Showing 153001 words to 156000 words out of 249515 words
kallon Mayraah dake kokarin dauko abubuwan da suka dawo da shi daga asibiti tace "Yi wucewarki ki kwanta duk zan kwaso su, ina kika ga karfin jidan kaya" Juyawa Mayraah tayi ta nufi cikin gidan, Mama Ladi ta koma kusa da Abba tayi kasa da murya tace "Mamuda kasan bayan ƙin zuwa da wannan matar tayi har 'ya yanta ma ta hana su zo duba baiwar Allahn nan a asibiti? Wannan wace irin rayuwa ce fisabilillahi?" Abba ya dan yi murmushi yace "Ina sane Mama, tasa ai Usman da Umar sun bar gidan nan yanzu haka basa nan" Mama Ladi ta saki salati tana tafe hannu, Abba yace "Amma zan dau mataki nan ba da dadewa ba in sha Allah, duk zan yi maganinsu har Maheer din" da sauri Mama Ladi tace "Aa don Allah kayi hakuri, nasan kayi hakurin nan kuma kana kan yi, amma don Allah ka ci gaba da yi sai kaga duk kamar ba ayi ba wllh, kaga ai ni bana goyon bayan mugun abun nan da suke, don haka sai kaji sanyi ta bangarena, ita kuma Ammi ka rabu da ita kar ka biyeta akwai ranan kin dillanci, su kansu mazan ka bar su su ci gaba da taya uwarsu goyon bayan rashin gaskiya su ma akwai ranan kin dillanci da ina masu kallon masu hankali ashe duk yan iska ne munafukai ace har Mashir yaki takowa ya duba marainiyar nan a gadon asibiti, amma ba komai, ita kuma Mera ni da wannan matar taka me hankali mun isheta a yanzu dai, kayi hakuri komai zai wuce in sha Allah" Abba da yayi shiru kansa a kasa yana sauraronta, ya sauke ajiyar zuciya yace "Toh shikenan Mama nagode sosai" Mama Ladi tace "Yauwa Allah maka albarka, ka ci gaba da hakuri dan nan, duk me hakuri na tare da Allah" Ko da Mama Ladi ta shiga gidan dakin da Mayraah take ta tafi, nan taga Hajiya Amina har ta kai ma Mayraah abinci sama, Mama Ladi ta zauna kan darduma tace "Ni ma kawo min nawa nan kawai er nan" Hajiya Amina ta gaisheta tana mata sannu da zuwa sannan ta fita taje dauko mata nata abincin bayan ta ajiye ta fita. Hajiya Amina na kallon Abba bayan ta ajiye masa abincinsa tace "Alhaji ina da suggestion plss idan baza ka damu ba" Abba ya kalleta yace "To ina jin ki Amina" Ta ɗan yi murmushi tace "Alhaji ina ga fa kamar zamana a gidan nan ba mai yiwu bane with the way things are going, why not kawai ka bar ni in koma gidana kai ka dinga zuwa can din, idan kuma baka son zuwa gidana ne ko haya ne sai ka kama min ko da daki biyu ne Alhaji, ita kuma Mayraah zata iya dinga switching daga gidana zuwa nan gidan ta yanda uwar goyonta bazata kullaceni ba bazata kullaceta ba don yanzu koma waye gani zai yi kamar na zo ina shisshigin rabata da yarinyar ne which is not so, ina ga kamar wannan shine masalha kawai Alhaji, don a gaskiya abubuwa baza su daidaita ba haka sai dai su kara rikicewa, kaga ina dawowa gidan nan duk sons dinka sun bar gidan u just confirm that this morning, to saboda ni kuma kaga ai bai cancanci su bar comfort zone dinsu ba" Abba ya girgiza kai yace "Babu inda za ki Amina, u remain in this house, duk wanda bazai zauna saboda kina gidan ba ya tattara ya tafi duk inda za shi, as far as Mayraah is going to be comfortable bani da damuwa da haka, kowa yayi abinda ya ga dama gatan da suke da shi a yanzu dai ita bata da shi so my major concern now is Mayraah, kamar yanda nace su suna da gata ita kam bata da shi, zan bar su su yi duk yanda suke so....." Hajiya Amina tayi shiru bata sake cewa komai ba tana kallon Abba, har yau fa common gaisuwan nan Ammi taki bari ya hada su, iyaka ta shigo kitchen tayi abinda zata yi ta wuce sama babu annuri a fuska. A daren Mayraah na kwanciya ta kashe wayarta ta rufe har kanta da bargo amma har karfe dayan dare idonta biyu ta kasa bacci, tana jin Mama Ladi na ta minshari a shimfidar da Hajiya Amina tayi mata a kasa, Mayraah bata ji dadin kwanciyar da Mama Ladi tace zata yi a dakinta ba cause she needs privacy a wannan moment din. Mayraah na zaune kan darduma bayan ta idar da sallan asuba taji Mama Ladi na wanka a bandaki bayan ita ma tayi sallan, Mama Ladi na fitowa ta bude akwatinta wanda suna dawowa daga asibiti jiya da daddare taje bangaren Ammi ta daukosa ta ajiye a dakin Mayraah, Ammi bata tambayeta ya mai jiki ba ita ma bata ce mata ci kanki ba, iyaka ta amsa gaisuwar da Ammin ta mata ta fita daga bangaren, Mayraah na ta kallon Mama Ladi har ta gama saka kayanta, ta yafa gyalenta tana kallon Mayraah tace "Ko zaki leka kasa kiyi ma wancan matar magana ta kawo min kumallo don ina da inda zanje yanzu haka" Mayraah tace "Toh" tana fita dakin bayan some minutes suka dawo tare da Hajiya Amina ta ajiye breakfast din hannunta ta durkusa tana gaida Mama Ladi, Mama Ladi ta amsa tace "Lafiya lau wllhi ke dai, dama zan je gidan yayata ne in gaisheta shi yasa zan karya kafin in fita kada in fita ba komai a cikina" Hajiya Amina tace "Hakan ma yayi Mama, bari a hada maki shayin" Bayan Hajiya Amina ta hada mata shayin ta zuba mata abubuwan da tayi for breakfast a gidan ta mike ta fita, sai da Mama Ladi ta tilasta Mayraah suka yi breakfast din a tare, Mayraah dai shayin kawai take sha da kyar, har Mama Ladi ta gama ta mike tayi gyatsa ta dau katon handbag dinta tana kallon Mayraah tace "Zuwa karfe goma zaki ga na dawo idan na gama abinda ya kai ni, kina shan maganinki ki fitar ma Amina da kwanukan ki ajiye mata can kitchen ki dawo ki kwanta kiyi bacci abun ki kinji" Mayraah felt so much relieve tana kallon Mama Ladi a hankali tace "Toh Allah ya tsare" Mama Ladi tace "Ameen daga haka ta fita daga dakin" Mayraah na ganin fitan Mama Ladi ta sauko daga kan gadon a hankali ta shiga bandaki tayi wanka a gurguje, tana fitowa bayan ta shirya shima sharp sharp, ta nufi jakarta maidaidaici ta dauka, ta dau kwalayen phones din da Usman da Maheer suka siya mata kwanaki ta saka su a cikin jakar, sannan ta dau Atm card da Usman ya taɓa bata da nata Atm card din su ma ta saka a jakan, bin dakin ta dinga yi da kallo, ta shiga bandaki ta dau tooth paste da tooth brush dinta da sabulu da sponge ta saka su a Wani leda ta sa cikin karamin jakar, ta bude press dinta ta ciro iron hijabs dinta uku da dogayen riguna uku duk ta saka a jakan with few of her undies, ta dau perfumes kanana su ma ta saka a jakan sannan ta rufe jakar ta ajiye gefe daya, a hankali ta bude kofar dakin ta fita ta sauka downstairs tana kalle kalle, bata ji motsin kowa a kitchen ba, ta dawo sama da sauri ta dau handbag dinta ta rataye bayan ta sa charger dinta da power bank with lip gloss a ciki, sannan ta dau karamin jakar ta fita daga dakin gabanta na faduwa ta sauka downstairs ta nufi kofar fita, da sauri ta fice daga compound din gidan ta nufi bakin titi tana waige waige kamar munafuka ta samu adaidaita sahu yana tambayarta inda zata je tace "Tasha" sannan ta shiga da sauri. Hajja na kallon Mama Ladi da ta ki zama tace "Ke wa ya gaya maki wannan maganar Ladi?" Mama Ladi tace "Ka ji ki da wani zance kuma Hajja, nace maki Mashir din da kansa ya kirani tun jiya da daddare, shine naga kema ya kamata kije ki dubota idan ya so sai ki bar ni a can kawai ki dawo gida, babu wanda dae zai ce baki je ba, yace yan uwanta kawai ke zuwa dubata kuma hakan ba dadi, ki tashi kawai mu wuce ban sallami me adaidaita sahun ba yana jiranmu" Hajja tace "Subhanallahi, to yanzu asibitin da aka kwantar da ita za mu je kenan?" Mama Ladi tace "Aa yace a nan gida aka sa mata ruwa, ni dama ba sanin gidan nayi ba ke kwanaki naji kina cewa za ki gane gidan, Hajja lokaci na ta wucewa kada yaga kamar ban damu da damuwarsa ba ki tashi mu je don Allah tunda tun jiya ya kirani ya sanar min" Hajja tace "To bari in tashi, to ko laulayi take Haseenar?" Mama Ladi tace "Ni ma nafi tunanin hakan gaskiya" Haka nan Mama Ladi ta ja Hajja suka kama hanyar gidan Maheer a daidaita sahu, Mama Ladi sai girgiza kafa take a adaidaita sahun, abu biyu yasa ta zo ta tafi da Hajja, na farko so take duk tonan sili da zata tayi ma Haseenah a gidan da turaren da zata kunna ace a gaban Hajja za ayi komai taji yanda Haseenah zata tona ma kanta asiri da kanta, na biyu kuma dama ita bata san gidan ba dole sae ta samu mai kai ta wannan yasa ta zo ta tattago Hajja ta lafta mata karya wai Haseenah ba lafiya inji Mashir, Hajja ta kalli Mama Ladi tace "Duk na samu labarin abinda Mamuda yayi Ladi, ke kuma don baki da zuciya baki san inda ke maki ciwo ba kin je kin sake mike kafa a gidansa kin zauna, to in na isa dake Ladi daga gidan Maheer gida za mu komo tare baza ki sake komawa gidan Mamuda ba, sannan zaman da Ammi take yi yanzu haka a gidan bai san albarkacina bane don da ba don ni din ba da tun a jiya Ammin bazata kwana gidansa ba ni nayi mata magana ta waya, dama can yana da niyyar aurensa ya fake da wannan matsala amma babu komai, jiya na hana idona bacci ina me yi ma Ammi addu'an Allah yayi mata abinda yafi alkhairi a rayuwarta kuma Allah ya saka mata wannan zalunci da Mamuda yayi mata cikin gaggawa, kuma albarkacin wannan hawayen nawa da na zubar wllhi Ammi zata ga sakayyan abin nan da Mamuda yayi mata babu dadewa, ita kuma Mayraah idan har mu muka cuceta Allah ya saka mata duniya da lahira, idan kuwa ita ce ta cuce mu ta rikita mana zuri'ar ta lalata zumuncin mu to Allah Ubangiji ya saka mana cikin gaggawa wallahi, da Ammi tasan ta dalilinta Mamuda zai mata wannan walakancin wataran me zai kai ta rikonta? Ai sanin gaibu sai Allah" Mama Ladi dai ko kallon Hajja bata yi ba balle ta bata amsa, Allah Allah kawai take taga sun isa gidan Maheer. Haseenah ta fito daga dakinta kamar mahaukaciya tana bubbuga kofar dakin Badiyyah, Badiyyah dake bacci ta tashi da sauri ta bude kofar da mamaki tace "Waye haka?" Haseenah na huci tace "Badiyyah kin san ni, na sanki, tun wuri kada ma third party ya jiyo mu ki fiddo min atamfofina set bakwai da lace uku da shadda daya da mayafi kala uku, da jaka da takalmin su ma set biyu da kika dauka a cikin akwatin lefena, daga ni sai ke a gidan nan sannan kin san nafi kowa sanin halin ki ciki da bai, kin zata duk ban san kan kayana bane zaki min wannan gagarumin satar?? To wallahi shiga ki fito min da kayana kada in maki abinda baki yi zato ba kuma baza ki taɓa mantawa a rayuwarki ba" Haseenah dake ta mata wani shegen kallo daga sama har kasa tace "Amma ke shashasha ce dabba wllhi, fataran kayan sa wa kika ga ina yi da zaki min sharrin na taɓa maki gantalallun kayan lefenki? In taba maki lefe inyi me da shi, ni za ki yi ma kazafi a gidan ɗan uwana?" Maheer ya bude kofarsa jin hayaniyar tasu ya tsaya nan bakin kofar yana kallonsu hannunsa rike da wayarsa, Haseenah ta nufesa tana huci tace "Maheer tun wuri kace ma barauniyar kanwarka ibilishiya mara tsoron Allah a zuciyarta ta fiddo min kayan lefe na da ta sata, in tana ma wasu sata tana kwana lafiya to ni wallahi bazata min ta kwana yau ba ka dai ji na rantse" Ko rufe baki bata yi ba Badiyyah ta sauke mata wani lafiyayyen mari tace "Don kaza kazanki ni kike ce ma barauniya?" Haseenah ta dafe kuncinta with shock tana kallon Badiyyah baki bude, Badiyyah na tafe hannu tace "Gwara dai ni kowa yasan ba zuwa gidan bokaye da malamai nake yi ba a Zaria, malamin nan naki..." Haseenah bata ba Badiyyah daman karasawa ba ta cakumota nan suka fara dambe a wajen suna kai ma juna duka iya karfinsu, Maheer dai na tsaye yana kallonsu bai ko motsa a inda yake ba, kawai ya juya ya koma dakinsa ya kulle, dai dai nan aka bude kofar parlon da sallama, Hajja da Mama Ladi suka yi tsaye bakin kofar bayan sun shigo jin hayaniya ya cika gida, Mama Ladi ce ta fara hangosu Haseenah dake zabga dambe ta gwalo ido tace "Innalillahi, menene zan gani haka?" da gudu ta nufesu Hajja ta zaro ido ita ma jikinta ya dau rawa ganin yanda Haseenah ta saka kan Badiyyah a hammata kamar zata kasheta tana duka, Hajja ta bi bayan Mama Ladi a gigice tana cewa "Innalillahi kar ta kasheta Ladi" Ihu Badiyyah take tana cewa "Wallahi yau sai na tona maki asiri a gidan, sai na fadi duk mugun abubuwan da kike yi, Mama Ladi wallahi boka da malamai take bi in ma kun ce in kai ku gidan malamin da take zuwa a zaria sai in kai ku har can, don ta kai ni wajensa wai nima yayi min aiki, Malamin har ce min yayi asiri take ma surkarta ya bata wani asirin ta kai dakin Ammi don ta raba Ammi da Mayraah yanzu haka asirin na nan a dakin har yanzu, kuma wallahi gold din akwatin Mayraah ma ita ta sa na sato na kawo mata har yau taki bani kuma taki bani kudin....." Haseenah duk ta gigice da maganganun da Badiyyah ke yi har hakan yasa ta fara loosing stamina, wanda wannan ya ba Badiyyah dama ta dinga hade kanta da bango da mugun karfi sai kace an aikota, kan kace me sai ga jini kamar an buda pampo, Mama Ladi da Hajja ihu suke a tare kamar rubabbu suna salati amma sun kasa matsawa kusa da su, Ciwo ba na wasa ba Badiyyah ta ji ma Haseenah a kai don kan kace me jini ya malale corridor din kamar an yanka rago, Haseenah ta fadi kasa wajen a sume, Badiyyah sai zare ido take ganin kamar kwakwalwan Haseenah fa take hangowa, ihun su Hajja ne ya fito da Maheer daga dakinsa, tuni Badiyyah ta shige daki a guje ta saka hijab dinta ta dau wayarta da handbag ta fice daga gidan da gudu.....
MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
*Wato idan kina neman turaruka masu musulmin kamshi, irin turaren nan da komin bacin rai dole ya narke yabi ruwa🫠 kiji kamar kinyi bargo da gajimare. Toh ki nemi Scentmania_by_sana by sana 07065525409 kawai kice ta baki 'The Empress combo'. Irin turaren dake sa maigida ya nemi shiri cikin gaggawa. In kinason kiyi activating din inner gimbiyarki👸🏽instantly wannan combo din shi ya dace dake.*
[7/13, 10:08 PM] Khaleesat Haiydar💖: Maheer ya mike ya nufi wani likita da ya fito daga emergency ward kafin yace komai likitan yace "Kai ne mijin nata?" Maheer yace "Eh ni ne" likitan yace "To mu je office" Bin bayan likitan Maheer yayi har suka karasa office dinsa, Mama Ladi da Hajja dai suna tsaye sai zazzare ido suke tun zuwan su asibitin kusan awa biyu da rabi kenan, Mama Ladi ta fashe da kuka bayan sun bi likitan dake tafiya tare da Maheer da kallo, ta rike kanta tace "Rabon ayi kawai, dama kuma ance sanin gaibu sai Allah, banda haka ni in nasan abinda zai faru kenan me zai fito da ni daga gidan Mamuda da sassafe ina cikin rufin asiri na? Wallahi ko koshi ban yi ba na fito ashe wannan fitinar ce ke kirana, Yanzu in yarinyar nan ta mutu ai har mu sai an kai kotu mun bada shaidan abinda ya faru, wai don ma Allah ya so ban karasa shiga ciki ba abun ya faru, da ya zan yi da raina yau ni Ladi, to wallahi da kyar in ba rataye Badiyyah za ayi ba in har wani abu ya samu matar nan, ni dai Allah ya so ban shiga parlorn ba" Hajja ta juya da sauri ta kalli Mama Ladi jin abinda tace, a fusace tace "Ke dai mugun alkaba'in ki yawa garesa Ladi, kuma bakin ki ya sari danyen kashi, ita Badiyyar kike ma fatan a rataye saboda shaidan ya shiga tsakaninta da matar Maheer, kawarta ce fa kowa ya sani, da gangan Badiyyah bazata ji mata wannan rauni haka ba, ko ke baki ga yanda matsiyaciyar matar ta shaketa a wuya ba da farko har sai da Allah ya ba Badiyyan sa'an bugata da bango, ni dama tun da naga Maheer ya daina walwala tun bayan auren sa da yarinyar nasan akwai lauje cikin nadi, har muka yi ta kumfan baki ya saketa akan Mayraah ashe matsiyaciya ce bamu sani ba, to ga dai maganganu tiryan tiryan a bakin Badiyyah kuma wllh ko rantsuwa nayi bazan yi kaffara ba Badiyyah bazata mata sharri ba, amma dai bari a gama da asibitin nan tukunna mu san ta kwatanci...." Mama Ladi na girgiza kai tace "Aa ba dai Mera ku ka mayar er iska ba mara galihu saboda bata da uwa bata da uban nunawa a duniya, mu je dai zuwa" Hajja ta mata wani kallo