Showing 144001 words to 147000 words out of 249515 words
Shine yanzu zaka saka mata da wannan tozarcin Mamuda?" Abba dake sauraronta yana kallon TV, ya ɗan yi murmushi ya girgiza kai yace "Baaba ban kara aure don in tozarta ta ba, na karo aure ne saboda babu yanda zan yi hakan shine kadai mafita a gareni da yarana, baaba a duk abubuwan nan da suka faru in za ayi alkalanci tsakani da Allah ke kanki kinsan na kauda kai nayi hakuri na kuma nuna komai ba komai bane...." Mama Ladi ta share hawayenta tace "Sarai nasan wannan, don juya ka suka dinga yi kamar sun samu waina, su ce wannan su ce wancan kuma kana ta bin su babu musu har na so inji haushinka wallahi" Abba yace "Yauwa baaba, na bi su yanda suke so a lokacin nan don a zauna lafiya, duk yanda suka ce haka ake yi, a tsarinsu na karshe ne naga bazan iya ci gaba da goyon bayan zalunci ba, na kuma nuna ma ita Ammin bazan yarda da haka ba shine ta debi kayanta ba fada ba komai ta bar gidan nan, baaba fisabilillah akwai wanda Mayraah ta sani a duk duniyar nan bayan mu?" Mama Ladi ta gyara zama tace "Ina fa?? Yarinyar da ku kanku baku san asalinta ba balle ita da sai kwanan nan ma tasan ba ku ne iyayenta ba" Abba yace "Kinga da farko Ammi ta nuna Hajja tace bazata sake rikon Mayraah ba, na danne zuciyata na nuna ba komai tayi ma mahaifiyarta biyayya kawai, nace Mayraah ta koma gidan kanina wato ɗan yayan mahaifina shi ma iyalansa suna nan garin kano shine dai yake legas, Maheer ya nuna gidan yayi nisa daga makarantar ta sai dai ta zauna gidansa kawai, duk aka amince saboda dai Ammi ta samu kwanciyar hankali gun mahaifiyarta, wannan duk bai isa ba sai gashi sun billo da wata maganar wai bazata zauna gidan Maheer ba sannan nan din ma Ammin bazata riketa saboda son zuciya irin nasu da rashin binkicen asalin abinda ke faruwa, ina ake son yarinyar ta tafi fisabilillah ga jarabawarta na karshe zata zana? ban da ni me hakuri ne wa za ayi ma haka a zauna lafiya Baaba? Yarinyar da tun tana jaririyarta ake tare da ita yanzu da girmanta a billo mata da haka don ma tana da strong mind? Ina ake son in kai ta to?" Mama Ladi tayi kasa da murya tace "Ka ma yi kokari wallahi Mamuda don ba ko wani namiji bane zai dauki wannan iskancin ba zancen gaskiya, kuma Allah ya maka albarka yanda ka dinga bin duk abinda suka ce da farko kana ta kauda kai...." Abba yace "Auren nan kuma da nayi, nayi sa ne kawai saboda babu yanda zan yi, Baaba kema kinsan babu ta yanda za ayi kana tare da mace babu zagi ba cin mutunci ta tattara kayanta ta koma gidansu kuma mahaifiyarta na kallonta amma tayi shiru ta barta ta ci gaba da zama bata saka ta koma gidanta ba" Mama Ladi tace "Ita fa Hajja ka rufa ma kanka asiri ka daina sa ta a sabgar nan, don wllhi gobe ma nake son mu kai ta asibiti a duba mana kwakwalwarta don tsufan duk ya rikirkitar da ita abun dai ba kyau" Abba ya sauke ajiyar zuciya yace "Na ƙaro aure ne saboda bazai yiwu ace Mayraah na gidan nan babu babban mace dake saka mata ido ba, sannan yayyinta duk ba gidan suke ba a ko da yaushe, in ma suna gidan to yanzu duk sun san su ba muharraman juna bane.... Kin ga ai abinda zai yiwu shi ake yi" Mama Ladi tace "Kul, kar ka sake cewa ka karo aure saboda Mayraah ka kara goga mata baƙin fenti a shiga uku, me ya kai ka fadan haka? kai dai kawai kace ka karo aurenka saboda baza ka iya zama babu mace ba, kai ni ban ma yarda cewar saboda wannan ɗan matsalar ka tashi kaje kayi wannañ gantalallen auren ba Mamuda, dama can kana da bazawararka a boye kuna tadinku, kar ka raina min hankali kawai" Abba yayi murmushi yace "Ko daya, hada ni aka yi da ita ma" Mama Ladi tayi mitsi mitsi da ido tace "To Allah ya tsine ma koma wanene ya hadaka da ita" Shi dai Abba bai ce komai ba, Mama Ladi tace "Kuma yanzu ka tashi mu koma can bangaren Ammi da bakinka ka gaya mata ka kara aure, don babu rashin mutunci ace namiji ya dankara ma mace kishiya babu saninta, ko mata dari zaka aura baka da sama da Ammi kaji in gaya maka, maza tashi mu je ka bata hakuri sannan kasan inda zaka kai kishiyar don baza su zauna gida daya ba suna gogan kafada da katuwar matar da ka auro, ai na ganta wata sandan sandan kamar er Ghana" Abba dai kallonta kawai yake, ta mike tana gyara yafin gyalenta tace "Ka tashi mu tafi nace ko" Ya ɗan yi murmushi don bai son yi mata musu amma ba don yayi niyyar hakan ba ya mike ya bi bayanta suka koma main house zuwa bangaren Ammi, Mama Ladi ta bude kofar taga akwatunan Ammi an sake fito da su parlon, Mama Ladi ta rike haɓa tace "Ji shashasha...." Abba dai ya nemi kujera ya zauna babu yabo babu fallasa, Aunty Mariya ta leko daga dakin jin muryar Mama Ladi tana ganin Abba ta hade rai ta koma cikin dakin Ammi, Mama Ladi ta shiga dakin tana kallon Ammi dake kulle last box dinta tace "Fito fito, hada akwatuna ba naki bane" Daga haka ta bar dakin, Ammi ta fito tare da last box dinta, tana ganin Abba cikin bacin rai tace "Me ka biyo ni nan ka gaya min kuma? Dama in kasan ba takardata ka kawo min ba ka tashi ka fita bana bukatar ganinka, takardan kuma in ma kaki badawa to za mu hadu a kotu ne" cikin tsawa Mama Ladi ta kunduma mata zagi tace "Takardan uwaki? Baki san gidan mijin shine rufin asirinki ba gode gode dake? A baki takardanki ki tafi ina wai? Ai yanzun ma kawai kin hada akwati ne a banza don in har na isa dake to babu inda za ki, kin dawo dakin ki kenan, don mu ba kananun mutane bane, kuma mu ba gantalallu yan iska bane" Cikin kuka Ammi tace "Wallahi ban dawo ba Mama Ladi don minti biyar bazan kara a gidan nan ba, Maheer ne kawai ya cuce ni ya takura rayuwata na dawo banda haka wallahi har abada ni da gidan, kuma a yanzu zan sake komawa inda na fito ya zauna da warce ya auro, idan nayi masa halacci a rayuwa zai sani wataran...." Mama Ladi tace "Kaji mahaukaciya, to wallahi ko Hajja bazata maki baki ya kamaki ba kamar yanda ni zan maki ya kama ki, tunda naji ance ranan gobe kiyama ma ni zaki gani ba Hajja ba, haka dai naji ance, don haka in kin isa ki fita gidan nan mu ga, tun farko da kin ji ta nawa ai da duk haka bai faru ba Ammi, kishiya kuma dama nace masa baza ki zauna da ita ba, in ma ta bar maki gidan ya kama mata haya ko kuma ke ki bar mata gidan ya gina maki wanda yayi ukun wannan, ai shi Mamudan ba ɗan iska bane yasan abinda ya kamata..... Karfe biyu saura Mama Ladi ta sauko downstairs daga part din Ammi duk ta hada zufa tsabar sulhun da take ta kokarin yi tun karfe sha daya take abu daya har yanzu da ta fito shi ma saboda lokacin sallah ne yayi Mamuda zai je masallaci, tana fifita da gyalenta cikin bacin rai tace "Tirrrr, tunda uwata ta haifeni ban taɓa kai wa warka ban ci abinci ba akan abinda bai shafeni ba, tun shayi da ɗan burodi da na ci da safe fa, ita kuma wannan mata Ammi Allah wadaranta, Allah wadaran hali irin nata, don wannan taurin kai ko a kafurai ba a samun me shi gaskiya, kai ko a dabba ma yanzu a daina samun masu taurin kai haka, ni ko nace in ta haifu cikin Sadiya da Ubale ta bar gidan nan taga tsiyar da zan mata wallahi, ita ko ɗan kuturun gidan Hajja bazai sa ta hakura ta zauna cikin rufin asirinta ba, mata sae kace kanwar shaidan don ma Mamudan me hakuri ne, to uban wacece ita da baza a ma kishiya ba ma dai tukun, kishiyar da rubabbiyar uwarta ce ta ja mata kowa ya sani, sam ni Ladiyo bana goyon bayan rashin gaskiya, abinda shegiyar amaryar da ke tafiya tinkis tinkis da duwaiwuka ba kanki zata zauna ba ina ruwanki da ita, to ni dai ba ruwana na daina asaran kudi na kan Ammi, in ma taki jin maganata ta koma kuturun gidan Hajja ni dai ina nan wallahi tallahi" Hajiya Amina ce ta sauko downstairs ita ma, Mama Ladi tayi tsit tana bin ta da kallo, Hajiya Amina tace "A kawo maki darduman nan ne Mama?" A fusace Mama Ladi tace "Ke ni fa ban ci komai ba fa sai ɗan burodi da shayi da safe" Hajiya Amina tace "Toh kiyi sallan zan hado maki abincin yanzu in sha Allah" Mama Ladi tace "Aa bari dai in fara ci don yunwar ta gigita ni wllh, kada inje sallan bai yi dai dai ba" Hajiya Amina tayi murmushi kawai ta shiga kitchen, Mama Ladi ta dinga murmushi ganin uban liyafan abincin da Hajiya Amina ta hado mata kamar wata matar sarki, babu abinda bata taɓa a abincin ba don sai da ta kusa cinye duk abincin tass, ta kwankwade shayi me ƙauri da ta hado mata sannan ta tafi bandaki tayi alwala tana cewa "Alhamdulillah" ko kafin ta fito Hajiya Amina ta shimfida mata dardumanta me laushi da kamshi, bayan Mama Ladi ta idar da sallah ta koma bangaren Ammi tana ta murmushi tunda ta koshi, har a sannan Ammi kuka take a parlor, Aunty Mariya na ta bata baki, Mama Ladi ta kyabe baki ta kishingida kan carpet tana sakace hakori tace "Mariya ga abinci can me shegen dadi Aminar ta dafa da zuka zukan kaji ki rufa ma kanki asiri kije ki deba ki ci kar ya kare, na ji tace har da na Umar Usman yaje daukosa a filin jirgi sun iso" Ko kallonta Aunty Mariya bata yi ba ta koma daki don tuni Ammi ta mike ta shige daki, Mama Ladi tace "Kishiya sai kace kanki farau, abinda na ga Aminar ma na da hankali da biyayya, ina laifin wanda ya mutunta naka, tun dazu take ji da ni a parlor, sai kinga liyafar da ta hada min na abinci ko iya cinyewa ban yi ba, to ni dai ba ruwana wllh..." Mayraah dake kwance ta daga kai tana kallon Hajiya Amina da ta shigo dakinta, mikewa zaune tayi tana kallonta, Hajiya Amina tace "Ko dai baki da lafiya ne Mayraah?" Mayraah ta girgiza kai tana murza ido don ko kallonta bata son yi tace "Bacci nayi" Hajiya Amina tace "It's almost 3pm ki fito ki debi abinci ki ci" kai kawai Mayraah ta gyada mata, ganin Hajiya Amina taki fita yasa Mayraah ta sauko daga kan gadon, har sannan taki yarda ta kalleta, Hajiya Amina ta bude kofar dakin ta fita Mayraah ma ta fito tana tafiya a hankali, ita kanta tasan she is not okay she is just trying to be fine, Hajiya Amina ta shiga nata dakin, Mayraah ta sauka downstairs, tun da tayi ido hudu da Ammi bata sake bude dakinta ba sai yanzu da Hajiya Amina ta shigo, bude kofar parlon aka yi Usman ya shigo Umar na biye da shi da jakansa a hannu, Umar na ganinta ya ajiye jakarsa yana kallonta, can ya nufeta yana murmushi, duk da maganganun da Usman da Maheer suka masa na ringing a kansa hakan bai hanasa rungumeta ba kamar yanda ya saba duk sanda ya dawo, yace "Me kika dafa min Mimi?" Usman dai na tsaye yana kallonsu, Mayraah tayi murmushin karfin hali kawai ta kasa ce masa komai ya daga kanta yace "Are you sick?" Kai ta gyada masa tace "Amma da sauki" bata jira cewarsa ba ta nufi jakarsa ta dauka tace "Welcome back home bro" Daga haka ta tafi dakinsa dake downstairs, Umar ya bi ta da kallo sannan ya kalli Usman, zaunawa yayi kan kujera ya rike kansa, Mayraah na zuwa dakinsa wanda tun da sassafe Hajiya Amina ta gyara masa ta ajiye jakarsa sannan ta fito, bata sake kallonsu ba ta shiga kitchen, Usman ya bi bayanta, yana shiga kitchen din ta juya ta kallesa, yayi kasa da murya yace "Kin shiga kin gaida Ammi?" Ta girgiza masa kai alamar A'a, ya ɗan yi shiru sannan yace "Yanzu me za kiyi?" Tace "Abinci zan zuba ma Ya Umar" Yace "Ke kin ci abincin?" Ta girgiza masa kai, yace "Debi naki kawai ki wuce daki, idan kin gama ci ki tafi ki gaida Ammi" Ta gyada masa kai, kasa cin abincin Mayraah tayi bayan ta deba ta tafi dakinta, can dai ta rufe ta mike ta fita daga dakinta ta nufi bangaren Ammi tana tafiya a hankali gabanta na faduwa, parlor ta bude a hankali kamar me tsoron taɓa handle din, tana shiga Mama Ladi dake ta zuba gyangyadi ta bude ido, gyara zamanta tayi da mamaki tace "Mera? wai dama kina gidan nan?" Mayraah ta gyada mata kai ta zauna kasa cikin sanyin murya tace "Ina wuni" Aunty Mariya da har a lokacin bata gaji da ba Ammi hakuri ba ita kanta tayi mamakin jin muryar Mayraah don ta ma mance ta tambayi Maheer ko ya dawo da ita, Ammi dake zaune gefen gado bata daina kuka ba ta mike ta nufi kofar dakinta ta saka makulli, jikin Aunty Mariya yayi sanyi ta bi ta da kallo, Mama Ladi ta kalli kofar dakin jin an kulle da makulli, taɓe baki tayi tace "Tashi kiyi tafiyarki in baki ci abinci ba ki samu Aminar kice ta baki abinci, ta girka lafiyayyen abinci me kyau, nima ban dade da gama ci ba" Mayraah dai sai kallon kofar dakin Ammi da taji an sa makulli take, Mama Ladi tace "Ko kin ci abincin?" Mayraah bata son taga hawayen da ya kawo idonta ta mike tace "Aa, zan ci yanzu" Daga haka ta juya ta fita ta koma dakinta, fadawa tayi kan gado ta dinga kuka tana jin zuciyarta na mata zafi... Babu yanda Aunty Mariya bata yi da Ammi kan ta gyara mata bangarenta ba don yayi ƙura Ammi ta ki daga karshe ta rufe Aunty Mariya da fada, Aunty Mariya ta ja bakinta tayi shiru.... Wajen karfe shidda Aunty Mariya ta fito rike da handbag dinta da akwatin Mama Ladi tana kallon Mama Ladi dake ta kallon TV a parlor ga bowl din fruits cike a gabanta tana sha, ganin Aunty Mariya ta washe baki, bata ko lura da akwatinta dake hannunta ba tace "Kin ga yanzun nan ta kawo min wannan Mariya, anya kuwa ba er kirki bace matar...." Aunty Mariya ta wani hade rai tace "Za mu koma gidan Hajja ne" Sai a sannan Mama Ladi ta lura da akwatinta dake hannun Aunty Mariya, ta ajiye slice din kankanan hannunta tace "Ajiya kika min a akwatin ne kika dauko min?" Aunty Mariya tace "Ae tashi za ki yi mu tafi magariba ya gabato" Mama Ladi ta matsar da bowl din gabanta kamar zata yi kuka tace "To gidan uwarki na zo da za ki ce in tashi mu tafi Mariya? Ko ina ruwanki da ni fisabilillahi idan ba neman magana ba?" Aunty Mariya tace "Yanzu Mama Ladi ko wani yace ki kwana gidan nan sai ki kwana bayan kin san abinda ke faruwa?" A fusace Mama Ladi tace "Aa ban san komai ba wallahi, wani sabon abun ya faru ne bani da labari? Ke ni fa ba yarinya bace Mariya da zaki kawo min raini zan ci uwarki la'ada waje wallahi, shi kansa Mamudan sai da ya tambayeni yace amma zan kwana biyu kafin in koma ko, nace masa to tunda yace haka bari in zauna zuwa kwana biyun kuma shine zaki zo min da rainin wayo da maganar banza, ina ruwanki da sabgata, gidan uwarki ko gidan mijinki?" Ajiye akwatin Aunty Mariya tayi ta fice daga Parlon ta bar gidan, Mama Ladi tace "Yau naga fitinanniyar yarinya kai, haka zan kama hanya in tafi in bar Ammin cikin wannan damuwan bazan zauna in dinga kwantar mata da hankali ba, sannan ga maganganu cike cikina da zan gaya mata game da tsinanniyar surkarta warce ni da kaina zan ja Hajja mu je gidan Mashir din da sassafe bayan na laka ma Hajjan karya Sanisar bata da lafiya rai a hannun Allah daga nan zan turketa ta fadi mugun abinda tayi da bakinta dama ga turarena da kasko na taho da shi a jaka, to ga dai na kishiya ya tabbata ko daga nan ai bai kamata a dinga shashantar da lamarina ba, ni ba boka nake bi ba Malaman gaskiya da suka san addini nake mu'amala da" Mama Ladi ta kare tana huci ta jawo bowl din fruit dinta tana sha..... Throughout ranan sai bayan magrib Maheer ya shigo gidan tun da ya fita da Haseenah da Badiyyah, dawowar da yayi yanzun ma don Ammi ta kirasa yafi sau uku tana son ganinsa ne amma da bazai zo ba, yana shigowa parlor ya tadda Mama Ladi da Hajiya Amina zaune parlon ga malmalan tuwo biyu a gabanta da miyan vegetable da yaji nama, Maheer ya karasa ya gaishesu, Hajiya Amina ta amsa, Mama Ladi tace "Ta zubo maka tuwon ne kai ma?" Maheer yace "Aa ai daga gida nake" Sama ya haura, direct ya nufi bangaren Ammi, zaune ya ganta a Parlon da Usman da Umar, alamar dai shi kadai ake jira, zaunawa yayi don tun dazu sun hadu da Umar a gidansa, sai da ma Usman ya fara kai sa gidansa har suka sanar masa abubuwan dake faruwa kafin su taho gida tare da Usman, a