Showing 48001 words to 51000 words out of 249515 words
san ba mu muka haifi Mayraah ba kenan?" Bata jira cewar Abba ba ta juya zata fita daga parlon amma tun kan ta kai bakin kofar taga kofar da ma parlon na juya mata gaba daya, Abba ya nufeta da sauri... Mayraah ta dinga bin sa da kallo har ya kashe motar ya sauka, bata taɓa jin tsoro irin na wannan lokacin ba, ya zaga side din da take zaune ya bude motar, duk da yanda gabanta ke mugun faduwa ta marairaice cikin rawan murya tace "But i don't understand the meaning of this sir, ina ne nan ka kawo ni plss? This i almost 8pm, nasan ana ta nemana a gida" Tana kai wa nan ta fashe masa da kuka sosai, Musharraf dake ta kallonta yace "Kin zata son da nake maki iya baki kadai ya tsaya? An gaya maki na taɓa yi ma wata mace irin son da nake maki banda mahaifiyata? You think i have d strong heart to loose you just like that? You think bazan yi duk wani abu da zai sa in mallake ki ba?" The way he is talking kadai ya isa ya kara tsoratata, ita dai ta kasa cewa komai sai kallonsa take da manyan idanuwanta, kawai taga ya kamo hannunta ya sauko da ita daga cikin motar ya kulle, bugun zuciyarta ya tsananta she was so afraid of him a moment din nan, he doesn't look the gentle Dr Musharraf she knows, bin sa kawai take yana rike da hannunta, she don't think he is even okay, sai da ya fara kunna solar din gidan sannan suka iso entrance din parlon gidan, ta ga ya ciro makulli ya bude kofar, suna shiga ya sa ma kofar key ya zare, bata san sanda ta fashe masa da matsanancin kuka ba ta durkusa gabansa tana girgiza kai tace "Na shiga uku, sir don girman Allah tell me the meaning of this? Ina ce gobe ne fa daurin aurenmu, menene ya sa kuma zaka kawo ni wani waje da daddaren nan daga ni sai kai?" Musharraf ya girgiza mata kai yace "They are not prepared su daura mana auren gobe...." Yana fadin haka yayi hanyar dakunan dake parlon, Mayraah that was so confused ta bi sa da kallo zuciyarta na bugawa, gashi ya amshe mata waya ya kashe tun suna hanya, tayi zaman dirshan a wajen ta hade kai da gwiwa tana kuka cikin tashin hankali, ko dai dama ba sonta Dr Musharraf yake ba kawai yaudaranta yayi, sai kusan karfe takwas da rabi ya fito daga dakin da ya shiga, yanzu kam wani mugun tsoronsa take ji har cikin ranta, yana kallonta yace "Tashi ki je kiyi sallah" Ta kasa kallonsa tsabar tsoro kuma bata motsa daga inda take ba, yace "Ba ki ji me nace bane" Mikewa tayi zuciyarta na bugawa, ya nuna mata daki da zata shiga, kamar munafuka ta shiga inda ya nuna mata tana waigensa. Har Mayraah ta idar da sallah hawayen dake sauka idonta bai tsaya ba, ta takure waje daya saman darduman da take zaune wasu sabbin hawayen na saukowa idonta, what will she tell her parent and her brothers, ina zata ce masu ta je tun wajen karfe biyar har gashi yanzu tara ake nema na dare, kafin su zo nan tafiyar kusan awa daya da rabi suka yi a hanya, yanzu idan yace zai maidata gida ai sai wajen goma da rabi kilan za su isa ko sha daya, is he even ready to take her back home today? Tunanin hakan ya sa ta fashe da kuka sosai, bude kofar dakin aka yi, ta hadiye kukan da take ta koma baya a tsorace taki barin su hada ido da shi, ya shigo cikin dakin yana kallonta, ta sunkuyar da kanta hawaye wasu na bin wasu a cheek dinta ga wani faduwa da gabanta yake, ya duka dab da ita ya ajiye cup din fresh milk dake hannunsa a gefenta, he was just staring at her for almost a minute, cikin raunin murya yace "Saboda ina sonki yasa nayi haka Mayraah, wallahi i can't imagine me without you, ni kaina bansan irin son da nake maki ba Mayraah, plss kiyi min uzuri i only have this option...." Sai a sannan ta daga idanuwanta da suka yi ja tana kallonsa, kamo hannunta taga zai yi tayi saurin matsawa a tsorace without noticing d cup he kept by her side ta wuntsular da shi gaba daya milk din ya malale kasa, tun kan ya dagata har yayi soaking hijab din jikinta, yayi kasa da murya yace "I am sorry" Ta dake muryarta na rawa tace "Bana son kana taɓa ni don ni ba muharramarka bace" tana fadin haka ta juya masa baya duk da yanda gabanta ke faduwa, kallonta kawai yake, can ya juya ya fita daga dakin, Mayraah ta shiga bandaki da sauri ta cire hijab din jikinta, er doguwar riga ce a jikinta mara nauyi, ta wanke hijab din da detergent da ta gani a bandakin snn ta shanya inda taga towel a ajiye, har zata fito sai kuma ta koma ta dau towel din ta lullube jikinta da shi tana fitowa dakin ta gansa yana goge inda madaran ya zube, ta sunkuyar da kanta ta koma daya side din ta zauna kan carpet tana kallon agogon dakin, bayan ya gama goge wajen ya fita da mop din. Mayraah bata sake ganin Musharraf ba har kusan sha biyun dare, sau uku bacci barawo na sace ta tana farkawa a tsorace don babu kwanciyar hankalin yin bacci, ga duk tunaninta yana wajen Amminta, ko wani hali take ciki yanzu, daga karshe ganin karfe daya yayi ta mike a hankali ta nufi kofar dakin ta bude making sure bai yi ƙara ba, ta dinga bin corridor din dakunan da kallo, can tana tafiya a hankali ta shiga parlon gidan, a mugun tsorace da shock ta koma baya ganinsa kwance tsakiyar parlon idonsa a lumshe daga shi sai singlet with 3 quarter, ga empty kwalaben alcoholic wine guda uku a gefensa da roban fresh orange juice wanda shi kadae ne bai gama shanye wa ba, tsabar gigicewa bata san sanda ta karasa parlon ba don tabbatar da kwalban me take gani haka, ta durkusa ta dau kwalba giyan daya ta zaro ido tana karanta rubutun jiki, bata san sanda ta saki kwalban ba har sai da ya tarwatse tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" mikewa taga yayi zaune da sauri yana kallonta da jajayen idanuwansa, a guje ta tashi ta koma dakin da ta fito jikinta na rawa zata saka key amma taga babu key jikin kofar, ta durkushe kasa tana zaro ido tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku" Bude kofar dakin taga yayi ta mike da gudu ta koma can karshen gado ta fashe da kuka don tsoro ta kasa cewa komai ta hade hannuwanta biyu tana kallonsa, kana ganin idanuwansa kasan he is drunk amma kuma he is calm at the same time duk da tafiyar ma da kyar yake yi amma he is not staggering, saboda gigicewa Mayraah bata san sanda ta shige bayan labule ba da taga ya nufota tana cewa "Don girman Allah kayi hakuri ka rufa min asiri sir" Ya bude labulen ya janyota ta rirrike hannunsa cikin kuka tace "Nooo don Allah ka rufa min asiri sir, i am begging you pls..." Yayi hugging dinta cikin calm voice dinsa that is shaking yace "Kar ki bari a rabamu Mayraah, i don't know what will become of me, i...." Kasa ci gaba yayi, ita kuwa ko ina na jikinta rawa yake, ya jinginar da ita da bango underneath his breathe yace "Say something pls wife" Bakinta na rawa tace "Bazan bari a rabamu ba, i promise you, trust me" Yana kallonta da lumsassun idonsa yace "Can i kiss you pls?" Ta rike hannunsa ta wani zaro ido har sannan jikinta na rawa amma cike da karfin hali ta dake ta masa murmushi tace "Not now, u need to brush and freshen up first, i just caught u with bottles of wine isn't it...." Ya hade goshinsa da nata, da kyar yace "Orange juice was the last i drank..." Ai kam she could perceive the flavor of orange as he speaks, bata ankara ba sai jin bakinsa tayi a nata, she struggled to free her self amma ta kasa saboda irin rikon da yayi mata, hawaye ya dinga sauka idonta duk jikinta na rawa, bata kara gigicewa ba sai da taga ya fara canza salo, bata san sanda wani dakewa ya kuma zuwa mata ba tace "Ermm, i am very hungry pls sir, ina son in ci abinci kasan ban ci komai ba" Tana fadin haka kuwa ya saketa, she was still shaking don lokaci daya gaba daya yanayinsa ya canza, kamar me counting din words dinsa yace "Should... i.... get you some fresh.... Milk?" Ta gyada masa kai da sauri bakinta na rawa tace "Yes, yes yes plsss, i need it" Juyawa yayi ya nufi kofa, ta fara kalle kallen dakin, tana ganin ya fita ta nufi bandaki da gudu ta shiga taga babu key shi ma a ciki, sosai hankalinta ya tashi ta sake fitowa a gigice ta fita daga dakin, sauran dakuna uku dake corridor duk ta ji su a kulle an sa makulli, ta daura hannu a ka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku, wayyo Ammi" Tana nan tsaye sai gashi ya taho rike da cup din fresh milk din, ta sauke hannunta ta hadiye kukanta da sauri trying her best to stay calm duk da yanda kirjinta ke heaving, ya nufota yana mika mata milk din, Mayraah ta amshi cup din tana kirkiran murmushi tace "Thank you so much, babu bread or chin chin?" Jingina yayi da bango alamar tsayuwar na neman gagararsa yace "Ba...bu" Ta hadiye wani abu da kyar tace "Ohk, let me sip it little by little don yayi sustaining dina" Yana kallonta da idonsa da suka dawo so sexy murya can kasa yace "Ohk, ok..." Dukawa tayi nan kasa ta zauna tana satan kallonsa ta kai cup din baki tana kurban madaran da taji sa kamar magani a bakinta, da kyar ta hadiye banda bugawa babu abinda zuciyarta yake, still bata fasa satan kallonsa ba taga shi ma ya zauna nan kasa yana facing dinta kamar zai hadiyeta saboda kallo, yau sai taji bata son kamshin turarensa dake kara mata sonsa a da, tunanin yanda zata janye hankalinsa daga abinda taga alamar yake son yi ta shiga yi don bata ga alamar kuka da pleading dinta zai canza masa wannan ra'ayin ba she just need to use her brain, shi ko bai fasa kallonta ba, Can dai dubara ya zo mata bayan ta kara kurban madaran a hankali tana kirkiran murmushi tace "But tell me sir, me yasa kake tunanin za a raba mu bayan kasan ina sonka sosai, kai ma kuma kana so na" Ya gyara zama kamar me rada yana maganar da daddaya da daddaya yace "Ba a son mu yi aure Mayraah, ance ba su Ammi da Abba bane suka haife ki, they said they are not ur Biological parent...." Mayraah ta sauke cup din bakinta tayi still tana kallonsa babu ko kiftawa jin abinda yake cewa, ya kalleta yace "Ko in kawo maki note din da aka dinga kawowa gidanmu akanki" Mayraah ta maida cup din milk gefenta tana gyada masa kai tace "Kawo min" Mikewa yayi taga ya shiga parlor this time around he is staggering alamar giyan ya fara hitting dinsa hard, ta bi sa da kallo babu ko kiftawa abinda ya fada na kai koma a kanta, bayan few minutes sai ga shi ya dawo ya zube mata Envelopes har hudu a gabanta ya zauna yana kallonta, Mayraah ta dauki daya ta bude da sauri ta fara karanta content din, ta fi minti daya tana sake nanata karatun kamar dai tana son fahimtar abinda ake nufi, can ta dau wani ta bude shi ma ta nanata yafi sau hudu, haka Mayraah ta dinga bi tana karanta duk takardun cikin envelope din, kana ganinta kasan she is confuse at this point, Musharraf ya kamo hannunta yana murzawa a hankali yace "Abbanki bai musa ba, yace haka ne, ba su ne suka haifeki ba, shine dangin babana suka ce bazan aureki ba don baki da asali, Mayraah even if u were born out of wedlock ni Musharraf bazan taɓa rabuwa da ke ba, ko ma wacece ke a haka nake son ki nothing can ever change that, Baby don Allah kar ki bari a raba mu, kawai mu yi rayuwanmu just i and you... we can go to Abuja a daura mana aure daga nan i will take you to Maldives mu yi rayuwarmu a can ki haifo min cuties kamar ki, i know my Mami won't be against that...." Mayraah ta zame hannunta a hankali daga nasa don duk abinda yake cewa bata ma san yana yi ba, kawai abun da ta gama karantawa ne ke ta mata yawo a kai tana sake nanatawa a zuciyarta, bata san sanda ta matsa daga kusa da shi ba tana girgiza kai tace "Noo, kawai dai ana son raba mu ne amma Abba da Ammi su ne suka haifeni they are my parent, it's all a lie" lokaci daya har hawaye ya cika idonta, Kawai gani tayi ya rungumeta a rikice yace "Yes love, karya suke yi, kawai suna son rabamu ne, plss don't let that, permit me to show u how much i love you today, tomorrow and forever..." Tashin hankalin Mayraah ya dawo sabo fil ganin ya dawo mata kamar wani zautattce, ganin abinda yake kokarin yi, ta dake tana gyada masa kai da sauri tace "Toh, to, to amma pls ka bari in yi wanka, kai ma kaje kayi wanka first...."
_Double update for june 10_🎊
*Alhamdulillah, it's another June 10🎉🎊🎈 for me, Allah ya karo min shekaru masu albarka, Thanks for d well wishes fams, i appreciate u now and always, Allah ya saka da Alkhairi... Nayi discount for the book Mayraah yau, every other book nakan yi haka on every june 10, so you can pay just 300 naira into*
3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
To gain access to reading the book till the end hankalinki kwance babu burden or hakki akan ki....
Ur evidence of payment via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
[6/10, 8:43 PM] Khaleesat Haiydar💖: Mayraah bata tsaya taji abinda Musharraf zai ce ba ta kama hannunsa duk da yanda gabanta ke faduwa ta nufi Bedroom da shi tana cewa "Zan saka maka warm water kayi wankan yanzu so u can feel much better" Bin ta kawai yake zuwa dakin yana kallonta babu ko kiftawa, suna isa bandakin ta kallesa tace "Wait for me here" Ba musu ya Jingina jikin kofar bandakin yana bin ta da ido, zuciyarta na bugawa ta karasa can ciki tana ɗan satan kallonsa sannan ta shiga tara masa ruwa a bathtub, har ta gama sannan ta juya tana kallonsa, a lumshe taga idonsa a yanda yake jingine da kofar, ta nufesa tayi kasa da murya tace "Kaje kayi wankan" Ya buda ido bai ce komai ba, bude kofar bandakin tayi a hankali ta fita sannan ta kulle, ta sauke wani ajiyar zuciya feeling a bit relieve now, sai kuma ta fara tunanin what next, da sauri ta fita zuwa parlor, nan ta hau dube duben makullin da ta ga ya zare sanda suka shigo gidan, amma babu shi babu alamarsa a parlon, lokaci daya jikinta yayi sanyi, ta zauna nan kasa hawaye cike idonta tana tunanin yanda zata yi to keep on distracting him daga intention dinsa, a sanyaye ta mike ta nufi wani kofa da ta gani a parlon, kitchen ta gani ta dinga bin ko ina da kallo, can ta nufi fridge ta bude, tsoro ne ya kamata ganin cike yake da alcoholic wine irin wanda ta gani a parlor sae orange juices, lokaci daya jikinta yayi sanyi sosai, fitowa da wine din ta dinga yi tana ajiye su a sink with tears in her eyes, duk sai da ta bi ta bude su ta tuttular a cikin sink din ta bar kwalaben wajen ta fita daga kitchen din duk jikinta a sanyaye, corridor ta koma idonta ya sauka kan takardun da Musharraf ya dauko ya ajiye mata wani mugun faduwa gabanta ya sake yi, maganganun da ya gaya mata akan takardan ya dinga mata yawo a ka, wai an fasa aurensu saboda abinda aka rubuto a takardun nan, amma me yasa iyayensa za su yarda da wannan karyan da makirci, ta yaya bayan kowa yasan su waye iyayenta amma za a rubuto wannan karyan har su yarda, hawaye taji ya kawo idonta da ta tuna yace mata parent dinsa sunce bazai aureta ba, kenan dama gobe baza a daura masu aure ba? But did her parent know about what is happening? ta fi minti daya tsaye tana kallon takardun hawaye na bin kuncinta, can ta durkusa a hankali ta daukesu gaba daya, sae da ta sake karancesu sannan ta jefar wajen ta saka kuka, amma how will somebody just sit down and forge this lies har a yarda?? Ta hade kanta tana ci gaba da kuka a hankali, sosai taji zuciyarta ya mata rauni, Kakarin amansa ta dinga ji daga bandaki, ta daga kanta amma bata motsa daga inda take ba, jin shiru har bayan minti talatin ta mike a hankali ta leka dakin, kwance ta gansa nan tsakiyar dakin yayi ruf da ciki idonsa a lumshe, ta lallaba ta koma ta sake zama a corridor din tana jin zuciyarta na bugawa, yanzu ya zata iya idan ya sake riskanta a nan? ko da wasa wani yace mata Dr Musharraf na shan giya baza ta taɓa yarda ba, don bai yi kama da masu sha ba, he is too gentle and calm for this, mutumin da ko magana ma bai damesa ba how on earth zai zama mashayin giya??? ta fashe da kuka mara sauti don abubuwan yanzu sun taru sun dagula mata lissafi, maimakon