sosa kai yace "Ok i am sorry, i was only asking Mimi ai ban sani ba" Ba tare da ta kallesa ba tace "Ni kadai aka kawo ma dama ae" Yace "Ohk then" juyawa yayi zai fita, ta daga kai tana kallonsa, a hankali tace "To zan tsam maka amma a nan" Ya juya ya kalleta yace "Ohk" Ta sa masa naman guda hudu a plate ta mike ta kai masa, amsa yayi yana kallonta yace "In je parlor da shi?" Ta ɗan yi shiru sai kuma ta juya tace "Ohk" Yace "Thanks Mimi, good night" Fita yayi daga dakin, ta koma ta debi wanda zata ci, bata wani ci naman da yawa ba, ta ci shawarman da Usman ya siya mata sannan ta tafi bandaki ta wanke bakinta ta fito, ta kwanta kenan kiran Musharraf ya shigo wayarta dake gefenta, ta dinga kallon call din kafin ta daga ta kai kunne tayi shiru, Musharraf yace "Na maki laifi ne Dear?" Tace "Laifi kuma na me?" Shiru yayi, ita ma haka, can yace "Kiyi hakuri, in ma na bata maki rai unknowingly, may be i should have gotten the food for u my self, i am sorry Mayraah" lokaci daya ta ji jikinta yayi sanyi, yace "Dama kira kawai nayi in baki hakuri, sae da safe" kasa ce masa komai tayi har ta ji ya katse wayar, a hankali ta rufe idonta tana karanto addu'ar bacci, sannan ta ajiye wayar a bedside drawer ta rufa da duvet, amma for almost an hour ta kasa bacci sae juye juye take, daga karshe ta jawo wayar tayi dialing numbersa, yana dagawa a hankali tayi karfin halin cewa "I am.... I'm sorry too" Har kusan karfe biyun dare Mayraah bata kwanta ba kuma babu alamar bacci ko kiris a idonta, yau kam sun yi hira sosai da Musharraf a waya, they talk about so many things, basu taɓa dadewa a waya irin yau ba tun fara dating dinsu, she is just realizing Musharraf is different in many ways, kawai suna tare ne amma bata san abubuwa da yawa game da shi ba sai yau da yake gaya mata, he told her how he lost his father and his sister that was 13 years old in a car accident, how he cherish his Mami soo much, he gist her about his group of frnds da irin rayuwar da suka yi a kasan waje sanda suke karatu... har labarin Farrah da aka so hada shi da a family sai da ya bata, Mayraah enjoyed every bit of their conversation that night, wani taji tausayinsa, wani taji haushinsa, wani kuma ya bata dariya, wani ya bata mamaki, at the end yace "But trust me Mayraah, no matter who my frnds are back then, Billah ban taɓa zina ba, even this common kiss ni ban taɓa yi ma ko wace mace ba sai ke, i will gain nothing if i lie to you, ni ina da kyankyami sosai shi yasa sai in ji mace bata burgeni ko inji feelings na mace, but surprisingly that stop immediately after i met u, bayan ke kuma ni bana yi ma ko wacce mace kallon sha'awa, Alcohol kuma the weather in Canada lured me and some of our friends into taking it, muna fatan Allah ya yafe mana, mind you... har ma da peer pressure, though ni dai na sha wahala sosai kafin in saba da weather din Canada, amma billah tun bayan dawowata Naija na daina shan alcohol Mayraah, back in Canada ma sai inyi many weeks ban sha ba sai in na gani gun abokan mu, many of my friends basu daina ba har yau, i don't know what came over me da har na sha ranan da daddare a zaria, may be it's because i was loosing my self, Mami bata taɓa sanina da alcohol ba har yau...." Mayraah dai tayi shiru tana sauraronsa, Bayan few seconds yace "Now tell me how u felt the first day we met" Murmushi Mayraah tayi ta kasa ce masa komai, can dai tace "Some other time" Yace "Ohk, ina son kuma zan tambayeki...." Tace "Ina ji" Yace "I tot u once told me Badiyyah er gidanku ce or so" Tace "Sure...." Yace "But da safe da ta shigo office naga kun yi kamar baku san juna ba, why?" Mayraah tace "Ai mun riga mun gaisa da ita a downstairs... And wajenka ta zo a office ba wajena ba" Dr Musharraf yace "Ohkk then, it's already late, ki kwanta.... ni zan yi sallah" a hankali Mayraah tace "Ohk"