Showing 39001 words to 42000 words out of 249515 words
tace "Cabb zaku sha tsada kuwa...." Haseenah tayi er dariya tace "Yes we can afford it" Cousin dinta da zata kusa shekara 39 me suna Jamila tace "Banda ma zamani yaushe har zaki wani bi ango ana gobe daurin aurenku kuje siyo kaya, ai ace da ne tun ana saura sati biyu ko uku baza ku sake haduwa da shi ba sai dai a dakinki in an kai ki, amma yan matan yanzu ko a jikinsu babu kunya suke sabgar su" Haseenah taki kallon inda take kuma ta mata banza don shegen manyancen ta yafi ƙarfin ta, gashi dama ba wani shiri suke ba, Bata taɓa auren ba fa amma tsabar manyance tana maganar zamanin da, Samira ta mika ma Haseenah wayarta dake ringing, Haseenah ta amsa ganin Badiyya ce ke kiranta ta mike ta fita daga dakin ta kullo kofa tayi kasa da murya tace "Hello Badiyya ya aka yi?" Badiyya tace "Ke zan tambaya ya aka yi, ina ta kasa kunnuwa shiru ban ji feedback ba, ko baki kai kasuwan bane wai?" Haseenah tace "Sai bayan kin tafi na tuna fita fa zai min wahala Badiyya, kinsan jibi ne fa daurin auren, amma nayi ma shi customer din nawa magana yace zai zo har gida ya amsa gobe da safe, to idan ya zo zan san ta yanda zan fita in basa a kofar gida" Badiyya da hakan bai mata dadi ba tace "Gidan naku fa naga an fara taruwa Haseenah kada aje a samu matsala, kuma kinsan wllh wllh ba yarda zan yi ba ko" Haseenah tace "Haba dallah, yanzu haka maganar da nake maki ma jakar da na saka gold din gashi a makale a hammata ta, ko da wasa bazan bari inyi nesa da shi ba ai sai kace ban san meye a jakar ba" Badiyya tace "To don Allah ki takura sa har sai ya zo goben ya amsa nan ne hankalina zai kwanta" Haseenah tace "In sha Allahu, dama yace da scale zai zo a gabana zai auna, kinga yana gaya min price din zan kira ki ki turo account number" Badiyya tace "Toh shikenan Nagode" Daga haka suka yi sallama Haseenah ta koma dakinta.
Maheer ya shigo dakin Ammi da sallama yace "Gani Ammi" Ammi tace "Idan ka bude WhatsApp dinka zaka ga na tura maka picture din gold din nan, don Allah kai ma ka taya ni bincikawa ko..." Maheer yayi saurin katse ta yace "Ta ina Ammi? Ni da ba kasuwa nake shiga ba ba sanin komai nayi a kan Gold ba wannan ai sai mata" Ammi tace "To shikenan, Hajiya Safiyya tace min zata shiga kasuwan gobe ta duba, dama wallahi Maheer kudin account dina ne basu wuce 3.5M ba, shine nake so don Allah idan bazan takuraka ba ko 1M ne ka ara min in sha Allahu babu jimawa zan mayar maka, in dai na samu 1M din nan nasan sauran bazai gagara ba da izinin Allah, bana son Abbanku yasan komai a kan wannan abinda ya faru ne don abun kunya ne a gareni, amma nasan zai bani in na tambayesa, Usman kuma ni bana son fitinarsa gaskiya, ina gaya masa sai abun nan ya dawo sabo fil wallahi, don haka ka rufa min asiri Maheer duk da nasan hidimar da kayi na kashe kudi a yan kwanakin nan, kayi hakuri ka ji" Maheer dake ta kallon Ammi dama ya innata abinda ya sa ta kirasa kenan shine ta fara kame kamen wai ya nemo mata irin Gold din a kasuwa, yasan ba dalilin kiran ba kenan tunda dai tasan shi ba kasuwa yake shiga ba, she just beat about the bush kafin taje main point dinta, ko kadan Maheer bai son duk abinda zai daga hankalin Mahaifiyar tasu, yace "Shikenan Ammi zan tura maku in sha Allah, Allah ya rufa asiri" Ammi tace "Ameen, Allah maka albarka Maheer, Allah ya sa 'ya yanka su maka biyayya yanda kake min, Allah ya kara maka budi" Bai wani jima a dakin ba ya fita...
Washegari Thursday karfe tara da rabi Maheer ya fita gida zuwa gidansu Haseenah don kai ta su siya kayan dinner dinta tunda na farkon tace masa bata so, jiran kusan minti ashirin yayi mata a mota sai ga ta ta fito ta shiga front seat tana masa wani kallo tana blushing tace "Good morning Sweedy" Ya jinginar da kansa jikin kujeran motar yace "Nace maki akwai inda zan je amma kika bata min lokaci Madam" Ta wani karyar da kai tace "Ita fa amarya bata laifi Baby, ko ka manta ne?" Tada motar yayi suka bar layin, waje me shegen tsada ta kai sa za ta siya ready made din dinner wear din wanda tun a IG ta sa suka turo mata ta zabi wanda take so, kawai yanzu zuwa zata yi ta gwada in akwai ɗan wani adjustment da za ayi sai a mata nan take, shi dai bai ce mata komai ba har suka shiga Lounge din wajen, bayan some minutes aka yi attending masu, wani ubansun dress ya ga an dauko mata wanda ko ba a fada maka ba kasan sai aljihu ya girgiza, ta amsa tana wani murmushi aka yi leading dinta zuwa inda zata je ta gwada, Maheer ya sauke wani ajiyar zuciya a ransa yace ai ko za su yi bala'i da ita don in har kayan nan ya wuce 200 zuwa 250 to sai dai a fasa siya, ya dau ruwan da aka ajiye masu yayi sipping yana jiran jin price din kayan, wayar Haseenah dake cikin jakarta ne ya fara vibrate, ya kalli jakar dake gefensa sannan ya dauke kai, har dai kiran ya katse, sake kira aka yi nan ma dai bai yi attempting ya ga me kiran nata ba, sai da aka yi kira kusan sau hudu, sannan ya sake kallon jakar da mamaki, jawosa yayi kusa da shi ya bude ya ciro wayar, yana cirowa kuwa yaga wata babban sarka sai daukan ido yake can kasar jakan, ya sa hannu ya ciro sarkan yaga hade yake da dankunnensa da zobe, da ɗan mamaki yake jujjuya sarkan, wayar Haseenah da ke daya hannunsa ya fara vibrate, yana dubawa yaga Badiyya ce, sake kallon sarkan yayi kamar me observing din wani abu, da sauri ya ajiye wayarta ya dau nasa ya shiga WhatsApp ya shiga chat dinsa da Ammi yayi downloading image da ta turo masa jiya don dama bai yi downloading ba, he was sooo shocked ganin exactly sarka da dankunnen hannunsa ne a picture din, ya dinga kallon hoton gold din wayar tasa da na hannunsa, banbancin kawai wanda Ammi ta tura masa a case dinsa yake, wannan kuma ba cikin case yake ba, kamar wanda ya tuna abu yayi saurin mayar da wayarta cikin jakarta ya ajiye jakar inda ta bar sa, ya fara tunanin yanda zai yi da sarka da dankunnen hannunsa, da sauri ya zura a aljihun wandonsa, and it was very obvious zata iya lura da aljihun nasa, can ya mike ya kai wayarsa kunne kamar yana waya ya fita daga Lounge din ya fito harabar wajen, motarsa ya nufa still pretending he is making call ya bude motar ya boye Gold din a ciki sannan yayi maza ya koma ya zauna inda yake zaune, bayan few minutes sai ga Haseenah ta fito tana wani murmushi tace "Baby transfer the 600k for them mu tafi, masu lalle nasan suna can suna jirana dama nace sai ana gobe daurin aure zan yi so that it will remain clean har a kai ni gidanka" Ya sakar mata murmushi yace "That is thoughtful of you, dress din ya maki dai ko?" Ta zauna kusa da shi tace "Sure dear, i love it soo much" Nan take yayi transfer din, bayan sun yi confirming payment din aka bata package din kayan suka fito tare da shi tana sakale da jakarta.... Direct gida ya maida ta yace sauri yake ana jiransa daga haka yayi reverse ya bar layin, Haseenah ta ciro wayarta bayan ta shiga gate din gidan ta zaro ido ganin miss call din Badiyya har biyar, dialing din number me siyar da Gold tayi tace "Haba Hamisu tun daxu fa kai nake jira wllh" yace "Ehh Hajjaju gani a hanya ai" tace "Toh sae ka Karaso" Ta kira Badiyya tace "Dadina dake takura wllh, gashi nan yanzun nan na kirasa yana hanya, kinsan basa fitowa kasuwa da wuri ne yau, don Allah kiyi calm down ya a isowa zan kira ki" Badiyya tace "Gaskiya ni dai yayi sauri Haseenah, wllh akwai wanda zan ba 200k ne duk ya addabi rayuwata yana neman min tonon asiri" Haseenah tace "Nan da minti kadan yana isowa bayan ya auna zaki ji alert abinda kin turo min acc dinki kawai be patient Baddiee" A haka suka rabu Haseenah ta shiga cikin gidan tana sauri ta je ta nuna ma kawayenta classy and unique dinner dress din da zata saka, amma fa tayi mamaki da lokaci daya Maheer yayi payment din bai ce kudin yayi yawa ba don shi kam ba mai son fake life bane, a ranta tayi concluding yasan abinda yake jira eagerly ai dole ya biya kudin dress sharp sharp babu musu. Haseenah bata bari an fara mata lallin ba saboda Hamisu dake hanya, wajen karfe sha biyu ya kirata yace yana waje, ta dau jakarta ta lallaba ta fice daga gidan babu wanda ya lura da ita, tana zuwa inda tace ya tsaya ya jirata ta bude jaka tana kokarin fiddo gold taga wayam, da farko ta zata idonta ne ya nuna mata haka, ta kikkifta idon ta sake wangale jakar still taga wayammm, wani azababbun zufa ne suka hau keto mata tana gwale ido tace "Hamisu, duba min jakar nan ka ciro Gwal din a ciki ni na kasa cirowa" tana fadin haka ta manna masa jakar a hannu tana zare ido, Hamisu ya mayar mata jakar da sauri yace "Ke me jakar baki gani ba sai ni Hajiya" Zazzage komai na cikin jakar ta hau yi a kan titi a rikice amma babu gold bBu alamar Gold, da karfi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku da Badiyya" Hamisu yace "Gaskiya Hajiya kin bata min lokaci ne kawai, ai da kin fara dubawa kafin ki kirani.... Gashi customers can na ta jirana na bar su na yo nan wajen ga Unguwan nisa, kawai ni bari in tafi kasuwa yanda ake ciki sai ki kirani" Yana fadin haka ya buga machine dinsa ya kara gaba. Kiris ya rage Haseenah ta saki fitsari a titin, ko ina na jikinta rawa yake tsabar tashin hankali, ta dai samu ta ruga cikin gida ta shige visitors toilet dake cikin compound tayi fitsarin, tana fitowa ta tafi can backyard din gidansu ta zauna zufa wani na bin wani a goshinta, ita ba abun tayi raising alarm ba asirinta ya tonu Mummy ta gano abinda ke faruwa, dazu fa kafin ta fita da Maheer sai da ta duba jakar yana ciki kuma tunda suka dawo bata ajiye jakar nesa da ita ba balle tace a dakinta aka dauke, Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, ko dai wajen siyan kayan ne aka mata sata da taje gwadawa?? Sai a sannan ta fashe da matsanancin kuka ta daura hannu a ka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku na lalace me zan ce ma Badiiya"
Ammi ta kasa motsawa daga inda take zaune tana kallon abinda Maheer ya ajiye masu saman gado ita da Aunty Mariya, Aunty Mariya ta mike a gigice tace "Ina ka samo wannan Maheer?" Shi dai bai ce komai ba ya koma gefe daya ya rungume hannunsa yana bin su da ido, Ammi ta kallesa tace "Maheer wannan daga ina? Ko sabo ka siyo ne?" Yace "Babu wani sabo, tsohon da ku ka sani ne dai" Ammi ta buda ido with shock tace "Daga ina??" Maheer ya ɗan yi shiru yana tunanin abinda zai ce masu don bai son fara painting Haseenah black wajen Ammi, he just have to cover her up in other not to create doubt tsakaninta da iyayensa, Aunty Mariya ta hade rai tace "Dallah ka mana magana ka yi wani shiru, where did u find this?" Ya shafa kansa yace "Ita warce Ammi bata son laifinta ta kai ma Haseenah ajiya, shine Haseenan ta bani dazu da naje gidan, Badiyya ta kai ma Haseenah sarkan ta ajiye mata" Ammi ta dafe kanta cikin tashin hankali tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Aunty Mariya kam buda baki tayi hangangan tsabar mamaki, Maheer ya juya ya fita daga dakin, Ammi ta fara hawaye tana girgiza kai ta kasa cewa komai, Aunty Mariya ta mike ta dau Gold din ta adana shi inda babu wanda hankalinsa zae kai wajen a dakin Ammi ita ma ta fita daga dakin.
Mami ce zaune parlonta a sama tare da yan uwan mijinta maza su biyar, Kawu Mansur yace "Maryam da girmanki da hankalinki bai kamata kina biye Halima kuna maida maganganu haka ba, shi sa muka ja ki muka dawo nan sama dake ayi magana ta fahimta...." Mami dai wani direction din daban take kallo kawai zuciyarta na tafarfasa, Kawu Mansur yace "Tsakaninki da Allah Maryam me kika sani game da gidan nan da Abdallah yake neman aure?" Mami tace "Au ashe ma yan uwana ne kenan da har zan san wani abu game da gidan, ka ga fa Yaya Mansur yanda ku ka samu wannan labari sama ta ka to nima haka nan ya riskeni, yanda duk aka bi ku da Envelope nima haka aka kawo min nan, sannan ina ganin ai ba wani zai zauna ma Musharraf da yarinyar nan ba, ko ma menene tunda yace yaji ya gani yana so ina ga a bar yaron kawai, he is old enough to make decisions for himself, shi ma ai an basa takardan kafin ma a kai maku and he wasn't bothered about it...." Kawu Faisal na kallonta kasa kasa yace "Tunda auren wasan yara ne da har zai bude baki yace yaji ya gani ba? Mu kuma gamu a banza, To abinda ke da shi baku sani ba shine, bai isa ya yanke ma kansa decision kansa tsaye as far as mu iyayensa muna raye, don haka ba shi da wani say a wannan lamari sai abinda mu manya muka ce, in kuma bashi da manyan ne sai ki gaya mana yanzu mu ji...." Mami ta masa wani kallo kafin ta kai ga cewa komai Kawu Mansur yace "Yanzu dai duk ba wannan ba, wannan lamarin da ake ta cukuikuyawa abu ne me sauki wllh, mu fa muka kai kudin nan ba wasu suka kai mana ba, mafi sauki shine mu sake komawa gidan don a warware mana abinda ya shige mana duhu daga bakin iyayen yarinyar nan da suka amshi kudi hannunmu, ai ba sai an tsaya ana cece ku ce ba, ga best alternative kawai na kawo" Mami tace "Ohh da an san da haka za a zo nan a daga min hankali saboda an raina ni? To wallahi ku ja ma Halima da Rumaisa kunne idan basu fita harkata ba ina me tabbatar maku hukuma ce zasu min iyaka da su, nan ba da dadewa ba kuwa" mikewa Kawu Saleh yayi ya fita daga parlon sauran ma duk suka mike suka bi bayansa parlon ya rage Kawu Mansur kawai, Kawu Mansur yace "Yanzu dai kiyi hakuri Hajiya, duk abinda ake ciki za ki ji kira anjima, ko kuma in zo da kai na" Daga haka ya mike ya fita daga parlon.... Abbansu Maheer na Bedroom dinsu yana duba wasu takardu, dawowarsa kenan daga Abuja saboda daurin auren 'ya yan nasa da za ayi gobe, Ammi ta shigo dakin tace "Yallabai wai kayi baki fa" Abba ya kalleta yace "Daga ina?" Ammi tace "Maheer yace kamar dangin yaron nan ne Musharraf, yace su suka kawo kudi" Abba ya ajiye takardun hannunsa yace "Toh lafiya, Allah sa dai ba cewa za su yi a daga bikin ba" Ammi tace "In hakan shine mafi alkhairi ai babu yanda aka iya" Abba ya dau wayarsa ya fito daga dakin ya fito compound don a nan parlon baƙin yake, yana shiga parlon duk aka gaggaisa, Maheer ya shigo ya ajiye masu carton din ruwa da lemo, Abba yace "Ya shirye shiryenmu?" Duk suka amsa da "Alhamdulillah mun gode Allah" Abba yace "To Madallah" Kawu Mansur yace "Dama wata magana ce ke tafe da mu Alhaji, sai dai za mu so kayi mana uziri kuma ka fahimce mu, don ko kaine a shoes dinmu iyaka hakan kai ma zaka yi" Abba da yayi jim, can yace "Ikon Allah, to ina sauraronku Alhaji, Allah sa dai lafiya" Maheer dake kokarin fita daga parlon jin abinda Uncle din Musharraf yace sai ya kasa fita lkci daya jikinsa ya basa all is not alright, Alhaji Faisal ya ciro takardan aljihunsa ya mika ma Abba, Alhaji Mansur ma ya ciro ya mika masa, Alhaji Sale shima yayi haka Abba dae sae amsan takardun yake yana bin su da kallo cike da mamaki yace "Na menene wannan din?" Alhaji Mansur yace "Mu ma duk haka suka iso gidajenmu a yammacin jiya, ka duba ka gani Alhaji" Abba ya maida dubansa kan takardun baya ko kiftawa amma ya kasa duba ko daya ya karanta, Maheer ya karaso kusa da Abba zai amshi takardun Abba ya daga masa hannu, calmly yace "Zan duba" Yana fadin haka ya shiga duba content dinsu gaba daya, daya bayan daya yabi har ya gama karanta su, a hankali ya linke su duk ya ajiye gefensa yana kallon Uncles din Musharraf da suka zuba masa ido gaba dayansu, Abba ya ɗan kwantar da kansa jikin kujeran da yake zaune, trying all possible best to be calm yana kallonsu yace "Haka ne.... Duk abinda ke rubuce jikin takardun nan gaskiya ne amma banda abu daya zuwa biyu ..." Yana kai wa nan yayi shiru, Alhaji Faisal yace "To Alhamdulillah, sai dai fa Alhaji abu dayan nan zuwa biyu da kace is of no importance to us right now,