Showing 147001 words to 150000 words out of 249515 words
hankali Maheer ya gaida Ammi yana kallonta, duk wanda ya ganta yasan ta ci kuka ba na wasa ba ranan, Maimakon ta amsa gaisuwarsa sai cewa tayi "kun san dalilin kiranku nan?" Duk suka yi shiru suna kallonta, Banda Usman da kansa ke kasa, Ammi tace "To kun ga Mayraah?" Sai a sannan Usman ma ya daga kai yana kallon Ammi, ta girgiza kai as if counting her words tace "Babu ku babu ita har abada, ko magana ya sake hada ku da ita ban yafe maku ba, you 3 should just assume baku taɓa saninta ba, baku taɓa rayuwa waje daya da ita ba" Gaba dayansu kallonta suke babu ko kiftawa, da wani expression Umar yace "How Ammi? It's not her fault all this happen...." Tsawa Ammi tayi masa tace "Questioning dina zaka yi?" Yace "No, amma bai kamata ki ce haka Ammi ba, ni har yanzu zuciyata bata yarda ba ke ce kika haifi Mayraah ba to be sincere" Ammi ta mike tana kallonsa da kyau tace "To ba ni ce na haifeta ba Umar gashi ina gaya maka da kaina yanzu, ban hada komai da ita ba, don haka ina sake jaddada maku ko gaisuwa ya kara hadaku da Mayraah wallahi ban yafe maku ba gaba daya, sannan har yanzu ina kan bakata bazan zauna gidan ubanku ba, it's better ku samar min gida in koma don gidan Hajja ma bazan je ba" Tana kai wa nan ta shige Bedroom dinta.
MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
Wato idan kina neman turaruka masu musulmin kamshi, irin turaren nan da komin bacin rai dole ya narke yabi ruwa🫠 kiji kamar kinyi bargo da gajimare. Toh ki nemi Scentmania_by_sana by sana 07065525409 kawai kice ta baki 'The Empress combo'. Irin turaren dake sa maigida ya nemi shiri cikin gaggawa. In kinason kiyi activating din inner gimbiyarki👸🏽instantly wannan combo din shi ya dace dake.
[7/12, 8:11 PM] Khaleesat Haiydar💖: Usman ne ya fara mikewa after almost 5 minutes ya fita daga Parlon, Umar ya mike ya shige dakin Ammi yana kallonta ya girgiza kai yace "Gaskiya ni bazan iya ba Ammi, zancen gaskiya kenan.... Me ta mana za mu daina kulata yarinyar da muka taso tare ku ka koya mana daukarta a matsayin little sister dinmu, me yasa tun a sannan baku sanar mana wacece ita ba sai yanzu da rana tsaka ku ce mana ba ku kuka haifeta ba, that not being enough kuma all of a sudden kice mu daina kulata, how will that be possible?" Ammi ta juya tana masa wani kallo tace "Kasan dama i am against ur coming back for this holiday ko? To kuwa zaka koma inda ka fito, in kuma kana da wata uwar da zata gaya maka kaji ne sai ka tafi ka sameta, get out Umar" Juyawa yayi ya fice daga dakin, ya bar parlon ma gaba daya banging the door behind him, Maheer ya bi sa da kallo ya jinginar da kansa jikin kujera ya lumshe ido, gaba daya ya kasa tashi a inda yake, Usman na komawa dakinsa ya dau jakarsa ya hada duk abinda zai hada a ciki ya fice daga gidan ba tare da yayi ma kowa sallama ba, Umar bai ma san action din Usman ba don shima yana shiga dakinsa dama jakarsa is already set, ya dauka kawai ya fice daga gidan trying to check if there is any flight to Abuja that evening with his phone. Sai da aka kira Magrib sannan Maheer ya tashi ya fita daga parlon Ammi, yana idar da sallah a masallacin layin ya shiga motarsa ya wuce gidansa. Daren ranan Mayraah bata yi baccin kirki ba, gaba daya taji gidan yayi mata zafi, sai kusan asuba bacci barawo ya sace ta kan darduman da ta kwanta bayan ta idar da sallah, washegari kafin karfe takwas ta shirya, kawai tana son shiga school ta nemi waje ta zauna ko zata ɗan ji sanyi a ranta, to gaba daya ta ma rasa wa zata ce ma zata tafi school yanzu, har cikin ranta taji tana tsoron Ammi ba kuma ta son ma ta hadu da ita, ta mike daga zaunen da tayi gefen gado ta dau jakar makarantar ta duk da jirin da take gani ta nufi kofa a hankali ta bude, kamar ko da yaushe yau ma Hijab ne har kasa jikinta, sauka tayi downstairs dai dai nan Hajiya Amina ta fito daga kitchen tana kallonta da mamaki tace "Ina kuma za ki?" Mayraah ta gaisheta sannan tace "Ban gama project dina ba zan shiga school ne in je cafe" Hajiya Amina tace "Toh ai baki karya ba, ga breakfast can na gama ki je ki diba" Sai a sannan Mayraah ta tuna throughout yesterday fa kamar bata ci komai ba sai ruwa da tayi ta sha kilan ma shi yasa take ta jin jiri yanzu, a hankali Mayraah tace "Toh" karasawa kitchen din tayi kawai ta hada shayi ta fito ta zauna dining ta na sha bit by bit, Hajiya Amina dake zaune parlon tace "Aa Mayraah ki je ki debi abinci, in baza ki ci Irish din ba akwai doya da kwai ki deba" Mayraah ta girgiza mata kai ba tare da ta kalleta ba tace "Bana iya breakfast da sassafe, idan naje school zan ci abinci" Hajiya Amina tace "Toh shikenan" Mayraah ta gama shan shayin ta mike ta kai cup din kitchen ta wanke sannan ta dawo parlor, Hajiya Amina tace "Abban ya san za ki school yau?" Mayraah ta gyada mata kai still not looking at her, Hajiya Amina tace "To transport fa?" Mayraah tace "Ya tura min" Hajiya Amina tace "Toh Allah ya tsare" Mayraah tace "Ameen" Daga haka ta fita daga gidan. Har Mayraah ta isa school bata sani ba don tayi nisa tunanin da take, har sai da mai adaidaita sahun ya juya ya kalleta don yana ta ce mata sun isa amma shiru kuma yaga idonta biyu ba wai bacci ko wani abu ba, Juyowan da yayi ne ya dawo da Mayraah daga duniyar tunanin da ta fada, ta fara kalle kallen inda suke sae kuma ta sauka da sauri ta basa kudinsa ta shiga cikin makaranta, nesa da department dinsu ta zauna har sai da karfe goma yayi sannan ta mike da kyar ta tafi cafe don yin printing copies din project din nata gaba daya, bata bar cafe din ba sai kusan 12, ita kanta tasan her Temperature is rising gradually, she is becoming so weak, ga wani ciwo da kanta yake, da kyar ta tako har department dinsu taga Motar Musharraf a parking space, ta shiga cikin department din ta tafi sama, sai da ta fara zuwa office din project co-odinator dinsu tayi submitting masa copy biyu da zata basa, sannan ta fito da copy daya zata kai office din Musharraf, tsaye tayi for few seconds bakin kofar kafin tayi knocking, sai da ya mata izini sannan ta bude kofar ta shiga ya daga kai yana kallonta, ita dai bata yarda sun hada ido ba ta karasa kusa da table dinsa still not looking at him ta ɗan risina tace "Good afternoon sir, i came to submit my project" Musharraf ya sauke idonsa daga kallonta after a minute ganin bazata dago kai ba, can kuma yace "When did i ask u to submit?" Shiru tayi bata ce komai ba, on a serious tone yace "I am asking u Madam" Still kanta a kasa tace "I can't remember sir" Yace "Ok i see, go and come back around 5:40pm" Sai a sannan ta daga kai ta kallesa suka hada ido, lokaci daya ta dauke kanta ta juya ta nufi kofa, ya bi ta da kallo har ta fita ta kulle masa kofar sa. Mayraah na fita office din tana share hawayen da ya cika idonta ta sauka downstairs, ji tayi bata da strength din da zata ci gaba da zama makarantar har zuwa sanda yace, she is beginning to feel pain in all over her joint, nan da karfe biyar din da yace kusan awa biyar kenan fa, to ina zata je? In ma ta je masallaci zata takura masu sallah ne tunda kwanciya zata yi, Ummi ce ta tado mata, ta ciro wayarta a jaka bayan ta nemi waje ta zauna tayi dialing numberta, suna gaisawa cike da karfin hali tace "Ummi don Allah kina hostel?" Ummi tace "Wallahi ina school kinsan yau za mu yi final paper dinmu, kuma paper din 4pm ne, za ki je hostel din ne?" Mayraah tace "Eh na shigo inyi submitting project dina ne kuma supervisor din yace sae 5pm, to na gaji baxan iya zama school din har zuwa sannan ba" Ummi tace "To bari in zo department din naku in kawo maki key yanzun nan" A hankali Mayraah tace "To Nagode" Katse wayar tayi ta mayar jakanta, babu bata lokaci sai ga Ummi ta zo ta kawo mata makullin, Mayraah ta amsa ta mata godiya suka fita tare, Ummi ta koma department dinsu, Mayraah kuma ta wuce hostel, Mayraah na isa hostel din taji zazzabi ya rufeta, da kyar ta iya yin alwala saboda sanyin da ta fara ji, ta jira har lokacin sallah ya karasa sannan tayi sallah bayan ta idar ta kwanta ta rufa da bargon Ummi nan da nan bacci ya dauketa... A hankali Mayraah ta bude ido ta dalilin taɓata da taji anyi, da sauri ta mike zaune tana kallon Ummi, da damuwa Ummi tace "Baki da lafiya ne naji jikinki yayi zafi" Mayraah ta buda ido sosai tace "Karfe nawa pls?" Ummi ta kalli wayar hannunta tace "5:30" Mayraah tace "Innalillahi ban yi sallah ba, and i have to submit my project" Tana sauka daga kan gadon taji wani jiri ya debeta ta koma da sauri ta zauna ta rike kanta, Ummi ta rikota tace "You look very sick, kawai ki kira Supervisor din naki kice u are not feeling fine.... temperature dinki is so high" Mayraah ta girgiza kai da sauri tace "Aa zan iya" Daurewa tayi ta mike tana kallon flask din Ummi tace "Akwai ruwan zafi zan yi alwala" Ummi tace "Bari in daura maki" daga haka ta mike ta daura mata ruwan a kan gas, duk karfin hali kawai Mayraah ke yi amma duk jikinta ciwo yake mata, a haka tayi alwala ta dawo tayi sallah sannan ta dau jakarta tana kallon Ummi tace "Bari in je inyi submitting" Ummi tace "To za ki wuce gida daga can ne?" Mayraah ta gyada mata kai sannan ta mata godiya ta fita, ita kanta bata san da yanda ma ta iso department din nasu ba tsabar yanda take ji a jikinta, har a sannan Musharraf na school din don ta ga motarsa a parking space, the department was so quiet except for some few Lecturers dat are still around, alamar yau ba ayi exams din karfe hudu ba a department din or probably duk yan department din sun gama exams dinsu, hawa stairs kadai took her almost 7 minutes don sai ta huta take ci gaba da tafiyar, a haka har ta isa office din Musharraf tayi knocking, yana mata permission din shigowa ta shiga office din ta kulle kofar, wani mugun sanyi taji na shigarta saboda AC dake kunne, cike da karfin hali ta karasa gaban table dinsa taki kallonsa ta ajiye masa project work din nata kan table tace "Good evening sir" Shi dai kallonta kawai yake, ganin yaki ce mata komai gashi ta gaji da tsayuwar don jiri kawai take gani, ga sanyin da yasa ta fara shivering kawai ta zauna kan kujeran wajen, mikewa yayi ya zagayo ya zauna kujeran dake facing dinta yana kallonta a hankali yace "Are you okay?" Still taki barin ta hada ido da shi, he notice she is shivering, ya dau remote ya kashe AC din office din yana kallonta yace "Mayraah" Sai a sannan ta daga kai ta kallesa, and he saw how pale she look, mikewa yayi da sauri ya dafa goshinta ya hau jero mata tambayoyi without waiting for answer yace "Baki da lafiya ne? Your temperature is so high, have u been sick?" Duk da halin da take ciki ta wani hade rai ta cire hannunsa da sauri a goshinta, ta mike da nufin barin wajen ta ji wani dizziness tuni ya kamata ya zaunar da ita kan kujeran nan da nan hankalinsa ya tashi, still holding on to her yace "Tun yaushe ne baki da lafiya Pls??" Mayraah ta hade kanta da table bata ce komai ba, da sauri ya koma ya bude drawer dinsa ya ciro Blood pressure gauge ya dawo, ya duƙa gabanta ya kamo hannunta, janye hannun tayi nan da nan hawaye ya cika idonta amma ta kasa cewa komai, cike da damuwa yace "Pls ki bari in duba B pressure dinki..." Haka nan ta bari ya dubata, yayi unwrapping din inflating rubber cuff din da sauri ya zauna kujeran da ke kallon wanda take, a bit shocked yace "Subhanallah, ur blood pressure is beyond low, Baby what's wrong with you? Me yake faruwa?" Mayraah dai bata dago kanta ba hawaye ne kawai ke zuba idonta, Mikewa yayi ya dauko mug dinsa ya dauraye ya zuba ruwan zafi ya hada mata coffee drink ya ɗan yi diluting dinsa da bottle water ya dawo gabanta ya dagota yace "Drink this plss dear, it's a first aid, sae mu tafi hospital right away" Hannunta na rawa ta amshi mug din, ganin haka yaki sake mata ya fara bata coffee din da kansa, sae da ta kusa shanyewa ya kyaleta ya ajiye cup din, ya kashe fridge din office din ya sake curtain din windows ya dawo ya dau makullin motarsa amma sae ya tuna ba lallai ta iya tashi da kanta ba, assuming ba department suke ba he will definitely assist her, kawai ya fita office din hoping zai ga wani student mace or even a female Lecturer da zata rike Mayraah zuwa Motarsa, Dr Asma'u ya samu office dinta, ta biyosa har nasa office din bayan ya gaya mata abinda ke faruwa, ta dago Mayraah tana mata sannu suka fito daga office din har zuwa parking space tana rike da ita, back seat ta bude mata tana kallon Musharraf tace "Dr ko zaka jira in rufe office dina mu tafi asibitin tare?" Yace "Toh ba damuwa" Ta koma cikin department din, sannu kawai yake ma Mayraah da ta hade kanta da seat din motar, a haka Dr Asma'u ta dawo ta samesu da jakarta ta shiga back seat din ta dago Mayraah tana mata sannu, Musharraf ya shiga motar suka kama hanyar asibiti. Tun da aka yi ma Mayraah allurai aka sa mata drip take bacci, Dr Asma'u suna isowa asibitin bayan anyi admitting Mayraah dama ta wuce gida, Musharraf na ganin karfe takwas yayi kawai yayi deciding ya kira Maheer cause definitely yasan za a kikkira Mayraah a waya kuma jakar na office dinsa, he was even surprise da ya ga har a sannan Maheer bai kirasa ba tun da zuwa yanzu dai yasan dole za a san bata koma gida ba, Maheer na daga kiran bayan sun gaisa, Musharraf yace "Mayraah ce bata da lafiya anyi admitting dinta hospital since around 6:30...." Maheer yayi shiru, sai kuma a hankali yace "Subhanallah, bana gari but zan tura maka number Abbanmu right away, nima ban jima da kunna wayar ba kilan Abban ya neme ni bai sameni ba, let me send u his contact now" Musharraf yace "To ina jira" Babu bata lokaci Maheer ya tura masa number Abba, Musharraf yayi dialing bayan Abba yayi picking, ya gaishesa sannan yayi introducing din kansa tare da sanar masa dalilin kiran duk a lokaci daya, Abba yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, tun 6 ake kiran layinta no response...." Musharraf yace "Eh i think jakar nata na makaranta" Abba yace "Wani Asibitin ne?" Musharraf ya sanar masa, Abba yace "Gani nan zuwa yanzu, thank you" Daga haka ya katse wayar. Hajiya Amina ta fito daga dakinta sanye da hijab bayan Abba ya sanar mata Mayraah na hospital, sai ga Mama Ladi ta taho daga bangaren Ammi rike da kwanon abincin da ta ci zata kai kitchen, Hajiya Amina tace "Mama wai malamin makarantar su ya kira tana asibiti an kwantar da ita, yanzu Abban nasu ya kirani yake gaya min" Mama Ladi ta saki salati tace "Mun shiga uku, asibiti kuma, me ya sameta? to ke yanzu ina za ki da hijabi?" Hajiya Amina tace "Asibitin za mu tafi, yana waje yana jirana" da sauri Mama Ladi tace "Jirani in dauko gyale mu tafi tare kawai, ai hankalina bazai kwanta ba idan ban bi ku ba" Hajiya Amina tace "Toh zan jira ki a kasa Mama" Da sauri Mama Ladi ta koma bangaren Ammi, Ammi na zaune kan darduma a parlon, Mama Ladi ta ajiye mata kwanon hannunta ta figi mayafinta tace "To ga Mayraah can bata san inda kanta yake ba a asibiti rai kwakwai mutu kwakwai, yanzun nan aka kira daga asibitin aka sanar za mu tafi da su Mamuda" Ammi ta juya da sauri ta kalli Mama Ladi da har ta fice daga Parlon da gudu da mayafinta. Ko da suka isa asibitin har a sannan Mayraah bacci take, Musharraf ya mike daga kan plastic chair da yake zaune yana ma Abba sannu da zuwa da ladabi, kallo daya Abba yayi masa ya amsa ya karasa gadon ward din yana kallon Mayraah, Musharraf ya gaida Mama Ladi da Hajiya Amina da ladabi, Hajiya Amina ce kawai ta amsa, Mama Ladi ta dafe kirji cikin rawan murya tace "To me ya sameta ni Ladiyo? Ko dai hatsari tayi? Don lafiya ta fita gida" Abba ya kalli Musharraf yace "I want to see the Dr" Musharraf yace "Toh yana office Abba" Abba ya bi bayansa suka fita zuwa office din likitan. Har karfe sha dayan dare Mayraah bata farka ba, Hajiya Amina ta koma gida ta kawo mata blanket da kayan shayi da flask ta dawo, babu yanda Abba bai yi da Mama Ladi