Showing 63001 words to 66000 words out of 249515 words

Chapter 22 - Mayraah Hausa Novel Complete

20 Nov 2024

1526

dangin uwa gareni a can ko na uba, daga dai aure ya kai ni can miji ya mutu ya bar ni yau shekara goma sha biyu, to ina ruwana kuma da wani karaye, Badiyya ce dai sai an mata hukuncin da ya kamata don ko rantsuwa nayi bazan yi kaffara ba zata iya kashe mutum, ke kuma da kike daure mata kugu idan ba ayi hankali ba sai ta iya zama ajalinki, ni tsoronta ma nake yanzu wllh, duk wanda zai iya lalata aure babu abinda bazai iya aikatawa ba a duniya, kuma Mamuda ne kadai ya isa ya koreni a gidan nan" Tana kai wa nan ta fice daga dakin, Hajja dai kuka kawai take, cike da karfin hali Ammi tace "Shikenan Hajja in sha Allah maganar nan ta wuce, babu me tada sa kuma, har su Maheer din zan masu magana, sannan kamar yanda kika bukata na maki alkawarin Mahmud ma bazai ji wannan maganar ba in sha Allah, Allah Ubangiji ya shirya mana ita" Hajja na share hawayenta tace "Ameen, Allah ya maki albarka Hajarah" Aunty Mariya kasa cewa komai tayi tsabar bakin ciki da takaici, can ta mike ta fice daga dakin, Hajja ta kalli Ammi tace "Ki tashi ki koma dakinki, Allah ya maki albarka, Allah ya baki lafiya ingantacce" Ammi tace "Ameen" sannan ta mike ta fita daga dakin, downstairs ta sauka don she needs to find a place tayi kukan nan ko zata ji sanyi a ranta, ta shiga dakin baƙi dake parlor ta tadda Aunty Mariya tayi tagumi, Ammi ta zauna dakin ta fashe da kuka tana girgiza kai tace "Shekara kusan ashirin da biyu kenan ake a haka, sau dayawa ina yin abinda nake ne don kada Hajja taga kamar ina fifita Mayraah da ban haifa ba akan Badiyyah da take jinina, don Hajja mahaifiyata ce nasanta ciki da bai, sai ku ga kamar ina goyon bayan Badiyyah a ko da yaushe amma ba a san duk don a zauna lafiya nake yin haka ba tunda gani za ayi na fifita Mayraah a kan er kanwata uwa daya uba daya, yanzu dai kinga yanda ta bi ta kakkare ta rufe wannan maganar ko?" Aunty Mariya da zuciyarta ke tafarfasa tace "Kuma wllh kada kice ma su Maheer komai, Allah ya kawo Badiyyar gobe da safe su fara ball da ita tun daga bakin gate" Ammi tace "Ki rufa min asiri Mariya, tun da tace in ja masu kunne gwara in ja masu babu ruwansu duk su zuba ido kawai, Allah shi yasan dai dai" Wajen karfe tara da rabi Maheer ya bude kofar parlon Ammi ya sameta zaune da Hajiya Safiyya ga plate din abinci a gabanta, yanxu kam she looks much better tun da gashi har tana cin abinci, ya zauna saman kujera yace "Ammi ya jikin?" Ammi na kallonsa tace "Alhamdulillah" Shiru yayi, yana son tambayar Mayraah amma ya kasa, can dai ya mike daga karshe ya fita, a stairs ya hadu da Aunty Mariya tana haurowa sama yace "Aunty Ina Mimi?" Aunty Mariya tace "Tana dakin Ammi" yace "Okay" Aunty Mariya tace "Wai ka ci abinci ma kuwa Dr?" Yace "Zan ci" Daga haka ya koma parlon Ammi, Bedroom dinta ya nufa direct ya bude kofar ya shiga, kwance ya sameta kan gado idonta a lumshe har ta fara bacci, ya karasa kusa da gadon ya zauna gefenta yana kallonta, hannu ya kai forehead dinta yaji her temperature is a bit high, ta bude ido da sauri suka hada ido, sai kuma ta mike zaune ta matsa daga edge din gadon ba tare da ta bari sun kara hada ido ba, yace "Kin ci abinci?" Ta gyada masa kai, yace "Ur injections and medicine" Ta girgiza kai tace "Aa maganin kawai zan sha" Yace "Ai maganin guda daya ne, kuma alluran ya kamata a maki" Mikewa yayi ya fita daga dakin, ba a dau lokaci ba ya dawo da ledan dake dauke da alluran da magani, tana kallonsa ganin ya fara hada alluran, tayi gathering courage tace "Zan yi alluran da kai na" Ya kalleta a bit surprise, Bata sake barin sun hada ido ba, Bayan few seconds ta sake cewa "Kawai idan ka gama hadawa ka bani inyi" Still shi dai bai ce komai ba, tun daga sanda ya zama likita har zuwa yanzu shi ke mata allura idan bata da lafiya, yawanci every month end sai yayi mata alluran cramps, ya ajiye syringe din bayan ya rufe sannan ya juya ya nufi kofa ta bi sa da kallo, ita kanta duk jikinta yayi sanyi, Yana fitowa parlor ya kalli Hajiya Safiyya da yake nurse ce, yace "Mama ana jirana a waje yanzu, ga alluran da za ayi mata can na sa a syringe" Daga haka ya fice daga parlon Ammi ta bi sa da kallo, Hajiya Safiyya ta mike ta shiga dakin, bayan ta gama yi ma Mayraah alluran ta fito, sai a sannan Mayraah ta lura da wayarsa da ya ajiye bedside drawer, ta dauka tayi searching number Musharraf sannan tayi dialing, a kashe ta ji wayar, lokaci daya jikinta yayi sanyi ta ajiye wayar ta koma a hankali ta kwanta da tunani iri iri a ranta... Washegari wajen karfe tara da rabi Aunty Mariya ta shigo parlon baƙi da sallama duk aka amsa mata, kallo daya tayi ma Badiyya dake zaune kasa ta sunkuyar da kai kamar algunguma ga Hijab har kasa a jikinta, Aunty Mariya ta nemi waje a parlon ta zauna ta gaida yan uwan mahaifin Badiyya da kanwarsu Hajiya Murja dake zaune parlon, ko minti ashirin ba ayi da zuwansu gidan ba, dama Aunty Mariya sai da ta tsaya ta gama sallaman su Haseenah da yan uwanta with breakfast sannan ta shigo parlon bakin shi ma don kada Hajja tace bata je bane banda haka da ko keyarta baza su gani ba, Hajja na zaune kasan carpet tayi tagumi, Ammi ma na parlon a zaune, sai Maheer da zuciyarsa ke ta tafarfasa, shi kam Usman dama kin zuwa yayi, Mama Ladi kuma Hajja tace in ta shigo bata yafe mata ba, Alhaji Nura ya daka ma Badiyya tsawa rai bace yace "Baza ki bude baki kiyi magana ba kina bata mana lokaci" Ta fashe da kuka me karfi tana bubbuga kafa tace "Wallahi kawu nace maku ban san komai kan zancen nan ba, kaji har na rantse, ni babu wanda nabi na kai ma wani takarda, a ina nasan su? balle in kai takarda?" Kuka take sosai tana rantse rantse bata san zancen ko wani takarda ba ita, Alhaji Garba yace "To a ina kika samu labarin an daga aure har kika gaya mana?" Cikin kuka tace "Matar yaya Maheer kawata ce ita ta kirani take ce min an daga aurensu ni kuma sannan ina Bichi, kilan kawai bata son in zo bikinta ne, zuciya daya na yarda da abinda tace min ni kuma na gaya maku, amma ni ban kai ma kowa takarda ba, to ma a ina nasan gidajensu? in kuma ana ganin karya nake a kai ni gidajen da suka ce an kai masu sai su fadi ko ni ce na kai masu, kawai don an ga ni marainiya ce bani da kowa sae Allah" Tana kai wa nan ta fashe da matsanancin kuka har da kifa kai a carpet tana shessheka kamar ranta zai fita, Aunty Mariya tsabar mamaki ta kasa rufe baki tana kallon Badiyya, Maheer ji yayi kamar ya tashi ya tattakata a wajen ya rufeta da duka, Ammi kuwa dama bata dago kanta ba, Hajja na matsar kwalla tace "Ni dama ina ta tunanin ta inda za ace Badiyya tasan gidajen mutanen nan da suka ce an kai masu takarda, Badiyyar da kowa yasan babu inda take zuwa daga gidana sai Bichi sai gidan kawarta wato matar Maheer da aka daura aure jiya, don ko gidan nan wllh sai nayi da gaske take zuwa, amma to an bi ance ita ce ta dinga kai ma jama'a takarda...." Kowa dai yayi shiru a parlon, Maheer yayi da ya sanin zaman nan da ake yi da shi, he wish bai shigo ba, kuma banda bai son daga hankalin Ammi babu abinda zae sa yayi shiru a wajen, Aunty Mariya tayi saurin mikewa tace "Lahh na fa daura abu a kitchen Ina zuwa..." daga haka ta samu ta fice daga parlon don kar takaici ya kar ta..... Bata san yanda aka karke ba dai daga karshe sai ga Badiyya ta shigo main parlor Hajja na biye da ita a baya tana gaya mata dakin da su Haseenah suke, Badiyyah sai wani hade rai take tana kumbure kumbure, kuma ko gaida Aunty Mariya bata yi ba ta haura sama, sai a sannan ta sauke wani bayanannen ajiyar zuciya tana murmushi ta nufi dakin da su Haseenah suke tana bude kofar ta saki guda....



MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah


Ur evidence via 07087865788



*Assalamualaikum everyone... ina sanar da ku cewar muna saida samosa WRAPS masu gardi da crispy 50 pieces for 2000, Spring rolls wraps 50 pieces for 2800, i assure u Samosa and spring rolls wraps din masu kyau da inganci ne Plss patronize us via*👇🏻

09014996620 location kaduna....
Thank you ❤️🙏


+234 901 499 6620
[6/14, 7:15 PM] Khaleesat Haiydar💖: Badiyyah na shiga dakin da su Haseenah suke bakinta har kunne ta gaida Aunties din Haseenah sannan ta ɗare saman gado ta zauna kusa da Haseenah da Zaliha tana kyalkyala dariya ta ba ma Zaliha hannu suka cafke, sannan ta juya tana kallon Haseenah ta rike haɓa tace "Amarsu ta ango, kin ga yanda kika yi kyau kike wani glowing kuwa? anya Maheer zai gane ki idan ya ganki irin wannan canji haka? Ke wai me ya samu wayarki ne nake jin sa a kashe duk sanda zan kiraki" Haseenah da ta hade rai ta sauke ajiyar zuciya tayi kasa da murya yanda Aunties dinta baza su jiyo ta ba tace "Badiyya duk ke kika ja bikina ya dawo kamar na wata gantalalliya mara galihu, ban taɓa ganin warce aka ma irin wannan auren da aka min ba ko a kauye, kawaye na sai dariya suke min a bayana saboda cika bakin da na dinga yi akan bikin nan, daga karshe wae ace babu wani occasion da aka yi, a whole of my wedding? gown din dinner da na ci burin sa wa ya tashi a banza a hofi, banda Zaliha dake tare da ni da depression ya kama ni wllh" Tana kai wa nan ta fara matsar kwallan baƙin ciki, Badiyya ta ɗan kyabe baki tace "Ni duk ba wannan zancen ba, ban ga kin turo min kudin Stuff din nan ba har yanzu abu kusan kwana uku yau fa" Haseenah tayi mata wani shegen kallo a fusace tace "Ai kya bari a fitar da ni daga gidan nan tukunna dai ko? Wato ina gaya maki matsalata irin ke bai ma shafe ki din nan ba alhalin duk ke kika janyo wannan abun dake faruwa, tun fa jiya har yau ban sa Maheer a ido ba a matsayinsa na mijin da aka daura min aure, ko damuwa ya gan ni ma kamar baya yi" Zaliha ta sauke ajiyar zuciya tace "Kema Badiyya yanzu ba lokacin wani magana bane, kwantar mata da hankali za ki yi before anything" Badiyya ta taɓe baki tace "To ba dai tace ta ji ta gani ba, duk yanda na so ta hakura da Maheer din nan Allah ya bata wani Haseenah taki fahimtata, don daga karshe ma gaba ta dauka da ni, ɗan uwana ne fa, kuma baza ta ce min ta fi ni sanin mugayen halayyarsa ba, kawai mu dai fatan alkhairi za mu maki... Yanzu dai naji Hajja na gaya ma Uncles dina zuwa nan da sha daya za a tafi kai amarya gidanta...." Haseenah tayi tagumi murya can kasa tace "Badiyya duk ba wannan ba, wllh tun shekaranjiya hankalina ya kasa kwanciya, bazai kuma taɓa kwanciya ba in har da yarinyar nan Mayraah, na kasa samun sukuni idan na tuna matsayinta yanzu...." Badiyya ta rike haɓa tace "Yanzu nake samun labari ashe dai ta dawo daga guduwan da tayi, in dai kan wannan karamar alhakin ce ki kwantar da hankalinki da kafarta zata sake guduwa na har abada kuwa, wai baki yi trusting dina bane, tunda har na san yanda na bi aka fasa auren da Dr Musharraf kinsan ai babu abinda bazan aikata ba, haba ashe shi yasa kwata kwata na tsaneta tun tana karama, dama babu abinda muka hada da ita er tsintuwa ce kawai warce bata da asali, wa ma ya sani ko cikin shege uwarta tayi ta haifeta sannan ta jefar da ita ta gudu, da gani kasan ba er halaq bace yarinyar, shine saboda rashin tsoron Allah har ake fifitata a kai na a family, ai kam wannan duk ya kare yanzu tunda na gano wacece ita" Sauka Badiyya tayi daga kan gadon ganin flask ta bude tace "Ni fa ko karyawa ban yi ba muka taho...." Aunty Fauziyya tace "Ai ko duk an fita da sauran kayan kumallon sai dai kije kitchen" Badiyya tace "Bari in hado shayin" Badiyya na fitowa daga dakin Aunty Mariya kuma na kokarin shiga don sanar ma yan uwan Haseenah yanzu za a tafi kai ta gidanta su shirya, Badiyya taki barin ta hada ido da ita tayi saurin barin wajen ta sauka downstairs, Usman ta hango zaune kan dinning area, lkci daya ta juya ta koma sama ta fasa zuwa kitchen din..... Kaya kawai Badiyya ta canza ta fess uban turare ta yi daurin ture ka ga tsiya tana taunar cingam, hannunta rike da Mayafinta da handbag suka fito daga daki tare da yan uwan Haseenah da ita kanta Haseenar dake sanye da lapaya ta rufe rabin fuskarta, sai da aka fara kai ta tayi ma Ammi sallama sannan aka kai ta dakin Hajja, Badiyya ta zauna kusa da Hajja kamar zata shige jikinta, bayan Hajja ta kara yi ma Haseenah nasiha yan uwanta suka fita da ita daga dakin, Badiyya ta mike tana kallon Hajja tace "Kinga ki bani makulli kawai, don daga can gida zan tafi bazan dawo gidan nan ba gaskiya" Hajja tayi kasa da murya tace "Aa Badiyyah, ke dai ki dawo don sai gobe za mu tafi gida gaba daya har Ladi, so nake in kara ganin yanayin jikin Ammi yau" Badiyya ta wani murguda baki tace "To ina Mama Ladin?" Hajja tace "Kilan tana can gantali gidajen makota, daga zuwa unguwan mutane ta shiga gida yafi a kirga yanzu haka" Badiyya tace "Gaskiya ni dai gwara in koma Bichi in har da ita za mu tafi gida, wai ba an gama bikin ba me kuma take jira?" Hajja tayi kasa da murya tace "Banda abun ki ai jiya aka yi biki Badiyya, nasan nan da gobe zuwa jibi zata koma ita ma" Badiyya ta juya ta fice daga dakin tana murguda baki... Aunty Mariya na kallon Mayraah dake dakin Ammi tace "Ni ma kaina ai ba zama zan yi ba, ana kai ta zan juyo" Ammi dake zaune dakin tana jin su tace "Ki bar ta kawai Mariya tunda tace baza ta ba, kinga ita ma ba dadin take ji ba ai, daga baya idan Allah ya nufa sai taje ganin dakin amarya" Aunty Mariya tace "To shikenan sai na dawo" Dama tayi insisting ne Mayraah ta shirya su tafi don bata son tayi feeling neglected duk gidan an tafi kai amarya babu ita, don yanzu kamar taki sakin jiki a gidan, komanta sanyi sanyi take kuma a dar dar kamar dai bakuwa, tuni duk gidan aka watse kai Haseenah dakinta, Mayraah damuwar ta ya kasu kashi kashi yanzu amma babban abinda yafi tsaya mata a rai shine yanda bata samun Musharraf a waya, tun wayewar gari ta kirasa ya fi a kirga da wayar Ammi amma sai taji wayarsa a kashe, tana gama kiransa dama take clearing kiran a call log kar Ammi ta gani tunda tana da numbersa... saboda yanda ta sa abun a rai har ji tayi kirjinta ya fara mata ciwo, tana kwance bayan azahar idonta a lumshe duk da ba bacci take ba Ammi ta shigo dakin, Ammi ta zauna kusa da ita tana shafa kanta a hankali tace "Bacci kike daughter" Mayraah ta bude idonta sannan ta mike zaune tana girgiza mata kai, Ammi dai sai kallonta take, Abba ne ya karaso cikin dakin, lkci daya Mayraah taji zuciyarta ya karaya bayan sun hada ido, amma tayi kokarin ganin hawayen da ya makale idonta bai taho mata ba, Abba ya karaso har kusa da gadon he couldn't even look at her in the eyes again, bayan shirun few seconds yayi karfin halin cewa "How are you feeling daughter?" Ta kasa amsa masa sai gyada kai kawai tayi don tana buda baki tasan zata fashe da kuka, Ammi ta kalli Abba a hankali tace "Bacci take ne, anjima in ta tashi sai ku yi magana..." Abba dai bai ce komai ba, bayan few seconds ya juya ya fita daga dakin, Ammi ta mayar da ita ta kwantar tace "Or you need anything?" Mayraah ta girgiza mata kai hawaye na gangaro mata, Ita ma Ammi tuni hawayen ya kawo idonta, Mayraah ta riko hannunta tace "Ammi kin sha maganin?" Ammi ta gyada mata kai sannan ta mike ta fita daga dakin tana goge hawayen dake zuba idonta. Bayan Magrib Mayraah na zaune dakin Ammi ta idar da sallah, zuwa sannan babu kowa gidan duk yan biki sun watse, Ammi na parlonta ita ma ta idar da sallan tana zaune kan darduma, Mayraah taji Ammi na cewa "Baka tafi gidan ba bawan Allah?" Muryar Maheer taji yace "Zan duba jikin Mimi ne" a hankali Ammi tace "Naga ma bata cin abinci yanzu, ko maganin cin abinci za a bata?" Maheer yace "Bari in tambayeta ko da abinda take so ne" Ammi bata ce masa komai ba ya karasa cikin dakin, tun da ya shigo Mayraah bata bari sun hada ido ba, ya zauna gefen gado yana kallonta don tunaninsa addu'a take saman darduman, jin bai ce komai ba ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login