Showing 180001 words to 183000 words out of 249515 words
ta bi bayansa har a sannan kuma bata daina jin dizziness ba, awa biyu kawai tayi a theatre da wasu daga manyan likitocin asibitin har da wani ba indiye a cikinsu all trying to save the the lives of 4 people da suka yi mummunan hatsarin mota irin 'ya yan masu kudin nan, kawai daga taje mika wasu allurai da Matron ta bata ta kai wani likita ya tsayar da ita alamar bai ma san ranan ta fara aiki a asibitin ba, haka nan gabanta ya dinga faduwa duk da ko da suka yi clinical rotations dinsu back then in school she was one of the best student, but yanzu kam she is so nervous and afraid amma haka nan tayi composing kanta a wajen aka fara aiki da ita, Daga nan kuma bayan aikin awa biyu bata san sanda ta sulale kasa ba tsabar gajiya da dizziness shine likitocin dake wajen suka yo kanta da sauri. Mayraah na fitowa reception bayan Hafsat ta dauko mata jakarta da ledan uniform dinta tace "Allah ya sauwake Nurse Ilham, hope you are much better now?" Mayraah tace "Alhamdulillah naji sauki" Sauran nurses din dai sai kallonta suke kuma babu wanda dai yace mata sannu, Nurse Hafsat tace "Sae gobe kenan?" Mayraah tace "In sha Allah" Dai dai nan Dr Khalil ya sauko da makullin motarsa ya fita, Mayraah ta kara yi ma Hafsat sallama ta bi bayansa, nan ma duk aka bi ta da ido, suna barin hospital din bayan sun hau hanya Khalil yace "Amma a wani asibiti kika koyi aiki Ilham?" Sosai gabanta ya fadi tana kokarin tuna ko wani asibiti ta fada masa, ai ko nan ta kirkiro suna babu bata lokaci ta basa, yace "Wani gari kenan?" Ta ɗan kallesa tace "But i told u, a Bauchi nake" Yace "Yea na tuna, Shekara nawa kika yi kina koyan aikin?" Tace "Na ɗan dade fa" Yace "No wonder! but...." Mayraah taji gabanta ya fadi tana jiran jin but what, sai kuma ya karyar da kai ya fasa fadin abinda zai fada yace "Anyways it's fine.... u did a very good job dazu a theatre i was so impress kin ma fi wa enda suka yi karatun nurse din nutsuwa wajen aiki, you are so composed" Ta ɗan yi murmushi tace "Nagode sir" Yace "You are welcome" Bai sake ce mata komai ba har sai da suka yi tafiyar kusan minti ashirin ita dai sai bin cikin garin Abuja take da kallo, sai da suka shigo wani anguwa yayi horn bakin gate din wani gida aka bude gate din, ita dai har a sannan bata ji gabanta ya fadi ba ko kuma taji tsoro she don't even get the kind of trust she have for him daga haduwan sati daya da kwanaki, yana parking ya bude motar ya sauka ita ma ta sauka rike da ledan uniform dinta, wasu yara maza biyu yan shekara sha uku ne wanda da alama yan biyu ne ke ta ball a tsakar gidan suna ganinsa dayan ya dau ball din nasu ya rike a hannu a tare suka ce "yaya sannu da zuwa" Dr Khalil yace "Ba islamiyya?" A tare suka ce "Ai mun dawo" Gaida Mayraah suka yi ta amsa tana kallon kyawawan yaran, Dr Khalil ya kalleta yace "Mu je" Ba musu ta bi bayansa har suka shiga cikin parlon gidan, Wata elderly woman ce da bazata haura shekara 56 ba zaune parlon da mai aikin gidan suna hira, Khalil ya zauna kan kujera yana kallonta yace "Ummi ina wuni" Mayraah ta zauna kasa tana kallon matar da yace ma Ummi ita ma ta gaishta, Ummin tace "Aa tashi ki hau kujera mana" Mayraah ta ɗan yi murmushi tace "Aa nan ya isa" Ummi ta kalli Khalil din tace "Ashe kuna hanya ma ka kirani kenan" Yace "Aa ko fitowa ban yi daga office ba, Ummi za mu shiga theatre after magrib zan koma" Ummi tace "To Allah ya bada nasara" Yace "Ameen" Ya kalli Mayraah yace "Ilham feel at home" Daga haka ya mike sai kuma yace "Ummi ya jikin Inna?" Ummi tace "Ai bacci ma take ina jin" Yace "Ohk, kilan sai gobe zan shigo" Daga haka ya fice daga parlon, Ummi na kallon Mayraah tace "Sannu da zuwa Ilham, ya aikin?" Mayraah na murmushi tace "Alhamdulillah" Ummi tace "Yace min suleja kike ko" Mayraah tace "Eh" Ummi tace "Suleja kam ai yayi nisa, sai dai ki nemi alternative, Karima ki kai ta daki ga magariba ma ya gabato" Mai aikin ta mike tace "To Hajiya" Wani daki da ba kowa Karime ta kai Mayraah, Mayraah ta shiga ta zauna gefen gadon dakin. Bayan isha Mayraah na dakin da aka sauketa, wata yarinya kyakkyawa da bazata wuce 11 years ba na cikin dakin ita ma sai labari yarinyar ke ba Mayraah da turanci, tun da yarinyar ta kyallara ido taga Mayraah shikenan bini bini zata shigo dakin, Mayraah na kallon yarinyar tace "Har yanzu ai baki gaya min sunanki ba" Yarinyar ta kyalkyale da dariya tace "My name is Fatima amma ana ce min Mimi" Mayraah ta gyada kai tace "Nice name..." Yarinyar ta dawo kusa da Mayraah tace "Aunty ke ya sunanki?" A hankali Mayraah tace "Ilham" Dai dai nan wayarta ya fara ring, Mimi ta mike da sauri ta dauko mata ta kawo tace "Aunty in kin gama wayar ki kirani" Mayraah tace "Toh zan kira ki" Daga haka yarinyar ta fita daga dakin, Mayraah tayi picking call din don Dr Khalil ne ke kiranta, bayan sun gaisa yace "Hope you are comfortable Ilham?" Mayraah ta gyada kai tace "Sure, Nagode sosai" Yace "That is my in-laws house" Mayraah ta buda ido tace "Ban gane ba" Yace "Gidansu matana mana, that's her mother" Mayraah was shocked ta ma rasa abinda zata ce masa.....
[7/20, 7:06 PM] Khaleesat Haiydar💖: Washegari da safe Mayraah na zaune dakin da aka bata bayan tayi wanka amma ko leka parlorn gidan ta kasa yi, tun da Dr Khalil yace mata gidansu matarsa ne ya kawota jikinta yayi sanyi ta kasa samun nutsuwa har gari ya waye, Karime ce ta shigo dakin da sallama, Mayraah ta gaisheta Karime ta amsa da fara'a tace "Hajiya na kiran ki a parlor" Mayraah ta mike sanye da hijab dinta ta fita parlor, da ladabi ta gaida Ummi, Ummi ta amsa tace "Baza ki je aikin bane naga baki fito ba har takwas yanzu" Mayraah ta sunkuyar da kai tace "Zan je" Ummi tace "To ki shirya ki fito kiyi breakfast kafin nan driver ya dawo daga ajiye yara makaranta sai ya sauke ki asibitin" Mayraah tace "Toh Nagode" Daga haka ta mike ta koma dakin da ta fito, karfe takwas da rabi Mayraah ta sake fitowa parlor bayan ta shirya cikin uniform, tana fitowa Karime kadai ta tarar tana ta aikace aikace a parlon, Karime ta nuna mata dinning area tace "Ga kumallon naki can na kai maki" Mayraah ta mata godiya sannan ta karasa ta zauna, shayin ta hada, ta debi irish da kwai ta fara ci, ko bayan da ta gama breakfast din tana ta zaune parlor sai ga driver yana sallama bakin kofar parlor, Karime tace "Yauwa ga Dreban ya dawo, Hajiya ta shiga ciki ta kwanta tace ince maki Allah ya tsare" Mayraah ta mike tace "Toh nagode" Daki ta koma ta dauko handbag dinta da wayarta sai ledan scrub din ta sannan ta fito ta kara yi ma Karime sallama ta fita. Driver na ajiyeta bakin gate din asibitin ta sauka tace masa "Nagode" Yace "Allah ya tsare Hajiya" Daga haka ta shiga gate din asibitin. Kamar jiya yau ma haka Mayraah ta jigata a asibitin don daga shigowarta da safe wani Dr Balogun ya aika a kira ta zuwa theatre, ba kuma wani aiki tayi ba kawai surgical equipments suke kira by their names ita kuma babu bata lokaci take mika masu Instruments din, kuma ko sau daya bata yi mistake din ko daya ba, wani ma bata jira a tambaya take mika wa sanin function dinsa, 2 other senior nurses ne tare da likitoci biyu a theatre din giving them assistant, ba su suka fito theatre din ba sai bayan azahar, Dr Balogun na kallon Mayraah yace "Ur alma mater Madam?" Sosai gabanta ya fadi, sai ga wani Dr ya zo yana ma Dr Balogun din magana, sum sum ta bar wajen da sauri ta koma reception tana zare ido, Nurse Hafsat tace "Sai yanzu, sannun ku da aiki" Dai dai nan Wata nurse ta ajiye telephone din hannunta saman desk tana kallon Nurse Hafsat tace "Who is Nurse Ilham?" Nurse Hafsat ta nuna mata Mayraah, Nurse din ta kalli Mayraah ta sanar mata Dr Khalil na nemanta a office dinsa, Tun da Mayraah ta shigo asibitin basu hadu ba bata ma san ko ya zo ba ko bai zo ba, sai da tayi sallan azahar sannan ta tafi sama zuwa office dinsa, bayan ta shiga ta kulle masa kofa ta karasa har bakin table dinsa ta gaishesa, ya ajiye aikin da yake yi a laptop yayi mata izinin zama sannan ta zauna ta sake gaishesa ya amsa yace "You looked stressed, ai tunda kika bari Dr Balogun ya gano ki sai kinyi hakuri da shi, haka yake in dai ya lura nurse bata basa problem wajen aiki and she is composed kuma ta san abinda take shkkn duk zai yi aiki sai ya sa an nemo masa ita sai dai in bata duty ranan" Mayraah dai bata ce komai ba sai murmushi da tayi, yace "Nasan baki ci abinci ba ko?" Bai jira cewarta ba ya dau ledan takeaway ya mika mata, ganin bata amsa ba yace "Karbi mana" Ta sunkuyar da kanta tace "Bana son ina daura maka burden dina, i am suppose to get food my self ba wai ka siya min ba" Yace "Ki tambayi Nurse Hafsat in dai ban siya mata lunch ba to probably ban zo asibitin ba ko kuma bana duty ranan, i do this for most of the nurses, it's nothing a wajena" Mayraah ta amsa a hankali tace "To Nagode Allah ya saka da Alkhairi" Yace "Ameen, ya kika baro su Ummi" Mayraah ta kallesa da sauri, sai kuma tayi kasa da murya tace "Amma me yasa zaka kai ni gidan in-law dinka?" Yace "Bayan in-law nima mamata ce ai, bani da kamar ta a duniya...." Kallonsa kawai Mayraah take, yace "Ina da shekara biyar Mom dita ta rasu ta bar ni gun stepmom dina, i still remember vividly the maltreatment from my stepmom, yes it is still in my memory, duk abinda tace shi Dad dina yake yi ba shi da wani say may his soul rest in peace, dangin Mom dina sun so daukana a lkcn stepmom ta saka dad dina yaki amincewa su tafi dani, to cut everything short, Ummi that was our neighbor then ita ta daukeni ta kawo ni cikin nata yaran bayan tayi threatening stepmom dita zata kai ta kara kotu cause barrister ce, Babansu zainab ma haka, kowa na shakkar shiga sabgarsu a layin, even my dad couldn't confront her duk da gidan su Ummi was opposite to ours, few years later dad din nawa shi ma Allah ya masa rasuwa, Ummi and her husband are the reason i am who i am today, and after everything they gave me der daughters hand in marriage... though Zainab father is also late bayan aurenmu da shekara biyu..." A hankali Mayraah tace "Allah ya ji kansa, Allah ya ji kan iyayenka kai ma" Yace "Shi yasa naji tausayinki da kika ce min ur parent were late" Nan da nan hawaye ya cika idon Mayraah, yace "Ya ku ka yi da aunt dinki about inda zaki zauna saboda aikin?" A hankali Mayraah tace "Dama tace kayi min recommending area da zan iya samun wajen zama a nan since mu bamu san Abuja ba kai kuma a nan kake" Dr Khalil na kallonta yace "Ohk akwai kudin kama wajen da zaki zauna din kenan?" Ta gyada masa kai, yace "Meye Budget din ku?" Ta ɗan yi shiru, sai kuma tace "Ai ban san nawa bane ake renting waje a nan" Yace "Nasan baki sani ba, amma nawa ku ke da shi a kasa don in san irin wajen da za a samar maki gidan" Tace "Like 300k yayi?" Khalil ya gyara zama yana kallonta da kyau yace "Yanzu akwai 300k din a kasa?" Ta gyada masa kai, kallonta yake ko kiftawa babu, hakan yasa ta sunkuyar da kanta, Yace "Ilham" Ta daga kai ta kallesa yace "Kuna da 300k din kama gida me yasa baki yi registration din admission da kika ce an baki ba?" Ta hade rai tace "I told u sai da aka tara kudin na taho, kuma da na zo naga an riga ma an rufe portal na registration har ma sun kusa fara exams, kaga ai dole za a soke admission dina" Dr Khalil yace "Wani makaranta ne? And where is the admission list?" Mayraah taji wani zufa na keto mata amma ta wani daure fuska, dai dai nan aka kwankwasa kofar office din ta mike da sauri kamar jira take tace "Kilan patient ne...." Yayi izinin shigowa sai ga wata patient da yake da appointment da ita ta shigo office din, tuni Mayraah ta fice daga office din nasa, gaba daya ta kasa samun nutsuwa a asibitin har aka yi la'asar, Dr Khalil na shigowa daga masallaci Mayraah ta ki barin su hada ido a reception din sai duba file din wata mata take a shelf, ya wuce sama, komawa tayi ta zauna a hankali tana Allah Allah karfe shidda lokacin da yan evening za su amshi duty yayi ta kama hanyar suleja komin dare kuwa, 6 nayi dot Dr Khalil ya sauko ita ko har ta fito daga changing room rike da jakarta, tana ganinsa ta wani hade rai taki yarda su sake hada ido, duk yana kallonta, makullin office dinsa ya mika mata yace "Get me my laptop and bring it to the parking space Nurse Ilham" Ta amshi makullin ya fita daga reception din, ko da ta iso parking space bayan ta mika masa laptop din yace "Ina za ki yanzu?" A takaice tace "Gida" yace "It's late ki ce zaki kama hanyar suleja yanzu, so kawai gidan Ummi....." Katse sa tayi da sauri tace "Aa ni bazan je ba gaskkya" yace "Saboda me?" Tace "Gidansu matarka ce fa" Yace "It's nothing, nace maki nima gidanmu ne, matata tasan wanene ni, ko dazu da muka yi waya da Ummi ta tambayeni ke, i told her anjima zaki je can cause nasan baki da inda zaki zauna nan Abuja yau din ma" it took more than 10 minutes kafin Dr Khalil yayi convincing Mayraah ya kai ta gidan surkarsa, duk jikinta a sanyaye ta shiga gidan kamar munafuka shi ko dama yana ajiyeta ya juya, Ummi na parlor da sister dinta Rabi'ah warce ita ma ranan ta zo, Mayraah ta zauna kasa ta gaida Ummi, Ummi ta amsa da fara'a tace "Ya aikin?" Mayraah tace "Alhamdulillah" Ummi tace "To maa sha Allah, yace min har yanzu baki samu wajen ba ko?" Mayraah ta gyada mata kai, Ummi tace "To in kin ga babu damuwa kiyi zamanki a nan mana sai ki dinga komawa gida weekend, ni dama da yace wai gida kike nema ki zauna hakan bai min ba kina 'ya mace, dama hostel ne cikin makaranta da sauki wannan, amma gida kam bai kamace ki ba" Mayraah dai kanta na kasa, Ummi tace "Sai ki ma iyayen naki bayani in sun gamsu ba wani takura sai ki zauna nan abun ki kina zuwa aikin ki, abinda in kin fita tun safe sai karfe shidda, weekend kuma sai ki je masu gida tun da naga Auxiliary nurses basu fiye aiki weekends a asibitin ba" Mayraah ta daga kai tace "Toh Nagode sosai, Allah ya saka da Alkhairi" Ummi tace "Ameen sai ki shiga kitchen ki debi abinci" Mayraah tace "Toh, nagode" Mikewa tayi ta nufi dakin da aka sauketa, Rabi'ah da ta bi ta da kallo tace "Ummi wacece?" Ummi tace "Bakuwa ce" Daga haka ta mike tace "Bari in je lokacin sallah yayi" Mayraah ta kai minti sha biyar tana nazarin zaman gidan da Ummi tace tayi, anya zata iya kuwa, though taga matar is very kind amma ita sai abun yayi mata wani iri a kai, shi ko tsoro baya jin kar su zargi wani abu ko ayi tunanin budurwarsa ce ita, kauda zancen tayi kawai a ranta daga karshe ta mike ta shiga bandaki. Da daddare Mayraah na daki Ummi ta shigo dakin tace "Ilham zo ki duba magungunan nan da Khalil ya bada aka kawo dazu bai bada prescription ba" Mayraah tace "Toh" Mikewa tayi ta bi bayanta suka fita zuwa wani daki, Wata tsohuwa ce zaune dakin kana ganinta kasan bata da lafiya, Mayraah ta zauna tana kallonta tace "Ina wuni kaka" Tsohuwar bata amsa ba, Ummi tace "Hajiya ba lafiya Ilham, duba magungunan ki ga" Da kyar tsohuwar ta bude baki tace "Kar ki sake sa ni a bakin duniya kice bani da lafiya Zuwaira, na kuma samu lafiyata babu abinda yake damuna yanzu, aniyar kowa ta bi shi" Ummi na kallon Mayraah tace "Ilham in kin bude maganin sai ki bata" Daga haka ta fita daga dakin, Tsohuwar na kallon Mayraah cikin rawan murya tace "Ke kiji rainin wayo, ita da 'ya yanta fa suka sa min guba yau sati uku kenan ina fama jiki yaki dadi, amma duk wanda ya zo sai tace masa Hajiya ba lafiyaa, sai terere take min" Tana kai wa nan ta fashe da kuka, Mayraah dai sai kallonta take ta ma kasa cewa komai, ta karasa buda mata maganin ta mike mata, hannu na rawa ta amsa ta dau cup din ruwa, Mayraah tace "Sannu, amma jikin da sauki ko?" Tsohuwar tace "Ke ba wani sauki, yanzu haka duk jikina ciwo yake er nan, banda yaron nan Halilu ɗan albarka ai da na mutu mushe a dakin nan,