Showing 231001 words to 234000 words out of 249515 words
don girka masu Breakfast, babu abinda babu a kitchen din na foodstuff, bayan ta gama girkin ta kai dinning table ta jera kan table din, Ammi ce ta sauko downstairs Mayraah ta karasa ta gaisheta da ladabi, Ammi tace "How was ur night?" Tace "Alhamdulillah, Ammi ga breakfast na gama...." Ammi tayi murmushi tace "To sannu da aiki daughter, shiryawa za ki je kiyi yanzu ko? naga karfe takwas ya wuce kar ki makara" Mayraah ta gyada mata kai tace "Eh yanzu zan je in shirya" Ammi tace "To kiyi maza" Mayraah ta wuce sama don yin wanka, sai karfe tara ta sake saukowa downstairs sanye cikin black Abaya da handbag dinta sai envelope me dauke da credentials dinta, har ta mance rabon da ta sa Abaya sai Hijab, she look so cute and stunning kuma Abayan ya haska farin fatarta ta dawo kamar wata balarabiya duk da bata yi make up ba sai eye pencil da ta sa a ido, da lip gloss da ta goga a lips dinta, Ammi da Abba na dinning area ta samesu, Ammi na ganinta dama ta fara hada mata tea, Mayraah ta durkusa ta gaida Abba ya amsa da murmushi yace "Kin tashi lafiya?" Tace "Alhamdulillah" Yace "You look cute my dear" Mayraah tayi murmushi tace "Thank you Abba" Ammi ta nuna mata kujera tace "Zauna kiyi breakfast, u are already late" Mayraah ta mike ta zauna sannan ta dau shayin da Ammi ta hada mata, Ammi ta ajiye mata plate din irish a gabanta, tace "Amma after the interview za ki dawo ai, nasan ba yau za ki yi resuming aikin ba dai" Mayraah ta gyada mata kai, Ammi tace "Sai dai a samu food warmer ki dinga tafiya da abinci saboda lunch" Mayraah ta zaro ido ta turo baki tace "Food warmer kuma Ammi kamar er yarinya" Ammi tace "To da yunwa zaki je kina aikin, don nasan ba siyan abinci zaki dinga yi ba" Mayraah tace "To ai har na gama school bana zuwa da abinci fa" Abba dai yayi murmushi yace "In bazata dinga zuwa da shi ba sai drivern ya dinga kai mata abincin da rana kawai" Mayraah dai bata sake ce masu komai ba a ranta kuwa har ta gama deciding in dai drivern za a ce ya dinga kai mata abinci kawai ce masa zata yi yana fitowa ya cinye a hanya ya koma gida da warmer din don babu abinda zata yi da abinci a wajen aiki kamar wata baby, Tana gama breakfast din ta mike zata kai plate da cup din kitchen Ammi tace "Aa bar shi, lokaci ya wuce" Abba yace "Driver zai yi dropping dinki a asibitin, jiya a airport ai wayarki ya kira yaje ya dauko ku so i assume you have his number idan kin gama abinda kike yi sai ki kirasa yaje ya dauko ki, he is ur driver from henceforth" Mayraah tayi murmushi a hankali tace "Nagode Abba" Abba yace "You are welcome dear" Sallama tayi masu ta dau jakanta da Envelope, Ammi ta mike tace "Kiyi addu'a kafin ki fita" Mayraah ta gyada mata kai, har bakin kofar Ammi ta rakata tace "Allah ya bada sa'a daughter, stay safe pls" Mayraah ta ciro black glasses dinta ta saka tace "Ameen Ammi, in sha Allah" Murmushi Ammi tayi tace "Yau dai gayu kike ji daughter" Er dariya tayi ta fita compound din taga driver zaune yana jiran ta, ya sauko da sauri ya gaisheta da ladabi, maimakon ta amsa sai ta gaishesa ita ma sannan ta bude front seat ta shiga don bazata zama comfortable tana baya yana driving dinta ba, bayan sun bar gidan ganin ya kama hanya bai tambayeta inda zai kai ta ba sai kawai ta gaya masa, yayi kasa da kai yace "Ranki shi dade ai Alhaji ya sanar min tun a jiya, nasan asibitin ma, da yake na taɓa yin aikin Uber" Mayraah tace "Ohk" Agogon wrist dinta ta duba taga karfe tara da rabi, tafiyar minti talatin suka yi zuwa asibitin, Mayraah na fara hango babban building din hospital din ta ji gabanta ya fadi, yanzu zata je ta hadu da wancan jarababben mutumin ita wallahi ko irin farin cikin ta samu aiki a asibitin ma bata yi, she is not even excited don gaba daya ya sa taji bata son asibitin a ranta but bata son tayi shunning effort din Dr Khalil ga kuma Abbanta dake ta farin cikin ta samu aiki da ma brothers dinta, wnn ne kawai ya hanata cewa bata son aikin tun a kano, bayan drivern yayi parking ɗan gaba da gate din asibitin don kar yayi hindering masu shiga da mota, Mayraah ta bude motar ta sauka tace "Nagode, idan na gama zan kira ka" Yace "Toh Hajiya Allah ya bada sa'a" Tace "Ameen" Tana juyawa ta ga wani lafiyayyen mota ya taho zai shiga asibitin, tuni masu gadi suka bude gate din suka ɗaga karfen gaban gate din inda motar zata wuce, bata ga wanda ke cikin motar ba don tinted glass ne, bayan motar ya shiga ta bi ta inda ake bi a shiga cikin asibitin da kafa, tana tafiya a hankali, Tana shiga reception din ta gaida nurse din dake wajen sannan ta tafi sama not minding yanda aka bi ta da kallo, ko basu ganeta bane oho, office din Dr Khalil ta nufa duk da bata ga motarsa ba a parking space, knocking tayi to be sure if he is around ya mata izinin shigowa ta bude kofar, yana ganinta ya mike tsaye cause da farko bai gane ta ba yace "Mayraah...." Ta ɗan yi murmushi ta karasa tace "Ina kwana" Yana gyada kai yace "Lafiya lau, ashe haka kika iya gayu, ai ni ban gane ki ba wallahi" Murmushi kawai tayi ta zauna, yace "Maa sha Allah, you look cute, jiyan ku ka shigo kenan?" Mayraah ta gyada masa kai, yace "That's good, Jiya Ceo ma ta shigo kasar, i think she will be around today kinsan gobe za mu je workshop din lagos" Mayraah tace "Oh ok, ya twins?" Yace "They are fine Alhamdulillah, are you together with the credentials?" Ta gyada masa kai yace "Ohk let me have a look first" Mika masa Envelope din tayi, ya amsa yana ciro takardun ciki yace "MD din ma yana nan ai, tare muka shigo dazu, sai da naje na daukosa a motar sa, shi yasa ban ma zo da tawa motar ba...." Statement of result dinta ya fara dubawa, ya dinga kallon result din babu ko kiftawa, can ya nemi kujera ya zauna ya kalleta ya buda ido sosai da mamaki yace "Really?" Ita dai Mayraah tayi shiru bata ce komai ba, buda baki yayi yace "First class?" Still ta ki ce masa komai, Yace "Ikon Allah.. this rare, are you this intelligent Mayraah? I am really surprise wallahi" Mayraah ta ɗan masa murmushi kawai, ya gyada kai yace "Maa sha Allah, i am really impressed, ai duk nan ina ga banda MD we don't have any staff with first class na degree..." Sai kuma ya fara dariya kamar wanda ya tuna abu, Mayraah dai taki ce masa komai har da ɗan daure fuska, Dr Khalil ya duba other credential din nata sannan ya maida su cikin Envelope yana murmushi yace "Za mu shiga theatre nan da minti talatin, bari in samesa if u can go for the interview now, don banda shi za mu shiga theatre din" Mayraah ta gyada masa kai tace "Ohk" Ajiye envelope din yayi ya fita office din zuwa office din MD, a long pavement din saman ya samesa ya fito daga office din CEO walking towards his office, Dr Khalil ya jirasa
har ya iso MD yace "3 nurses, 5 Dr's for tomorrow's workshop, zaka yi booking flight din yau, 10 ticket in all" Dr Khalil dai na biye da shi har suka shiga office dinsa, MD ya zauna letting out a sigh yace "Yanzu zaka ga ta sake biyo ni nan" Dr Khalil yayi dariya yace "Amma ana gama workshop din zata koma ne?" MD bai ce masa komai ba ya mike ya dau tea cup dinsa ya tafi ya wanke ya dawo ya zauna yace "Nan da sati biyu ne Conference din da tace a England ai, or is it even US, na dai manta" Har ya bude flask din sai kuma ya sake kallon cup din ya mike ya tafi ya kara wankewa ya dawo, Dr Khalil yace "Ohk ku biyu za ku yi attending Conference din kenan?" MD yace "No pls... Dr Balogun should go" Dr Khalil yace "Kai ma kasan she can't do without u in anything ai" MD ya kalli wayarsa dake ring ya dauka yayi picking call din ya kai kunne, cikin minti biyu ya gama wayar ya ajiye, ya kalli Dr Khalil yace "What were u saying?" Dr Khalil ya kalli agogon office din saboda theatre da za su shiga he is cautious of time, MD ya sake tashi ya tafi ya wanke tea cup din hannunsa ya dawo, kiran Ceo ne ya shigo wayarsa ya zauna ya daga yana sauraronta, sai kuma yace "Ohk ma, i will bring them in 30 mins time" Bayan ya katse wayar ya tashi ya sake wanko cup din ya dawo, Dr Khalil ya taɓe baki ya mike yace "Are you ready? Za ta shigo interview din yanzu, cause she is around" MD ya daga kai ya kallesa, sai kuma ya hade rai yace "Waye haka?" Dr Khalil yace "You insisted she should come for the interview last week, so she is around today" MD yace "Ohh shine yasa CEO ke tambayana ita da naje office dinta yanzu kenan, ashe ta ganta ne, ita dai ta dage lallai sai tayi aiki a asibitin nan, ko dai mayya ce yarinyar nan?" Dr Khalil yace "Ga dai ta nan with her credentials kamar yanda ka bukata, so i will send her right away, don ni zan shiga theatre" Ko tankasa MD bai yi ba ya sake tafiya ya dauraye cup da zai sha coffee, kafin ya dawo har Dr Khalil ya fita daga office din, yana komawa nasa office din ya kalli Mayraah yace "You can go to his office, but plss Mayraah be a good girl, kiyi abinda ya kamata he is our boss, and he is employing you, speak to him with respect and calmness, kalmominki kar su wuce Yes sir, Ok sir, sorry sir, thank you sir" Murmushi Mayraah tayi tana kallonsa ta rasa dalilin da zai dinga cewa she should be a good gal in zata je gun jarababben mutumin can, to tayi kama da bad girl ne? Ta sunkuyar da kai tace "Toh Dr" Yace "You can go now, yana jira" Mikewa tayi ta dau jakarta da Envelope din takardunta, ga cire glasses dinta zata saka a jaka, Dr Khalil yace "Me yasa kika cire, ki maida abun ki" Mayraah ta kallesa yace "Ki sa mana, ai ya maki kyau" Ɗan murmushi tayi ta maida glasses din sannan ta nufi kofa, har ta rike handle din sai kuma ta juyo tana kallonsa a hankali tace "But do u have any idea akan abinda zai tambayeni" Dr Khalil yace "Ki kwantar da hankalinki and be calm, ba wani tambayar da zai maki na sani, kawai zai duba takardunki sai kuma ya tambayeki informations dinki to be imputed, yana ganin result din ki ma nasan sai ya rasa tambayar da zai maki don mamaki.... So just go" da murmushi ya kare maganarsa, Mayraah ta sauke idonta kasa ta juya ta fita daga office din, last floor ta tafi zuwa office din MD, gently tayi knocking kofar har sai da ya amsa sannan ta bude ta shiga, Coffee dinsa yake sha bai kuma daga kai ba balle ya kalleta, ta karasa har gaban table dinsa ta tsaya calmly tace "Good morning sir" Dago kai yayi, kiris ya rage ya saki cup din coffee din hannunsa don har sai da ya ɗan zube masa a white shirt dinsa, mikewa yayi da sauri ya ajiye cup din yace "Kee, why will u just badge into my office are you okay? Ance maki kasuwa ne nan?" Bai jira me zata ce ba ya shige Bedroom dinsa dake office din, Mayraah ta bi sa da kallo, can ta taɓe baki a ranta tace kilan dai Dementia garesa, cause sai da tayi knocking ya bata permission din shigowa kafin ta shigo, tana ta tsaye har ya fito bayan minti biyar with another white shirt, ya wani daure fuska kamar bai taɓa ko murmushi ba, ita dai bata yarda ta kallesa ba har ya karaso table dinsa ya dau cup din coffee din ya tafi ya zubar ya dawo, still yaki kallonta yace "Me kike jira har yanzu?" Calmly tace "I came for the interview u ask me to come for, here are my credentials" Bata jira me zai ce ba ta ajiye envelope din kan table dinsa sannan ta koma gefe ta tsaya, yace "Ohk shi Khalil din ne yace maki kina zuwa ki ajiye CV din kan table dina?" Mayraah bata ce komai ba, ta dau envelope din ta nufesa ta tsaya a gabansa tana mika masa while looking at him, ƙin yarda ya kalleta yayi may be he wasn't expecting that, kawai taga ya bar wajen ya koma seat dinsa ya zauna, ta juya tana kallonsa still ya ki kallonta, kwankwasa office din aka yi, ya mike da sauri duk tunaninsa Ceo ce, Dr Balogun ya bude office din ya shigo da wani file, yana ganin Mayraah yace "Ohh Madam, where have u been all this while?" Mayraah ta gaishesa da ladabi, ya amsa da hausansa irin na yoruba yace "Kwana biyu baki zo aiki ba, ina kika tafi?" Mayraah ta ɗan yi murmushi tace "Ya ce in zo interview ne tukunna kafin in ci gaba" Dr Balogun ya kalli MD that was unnecessary clearing stuffs off his table, Dr Balogun yace "Ohk MD in je in dawo kenan after the interview, dama akan aikin da za mu yi da daddare ne..." Sai a sannan MD ya daga kai a takaice yace "You can interview her Balogun, i am a bit busy...." Dr Balogun ya kalli Mayraah yace "Are you with ur CV?" Ta gyada masa kai ta mika masa Envelope din hannunta, zaunawa yayi kan kujera ya nuna mata kujeran dake kallon wanda ya zauna yace "Sit..." MD yace "Why should she sit? She should take off those glasses we are not doing fashion here" Dr Balogun ya kalli Mayraah da ta cire glasses din idonta, sai kuma ya fara fiddo da takardun, Mayraah ta wani harari MD dake kallonta ta gefen ido, Statement of result dinta Dr Balogun ya fara dubawa, sai kuma ya kalleta da sauri yace "Waow, first class from this prestigious university? It's my alma mater also, nasan lecturers dinku sosai" Mika ma MD yayi, MD dake kallonsa yace "First class in Botany or what?" Dr Balogun ya zaro ido yace "Nursing Science Malam, ina jin fa department din nan rabon da a fita da first class zai kai shekara sha biyar ko ma ya fi, and she just graduated" MD dake ta kallonsa yace "Nursing Science?" Dr Balogun yace "Gashi ka duba" MD ya girgiza kai yace "Wani makaranta ne?" Dr Balogun ya gaya masa, MD yace "That's a lie" Da mamaki Dr Balogun yace "Ka taɓa ganin anyi forging result a makarantar nan?" MD ya dau wayarsa yace "I have a frnd that is a Lecturer in the department, i will confirm it now" Shiru Dr Balogun yayi yana kallon MD da ya amshi result din yana dubawa sannan ya dau wayarsa ya fara dannawa, Ita dai Mayraah ko kallon inda yake bata sake yi ba, har cikin ranta bata taɓa jin ta tsani mutum irin yanda take jin tsanar mutumin nan ba, she detest him with passion, ji take kamar ta fice daga office din amma bazata yi haka ba sbda Dr Khalil, tana ta jiran taji ya kira wayar sai kuma bai yi ba, ya maida wayar ya ajiye yace "I will confirm that later, Dr Balogun you can leave, we will discuss the issue at hand later" Mikewa Dr Balogun yayi, har sannan kallon Mayraah yake don ko kadan bai ji shakkan result dinta ba, bayan fitar Dr Balogun ya jawo laptop dinsa after some minutes ba tare da ya kalleta ba yace "Ur name?" Sai a sannan Mayraah ta kallesa, a takaice tace "Mayraah Mahmud" Ya hade rai ya kalleta yace "Kee sunanki zaki gaya min ba sunan gayunki ba, ko an gaya maki wajen wasa ne nan?" Tace "U can check the name in my result for ur self" ita kanta bata san sanda ta gaya masa haka ba, ya dinga kallonta, kawai ya rufe laptop dinsa yace "Get out" Bude office din aka yi Ceo ta shigo, ya mike da sauri yace "U need something Ma?" Karasowa ciki tayi tana kallon Mayraah cikin sanyayyen muryarta tace "Hello, how are you, i just asked of u not long ago" Mayraah ta gaisheta da ladabi, MD dai kallonsu kawai yake, Ceo tayi mata side hug, sosai gaban Mayraah ya fadi, Ceo na kallonta with calmness tace "Why are you not on scrub?" Mayraah ta kasa kallonta tace "I..." Sai kuma ta rasa me zata ce, Ceo ta kalli MD tace "Is there anything?" Da sauri yace "No, not really, just adjusting some mistakes in her data.... She is not on duty today" Ceo tayi murmushi tana kallon Mayraah a hankali tace "If he is done, Come make me coffee in my office Mary Ann" Mayraah ta gyada mata kai tace "Ok Ma" Daga haka ta ajiye takardun hannunta ta juya ta nufi kofa, Mayraah ta bi ta da kallo babu ko kiftawa, juyawa tayi suka hada ido da shi, lkci daya ya mike ya dau wasu textbook zai kai Library dinsa na office din, tace "Can i take my leave?" Wani shegen kallo ya jefa mata, hakan yasa ta fara kokarin tattara