Showing 75001 words to 78000 words out of 249515 words
yana kallon Ammi dake kallonsu... Cikin awa daya da wani abu Mayraah ta gama girkin tunda ɗan kadan zata yi dama, Ta dawo parlon Ammi tace "Ammi na gama" Ammi tace "To sannu da aiki" juyawa tayi ta fita, Maheer ya mike yace "Bari in je masallaci in dawo" Ammi tace "Daga can ka wuce gida Maheer, ya zaka fara barin yarinya ita kadai a gida daga kai ta, ai zaka bari ko sati tayi tukunna" Maheer dai bai ce mata komai ba ya fita daga parlon, dakinsa ya tafi ya dau ledan da ya ajiye sannan ya fito ya tafi dakin Mayraah, tana tsaye jikin window tana kallon waje ya sameta, Mayraah ta juya jin an bude kofar dakinta, ya karasa ciki ya zauna gefen gado yace "Ga sakon ki Mimi" Tana kallonsa tace "Na mene?" Yace "Amsa ki duba" Ta sauke idonta sannan ta nufesa ta amshi ledan da yake mika mata, tun bata bude ledan ba ta gane waya ce, tana kallonsa da murmushin karfin hali a fuskarta tace "Nagode sosai yaya" Ya girgiza kai yace "That smile is fake" Dariya ya bata wanda bata san sanda tayi ba, tace "Allah da gaske naji dadi yaya" Yace "Toh kinga wannan is not fake" Murmushi kawai take ta bude wayar taga wanda yafi nata na da ne ma, a hankali tace "Nagode sosai, Allah ya kara budi" yace "Everything for my Mimi" shiru duk suka yi, bayan few seconds a hankali yace "And... sorry about what happened dazu a gidana Mimi, you know i will neva let that slide...." Da sauri Mayraah ta katse sa tace "Aa ni ai ya wuce a wajena har na manta ma" kallonta kawai yake, ta fara bude kwalin wayar, yace "Za a san min tuwon Abban?" Ta kallesa tace "Ohk amma halve, sai in ba Ammi sauran halve din, dama leda uku ne nayi" Yace "Toh bari in dawo masallaci, ki ajiye min a daki" Tace "Toh" Mikewa yayi ya fita daga dakin, Mayraah ta dinga kallon wayar bayan ta bude, sosai yayi mata kyau ba kadan ba and she is so happy about it, taga har da sim card ya siya mata, ta jona wayar a caji sannan ta ajiye kwalin ta tafi bandaki don yin alwala.... Bayan Magrib tana zaune kan darduma aka bude kofar dakin ta daga kai tana kallon wanda ya shigo, ya karaso dakin ya ajiye ledan hannunsa gefen gado, tana kallonsa tace "Ina yini" Yace "Lafiya lau" Tace "Ana ta kiranka a waya" Tana fadin haka ta mike ta tafi ta dauko masa wayarsa da ya bata tun da yamma, ya amsa ya juya ya fita, Mayraah ta dau ledan da ya ajiye mata taga kwalin waya ne a ciki, ta buda ido da mamaki tana juya kwalin, exactly irin wanda Maheer ya siyo mata dazu color ne kawai daban da wancan, ajiyewa tayi gaban mirror ta fita dakin ta sauka downstairs, abinci ta saka ma Maheer kamar yanda yace mata, ta kai dakinsa, zaune ta gansa dakin yana kallo a laptop, yayi pausing movie din ta karaso ta ajiye masa abincin a gabansa tace "A kawo maka tea ne?" Yace "No... thanks Mimi" Ta mike zata fita yace "Ke kin ci abincin?" Tace "Aa anjima" zata fita dakin sai ga Ammi, Ammi tace "Wai Maheer baka tafi ba har yanzu?" Maheer yace "Ammi wai korata kike ne?" Ammi tace "Eh koranka nake, wannan wani irin abu ne haka? Kai in kanwarka aka ma haka zaka ji dadi?" Ya kalli Mimi dake tsaye yace "Aa bazan ji ba gaskiya, bari in gama cin abincin in tafi Ammi" Ammi tace "Gaskiya bana son haka, kar ka sake zuwa min gidan nan kwana kusa, ya zaka fara barin er mutane ita kadai daga kai ta jiya? Don't u have conscience" Muryar Mama Ladi suka ji tana cewa "O'o Allah, O'o Allah, ba fa yarinya bace amaryar nan da zaki wani daga hankalinki haka a kan an bar ta ita kadai a gida Ammi, jiya fa da muka je na kalli idonta da kyau wllh ba yarinya bace, da kyar in ma bata girmi Mashir din ba, ni dai nayi ta mamakin a inda ya samota har yaji sha'awan aurenta, ke fa baki mata kallon da na mata ba jiya, don haka kawai ki ja bakinki kiyi shiru in baki san abu ba" Ammi dai bata ce mata komai ba ta juya ta fita daga dakin Mayraah ta bi bayanta, Mama Ladi na kallon Maheer dake cin abincin da Mayraah ta kawo masa tace "Kai ko kamar wanda aka ma rufa ido, maimakon ka samu yarinya er dai dai warce bata wuce Mera ba zaka kare da uwar mata haka Mashir? Ko kai baka ganta ba wani saɓar saɓar da ita sai uban mazaunai, kyan fuska kawai gareta fa shi ma kamar mai ta shafa, wannan haihuwa daya biyu zata sukurkurce ta fashe, don irin kiɓan kazantar nan zata yi da tayi haihuwa daya, wanda da ta gifta zaka ji doyi" Mama Ladi ta kyabe baki tace "Allah dai yasa kada Usuman yayi irin wannan zaben tumun daren, ya samu yarinya er dai dai abunsa kamar Mera" Murmushi kawai Maheer yayi yana cin abincinsa, Mama Ladi ta juya ta fice daga dakin. Sai da Mayraah ta fara zubo ma Ammi abinci ta kai mata parlonta sannan ta tafi dakin Usman. Ya ajiye wayar da yake yace "Ya aka yi?" Tana jan fingers dinta tana tsaye jikin kofar dakin tace "Thank you so much for the phone yaya, Allah ya saka da alkhairi" Yace "Ameen, any other thing?" Ta girgiza masa kai tace "Kawai godiya zan maka dama" Yace "Accepted Mimi" Tayi murmushi ta juya ta fita daga dakin.
Da gudu Haseenah ta shige bandakin yaran Maman Bala jin muryar Hajja tana sallama a tsakar gida, Maman Bala ta fito tana amsa sallaman tace "Sannu da zuwa Hajja" Hajja tace "Allah sa dai nan Badiyya ta shigo Sahura" Maman Bala tace "Ehh gata can dakinsu Bala kuwa" Hajja ta nufi dakin, Badiyya ta hade rai tace "To ke Hajja meye na biyoni don Allah kamar wata er yarinya" Hajja tace "Ayya naga kunun har ya huce kin san flask din nawa ya fashe balle in juye maki a ciki" Badiyya tace "Toh ki tafi gani nan zuwa ni dai" Hajja tace "Toh" Daga haka ta juya ta fita, Haseenah ta fito tana zare ido kamar warce tayi ma sarki karya, Badiyyah tace "Yanzu da magariban nan kice zaki kama hanyar Zaria Haseenah, to wai ma wani waya kike da baza kiyi a gabana ba sai kin wani fita tsakar gida, in haka ne meyasa baki je wajen wanda ku ke wayan da baki son in ji ba, ina fama da kaina na fito saboda ke amma don munafurci sai ki wani dinga fita kina kus kus a saya" Haseenah ta marairaice tace "Wallahi ba haka bane Badiyya, duk bayanin da na maki nake yi a wayar da kika ga ina yi, Coursemate dita ce Fatiha fa" Badiyya dai ta kara kyabe baki ta dauke kai, Haseenah tace "Kuma ai da ban yarda dake ba bazan zo wajenki ba Badiyya, yanzu dai bari in maki transfer ki dauko Atm dinki ki cire kudin ki bani inyi maza in tafi" Badiyya ta mika mata hannu babu yabo babu fallasa tace "Haseenah bani sarkan nan da dankunne zanje kasuwan da kaina in siyar" Haseenah ta hadiye wani abu da kyar tace "Yana fa wajen me siyarwan account number kawai zan tura masa ya saka maki kudin wllh, hidimar bikin nan da ake ta yi ne yasa aka samu delay, yanzu dai don Allah gobe za mu yi maganar gold din ta waya, ki tashi muje ki ciran min kudi a account dinki inyi maza in tafi, zan tura maki dubu talatin yanzu" Badiyya na girgiza kai irin ba mutuncin nan tace "Gaskiya idan goben yayi da kaina zan je shagon me gwal din na gaji kuma haka, aban gold din ko kuma aban kudin" Haseenah tace "Ehh goben sai in baki kwatancen wajen mutumin ki je, ai sananne ne a kasuwan" Mikewa Badiyya tayi tana dingishi suka fita daga dakin Haseenah na biye da ita, Badiyya tayi ma Maman Bala sallama suka bar gidan, suna isa gate din Hajja Badiyya tace "Kinga kawai muje gun me POS din ki masa transfer ya baki kudin don ina shiga gida yanzu Hajja zata iya biyoni waje idan nace zan sake fitowa, kuma kince baki son tasan komai" Haseenah tace "Gaskiya kam, wannan sirri ne tsakanina da ke" Suna karasawa gun me POS Haseenah tayi transfer din aka bata cash, Tace "To sai mun yi magana Badiyya, ina isa Zaria zan kira ki" Badiyya tace "Amma dai wajen wa zaki a Zari'a ke da baki da dangin uwa balle na uba a can" Haseenah tace "Haba gobe fatiha zata sameni a Zarian ai, yanzu dai zanje gidan wata Coursemate dinmu ne tukun" Badiyya ta tabe baki tace "Toh Allah ya tsare" Haseenah tace "Ameen" Daga haka ta bar layin da sauri, Badiyya ta koma cikin gida, Hajja na ganinta tace "To kiyi sallah bari in zuba maki kunun" Badiyya ta taɓe baki ta zauna tana kallon Hajja tace "Hajja kin san matar Maheer ce ta zo muka shiga gidan Maman Bala kuwa?" Hajja ta kalleta tace "Matar Maheer? Wani Maheer din?" Badiyya tace "Wallahi kuwa in gaya maki, wai ya korata gida daga dai Mayraah taje gidan ta mata rashin kunya tace bazata dauka ba" Hajja ta dinga kallonta tace "Mayraah ta mata rashin kunya?" Badiyya tace "Wallahi nake gaya maki, ko gaida Haseenar ma bata yi ba da taje gidan tana ta abu Isa isa da gadara, shine Haseenah abun ya ɓata mata rai tace to gaskiya ita bata son haka ya za ayi ta shigo mata gida babu gaisuwa sai kallon walakanci, kar ki dada karki raga Maheer kawai ya dauketa ya maidata gidansu, shine fa ta shiga tashin hankali bata shiga gidan nasu ba ta yo nan hankali tashe" Hajja na tafe hannu tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Badiyya tace "Ace Mayraah bata zama annoba ba? Dubi tashin hankalin da take hadawa a family dinmu duk tana neman tarwatsa kanmu ta lalata mana zumunci" Hajja na gyada kai a hankali tace "Wannan gaskiya ne" Badiyya tace "To wannan magana tsakaninmu ne dake, kar ki ce ma kowa komai babu ruwanki, kinga dai ni ga abinda ta sa Usman yayi min don ma Allah ya so da sauran kwanana a gaba, Aunty Mariya na ji tana gani bata kwace ni ba kuma har yanzu ai kinga bata zo gidan nan ba balle ta duba halin da nake ciki, ita kanta Ammin bata kira taji ya jikina ba kuma ya kamata ita ma ace ta zo ta duba ni ai, ai kinga duk babu wanda ya zo, balle Mama Ladi dake ta goyon bayan abinda aka min duk akan wata banza wai Mayraah, yanzu gashi sabon auren da Maheer yayi tana nema ta kashe masa, ai wannan badluck ce a family dinmu wllh, ashe dama babu abinda muka hada da ita shi yasa tun farko na tsaneta jinina bai hadu da ita ba, Ammi tayi ta fifitata a kaina komai ace Mayraah, a gabana Aunty Mariya zata kira sai dai tace a ba Mayraah...." Hajja dai bata ce komai ba tayi shiru, Badiyya ta tabe baki ta mike da kyar ta shiga bandaki...
Washegari da safe Mayraah ta gama shiryawa don tana son shiga school ba don kowa ba sai don Dr Musharraf kilan zata gansa a school din, fitowa tayi zata sauka downstairs taje kitchen don hada ma Ammi shayi, babu wanda yasan zata school a gidan don dama so take sai ta kai ma Ammi shayi kafin tace mata zata je makaranta, a stairs ta hadu da Hajja dake haurowa, tayi murmushi ganinta tace "Ina kwana Hajja" Ko kallonta Hajja bata yi ba, Mayraah ta koma gefe ta bi ta da kallo in shock, Hajja ta nufi parlon Ammi ta bude kofar babu ko sallama, Ammi da Mama Ladi sai Aunty Mariya duk suka daga kai suna kallonta, shiga parlon tayi tana kallon Ammi da kyau tace "Hajara" Ammi ta kasa cewa komai ta dinga kallonta gabanta na faduwa don Hajja bata kiran sunanta kai tsaye sai dai ta kirata da Ammi, Hajja tace "Ina ce dai da yardata kika dau yarinyar nan kika rike har zuwa yau ko? Ina ce Mamuda ƙin amincewa yayi da farko, ni ce nan na karfafa masa gwiwa na rokesa Allah da annabi ya barki kiyi rainon yarinyar tun tana tsumma ko? To a yau nake son ki zabi ko ni ko yarinyar"
MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
[6/21, 8:09 PM] Khaleesat Haiydar💖: Gaisuwa da fatan alkhairi zuwa ga Sister Nafisat Sanda (Mom twins🥰) Allah Ubangiji ya raya mana twins mu taho biki Sakkwato muna daddaga shoulders😁 Hajiya Safiyya Usuman🤪 (Ummu Sultan) 5 gbosa for you, Allah ya karo arziki ki bude plazan kayan yara a titin anguwanku, Allah ya raya mana Noor in fara tara kayan kitchen 😁
My lovely fans ina maku fatan alkhairi for always being there for me, Allah ya raya maku zuri'a🥰
Mama Ladi ta saki salati ta mike ta dafe gwiwowinta tana kallon Hajja kamar ranan ta fara ganinta tace "Yau mun shiga uku, Me ya sameki haka Hajja? Ko dai ɓatan hanya kika yi ba nan zaki zo ba?" Hajja ta dakatar da ita tana huci tace "Kee babu ruwanki a maganar nan ki kama gabanki kar ranki ya baci Ladi, magana ce nake yi tsakanina da 'ya ta" Mama Ladi ta mike zumbur ta wangale hannu tace "Ba lafiya jama'a, to amma dai a yanzu ai kowa yasan ba Ammi ke da iko da Mera ba a gidan nan, sai dai in kije ki samu Mamuda dama bai fita ba, kije dakinsa ki samesa ki zazzage masa duk abinda ke ranki, haka kawai mata muna zaman zaman mu baza ki zo nan ki daga mana hankali ba gaskiya, ki tafi can dakin Mamuda kice ya maida Mera jikin masallacin da ya tsintota tunda shi ya tsintota ai ba Ammi ba, babu ruwan Ammi a wannan maganar gaskiya, ita umarnin mijinta ta bi take rike da Meran har yau don zaman lafiyanta da mijinta, in kuma kashe mata auren zaki yi ta koma gidanki to sai mu ce Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, don wannan hanyar kashe mata aure kika dauko" Aunty Mariya was speechless and shock, gaba daya jikinta yayi sanyi, ta ma rasa tunanin da zata yi balle tace wani abu, to in ma tana da abun cewan ba dai a gaban Hajja ba, don tsaff sai Hajja ta iya tsine mata, Ammi kam dawowa tayi kamar an dasa ta a wajen don ko kifta ido bata yi, that was the least she was expecting from Hajja, she was still finding it hard to believe Hajja ce yau ke fadan wannan maganan, is this really Hajja, her eyes where soo dry tsabar yanda maganar ya zo mata a bazata ita da hawaye bai da nisa daga idonta, kallon Hajja kawai take babu ko kiftawa, Hajja na kallon Mama Ladi tana nunata da ɗan yatsa take cewa "Nace ki cire bakinki a batun nan Ladi kada ki kai ni bango, ki cire bakinki a abinda ya shafi zuri'ata tunda baki da alkhairin da zaki fada, in dai har akan Mayraah abubuwa za su yi ta faruwa haka suna caɓewa a zuri'ata to na yanke shawara Hajara ta zabi ko ni ko ita kawai, ehh ta zabi ko ni ko ita Mayraahn, bazai yiwu a kan Mayraah a kusa nakasa Badiyya ba sannan har yau babu wanda yaje yace mana ci kanku balle ya duba halin da take ciki daga ku har shi munafukin da yayi dukan, bazai yiwu akan Mayraah 'ya yan Hajara su dau ƙaran tsana su dora ma Badiyyah ba, basu da makiyiya sama da Badiyya a duniya, sannan yanzu kuma a kan Mayraah banga dalilin da zai sa Maheer ya kora matarsa da duka duka kwananta daya a gidansa, wai fa duk saboda Mayraah, to ita Mayraahn nan duk abubuwan nan dake faruwa duk ta dalilinta alkhairi ce a garemu kenan?? ai a ganina an mata mai wuya tunda har aka riketa aka ciyar da ita kawo yanzu da tasan kanta, wani irin karatu ne bata yi ba gashi za a yaye su a jami'a kwanan nan, don haka bazan zuba ido in ga familyna na neman lalacewa akan wata da babu abinda muka hada da ita ba a duniya sai don zuciya irin ta musulunci da ya sa muka sakota cikinmu ba tare da mun kyamace ta ba, nayi hakuri na kauda kai, na nuna komai ba komai bane yau shekara ashirin da biyu kenan, tun daga kan yanda ake banzatar da Badiyya da lamarinta a kan yarinyar nan ma ai yaci ace na dau mataki, amma ban yi haka ba saboda zuciyar musulunci, don haka duk sanda Hajara ta yanke shawara sai ta zo gida ta sameni, Ko ni ko Mayraah, bazan mutu in bar baya da ƙura ba..." Hajja na kai wa nan ta nufi kofa fuuu ta fice daga parlon, Mayraah dake tsaye tun shigan Hajja parlon Ammi kuma duk ta jiyo abinda Hajja ke cewa ta juya da sauri ta nufi dakinta ta kulle ta jingina da kofa tana maida numfashi.... Sai a sannan hawayen tashin hankali ya kawo idon Ammi tana kallon Aunty Mariya da tayi tagumi tana furta Innalillahi wa inna ilaihi raji'un a ranta, Mama Ladi na tafe hannu tana zare ido tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una lalacewa ta samu Hajja, dama Hausawa sunce ba farkon ba karshen, yanzu dama haka Hajja ta koma ni ina can Karaye ban sani ba?? me ya sami yayata ta lalace da mugun hali haka?" Tana kai wa nan ta fice daga parlon ta nufi dakin Usman, Aunty Mariya tayi karfin halin cewa "Ammi ki kwantar da hankalinki, nasan cikin bacin rai Hajja tayi maganganun nan