Showing 60001 words to 63000 words out of 249515 words
Ammi ba ko? Muje in kai ku nasan yanzu ta farka tunda anyi magariba" Tana fadin haka ta mike, Aunties din Haseenah da sai kallon Mama Ladi suke, har dai suka daga Haseenah suka bar dakin, Mama Ladi ta bi Maman Shafa da harara ta ajiye ƙashin hannunta cikin kwano tace "Wai ita kuma wannan katuwar dake yawo da kodadden zani da yagunannen hijabi wacece ita fisabilillahi? Naga sai shigar min hanci take da kudundune tun da garin Allah ya waye, banda taron biki me zai hadani waje daya da ita mata kamar almajira kaya duk a yamutse" Rai bace Hajja tace "Ladi ke yanzu baza ki saka ma bakinki linzami ba, wllh kar ki bari in maki koran kare daga gidan nan, kin isheni kuma haka tsakani da Allah, wannan wani irin bala'i ne baki gyara abu sai dai ki tabarbare lamari" Mama Ladi tace "Wai kiyi ta cewa zaki min koran kare yaya, ni fa gidan Mamuda nake ba gidan kowa ba, daga magana sai a juya min a fassara abinda nake nufi ta wata tsigar? Ko don anga ban haihu ba balle in aurar da jika?" Tana fadin haka ta fashe da kuka ta jawo mayafinta tana matsar kwalla ta mike ta fice daga dakin da kwanon abincinta. Mayraah na biye da Aunty Mariya suka shigo parlon Ammi, babu wanda ya lura da shigowarsu gidan don ta baya suka shigo ta bangaren Abba, Ammi na zaune kan darduma bayan Hajiya Safiyya ta cire mata drip din hannunta tayi sallah har ta idar, ta daga kai tana kallon Mayraah babu ko kiftawa don bata ma san sun dawo gida ba, nan da nan Mayraah taji hankalinta ya tashi don daga fuska zaka fahimci Ammi na jin jiki, ta karasa da sauri ta durkusa gabanta ta riko hannunta tace "Ammi are you this sick??" Ammi ta rungumota jikinta amma ta kasa cewa komai, kuka kawai Mayraah take a jikinta, Ammi ita ma hawaye ne ke sauka idonta, Babu wanda yace masu komai a dakin, cause bond din exactly irin na uwa da ɗan ta, Aunty Mariya dai na tsaye bakin kofa ta ma kasa karasowa cikin parlon duk jikinta yayi sanyi, Kwankwasa kofar parlon aka yi, Maman Shafa ta leko tace "Za a shigo da amarya wajen Ammi" Aunty Mariya tace "Ohk to ana zuwa" Aunty Mariya ta nufi Ammi da damuwa tace "Plss kiyi composing din kanki Ammi, za a shigo da Haseenah" Aunty Mariya na fadin haka zata janye Mayraah daga kusa da Ammi a hankali Ammi tace "Ki bar ta, su shigo kawai ba komai" Aunty Mariya da Hajiya Safiyya suka yi mamaki sosai don fa tun safe Ammi bata yi ma kowa magana sai dai ta bi ka da ido kawai, Aunty Mariya ta koma tayi masu iso har cikin parlon don dama an shimfida tsadadden carpet babba, Haseenah da Aunties dinta suka zauna, Mayraah dake makale jikin Ammi ta daga kai tana kallonsu, cike da karfin hali Ammi ke amsa gaisuwarsu da ya jikin da suke mata, Haseenah kuwa sai leko Mayraah take ta cikin gyale don sarai ta ganeta, nan taji bacin ranta ya ninku, wato saboda wannan er iskar aka yi bikinta kamar ana zaman makoki yau ko? Frnd din Ammi ce tayi ma Haseenah nasiha wanda Ammi zata yi mata, amma duk Haseenah bata san me take cewa ba don gaba daya hankalinta na kan Mayraah da tunani iri iri da take yi a kanta....
Mayraah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788.... In kinsan baki biya for subscription na littafin nan ba kiji tsoron Allah ki zo ki sallami jikar inna marainiya.
*Assalamualaikum everyone... ina sanar da ku cewar muna saida samosa WRAPS masu gardi da crispy 50 pieces for 2000, Spring rolls wraps 50 pieces for 2800, i assure u Samosa and spring rolls wraps din masu kyau da inganci ne Plss patronize us via*👇🏻
09014996620
Thank you ❤️🙏
+234 901 499 6620
[6/13, 7:29 PM] Khaleesat Haiydar💖: Bayan fitarsu Haseenah da yan uwanta Mayraah ta daga kai tana kallon Ammi cikin sanyin murya tace "Ammi ko in maki shayi?" Aunty Mariya tace "Eh kawo mata" Mikewa Mayraah tayi Ammi ta bi ta da kallo har ta fita daga parlon, Hajiya Safiyya na kallon Ammi tace "Kin dai ga Mayraah Alhamdulillah ta samu lafiya, don haka kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki ki cire komai a ranki don jininki ya samu ya dawo dai dai" Da damuwa Aunty Mariya tace "Ai shine, just forget everything that happened we should face reality, there is surely reason for everything a rayuwar nan" Aunty Mariya na kai wa nan ta mike ta shiga dakin Ammi ta dauko babban duvet zata kai dakin da aka sauke su Haseenah da wa enda suka kawota.... Mayraah na kitchen tana dafa ma Ammi shayi da yaji kayan kamshi ga madaran gwangwani da ta juye ciki yanda dai tasan Ammi ke son ayi mata, ita kadai Ammi ta fi son tayi mata irin shayin, Absentmindedly ta ke aikin da tunani iri iri a zuciyarta, zuwa yanzu kuma ji tayi zuciyarta ya kasa yarda wai ba su Ammi suka haifeta ba, she is now just finding it hard to believe, ta yaya ma za a ace ba Ammi ce ta haifeta ba bayan ita kanta ta san irin son da Ammi ke mata, or are they pranking her? Ji tayi an bude kofar kitchen din, ba tare da ta juya ba ta gane wanda ya shigo don haka yake bude kofa a ko ina, daga baya kuma taji kamshin turarensa, bayan some seconds ta dan juya ta gansa ya dau plate yana zuba abinci, ta kashe gas din sannan ta dau tea pot din ta fara tsiyaya shayin cikin cup, ganin zai fita daga kitchen din ta juya ta kallesa suka hada ido sai kuma ta sunkuyar da kai tace "Don Allah ina son inyi amfani da wayarka" Yace "Yana daki" Daga haka ya fita ya kulle kofar, Mayraah ta ɗan yi goge goge a kitchen din sannan ta wanke hannu ta dau shayin Ammi ta fita, zuwa yanzu babu kowa a gidan sai baƙin da suka zo daga nesa, duk aka bi ta da kallo har ta haura sama and that made her so uncomfortable, yanzu kallon ba er gidan ba ake mata kenan, tana shiga parlon Ammi ta durkusa gabanta ta ajiye mata shayin tana kallonta ta zauna gefenta, cikin sanyin murya Ammi tace "Nagode" Maheer ne ya shigo parlon, ya zauna kujera yana kallon frnd din Ammi ya gaisheta, ta amsa da fara'a tace "Ango ka sha kamshi" Ya ɗan yi murmushi ya kalli Ammi yace "Ammi ya jikin" Ta dau shayin da Mayraah ta ajiye mata tace "Alhamdulillah" Yace "Allah ya kara maki lafiya" Tace "Ameen" Yana kallon shayin gabanta yace "Wannan kamar shayin Mimi" Frnd din Ammi tayi dariya tace "Ai kam yanzun nan taje ta yo sa a kitchen, ni ma kamar ince a tsammin" Mayraah ta kalleta tana murmushin karfin hali tace "Akwai saura bari in debo maki" Hajiya Safiyya tace "Aa zan je da kaina in debo, ke da ba lafiya gareki sosai ba" Mayraah ta sunkuyar da kanta tana wasa da darduman da Ammi ke zaune, Maheer dai sai kallonta yake, bayan few seconds yace "Kin ci abincin Mimi?" Ta daga kai tace "Na ci" Yace "Okay ina jiranki dakin Usman" Yana fadin haka ya mike ta bi sa da kallo har ya fita. Haseenah dake zaune kan gado da kawarta Zaliha dake mata magana kasa kasa ta fusata cikin daga murya tace "To wai ke sai ma kin bata bakinki sai kace baki san ni ba Zaliha" Kanwar mamarta Hajiya Farida dake zaune kasa inda aka masu shimfida da sauran sisters dinta ga abinci iri iri da aka dire masu ta daga kai ta kalli Haseenah rai bace tace "Wai ke wace irin mahaukaciya ce mara kamun kai kina daga mana murya a gidan surkai? Sannan ba nace ki dau mayafin nan ki rufe jikinki ba tunda ba daina shigowa suka yi ba, wato sai kin gama gwada ma kowa ke fitsararriya ce ko?" Haseenah ta hade rai tace "Aa ni gaskiya Aunty zafi bazai hallaka ni ba a banza, ai ba nan ya kamata a zo a jirge ni ba kamar wata mara galihu" Aunty Mama ta kyabe baki tace "To nima dai shi na gani, na zata in kin gaida surkar taki da kakarsa gidanki kuma za mu kai ki, amma sai naga an kawo mu daki anyi shimfida an dire abinci ga mayunwata, a ina ma aka taɓa haka? Aa ni ban taɓa ganin haka ba tunda uwata ta haifeni, Aure duk ba wani armashi kamar auren dole, ni wllh sai nake ganin kamar ma ba wani sonta yaron yake ba ita ce kawai ke haukanta a kansa, atoh tunda gashi ya fi ba matsalar gidansu Muhimmanci a kanta" Aunty Farida dai ta tabe baki tace "Ba tace taji ta gani ba, mu kuma meye namu, kina jin abinda tsamurarriyar tsohuwar can ta gama fada a kunnenmu ai, me yafi wannan walakancin? Ga Salmanu bawan Allah da ya nace mata kememe yarinyar nan taki wai bai yi boko ba sannan ba shi da kyau da qualities din da take so, to wa ke ta wani kyan banza yanzu in dai mutum na da nera meye kuma wani kyau, duk shekara fa Salmanu sai ya je hajji har ma ya biya ma wasu, gashi ba wai zata zauna da kishiyar bane tunda har ya nuna mata ginin da yake mata zai ajiyeta ita kadai, kuma gidajensa sun fi biyar a garin kano, ko rantsuwa nayi bazan yi kaffara ba yafi wannan da ta makalema arziki, shi wannan ina ga ubansa ne kaɗai ke da arzikin ma, duka duka nawa ne albashin likita" Bude kofar dakin aka yi duk suka yi shiru, Mama Ladi ta shigo tana rafka uban sallama, Haseenah ta fara kiciniyar yafa gyalenta ta rufe fuska da sauri, Mama Ladi na washe hakora ta dafe gwiwa tace "Sassannunku da hutawa fahh, in ji dai bakwa bukatan komai ko? Abincin ma idan bai isheku ba sai a kwaso maku sauran dama don ku aka girka, Ko katifa za a karo maku ku baje nan kasa?" Haseenah sai hararanta take ta cikin mayafi don har taji tayi mugun tsanarta, Aunty Mama na kirkiran murmushi tace "Aa hakan ma ya isa Babaa, mun gode sosai wllh" Mama Ladi tace "To bari a buda maku tagogi yanda iska zai shigo maku a wadace ba algus" Tana fadin haka ta tafi ta fara bude windows din har da net din jiki duk ta wangale sai ga su tsirara suna hango waje, duk suka dinga bin ta da kallo har ta gama ta fice daga dakin, Aunty Fauziyya ta rike haɓa tace "Anya tsohuwar nan na da lafiya ma kuwa, wannan ai sai sauro ya kashe mu kafin gari ya waye, ji wani shegen buda window fa da tayi kamar an sa ta, ga Ac a kunne meye na bude mana window" Aunty Mama ta ja tsaki ta mike ta tafi ta kullo windows din tana cewa "Wallahi in dai naga babu alamar kai ta gidanta gobe da safe to tafiyata zanyi ba da ni za a zauna gida nan har yamma ba kamar wata mara abun yi..." A hankali Mama Ladi ta bude kofar dakin da Hajja ke ciki tana lekawa don tun dazu da suka yi baram baram ta fita bata sake komawa dakin ba sai yanzu, ganin yanda Hajja tayi tagumi ya sa ta karasa ciki da sauri tace "Lafiya yaya da wannan uban tagumin? Naga jikin Ammin ai da sauki daga can ma nake yanzu haka har muka ɗan yi hira da ita, dake Meran na jikinta in gaya maki kamar ba ita bace ke kwance tun safe rai a hannun Allah, anya akwai shegen da zai iya raba Ammi da Meran nan kuwa naga wani azababben soyayya take mata, ba don ba don yarinya bace Meran ai da sai ince asiri ta ma Ammin" Hajja ta sauke ajiyar zuciya tace "Ladi ba nace maki haka kawai su Nura baza su ki zuwa daurin auren Mahir ba??" Mama Ladi tace "Wanene kuma Nura?" Hajja tace "Kanin mahaifin Badiyya mana wanda take wajensa a Bichi" Ladi tace "Aiho wnn guntun me hanci wargajeje dai da na sani?" Hajja tace "Ashe wai Badiyya zuwa tayi ta ce ma dangin mahaifin nata wai an daga bikin gaba daya sai zuwa bayan karamar sallah" Mama Ladi ta saki salati tana tafe hannu tace "Amma yarinyar nan anyi tantiriyar er iska" Hajja tace "Haba Ladi ki daina zaginta don Allah, shiriya za mu yi ta nema mata kawai, to na kasa hakuri yanzu na sa aka kira min lambarsa inji dalilin rashin zuwansa daurin aure sai yake sanar min gashi gashi abinda Badiyya tace masu ai, nayi salati hankalina ya tashi ainun, ban boye masa ba nan na labarta masa duk abinda ke faruwa da abinda ake zargin yarinyar nan taje ta aikata mana, yanzu gobe yace min da safe zai dauko Badiyyar su zo nan har da Garba yayansa" Mama Ladi ta saki baki da karfi tace "Wani zargi?? abinda kowa ya tabbata ya kuma shaida ita ce ta aikata wannan abu zaki ce zargi, wllh ko rantsuwa nayi bazan yi kaffara ba Badiyya ce ta aikata wannan zunubin, kuma gwara su taso keyarta ayi ta ta kare" a fusace Hajja tace "Gaskiya Ladi idan baza ki dinga yayyafa ma lamari ruwan sanyi ba to ki dinga jan bakinki kiyi shiru, ke duk wani fitina kin san yanda zaki tada shi a rayuwar nan?" Mama Ladi ta kyabe baki ta nemi waje ta zauna, Hajja tace "Sannan ni tsakani da Allah fargaban zuwansu da ita nake, kowa dai yasan yanda Usman da Maheer suka kullaceta abun ba kyau, kuma kinsan Usman dama tun asali ya tsaneta kada a zo da ita ya illata er mutane mu shiga uku...." Mama Ladi ta mike tsaye da sauri tace "Kin gan ki ko? To me kike nufi a takaice? A kyaleta a zuba mata ido kada a hukuntata kenan ta ci bulus?" Hajja tace "To hukuncin me kuma? Abinda aikin gama ya riga ya gama, kawai a dai ja mata kunne yanda ya kamata a gargadeta ayi mata jan ido, yarinyar nan fa marainiya ce, ba uwa ba uba" Mama Ladi tace "Ko daga kasa aka tonota karewar rashin uwa da uba sai an mata hukunci dai dai da abinda ta aikata don uwarta...." Bude kofar dakin aka yi Aunty Mariya ta shigo tana kallon Hajja tace "Gani Hajja" Hajja tayi kasa da murya tace "Ammin na iya lallabowa ta zo nan yanzu? Naga tana da baƙi kuma magana nake son maku" Aunty Mariya tace "Toh bari in je in gaya mata, zata iya zuwa ai" Hajja tace "Sannan har Maheer da Usman su zo" Aunty Mariya tace "In ji dai lafiya Hajja?" Hajja tace "Lafiya lau, duk dai ku zo" Aunty Mariya tace "Toh bari in masu magana" Daga haka ta juya ta nufi kofar, Hajja ta juya inda Mama Ladi ke tsaye tace "Ai kin ga gwara haka dai ko?" Wayam ta ga wajen... Mama Ladi na kallon Maheer da Usman tace "Don haka kashe wutan dakin kawai za ku yi kamar kun kwanta kada wanda ya fita wllh in da hali ma ina fita ku sa makulli, ni wallahi na ma fara zargin anya ba Hajjan bace ta turata ta aikata tsiyar nan? Aa gaskiya na fara tsoron Hajja kuma haka, dama tun asali an san na fita tsoron Allah tun muna yara" Usman da Maheer dai kallonta kawai suke, Maheer yace "Gwara da kika zo kika sanar min babu inda zanje" Mama Ladi tace "Atoh dai, dama shi Usuman tace azzalumi ne tun Badiyya na jaririya yake cutarta kiris ya rage wataran ya kasheta aka kama sa, Badiyyar da tsakaninsu bai fi wata 7 ba ko shidda, to ina ruwansa da ita kuma" Usman ya ci gaba da danna wayarsa dai bai ce komai ba, Mama Ladi tace "Dama shine nace bari in lallabo in zo in gaya maku kuyi ta kanku, babu gaskiya ko kadan a lamarin Hajja" Tana kai wa nan ta fice daga dakin, tana fita Usman ya mike ya sa ma dakin key, ai ko haka Aunty Mariya ta zo ta gaji da buga kofar babu wanda ya bude mata cikin shi da Maheer, Mama Ladi na komawa daki Hajja tace "Ina kika je Ladi?" Mama Ladi na kallon Ammi dake zaune kasa ta sunkuyar da kanta tace "Fyace majina na tafi yi a tsakar gida daga nan na leka makota ina ta masu ban gajiya kin san haka ake yi" Hajja ta maida dubanta kan Aunty Mariya da Ammi jin sun yi shiru bayan ta gama masu jawabinta, can Aunty Mariya tace "Haba Hajja, yanzu kina nufin shikenan sai a zuba ma Badiyya ido tayi ta abubuwa baza a dau wani kwakkwaran mataki a kanta ba?" Mama Ladi ta kyabe baki ta tafi gefen gado ta zauna, Ammi kam hawaye ne ke sauka idonta duk da kanta a sunkuye yake, Hajja ta fashe da kuka tace "To ya ku ke so mu yi ne?? Badiyyan nan fa ba bare bace, jininmu ce babu yanda muka iya da ita, ai hannunka baya rubewa ka yanke ka yar, addu'a kawai za mu dinga mata Allah ya shirya mana ita" Mama Ladi tace "Amma dai anya Hajja ba ke kika aika Badiyya tayi mugun abun nan da tayi ba yanda naga kina ta kakkare zancen nan, kamar kina tsoron a tona maki asiri ke ma..." Hajja ta kalleta sai ta rushe da sabon kuka tace "Allah ya isa tsakanina dake Ladi, kuma asuban fari na yi ki dau akwatinki ki koma inda kika fito, bana bukatar ki a nan kuma, har abada kar ki sake dawowa inda nake" Mama Ladi ta mike ta nufi kofa tace "Jama'a sai su ce basa son gaskiya kiri kiri, kuma kiyi ta cewa in koma karaye in koma karaye to