Showing 24001 words to 27000 words out of 249515 words

Chapter 9 - Mayraah Hausa Novel Complete

20 Nov 2024

1502

ba?" Prof Habibu ya kara kallon Mayraah yace "Ohh dama ita ce zai aura? Maa sha Allah, naji rumors wai a department din yarinyar take ashe haka ne...." Dr Mu'azzam yace "Gaskiya da alama Dr Musharraf na damun yarinyar nan kuma zai sa ta samu matsala, ke bari in gaya maki idan baki yi wasa ba zaki dawo 2.1 ne with the way i am seeing ur performance this semester" Prof yace "Kira min Musharraf din yanzu" Dr Mu'azzam yace "Ai na masa magana da nayi marking script dinta tun ran friday, i even showed him the script" Prof yace "Gaskiya ya bar yarinya tayi graduating da first class dinta, har muna tunanin zata breaking mana record din department din nan after 15 years" Dr Mu'azzam yace "That is my main concern wallahi prof, first class that she has been retaining tun daga level 1 sai yanzu a level 5 zata yi wasa da shi" Dr Mu'azzam ya kalleta yace "Madam leave my office, gwara tun wuri ki maida hankalinki" da kyar Mayraah tayi masu godiya ta juya ta nufi kofa, lkci daya hawaye ya kawo idonta, ita kanta bata san me ke damunta semester din nan ba, abinda Musharraf din ma sae yayi sati biyu bai je gidansu ba sae dai su hadu a school ko kuma su yi waya, Tana kulle kofar office din sae ga Dr Musharraf, taki yarda su hada ido ta juya ta bar wajen da sauri, ya bi ta da kallo.... Ranan al-hamis Mayraah na dawowa daga school ta tarar an kai lefen Haseenah, akwatuna set biyu Maheer yayi mata wato 12 boxes, ita dai Mayraah tun kayan na gidan ma bata damu taga abubuwan da aka zuba ba, wasa wasa an fara shirye shiryen biki a gidan babu kama kafar yaro don duk wani abu da za a bukata na taron Abba ya siya ya jibge a store, ita duk ba wannan ba babban damuwarta sunday da Musharraf yace zai kai ta gidansu ta gaida Maminsa, da ta tuna hakan sai taji gabanta ya fadi, gashi gobe za a kawo nata lefen.....
Mami ce zaune parlor tare da sisters dinta biyu Aunty Fatima da Aunty Baby dake zaune gefenta, sai su Anty Halima da Ruma'isa kusan dai su biyar ne ke ta fiddo da kayan cikin akwatuna set biyu me guda 7 each dake gabansu, Wasu dattijai mata biyu ma na zaune parlon, wanda daya yayar Dad dinsu Musharraf ce, daya kuma kanwar kakarsu, daya daga friend din Mami Hajiya Hafsah dake tsaye ita ma tana kallonsu Hajiya Halima tana ɗan murmushi tace "Ai ina ga ba sai an fiddo duk kayan nan gaba daya ba Hajjaju, maidasu bazai zama easy ba gaskiya, ga yamma ya gabato ga kuma drebobi na jiranmu a waje" Hajiya Halima ta daga kai tana kallon occupant din parlon gaba daya tace "To wai halan er gwal Musharraf zai auro da za a jibga mata wannan uban kaya haka tsadaddu kamar ɗan fashi? Shi bazai yi tanadi me kyau na rayuwarsa ba sai ya kare a zuba tsadaddun lefe ma yarinya? Ikon Allah! To ko fili ya kara cikin kadarorinsa ai ya karu karuwa ta har abada, amma duk a rasa wanda zai sa shi a hanya ya dinga wannan uban siyayyan? Da kyar idan kayan nan basu yi na Miliyan goma sha ba, da yake dama ita uwarsa duk harkar karya da nuna isa tana kan gaba gaba, banda haka ai ita me masa fada ne da taga yana jibga kayan nan ta tsawatar masa, Musharraf baya jin maganan kowa babu wanda ya isa ya saka shi ya hanasa a duk cikin mu, kuma ba kowa ke mara masa baya yake abubuwan nan ba sai uwarsa, ta dauki son duniya ta dora masa, duk ya bi ya raina mutane baya ganin kowa da gashi, yarinyar da aka ce a can wajajen kurnan ɗan asabe take kafin a karasa mil tara can hanyar Daura shine za a hada ma uban kayan nan? Local girl irin wannan ne za ayi ma wannan kaya fisabilillahi jama'a kuyi alkalanci fa?" Aunty Fatima da ranta ya riga ya gama baci tace "Gaskiya Aunty Halima babu abinda za a rage a kayan nan tunda babu sisin kowa a ciki, in ma akwai to nasan bazai wuce na mahaifiyarsa ba ko yayansa, don haka yanda kayan nan suke a nan haka za mu dauka mu kai su..." Aunty Halima ta mike a fusace ta dakatar da ita tace "Ke kar ki gaya min magana Malama, yanda kike ganin kuna da iko da Musharraf to mu mun ma fi ku iko da shi, bar ganin kunyi bake bake kan lamarinsa kun mayar da mu bare, to wannan karan bari kiji sai abinda mu dangin uba muka ce za ayi ba dangin uwa ba, ku kun gama playing part dinku kuma haka, wannan zancen aure ake ba na wasan yara ba don haka mune tsaye kyamm akan lamarin nan ko mutum ya so ko ya ki, kuma ni Hajiya Halima nace baza a fitar da duk kayan nan daga parlon nan ba sai an rage su tunda ba fashi da makami Musharraf din yake ba" Mami that was calming herself down tace "Yanzu ke meye ribar yin haka Hajiya Halima? Idan aka kai ma Farrah kayan nan dama ba da hannu bibbiyu zaki amsa ba?" Hajiya Halima tayi wani shewa tace "Of course da hannu bibbiyu zan amsa saboda Farrah tayi deserving dinsa, ita kuwa yarinyar da za a kai ma er talakawa ce bata yi deserving ba bata san value dinsu ba, iyaka ma ta walakanta su ta kashe su kafin shekara daya, ni nan da kike gani bana shakkar fadin gaskiya a ko ina wallahi ko a mutu ko ayi rai, yau da Yaya yana da rai ai shima bazai bar ɗan sa yayi wannan almubbazzarancin ba da sunan hada kayan aure, kayan auren ma na yar talaka" Tana fadin haka ta fara rage laces da atamfofin da suka fi tsada tana jefawa kan kujera a fusace, Aunty Baby ta rike haɓa tana ganin ikon Allah, Mama Harira warce ita ce yayar Abbansu Musharraf tace "Kinyi kuskure babba Maryam da har zaki bari yaron nan ya kashe kudi haka wajen hada kayan aure, yo wannan ko er gidan sarauta ai sai haka, banda an ware mu bama sanin duk abinda ke faruwa ai baza mu bar wanna abu ya kasance ba, don haka dole ne sai an rage kayan nan, kuma ko da mun kai kayan ba tare da an cire ko daya ba bana tunanin za su iya bamu tukuicin da ya kamata tunda naji Halima tace a Kurna yarinyar take, banda rashin tunani irin na Musharraf ina shi ina ita? Ga er uwarsa Farrah kowa yayi masa sha'awa amma yaron nan yaki, dama gida bai koshi ba a ina aka taɓa kai wa waje? To dai duk kece me babban laifi tunda baki nuna masa haka ba" Mikewa Mami tayi ta fice daga parlon ta wuce sama, Hajiya Halima da su Ruma'isa suka bi ta da harara, Daya dattijuwar Mama Karima tace "Sam abun dai babu tsari, an raina mu ba a dauke mu bakin komai ba, duk ku cire abinda ku ka ga ya kamata a cire ai ba er gwal bace" Friends din Mami gaba daya where speechless and shock, suka dinga kallon yanda Hajiya Halima da Rumaisa ke kwashe kayan lefen ba tsoron Allah, mikewa Aunty Fatima tayi ta bi Mami zuwa sama, zaune ta ganta a parlonta tana waya, Aunty Fatima ta rungume hannunta tana tsaye jikin kofa kana ganinta kasan she is boiling from inside ita ma, Mami tace "Ni bance ka kirasu ba Daddy amma wllh idan na tashi rashin mutuncina kare bazai dauka ba wllh, na gaji da abinda dangin babanku suke min, akan me? After so many years baza su bar ni in huta ba sai bibiyata suke da sharri?" Daga daya bangaren Daddy yace "Mami pls kiyi hakuri kar ki ce masu komai, ko kayan nawa suka cire ni zan tura kudi ayi replacing ko washegari ne sai a kai sauran kayan, and pls don't say anything to Musharraf kinsan halinsa" Mami tace "Wallahi na gaji, wannan ai cin mutunci ne da cin fuska a gaban kawayena fa" Daddy ya sauke ajiyar zuciya yace "Pls kiyi hakuri, everything will be okay in sha Allah"
Musharraf yayi parking ya sauka daga cikin motarsa yana kallon machine (Bike) din da yayi zoom off leaving the security guy a tsaye da envelope a hannunsa, Musharraf ya karasa gun security man din yace "Na meye wannan?" Mai gadin yace "Yanzu wani me babur ya bani wai a kai ma su Hajiya" Musharraf yace "Okay" Daga haka ya amshi envelope din ya shiga cikin compound din yana unsealing dinsa ya ciro takardan ciki ya warware yana jujjuyawa, he was surprise to see rubutu jikin takardan, babu bata lokaci ya fara karanta content din, ko 30 seconds bai yi da fara karantawa ba yaji ya kasa ci gaba da tsayuwa, yayi saurin jawo farin kujeran dake kusa da dakin mai gadi ya zauna, lkci daya yaji zufa na taho masa, kan kace me har ya gama karanta content din takardan sai kuma ya fara kokarin apprehending abinda ya karanta, after few seconds of trying to apprehend yayi squeezing din paper din a hankali ya cusa a aljihunsa.....



07087865788


WhatsApp only
[6/1, 2:56 PM] Khaleesat Haiydar💖: 💖💖 *MAYRAAH*💖💖




By _Khaleesat Haiydar_📚✍🏻



7......

Mikewa Musharraf yayi ya fita gate din gidan da sauri yana kallon security man din yace "Daga ina yace maka yake? And me yace maka da ya baka wannan?" Security man din ya karaso wajensa da ladabi yace "Bai gaya min daga inda yake ba ranka shi dade, kawai mika min yayi yace in ba Hajiya" Musharraf bai kuma sauraronsa ba ya nufi motarsa ya shiga ya bar layin, mai gadin ya koma ya zauna.... Bayan kayan cikin lefe har da akwati hudu su Hajiya Halima suka cire wai babu amfanin a tafi da akwatuna goma sha hudu, guda goma ya isa, Ita dai Mami bata sake sakkowa downstairs ba don ma kada zuciyarta ya kasa hakuri ta biyesu, Mama Harira tace "To yanzu kayan nan da aka rage ya za ayi da su, nan din za a bar su?" Hajiya Halima tace "A bar su suyi me a nan Mama, shi me yan uwa mata barkatai a family, tafiya za ayi da shi a ba kowa hakkinsa" Kawayen Mami babu wanda yace masu komai, kowa dai ya zuba masu ido, suka gama abinda za su yi sannan aka kira drivers su shigo su dau akwatunan su saka su a mota... Mami na kallon Aunty Fatima da tace baxata je kai lefen ba tace "Ki yi hakuri ku je Fatima, ai ba don su za ku yi ba, in don ta su ne ai baza a kai kayan ba" Aunty Fatima tace "Wallahi yaya yanzu yawanci maza ne ma ke kai kayan ba mata ba" Mami tace "To sun ce su za su kai ya za mu yi masu, kawai kiyi hakuri ku tafi, kowa yayi da kyau ai don kansa, abinda su ma suna da baya" Aunty Fatima ta sauke ajiyar zuciya bata sake ma yayar tata musu ba ta dau gyalenta da handbag ta fita, su Goma sha uku suka tafi kai kayan a motoci hudu, wanda kusan tara duk dangin Abbansu Musharraf ne, Hajiya Halima da Cousin sis dinta me suna Murja sai kyabe baki suke a mota ganin hanyar da aka nufa, Murja ta rike haɓa tace "Yanzu duk fadin garin kano yaron nan ya rasa inda zai je neman aure sai outskirt din kano, ashe girman kansa duk na banza ne, ai ko na raina ajinsa yanzu" Aunty Halima dake taunar cingam tace "Atoh, ba uwar ce me mara masa baya yake abinda ya ga dama ba, ga su ga yar kauye ai sai mu ga yanda za ayi zaman" Ruma'isa dake gaban mota a zaune tace "Kuma ina me tabbatar maku auren nan bazai je ko ina ba tunda ba class dinsa zai aura ba, shi da yake nuna yana da taste ashe duk na banza, balle ma yanzu fa an daina auren mai kudi da talaka, kowa lane dinsa yake tsayawa, kwarya tabi kwarya, ina me kudi ina talaka a wannan zamanin?" Murja tace "Toh wai ma ina ya hadu da yarinyar nan tukun? Zan so in ganta kuwa" Aunty Halima tace "Har yau nima abinda nake son sani kenan, me ya kai sa kurna har ya ga yarinyar yace yana so" Ruma'isa tace "Can ta matse masa dai, mu dai za mu zuba ido mu ga yanda abun nan zai yiwu" Motar su Aunty Fatima da frnds din Mami biyu ne ke leading sauran motocin zuwa gidansu Mayraah don shi yaje kwaso kayan lefen daga can, bayan tafiyar kusan 40mins suka iso anguwan, Aunty Halima tace "Ikon Allah, nan ne fa anguwan Murja, cabb ko a mafarki ban taɓa tunanin da abinda zai kawo ni area din nan ba" Duk suka yi shiru ana bin ko ina da kallo cike da takaici, har dai suka ga motarsu ta tsaya kamar yanda sauran motocin ma suka tsaya, Hajiya Halima na kallon wani lafiyayyen gidan dake gefensu tace "Wannan kuma wani hau ya fada masa duk girman kano ya rasa inda zai gina tanfatsetsen gidan nan sai a nan.... Ikon Allah" Murja dake kallon gidan ita ma tace "Nima shi na saki baki nake kallo, wannan ai bai yi dubara ba dubi almajirai sun masa cirko cirko a kofar gidan, to yanzu dai ina gidan da za a kai lefen?" Sauka duk suka yi daga motar ganin sauran ma duk sun sauko, Mama Harira dake toshe hanci tace "Wai ina dreban da aka ce yasan gidan ne an bar mu tsaye a walakance duk sai doyi ya bade mu cikinmu ya kumbura daga kawo kayan aure" Dreban ya taho da sauri yana nuna gidan da su Hajiya Halima suka gama magana a kai yace "Nan ne gidan ai Hajiya" Bai rufe baki ba aka bude gate din gidan sai ga wakeken compound gari guda na kallonsu, Hajiya Halima ta kalli Murja sannan ta kalli Rumaisa, ko wannensu na zare ido, Mai gadin gidan yace "Motocin duk za su shigo, bismillahn ku sannunku da zuwa" Duka drivers din suka koma cikin motocin da nufin shiga compound din gidan, Hajiya Halima dai ta koma gefe ta tsaya, sai kuma ta kyabe baki tana gyara yafin gyalenta dake wuya, Aunty Fatima da kawayen Mami sai satan kallon reaction din dangin mahaifin Musharraf suke, bayan motocin sun shiga da kafarsu suka karasa cikin gidan, sister din Ammi da yan uwanta na kusa da nesa da kawayenta sannan ga neighbors ne cike gidan suna jiran isowar family din Musharraf, yanda gidan yake a cike kai kace taron biki aka yi, Tarba irinta girma da karamci aka ma dangin Musharraf a gidansu Mayraah, Hajiya Halima dai na zaune babu yabo babu fallasa tana taunar cingam ga akwatuna an zubesu a tsakiyar parlon, sai bin ko ina take da kallo don kam kana gani kasan Naira ta zauna daram, familyn Mayraah sai duba kayan suke sama sama ana yabawa, Hajiya Hafsah frnd din Mami ta bude jakarta ta ciro set din sarka da dankunne na gold har da zobensa, Aunty Halima da mukarrabanta suka saki baki suna kallon ikon Allah don basu san da shi ba, kuma ba a nuna masu ba, they were shock, Hajiya Hafsah ta ajiye set din gold din saman akwatin jewelries, makotan Ammi suka dinga maa sha Allah ana guda cike da farin ciki, sai cewa suke yarinya tayi goshi, Alhamdulillah, Aunty Fatima ta fiddo 300k a cikin jakarta ta daura kan akwatin zannuwa tace "Wannan kudin dinki ne, duk da an dinka mata duk kayan fitan biki suna cikin akwatin, sannan a duba abinda babu a wannan kayan a sanar mana" Hajiya Halima ta wani maka mata kallo, Mama Harira tayi caraf tace "Ai mu babu abinda bamu zuba a kayan nan ba, sai dai son rai...." Aunty Rumaisa tace "Lallai kam son rai, ina ganin in dai babu wani abu to mu za mu koma don daga GRA muke gaskiya" Aunty Halima ta mike tace "Shine kam, kar dare yayi mana a hanya cikin tsukakken lokon nan, ni sai naji kamar barin kanon ma muka yi gaba daya wannan uban tafiya haka" Babu dai wanda yace masu komai a parlon sai Maman Shafa makociyar Ammi da tace "Ai ko dai, dama idan mutum bai saba fita ba sai yaga nisar zuwa nan din, amma a jirgi ma ai ana tafiyar awa da awanni, loko kuma a haka muke zaune cikin kwanciyar hankali babu karya ba komai" Hajiya Halima ta jefa mata wani kallo ita kuwa bata ma san tana yi ba don yaba kyan wani tsadadden lace dake cikin akwati ta hau yi, Small Chop da snacks iri iri da pepper chicken da aka ajiye ma yan kawo kayan nan wani sai yace na gidan biki ne, ga manyan coolers din abinci iri iri da yaji naman rago, ruwa da lemo kuwa yayi park 150 da aka jera masu waje daya abu dai irin na girma, aka kuma dau 300k aka basu tukuicin kayan da suka kawo, Su Aunty Halima basu taɓa zaton haka ba, kuma kana ganin reaction dinsu kasan hakan bai masu dadi ba ko kadan, kamar ana cunkulinsu suka fita daga parlon drebobin da suka zo tare suka dinga fitar da kayan abincin ana sakawa a motoci, aka rakosu har bakin gate cike da mutuntawa har suka shiga mota suka bar anguwan.... Ruma'isa na kallon Aunty Halima dake gefenta tace "Ikon Allah, ashe dai ba er matsiyata bace" Ko kulata Aunty Halima bata yi ba, Mama Harira tace "Amma duk yanda aka yi ubanta kasungumin ɗan kauye ne wanda yayi aziki sama ta ka, banda haka bazai shigo wannan anguwa haka ya kera gidan nan ba kamar ance masa jeka ka gani" Rumaisa tace "Dama mana, irin yan kauyen nan ne fa da suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login