Showing 156001 words to 159000 words out of 249515 words
tace "Ke da kike wnn maganar kika san yanda muka reni Mayraan har zuwa yau Ladi? Ina ruwanki da Mayraah? To wallahi kar ki gaya min maganar banza kar ranki ya baci" Mama Ladi ta taɓe baki, ta ja bakinta tayi shiru bata sake ce ma Hajja komai ba tana girgiza kafa. Likitan ya zauna yana kallon Maheer yace "Ana bukatar za a mata karin jini, don tayi loosing blood sosai, but Alhamdulillah Allah ya takaita bai yi affecting inda muke tsoro ba at first da aka kawota, but the wound is so deep gaskiya daga gefen kanta ne sai kuma goshinta da shi ma taji ciwo, mun mata stitching anyi dressing din wound din, gefen fuskarta kawai gurjewa tayi , i think that's all, in sha Allahu muna sa ran zata farfado zuwa nan da yan awanni, yanzu kawai jinin za a kara mata, idan jininka da nata yayi dai dai to sai kaje lab yanzu for test a deba, in kuma bai yi ba za ka siya mata a blood bank din mu" Maheer yace "To in sha Allah Dr, Nagode sosai" Tare suka fita office din da likitan, kafin Maheer ya karasa lab din asibitin ya taho gun su Hajja yace "Za ku iya tafiya gida kawai, jikinta da sauki za a mata karin jini ne yanzu" Hajja tace "Inji babu wani mummunan abun da ya samu kan nata?" Maheer yace "Rauni ne kawai ta ji, amma likitan yace da sauki" Mama Ladi ta rike haɓa tace "Waiii, amma Allah ya hore mata jini, yanda fa kasan an yanka saniya Maheer" Maheer bai tanka ta ba ya tafi zuwa laboratory, Mama Ladi ta mike tace "Kin ga tun da ba mutuwa tayi ba Hajja ki tashi mu tafi gida don ni yunwa nake ji yanzu haka daurewa kawai nake amma tun dazu cikina ke kugi..." Hajja tace "Mu dai babban fatanmu yanzu ta samu lafiya sai a san abun yi" Mama Ladi ta gyara yafin gyalenta ta fita daga asibitin Hajja ta bi bayanta... Karfe sha biyu saura Maheer na zaune dakin da aka kwantar da Haseenah da aka nannade kanta da tulin Bandage bayan an aske kusan rabin gashinta, ledan jini ne a hannunta, shi dai kallonta kawai yake maganganun Badiyyah na yawo a kansa, har a lokacin bai kira kowa a cikin yan uwanta ya gaya masu abinda ke faruwa ba, ya dai kira Ammi ya sanar mata Haseenah na asibiti not long ago, A hankali Haseenah ta bude idonta, Maheer dai sai kallonta yake daga inda yake zaune, suna hada ido tana kokarin mikewa da kyar tace "Maheer wallahi duk sharri Badiyyah ta min babu abinda ta fada da yake gaskiya" Maheer ya mike ya dakatar da ita yace "Na sani, you don't need to stress ur self koma ki kwanta" cikin rawan murya tace "Kasan halinta ae ko, wallahi karya kawai take min dama ta saba sharri iri iri, dubi sharrin da ta dinga bin Mayraah da shi, wallahi karya take min Maheer" Maheer ya mayar da ita ta kwanta yace "Duk na sani, do not worry ur self, u need rest" Haseenah tayi shiru tana jin kanta kamar ana buga mata guduma, Maheer yace "Bari in kira likita" Daga haka ya fita daga ward din, yana fita bayan few minutes sai ga wata nurse ta shigo ta karasa har kusa da Haseenah tana mata sannu, cike da karfin hali Haseenah tace "Nurse ji nake kan kamar ba nawa ba, yayi min nauyi nurse, ko dai bandage din da aka sa min ne?" Nurse din tace "Kiyi hakuri, zai maki sauki in sha Allah, sai a hankali zaki ji ya dawo dai dai, ki daina yawan magana kin ji" Haseenah dai sai hawaye take, Nurse din tace "Bari in dauko alluran da za a maki yanzu, mai gidanki ya fita samar maki abinda za ki ci kafin a maki alluran" Haseenah na son gyada mata kai amma ba dama saboda ya mata nauyi kan, cike da karfin hali tace "Ki ɗan ara min wayarki zan yi kira nurse" Nurse din tace "To ba damuwa" A aljihun uniform dinta ta saka hannu ta ciro wayarta ta mika ma Haseenah sannan ta juya zata fita, Haseenah tace "Don Allah ya sunan asibitin nan?" Nurse din ta gaya mata, bayan ta fita Haseenah tayi dialing number kanwar mum dinta Aunty Fauziyya, yana fara ringing Aunty Fauziyya ta daga, Haseenah ta fashe da kuka da kyar tace "Aunty ina asibiti" Aunty Fauziyya tace "Asibiti kuma? Subhanallahi, me ya sameki Haseenah? Wani asibitin kuma?" Nan Haseenah ta koro mata duk abinda ya faru tana kuka da kyar sbda azaban ciwon kai, Aunty Fauziyya ta mike tsaye daga zaunen da take tace "Kan bala'i, ita Badiyyar ce ta fasa maki kai? Kuma matsiyaciyin mijin naki ya kasa bugowa ya sanar mana abinda ke faruwa, wato ta fasa ma banza kai kenan? Wani asibitin kike yanzu?" Haseenah na gaya mata asibitin Aunty Fauziyya ta katse wayar, Haseenah tayi dialing number Aunty Farida ita ma sis din Mum dinta ce amma ta ji tana on another call, Cousin sis dinta Salma ta kira ita ma tana dagawa ta gaya mata abinda ya faru da asibitin da take, bayan ta gama sanar ma Salma sai ga kiran Aunty Farida ya shigo, Haseenah ta daga da sauri cikin kuka zata fara mata bayani cikin daga murya Aunty Farida tace "Fauziyya ta kirani ai ta gaya min komai, ga mu nan zuwa asibitin yanzun nan za mu ga uban da ya tsaya ma Badiyyah har ta maki haka" Daga haka Aunty Farida ta katse wayar. Ammi ta fito daga bangarenta bayan Maheer ya kirata ya sanar mata abinda ya faru, har zata sauka downstairs ta tsaya for few seconds, Mama Ladi dama ta gaya mata a dakin Maheer Mayraah take yanzu, kawai ta buda kofar dakin taga babu kowa ciki, hakan yasa ta sauka ta fita zuwa asibitin da Maheer yace mata aka kwantar da Haseenah, Ammi na isa asibitin ta kira Maheer ya fito ya shigo da ita ward din da Haseenah take, ko da wasa bai yarda sun hada ido da Ammi ba, ita dai Ammi na tsaye kan Haseenah dake ta juye juye tana wayyo Allah don Anaesthesia ya fara sakinta, gaba daya Ammi ta ma rasa me zata ce jikinta duk yayi sanyi ganin ashe ciwon ba na wasa bane ganin yanda aka nannade kan Haseenah da bandage wanda har ya fara staining sosai da jini, Bude kofar ward din aka yi sai ga Aunty Farida da Fauziyya da Aunty Murja warce cousin dinsu ce, sai kawar Aunty Farida sun shigo babu ko sallama fuska a murtuke basu ko bi ta kan Ammi da Maheer ba suka nufu gun Haseenah kamar wasu sojoji, Aunty Farida na huci tace "Kan bala'i, ita Badiyyar ce ta maki wanna aika aikan? Ita Badiyyar? To wallahi wallahi sai mun yi shari'a da ita, sai naga uban da zai tsaya mata a kano" cikin bacin rai Aunty Fauziyya tace "Wato ba don ke kin kira mu ba so suka yi sai kin mutu su kira mu su sanar mana mu xo mu dauki gawarki ko? Saboda 'yar su ce shine suke neman rufe abun ko? to wallahi sai mun ga uban da ya tsaya mata a kaf garin kano, mu je Farida, wallahi ko guduwa tayi ta bar kano sai mun sa an daure uwarta tayi mana providing dinta, ai ba kowa ake taɓawa a kwana lafiya ba" Aunty Murja ta kankance ido tace "Wallahi kasheta kawai tayi niyyar yi ko ince suka yi niyyar yi, uban me ta masu haka? wani irin family Haseenah ta fada haka?? Duka duka yau wata nawa da auren aka mata haka?" Ammi ta kasa cewa komai ta saki baki tana kallonsu da mugun mamaki, Shi kansa Maheer na tsaye jikin window yana kallonsu bai ce komai ba, Haseenah kuwa sai kururuwa take tana juye juye saman gado tana cewa wayyo Allah zata mutu, Aunty Fauziyya da Aunty Farida suka fice daga ward din Murja da kawar Aunty Farida suka bi bayansu, dama mijin Aunty Fauziyya babban dan sanda ne amma yana Abuja kuma daga kanon aka maida shi Abujan, tana fita ta kirasa a waya tana huci tace "Abban Ikram wallahi mun zo asibitin abun ba na wasa bane, ya wuce yanda muke tunani Abban Ikram, yarinyar tayi raga raga da kanta da kyar raunin bai taɓa kwakwalwarta ba zancen da nake maka yanzu haka, kuma abun takaicin har zuwa yanzu da muka zo asibitin babu shegen da ya kira mu ba balle su gaya mana abinda ke faruwa wato so suke su rufe case din mu kuma an cuce er mu an illata ta, ka kira division din da kace kawai muje yanzu a hada mu da yan sanda a bamu mota ai nasan gidan su yarinyar, wallahi ko ta gudu sai mun tafi da uwarta ta fito da ita" Haka nan duk suka shiga motar Aunty Fauziyya suka nufi police station, motar yan sanda guda aka basu, Aunty Fauziyya tayi ma motar yan sandan jagora har gidan Hajja a tata motar.... Mama Ladi na tsakar gida tana alwala tayi maza tayi sallah ta tafi gidan Ammi, Hajja kuwa na kitchen tana ta kokarin hada girki ta koma asibiti ko don saboda Maheer, yan sanda kusan biyar suka shigo tsakar gidan Su Aunty Fauziyya da Aunty Farida na biye da su a baya, Tsabar gigicewa sai da Mama Ladi tayi zaman dirshan a kasa tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una" Aunty Farida na huci tace "Ina Badiyyar take?" Bakin Mama Ladi na rawa tace "Wallahi ni me aikin gidan ce, ga kakarta can a kitchen bazata rasa sanin inda take ba, ni ban san komai ba" Yan sanda suka nufi cikin gidan su Aunty Fauziyya na biye da su, Hajja ta saki murfin tukunyar hannunta bayan taga yan sanda tsaye kanta a kofar kitchen, tambayar da aka jefa ma Mama Ladi a waje shi aka kara jefa ma Hajja wato ina Badiyyah, Jikin Hajja na ɓari tace "Wallahi wallahi Badiyyah bata dawo gidan nan ba" Wani ɗan sanda yace "Amma ai kin san abinda ta aikata?" Hajja ta fashe da kuka tace "A gabana aka yi komai ranka shi dade, amma don girman Allah ku yi mata hakuri ku yafe mata wallahi marainiya ce yarinyar ba uwa ba uba, bata taɓa haka ba tunda take" Cikin daga murya Aunty Farida tace "Iyyeee wato marainiya, ita Haseenar uba gareta aka ce maki? To wallahi sai an dau mataki a kanta bata illata banza ba" Wani ɗan sanda na kallon Hajja yace "Kinga wannan kalman da kika yi Hajiya ya nuna cewar kin san inda yarinyar take ko kuma kina goyon bayan duk abinda take yi, don haka ki fito mu tafi station idan kika yi providing mana yarinyar sai a sake ki, kuma kina sake buda baki a nan za mu yi using din shi against you" Kuka sosai Hajja take jikinta na rawa tana cewa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una, nace maku bata dawo gidan nan ba ku shiga duk inda za ku shiga a gidan nan ku duba ta, wallahi bata dawo ba, ku rufa min asiri tunda nake ban taɓa zuwa Caji opis ba" A fusace Aunty Fauziyya ta kalli yan sanda tace "Don Allah mu tafi tana bata mana lokaci officer, ta fa san inda yarinyar take sarai da hadin bakinta yarinyar ta gudu tunda tace ai tana wajen abun ya faru, don haka in mun je station din sai ta fadi inda yarinyar take sai a saketa" Haka nan Hajja ta saka Hijabi tana kuka yan sandan suka tisa keyarta zuwa tsakar gida, Mama Ladi dai sai wanke kayan da ta ga an jiƙa a cikin baho take ita a dole mai aikin gidan har aka fito da Hajja aka yi kofar gida da ita tana rusa kuka tana salati, gaba daya yan anguwa aka fito ganin motar yan sanda a kofar gidan Hajja sai ga kuma Hajja an fito da ita tana kuka wiwi an saka a motar yan sanda an tafi da ita, makociyar Hajja Maman Bala ta dau waya jiki na rawa ta kira Ammi ta sanar mata ga yan sanda sun zo da katuwar mota an saka Hajja a ciki an tafi da ita..... Ba karamin gigicewa Ammi tayi ba bayan Maman Bala ta kirata, ta fita ward din da sauri don Maheer yaje office din likita yana kiransa, A hanya suka hadu, ganin yanda Ammi ta rude Maheer yace "Ammi lafiya?" Ammi ta fashe da kuka tace "Yanzu Maman Bala makociyar Hajja ta kirani wai yan sanda sun zo sun tafi da Hajja Maheer" Sake baki Maheer yayi yana kallon Ammi with shock, ya kasa cewa komai, Tuni Ammi ta nufi reception tana kuka sosai, Maheer ya bi ta da sauri yace "To ina za ki Ammi" Ammi tace "Police station din zan tafi mana Maheer, su yanzu don basu da mutunci da tsufan Hajja za su tafi da ita station?" Maheer ya kama hannunta yace "To ai bamu san wani station din bane Ammi, ki kwantar da hankalin ki mu fara sanin wani station ne tukun" Ammi ta kasa ci gaba da tsayuwa ta zauna kujeran dake reception din tana kuka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una, wannan wani irin fitina ne, wace irin yarinya ce Badiyyah? Meye wannan ta ja mana fisabilillahi?" Maheer that was so confuse ya ciro wayarsa yana tunanin wanda zai kira. Hajiya Amina na zaune parlor wajen karfe biyu Abba ya shigo da sallama, mikewa tayi bayan ta amsa tana kallonsa tace "Ka sameta a wayan Yallabai?" Abba yace "Ban sameta ba, wai tun yaushe ke kika lura bata gidan?" Hajiya Amina tace "Dazu wajen karfe goma na safe na shiga dakin ban ganta ciki ba duk tunanina ko tana bandaki ne, sai na koma na kwanta kawai, sai yanzu da aka yi azahar na tashi na sake komawa dakin inji ko ta ci abinci still ban ganta a ciki ba, shine na duba bathroom naga it's empty...." Da mamaki Abba yace "Kuma bata ce maki zata makaranta ba yau?" Hajiya Amina ta girgiza kai tace "Gaskiya bata ce ba Alhaji, kaga jiya da zata tafi makarantar ai ta gaya min, Kuma ina parlor da safe Mama ta fita balle ince tare suka tafi" Call logs Abba ya shiga na wayarsa ya ga ko zai iya gane number da Musharraf ya kirasa da shi jiya, yayi tracing calls dinsa har zuwa yesterday evening trying to recognize Musharraf's Number before calling, dai dai nan kiran Maheer ya shigo wayarsa, Abba da kamar bazai daga ba sai dai kuma ya daga, Hajiya Amina ta juya ta bar parlon ta koma sama, a takaice Abba ya amsa gaisuwan da Maheer ke masa, nan Maheer yayi kasa da murya ya sanar ma Abba duk abinda yake faruwa, Abba yayi shiru with surprise, can dai yace "Police station? To kai kana ina duk wannan abun ya faru? Sannan ina Badiyyar take har suka tafiya da Hajjar?" Maheer yace "Basu ganta bane ai Abba, shi yasa" Abba ya sauke wani ajiyar zuciya yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, yanzu wani station din aka tafi da ita Hajjan?" Maheer yace "Ban san division din ba, makota suka kira yanzu suke sanar mana" Abba yace "To bari dai ina zuwa...." Yana katse wayar yana kokarin kiran number wani abokinsa ɗan sanda sai ga Hajiya Amina ta sauko da wata farar takarda a hannunta da ta gani a dakin Mayraah tana kallon Abba babu ko kiftawa, Abba na kallon takardan yace "Na meye wannan?" Bata iya ta ce masa komai ba bata kuma fasa kallonsa ba, Abba ya karasa ya amshi takardan ya warware yana duba na menene....
[7/14, 6:16 PM] Khaleesat Haiydar💖: Karfe biyu da rabi Mayraah ta sauka daga mota rike da karamin jakarta tana bin park din da kallo, kowa hada hadar gabansa yake cikin hanzari don hadari ne sosai a garin, muryar dreba da taji yana tambayar ko bata da kaya ne a booth din mota ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta tafi a inda take tsaye, ta girgiza masa kai ta nufi hanyar da ta lura nan ake bi a fita daga cikin tashar, tsaye tayi bakin titi tana makale da jakarta a dai dai sanda aka fara iska sosai ta dinga bin duk motocin da ke wucewa da kallo, yan adaidaita sahu sai tambayarta inda za ta suke, kan kace me aka fara yayyafi, ta fara dube duben inda zata raɓa kar ruwan ya jikata, wani shagon point of Sale da kuma accessories din waya ta nufa da sauri ta tsaya a ɗan rumfan shagon nan aka fara ruwa kamar da bakin kwarya, saboda karfin ruwan sai ya kasance da ma rumfan da take karkashi gwara babu, don ruwan har ya fara jikata, me shagon na ganin haka yace "Ki shigo ciki Hajiya, ai wannan jikewa zaki a wajen" Mayraah ta juya da sauri ta shiga shagon tace "Nagode" Kan plastic chair ya nuna mata ta zauna, ruwa aka yi sosai don sai kusan hudu da rabi ruwan ya ɗan tsagaita, me shagon har bacci yayi ya tashi, ita dai Mayraah na takure kan kujeran don wani sanyi take ji sosai ga gajiya da jiri da take ji, gaba daya tayi weak wanda ko ba a fada mata ba tasan symptoms din low bp ne, Mai shagon yace "Hajiya ko dai a tare maki Napep tunda ruwan ya ɗan tsagaita ki tafi gida, naga kamar sanyi kike ji, kuma babu alamar daukewar ruwan nan yanzu" Mayraah ta juya ta kallesa kamar baza ta ce komai ba, sai kuma a hankali tace "Ni daliba ce yau na fara zuwa garin ban san ko ina ba, ban san kowa ba, ina son zan kama gida irin na dalibai ne, to ban san ta yaya zan fara ba" Mutumin yace "Jami'ar nan da take gwagwalada?" Mayraah ta gyada kai da sauri, mutumin na gyada kai yace "Chabb ae ko gida wahala yake a garin nan