Showing 102001 words to 105000 words out of 249515 words

Chapter 35 - Mayraah Hausa Novel Complete

20 Nov 2024

1530

yayi kasa da murya yace "Sleep tight my love..." tace "Thank you..." Daga haka ya katse wayar Mayraah ta lumshe ido. Washegari har karfe takwas Mayraah bata tashi ba don bazata school yau ba tunda Dr Musharraf yace mata bazai je ba, dama kuma friday ne, tana tashi wajen takwas da rabi ta ga miss calls din Ammi tun 5am, kiranta tayi yana fara ring Ammi ta daga, sun kusa 15 minutes suna magana da Ammi daga karshe suka yi sallama, Mayraah ta sauka daga kan gadon ta shiga bandaki, wanke baki tayi, tayi wanka sannan ta fito... Bayan ta gama shiryawa wajen goma saura taji anyi knocking din kofar dakinta, ta mike ta isa bakin kofar ta bude a hankali, Maheer ta gani tsaye, yana kallonta with smile on his face yace "Good morning Mimi" Tace "Ina kwana yaya" Yace "Lafiya lau, how was ur night?" Tace "Alhmdlh" Yace "Yau baza ki school ba?" Tace "Eh" Yace "Ohk, fito ki debi breakfast" juyawa yayi ya bar bakin kofar ya koma parlor ta bi bayansa tana tafiya a hankali, zaune ta tadda Haseenah a parlor ga breakfast din da tayi ma Maheer a tsakar parlon tana kokarin hada masa shayi tana cewa "Baby special tea fa na dafa maka yau, bana jin ka taɓa shan irinsa wllh" ya zauna kan kujera yace "Really" Tayi er dariya tace "Sai ka dandana zaka gane..." Kamar ance ta daga kai taga Mayraah a parlon, nan da nan ta hade rai sosai, Maheer yace "A ina kika koyi dafa shayin?" Banza tayi masa tana saka cube din sugar a shayin, ya kalli Mayraah yace "Zauna mana Mimi" ta zauna edge din kujera tana kallon Haseenah tace "Ina kwana" Ciki ciki Haseenah ta amsa fuskarta a murtuke kamar hadari, Maheer ya sauka daga kan kujeran ya zauna kan carpet ya dau plate ya debar ma Mayraah irish din da kwai, sannan ya hada mata shayi me ƙauri, yace "Amma lectures ne baku da shi yau ko dai kawai zuwa school din ne baza ki yi ba Mimi" Mayraah tace "Kawai bazan je ba" Yace "Ohk sai kiyi karatu a gida, sauko kiyi breakfast" Mikewa Haseenah tayi fuuu ta wuce daki kamar zata tashi sama, Mayraah dai ta sauko kasa Maheer ya ajiye mata breakfast din a gabanta sannan ya fara hada nasa shayin da Haseenah ta bari, bayan ya gama hada shayin yace "Let me get my phone" Daga haka ya mike ya bi bayan Haseenah zuwa daki, Mayraah ta kyabe baki ta mike ta dau breakfast din ta kai daki ta ajiye sannan ta dau warmer din farfesunta na jiya ta tafi kitchen tayi warming, Maheer na shiga dakin ya kullo kofa yana kallon Haseenah cikin kwantar da murya yace "Me yasa kika taso Haseenah?" A mugun fusace tace "Bazan taso ba? Ta yaya zan sha wahala in tashi da asuban fari in mana girki ka debar ma yarinyar dake kwance tana bacci tun jiya da daddare?? Ko na ce maka ciki uku nayi ma breakfast din? It's just for me and you don ma kaji in gaya maka, Idan ba ma rainin wayo ba tsabar ka daure mata kugun ta raina ni yanda ta ga dama ta yaya ita bata tashi ta nema mana breakfast ba ni zan yi kuma ka debar mata?? Maheer tell me who does that??" Maheer yace "Amma fa jiya da na maki magana ce min kika yi kin fi so kiyi girkinki da kanki" Cikin daga murya tace "Toh sai nace maka har da ita zan yi ma girkin ko ita kuturwa ce da bazata nemi abinda zata ci ba a gidan? Maheer wllh na gaji da wannan walakancin daga yau na daina dauka sai dai duk abinda zai faru ya faru" Maheer yace "Ki daina daga min murya haka Haseenah, i am being patient all this days amma u are trying to push me to the wall" Ta mike tsaye tana huci kamar zata bangajesa tace "Har outside of the wall zanyi pushing dinka babu abinda ya sha min kai, wllh a duk duniya babu macen da zata dauki wannan abinda ake min in za a cire son zuciya, meyasa zan tashi da sassafe yarinya na bacci inyi wahala inyi breakfast ko bakina ban kai ba balle kai da nayi ma ka ci, zaka wani cika ma yarinya plate ka kwashi kwai ka lafta mata??? Duka duka irish din guda nawa na soya har zaka kwashe ka cika mata plate? Ko ita ta soya min??" Calmly Maheer yace "Toh ni bazan ci ba, ki cinye sauran tunda ba shi da yawa idan naje office zan nemi abinda zan ci, and you know what?? Gwara da haukanki ke tsayawa iya kaina Haseenah, don daga sanda kika yi gigin fara yi ma Mimi to za a ji kanmu gaskiya, ni za ki min inyi hakuri in shanye amma wllh kar ki kuskura ki ce za ki yi mata, ni ki ci gaba da min kawai i will endure, zan kuma ci gaba da baki hakuri" Yana kai wa nan ya dau makullin motarsa ya fice daga dakin ta bi sa da kallo baki bude.... Mayraah ta fito kitchen kenan da plate din kazarta da tayi warming, ganinsa a parlon tace "Yaya are you going to work?" Yace "Yea, u need anything?" Shiru tayi tana kallonsa, yace "Ko za ki je asibitin?" Gyada masa kai tayi, yace "Ohk, i will wait for you je kiyi breakfast dinki" Tace "Okay" Daki ta koma ya zauna parlor yana jiranta, Kuka wiwi Haseenah take a daki kamar ranta zai fita, yau kawai ji tayi da za a bata wuka wllh zata iya caka ma Mayraah ta huta, yanzu duk hakuri da ƙauda idon nan da take kamar yanda Salima tace ance tayi ya tashi a banza kenan, ita fa ba don umarnin Salima ba kilan da tuni tayi ma Mayraah duka a gidan duk abinda zai faru ya faru, amma ance ta bi komai a hankali, to tana ta kokarin kai zuciyarta nesa gashi yanzu rainin wayon da ake mata ma gaba yake yi maimakon baya, tana jin fitar motar Maheer a gidan ta fito da sauri tana huci ta shigo parlor tana leka compound ta tabbatar eh ya fita tunda taji ai yana cewa Mayraah baza ta makaranta ba, dawowa tayi ta koma kofar dakin Mayraah ta murda ta ji a kulle, kundume kundumen zagi ta fara tana jijjiga kofar kamar zata balla tana cewa "Shegiya tsintattciya mara asali ki bude kofar mana kiga ikon Allah yau, wallahi sai dai wata ba ke ba a gidan nan, hakurin da nake yi ya ci kaza kazansa, an daina hakurin daga yanzu, wallahi sai na canza maki kamanni ta yanda baza a gane ki ba yau" Bata fasa jijjiga kofar ba tana kundume kundumen zagi duk zaton ta Mayraah na ciki, kamar mahaukaciya ta fita daga gidan ta zaga bayan windown dakin Mayraah nan ma tana bubbuga glass din ta dinga cewa "Don kaza kazanki ki fito mana ki ga aiki da cikawa" Ta gama zuba haukanta ta koma ciki sai a sannan ta lura da babu takalmin Mayraah a bakin kofa, da sauri ta koma gun mai gadi tana tambayarsa ko Maheer kadai ya fita nan ya sanar mata ai har da karamar Hajiya, komawa ciki tayi ta baje a parlor ta dinga rusa kuka, wallahi Salimah ta cuceta da fa yanzu an wuce wajen, kilan da har an samar ma Mayraah wani wajen zama amma ba nan ba, daki ta koma ta dau wayarta ta kira Salima taji a kashe, ta zauna gefen gado tana kukan baƙin ciki da takaici, wata zuciyar ta raya mata to ko dai asibitin zata bi su ne, wani yace mata a'a a gida ya kamata ayi duk abinda za ayi a wuce wajen, ta share hawayenta tana nazari iri iri a ranta bata taɓa shiga bacin rai da baƙin ciki irin wannan ba, wayarta ne ya fara ring ta jawo da sauri a tunaninta Salimah ce, sai ta ga kawarta ce Zaliha, yanda take da Badiyyah haka take da Zaliha duk bata wani yarda da su ba bata gaya masu sirrinta, ta daga wayar ta kai kunne Zaliha tace "Meye duniya Haseenah daga aure sai kiyi watsi da mu ki canza layi?" Haseenah ta sauke wani ajiyar zuciya tace "Ba haka bane Zaliha ina cikin damuwa da tashin hankalin da baza ki gane ba, kuma ban canza layi ba wani lokacin kashe wayar nake ko zan samu sassauci" Zaliha tace "Ikon Allah, me ke faruwa Haseenah? Kuma gashi da yau zan zo gidanki, shine ma nace bari in gwada layin ki yau" Haseenah ta ɗan yi shiru sai kuma tace "Ke da wa za ki zo?" Zaliha tace "Ni kadai ce, yanzu haka ma na shirya wllh" Haseenah tace "Toh zan gaya ma mai gadi ya bude maki gate, sai kin zo" Zaliha tace "Toh shkkn, sai na iso" Haseenah na katse wayar ta fita zuwa gun mai gadi tace "Musa zan yi bakuwa idan ta zo ka bude mata gate" Yace "Toh Hajiya" Juyawa tayi ta koma ciki, wajen karfe sha biyu saura tana zaune parlor har sannan ta kasa shan ko ruwa, warmers din da ta ajiye na breakfast da tayi har sannan suna tsakar parlon taki kwashewa, knocking din kofar parlon ta ji anyi ta mike tana kallon agogo ta karasa ta bude kofar, sai da cikinta ya kusa shigewa cikinta ganin Badiyyah da Zaliha a tsaye bakin kofar....




MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah


Ur evidence via 07087865788
[6/29, 9:05 PM] Khaleesat Haiydar💖: Badiyya ta yi wani tsalle ta finciko kwalar rigar Haseenah ta ja ta zuwa cikin parlon tana huci ta cire gyalen jikinta da handbag tayi cilli da su cikin daga murya tace "Fito min da gold dina kar in maki shegen duka, yau karyar ki ta kare kuma tunda har Allah yayi na shigo gidan nan" Zaliha ta riko Badiyya da sauri tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una meye haka Badiyyah? Dama abinda yasa kika dage mu zo kenan, dama abinda kika shirya kenan salon ki sa Haseenah ta fara min wani gani gani, ni wllh da na san abinda za ki zo kiyi kenan bazan yarda mu taho tare ba, meye haka don Allah" Duk da tashin hankalin ganin Badiyya da Haseenah ta shiga a lokacin ko da wasa bata yarda ta nuna hakan a fuska ba, sai wani dakewa da tayi tana kallon wani wajen daban, Badiyya na huci tace "Zaliha kin san tun yaushe nake bin matar nan ta ta bani kayana amma ta maida ni er iska er wahala? To wallahi ko ta fito min da gold din nan yau ko kuma in nakada mata shegen duka yanda mijinta bazai ganeta ba idan ya dawo, haka akwai daga abun arzki? Tana da gado na ne ko kuma akwai bashi ne tsakaninmu? Har kofar gidan nan na zo ranan mai gadi yace ba kowa a gidan kuma jikina ya bani tana ciki kilan Maheer ne kawai baya nan, sannan in dai na kirata sai in ji waya a kashe, duk sanda na ci sa'ar samunta kuma sai taki daga kiran, kin ga alamar rashin gaskiya kenan ko? to wallahi bazan yarda ba tunda ba uwarta ta min hustling gold din ba, don haka a yau ta bani kudina ko gold, idan ba haka ba duk abinda nayi mata ita ta ja ma kanta" Haseenah ta wani kyabe baki tace "To cikani in dauko waya in kira mai siyan gold din yanzu a gabanki, idan ya kama in hada ku ma sai ki amshi number sa kawai" Cikin daga murya Badiyya na jijjigata tace "Ina ruwana da me siyan gold da za ki hadamu? Saninsa nayi ko meye hadina da shi? kawai abinda na sani shine a bani gold dina ko kuma kudi, idan ba haka ba hukuma ta rabamu" Zaliha ta rike hannun Badiyya tace "Don Allah kiyi hakuri ki saketa ta dauko wayar tukun Badiyya, kin fi kowa sanin halin Haseenah fa, wllh Haseenah bazata cuce ki ba...." Da kyar Zaliha tayi convincing Badiyya ta sake Haseenah tana huci, Haseenah ta juya ta nufi dakinta, da farko niyya tayi ta kulle dakin da makulli tayi zamanta a ciki idan sun gaji da jiranta su tafi, wata zuciyar tace kai in dai Badiyyah ce sai ta iya zama har magariba a gidan in kuma hakan ya faru Maheer zai iya dawowa ya sameta, ta san tsaf Badiyyah zata iya mata sharri tace ita ce ma tace ta dau gold din, ita kam tsoron Badiyya take... Haseenah ta dau wayarta tana zaga dakin tana tunanin yanda zata yi, nan da nan idea ya zo mata tayi dialing number wani tsohon saurayinta da sauri ta shige bandaki ta kulle, babu bata lokaci ya daga yace "A'a Big gal an tuno da ni kenan yau" Haseenah tace "Wani big girl Biliya ina cikin tashin hankali, na kiraka ne ka taimaka min" Yace "To faa, kar ki ji komai Big gal fadi abinda ke tafe da ke kanki tsaye...." Cikin minti daya biyu ta gama yi masa bayanin duk abinda ke faruwa tsakaninta da Badiyyah sannan ta sanar masa plan din da take so su yi tare da shi, yace "Ba ki da case, ina jiran kiran naki" Katse wayar tayi ta fito daki da sauri, a bakin kofa suka kusa cin karo da Badiyya zata shigo dakin, Badiyya na mata wani kallo tace "Dauko wayar ce kusan minti biyar??" A takaice Haseenah tace "Aa Malama ki saurara min, mijina ne ya kirani na tsaya nayi attending masa, kuma ni kin ban mamaki da har za ki bar Zaliha ta ji tsakaninmu, na zata abotanmu ya wuce haka da ke" Bata tsaya ta saurari Badiyya ba ta fito parlor ta fara dialing number Bilyah tana tsaye, Badiyya ta karaso parlon tace "To Zalihar uwata ce ita da zan ji tsoron gaya mata abinda ke tsakaninmu da ke, da kin bani Gold dina ta yaya ma Zaliha zata ji kanmu har za ki ce na baki mamaki da Zaliha ta ji kanmu??" Haseenah ta kasa cewa komai jin abinda Badiyyah ke cewa, Zaliha dake kallonta tace "Ohh gani bare ko Haseenah? To ai shikenan bari inyi tafiyata" Haseenah ta rikota tace "Aa Zaliha ba haka nake nufi ba, ki tsaya ayi komai gabanki ki zama shaida" Har kiran da Haseenah take yi ya katse Bilya bai dauka ba, Badiyya ta fara girgije girgije tace "Heheee, let it not be what i am thinking Haseenah, don wllh wllh bazan yarda ba, ko da uban wa kike yawo sai kin bani Gold dina ko kudina" Haseenah ta sake kira nan ma bai daga ba, hakan kuma duk yana daga cikin plan din nasu, sai da ta kirasa sau uku sannan ya daga yace "Ke wai ya zaki ta damuna kullum da kira kamar wanda zai gudu ne?? Why are u disturbing me plss sai kace bamu saba harka da ke ba" Haseenah tace "Ni dai ka dawo kasar ko baka dawo ba?" Yace "Ban dawo ba, nace maki ina dawowa za a bada kudin ko, kina abu sai kace ban san ki ba baki san ni ba" Haseenah tace "Me shi ne ta takurani wllh, tana ga kamar na cinye mata kudi ko wani abu..." Bilya yace "Ita da aka samu za a siya stuff din nata babu reciept, wa ya sani ma ko sato sa tayi za mu yi taking risk mu siya saboda ke shine kuma zata yi ta takura mutane, wllh ko wa zata kai ma gold din nan bazai siya babu reciept ba, sannan ba pure gold bane wllh, kinsan gold din step by step ne to nata karami ne" Zaliha ta zaro ido jin abinda Bilya ke cewa, Haseenah tace "Kai dai babu ruwanka da wannan kudinmu muka sani kawai, nawa ne kudin ma kace?" Yace "Sau nawa zan ce maki miliyan daya da rabi za a siya, kawai account zaki ajiye ina shigowa kasar inyi transfer" yana fadin haka ya katse wayar, Badiyya da tayi mitsi mitsi da ido tace "Kan uba, shi gold din da kika ce min ya kusa miliyan biyar ne naji ake cewa miliyan daya da rabi, ni za a cuta??" Haseenah na kallonta da kyau tace "Ke bari kiji in gaya maki Badiyyah, an fa daina siyan Gold babu reciept a garin nan, wannan ma alfarma kawai ya mana saboda ni, kuma ni kudina na yin har wata daya biyu a wajensa, ko kwandala bai taba cinye min ba" Badiyyah ta girgiza kai tace "Inaaaa, bazai yiwu ba gwara kawai a bani Gold din na fasa siyarwa wllhi tallahi, in ya kama ma sai in sa abina inyi kwalliya kawai" Haseenah tace "Toh sai mu jira ya dawo kasar, ina jin Umra ya tafi, wannan wani irin rayuwa ne, Cousin dinki ya daura min pressure, tsinanniyar yarinyar da aka kawo min gida ta daura min pressure, kema yanzu ga shi kin zo da naki, ke da ya kamata inji dadi ta wajenki, wai ya ake son inyi ne??" Badiyya ta zaro ido tace "Ita Mayraahn kika bari take daura maki pressure?" Kamar jira Haseenah take ta fashe da kuka amma ba hawaye tace "Badiyya da za a bani wuka ina jin babu abinda zai hanani kashe yarinyar nan in huta, ban taɓa jin tsanar mutum kamar yanda na tsaneta ba, ki tambayi Zaliha ko da ta kirani dazu ai kuka nake saboda abun duniya ya isheni" Zaliha tace "Kwarai kuwa, kuma na gaya ma Badiyyar haka amma da yake bata da mutunci ji abinda ta zo tayi maki" Badiyya ta nemi waje ta zauna tace "To ai ni na zata duk zance Zaliha ke min, ban san da gaske bane, wai sai kika yi shiru kika zuba mata ido Haseenah?" Haseenah ta zauna kasa tace "To bari ki ji me kankat Badiyyah, yau breakfast na tashi tun asuba nayi mana ni da shi, wallahi gari na wayewa ya kwashe ya bata kun ga sauran nan ko taɓawa ban yi ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login