Showing 105001 words to 108000 words out of 249515 words

Chapter 36 - Mayraah Hausa Novel Complete

20 Nov 2024

1573

saboda takaici, yanda kika san zai yi worshipping dinta a gidan nan haka yake yi, gashi tayi mugun raina ni bata ganina da mutunci, babu gaisuwa tsakanina da ita, sannan ko cup bata dagawa a gidan nan komai ni nake yi, kuma in nayi girki ya kwasa ya bata" Badiyyah tayi wani dariya tana tafe hannu tace "Wargi ma ai waje ya samu, da ace kin daidaici ranan da baya nan kin kama shegiya kin nakada mata shegen duka wallahi da kafafuwanta zata gudu ba sai wani yace ta tafi ba, ai ni na ma ga kokarinki da kike ta zaune da ita har yanzu under the same roof, kina fa koranta a gidan nan bata da inda zata je da ya wuce ta shiga duniya kuma, don har yanzu Hajja na kan bakanta wallahi, ko kiran Ammi sai nace ta daga take dagawa in ko na zugata nace kar ta daga to wllh baza ta daga ba, kin ga kuwa duk ranan da kika kori Mayraah bata da wajen zuwa a duniya" Haseenah ta marairaice tace "Wallahi dukan nayi niyyar mata yau naga ashe tare suka fita ina daki ina ta haukana, tun fa da ta zo bamu taɓa yini tare da ita a gidan nan ba, kullum sai taje makaranta, yau kuma naji tace bazata je ba daga baya kuma naga bata gidan kilan asibiti ya tafi da ita, kawai sun mayar da ni er iska a gidana, Babban tashin hankali na yanda kowa yasan da aure tsakaninsu yanzu, wallahi in na tuna hakan kasa bacci nake da daddare, har abinci sai in ji ya fita raina, kar wataran...." Kasa ci gaba tayi kawai sai ta fashe da matsanancin kuka, Badiyya ta rike haɓa tace "To bari ki ji har yau tana makale da lecturer din nan namu in gaya maki, Wllh jiya naje office dinsa na ganta ciki zaune yanda kika san office din ubanta, tana ganina kuma ta mike ta fita, ai ko sai da nayi minti ashirin a office din yana min bayanin course din da na kai masa nace ban gane ba, yanzu ran Monday zan sake duba wani topic in je in samesa a office again in ce ban gane ba a haka a haka har in shige masa, sai dai babban damuwata har yanzu bai taɓa tsayawa irin ya kalleni din nan ba, ko fuskata bai cika tsayawa ya kalla ba abinda ke gabansa kawai yake, sannan ganinta da nayi a office dinsa ya tsaya min a rai sosai kin ga kenan hakan na nufin basu rabu ba, to in basu rabu ba ta yaya har zai saurareni ni jama'a? Wllhi har da wannan yasa nace yau sai na san yanda nayi na zo na sameki tunda ke kadai ke bani mafita sai Zaliha, so nake ya rabu da ita kwata kwata ya ji ya tsaneta baya son ganinta, ta zama makiyiyarsa, ni kuma in shiga zuciyarsa farat daya" Haseenah tayi shiru tana kallon Badiyya, Zaliha tace "Tabdi, ai ko wannan dole sai an hada da Malamai, ta yaya zai ji ya tsaneta bata masa komai ba" Badiyyah ta juya tana kallon Zaliha tace "To ai malaman ne ni gani nake kudin mutum kawai suke ci wllhi" Haseenah ta sauke ajiyar zuciya tace "Nima dai haka nake gani, amma fa akwai wata kawata dake ta bani labarin wasu malamanta biyu ni dai nace Naira biyar dina bazai yi ciwon kai ba ba ruwana i am not interested, Malaman sun mata aiki akan wani mai shegen kudi a zaria da take so da aure, kuma aikin ya ci tun da yanzu haka maganar da nake maku ya saki matarsa, ita kuma kawar tawa saura sati biyu bikinsu har ta turo min IV... Kinga kuwa ai aiki ya ci" Badiyyah ta sauko kasa tace "Don Allah fa??" Haseenah tace "Wallahi kuwa in gaya maki, bayan nan still sun yi ma kawar kawar tawa aiki ita ma ta kori kishiyarta, yanzu daga ita sai yaranta a gidan, ga mota an mallaka mata" Badiyyah ta marairaice tace "Toh ko za ta hadani da su don Allah" Haseenah tace "Sai dai in kirata ta turo mana number, tunda ni dai nace mata i am not interested bata sake bin ta kaina ba, kinsan abinda mutum bai taɓa yi ba" Badiyyah tace "To don Allah ni dai kirata kawata, ni ban ki in kashe ko nawa bane in har zan mallaki Dr Musharraf" Haseenah ta mike tace "Bari in kirata don kinsan sirri ne, nima ta aminta da ni ne yasa ta gaya min, tana jin kawayena zan ba number sai ta iya hanani wllh don ba mutunci ne da ita ba" Badiyyah da har wani tsuma jikinta yake tace "Toh je daki ki kirata kawata" Haseenah ta shiga daki ta kulle kofa ta zauna gefen gado tana murmushi, shikenan yanzu za su wanye lafiya da Badiyyah ba wanda zai sake jin kansu, don number Malamin da ke mata aiki zata bata kawai, dayan Malamin kuma sai tace mata kawar ta hana numbersa saboda yafi iya aiki sai dai in ana son abu abi ta wajenta ita zata dinga gaya masa duk abinda yace kuma ta bada feedback, shkkn sai tayi using wannan opportunity din ta dinga ce ma Badiyya zata dinga bada kudin da haka da haka har ta ce mata kudin gold ya kare gun biyan malami.... Bayan wani lokaci Haseenah ta fito tace "Ohhh Mansura ko jaraba, da kyar ta bani number dayan Malamin in gaya maki, dayan kuma tace bazata bani ba don yafi iya aiki sannan ba ma wayar kowa yake dagawa ba sai manya manyan kasar nan, sai dai duk abinda nake so in gaya mata ita zata dinga masa magana sannan ta dinga feeding dina back, bata san ba ni bace kawata nake ma fafutuka" Badiyya tace "Wallahi na yarda, a ban number dayan, dayan kuma duk yanda tace ayi haka za ayi don ni yanzu mafita nake nema" A haka Haseenah ta ba Badiyyah number malaminta na Zaria, nan take kuma Badiyya ta shige dakin Haseenah ta kirasa tayi masa bayanin komai, sun kusa minti sha biyar suna waya sannan ta fito tana kallon Haseenah dake cin dankali da kwai ita da Zaliha, ta zauna gefen kujera a sanyaye tace "Haseenah yace in fara bada 150k for a start, ni kuma wllh ko dubu hamsin kudin account dina bai kai ba duk na biya bashi da kudadena" Haseenah tace "Tabb, a yanda fa Mansura tace min dubu dari uku yake fara cajin sa, ke ya ma maki da sauki kenan, shi kuma dayan malamin dama tace daga 500k zuwa sama yake fara cajinsa don aikinsa ba karya, ba irin malaman nan bane masu amsan dubu goma dubu ashirin su yi cefane a gida" Badiyyah ta hade rai tace "Gaskiya ki kara kiran me gold din nan ko dubu dari biyu ne ya fara turo min in biya ma kaina bukata, abu dai kusan sati biyu yau" Haseenah sai da taji dankalin ya makale mata a throat, can ta kalli Badiyya tace "Ai to baya kasan ne Badiyyah, yanzu abinda za mu yi zan baki aron dubu dari, sai ki ganganda ya zama 150k din ki tura masa" Badiyya ta washe baki tace "Yauwa kawata wallahi nagode sosai, shi yasa nake sonki bani da kamar ki, dama na ce masa nan da yamma zan tura masa" Haseenah tace "Zan maki transfer din kar ki ji komai" Badiyyah ta sauko kasa ta saka hannu tana cin dankalin ita ma tana jin ranta fari tassss, har ta fara hango kanta a gidan Musharraf a matsayin matarsa, tunanin hakan sent quivers all over her body, whatttt, murmushi kawai take ita kadai tana cin dankalin da kwai... Har bayan la'asar su Badiyya na gidan ba kuma su da niyyar tafiya, jikin Haseenah dai bai ga ta wanka ba yau, ta narko masu uban Indomie da kwai suka tashi da shi a parlon, plans iri iri ita da Zaliha ke kitsa ma Haseenah akan yanda zata yi maganin Mayraah a gidan har da bata shawaran ita ma ta ciro kudi ayi mata aiki kan Mayraah, Haseenah dake ta jin su tana masu kallon shashashai, ta girgiza kai tace "Aa gaskiya bani da kudin da zan ba Malami, bakina kadai ya isa ya sa Mayraah ta shiga duniya, dama can kuma ai a duniyar aka tsinceta" Su Badiyyah duk suka kwashe da dariya... Karfe biyar suka ji an bude gate din gidan, Zaliha ta zaro ido tace "Kaddai mai gidan ne ya dawo?" Badiyyah ta gyara zama tace "To sai me, ai ina ga daga yanzu sai dai yayi hakuri don kullum zai dinga ganina a gidan nan" Haseenah tace "Wallahi da kin kyauta kuwa, kyau ma ace kin kwaso kayanki kin dawo nan din da zama...." Badiyyah tace "Aa bazan kwaso kayana ba amma kullum kam zan zo, kuma bai isa ya hanani ba don wani bomb din zan kara hadawa wllh" Bayan few minutes aka bude kofar parlon Maheer ya shigo da sallama, bin parlon ya dinga yi da kallo don everywhere is so untidy, ga warmers din breakfast din safe ba a kwashe ba, ga tray din da suka ci Indomie har ya bushe, ga goran ruwa da lemo a yashe parlon, ga plate din su cin cin da alkaki, worst of all Parlon yayi wani dummm kamar babu ventilation don Ac a kashe yake, Zaliha na gyara mayafinta tace "Sannu da zuwa Dr" Yace "Yauwa sannu" Badiyyah ta dau cin cin daya tana ci tace "Ina wuni" Yace "Lafiya" Yana tsaye har Mayraah ta shigo Parlon rike da leda a hannunta, da ido duk ta bi su kafin tayi hanyar dakinta, Maheer ya kulle kofar shi ma ya wuce nasu dakin, Badiyyah ta kalli Haseenah tana zaro ido tace "Kan bala'i, kin ga kallon da tayi mana ta wuce kuwa?" Haseenah tayi murmushin takaici tace "To kullum haka take min a gidan nan Badiyyah" Badiyyah ta rike haɓa tana kallon Haseenah da mamaki, Zaliha tace "To kuwa komai ya kusa zuwa karshe in dai za ayi amfani da shawaranmu, ni dai yanzu ki tashi mu tafi Badiyyah yanzun nan zaki ji magariba" Badiyyah tace "Kawai kiyi tafiyarki, ni sai can da daddare, kilan ma zuwa za ayi a daukeni" Haseenah ta kalli Zaliha tace "Kema ki bari sai anjima mana" Zaliha tace "Wallahi kar in rasa abun hawa ne" Badiyyah tace "Kar ki ji komai in an zo daukata sai a fara ajiye ki" Zaliha tace "Nasan karfe nawa za a zo daukarki? Aa bari ku ga tafiyata yanzu" Sallama tayi masu ta dau jakarta Haseenah ta rakata bakin kofar parlor sannan ta dawo, Badiyyah tayi kasa da murya tace "Munafuka ce fa Zalihar nan, wllh ban so munyi wasu maganganu a gabanta ba, duk ita ce fa ta hada min plan din yanda zan zo in riske ki fa a gida, a gabana ta kiraki tace ga ta nan zuwa" Haseenah tace "Kaji shegiya, wallahi in dai kun yi magana da ita ko ta WhatsApp ki nuna mata ke kin ma hakura da ba Malami kudi yayi maki aiki zaki yi amfani da hikimarki kawai" Badiyyah tace "Ai ko haka zan yi, don ban yarda da ita ba, sai kinga yanda ta dinga zugani kan cewar kar in yarda in fito daga gidan nan yau sai da gold ko kudina" Haseenah tace "Kaji algunguma, to wllh bazan sake barin ta xo min gidana ba" Badiyyah tace "Da dai ya fi" Mikewa Haseenah tayi tace "Bari in je in ga sweetheart dina ko welcoming dinsa ban yi ba" Daga haka ta mike ta nufi dakinsu, Zaune ta tadda Maheer a dakin fuskarsa babu walwala, ta kulle kofa tana murmushi tace "Welcome back baby, ka dawo ka gan ni tare da baki" Maheer ya daga kai ya kalleta yace "Yanzu ke ko kunya baki ji ba yanda na tafi na bar ki haka na dawo na sameki a gidan nan Haseenah? Wannan wani irin kazanta ce? Are you not perceiving d odour coming out from ur body?" Haseenah ta hade rai ta dakatar da shi tace "Aa don't go there Maheer, kai yanzu banda tsabar sharri tun daga can ka jiyo odour dina? Kuma nace maka ban yi wanka bane yau?" Bai sake ce mata komai ba ya ci gaba da dannan wayarsa, ta juya ta fice daga dakin.... Ana kiran Magrib Maheer ya fito, ya bude kofar dakin Mayraah, karatu ya sameta tana yi, ya kulle kofar ya karasa parlor, har a sannan Badiyyah da Haseenah na zaune suna kus kus a parlon, kuma har lokacin basu kwashe kwanukan tsakar parlon ba, ya koma corridor ya bude kofar dakin Mayraah yayi instructing dinta ta kulle dakinta sannan yayi tafiyarsa masallaci, ko da ya dawo daga masallaci Badiyyah ce kadai zaune kan 2 sitter a parlor tana kallo, zuwa yanzu dai an kwashe kwanukan goran ruwa da lemo ne dai ba a kwashe ba, ta daga kai ta kallesa ta ci gaba da kallonta, zaunawa yayi kan 2 sitter din shi ma yace "Ya Hajja fa?" Sai da Badiyya ta kara kallonsa to be sure first, kafin ta ci gaba da kallonta tace "Tana lafiya" Yace "Kinyi resuming school din ko har yanzu kina nan kina gantalin ki?" Tace "Gantali kuma, ni ai kullum ina zuwa school" Yace "Ohk, kin dai ga final semester din ku ne you have to be very serious with ur studies, da alama yau ma yini ku ka yi a nan ko handout baki bude ba" Tace "Bayan ma bani da handout din duk ban san inda suke ba" Yace "A haka za ki yi exams din to?" Ta ɗan tabe baki bata ce komai ba, yace "To nawa ne handout din?" Kallonsa ta kara yi to be sure again, is this really Maheer?? can dai tace "Gaba daya fa kusan 15k ne, kasan handout dinmu akwai tsada" Yace "To tura min account dinki in sa maki kudin" Badiyyah ta kara kallonsa this time around with surprise on her face, Haseenah ce ta fito daga daki tayi wanka ta canza kaya sai baza kamshi take ta karaso parlon tana kallonsu ganin su zaune kujera daya suna kallon juna, Badiyyah tace "To ai ni bani da number ka" yace "Nima bani da taki" Yana fadin haka ya ciro wayarsa ya mika mata yana kallonta yace "Sa min numberki"




MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah


Ur evidence via 07087865788




*Wato idan kina neman turaruka masu musulmin kamshi, irin turaren nan da komin bacin rai dole ya narke yabi ruwa🫠 kiji kamar kinyi bargo da gajimare. Toh ki nemi Scentmania_by_sana 07065525409 kawai kice ta baki 'The Empress combo'. Irin turaren dake sa maigida ya nemi shiri cikin gaggawa. In kinason kiyi activating din inner gimbiyarki👸🏽instantly wannan combo din shi ya dace dake*
[6/30, 7:58 PM] Khaleesat Haiydar💖: Badiyyah ta amshi wayar da Maheer ke mika mata ta saka numberta sannan ta mika masa tana mamakin wai yau Maheer ne da amsan numberta, is this for real?? Haseenah ta dauke kai daga kallonsu ta karaso parlon ta zauna babu yabo babu fallasa tana kallon TV, Maheer ya juya ya kalli Haseenah yace "Babu Dinner a gidan kenan?" A takaice tace "Breakfast din da nayi maka ma ai baka ci ba..." Yace "Ohk" Daga haka ya mike ya bar masu parlon, Badiyya ta zaro ido ta mike da sauri ta koma kusa da Haseenah ta rike haɓa tace "Kawata ki ji wani sabon salo wai Maheer da amsan numberta, wai nan fa duk so suke Hajja ta fara kula Ammi kamar da, sulhu kawai su ke so da ni fa" Haseenah tace "Atoh nima abun ya daure min kai" Badiyyah ta kyalkyale da dariya tana tafe hannu tace "Ai in dai zuga ne yanzu na fara, in aka ga na daina to babu Mayraah a familyn gaba daya" Da sauri ta ciro wayarta dake ringing tace "Yauwa gashi nan ya zo kawata, bari in tashi in tafi... " Haseenah tace "To sai yaushe kenan?" Badiyyah tace "Gobe asabar zanje Bichi wajen kawuna in masa karya akwai practical da za mu yi na final exams in amso kudi wajensa da zan cika ma malamin nan, kilan in dawo a goben, in kuma ban dawo ba sai Sunday in sha Allah" Haseenah tace "Toh shikenan za mu yi waya, duk yanda kawata suka yi da shi second Malamin zan sanar maki" Badiyyah na murmushi tace "To kawata nagode sosai" Mikewa tayi, Haseenah ma ta tashi ta rakata har bakin gate sannan ta dawo gidan, dakin Maheer ta tafi ta ga baya ciki, dama tun da aka kawota a dakinsa ta tare, nata kuwa sai jefi jefi take shiga ko in tana bukatar wani abu ko in zata yi waya, bata gansa cikin dakin nasa ba, ta leka nata nan ma baya nan, ta fito da mamaki ta tsaya corridor tana kallon kofar dakin Mayraah, babu tantama yana ciki tunda bai fita daga gidan ba, karasawa tayi ta kasa kunne amma bata jin komai, fita tayi daga gidan gaba daya ta zaga ta bayan window din Mayraah nan ma ta kasa kunne, ba abinda take gani kuma bata jin komai saboda window a kulle yake sannan curtains din ba a bude suke ba, nan da nan taji zuciyarta na tafarfasa ta dawo cikin gida, kawai ta nufi kofar dakin ta bude, Mayraah na zaune kan darduma with her handouts, shi kuma yana duke gabanta explaining something to her from the handout, duk suka juya suna kallonta, kallon sama har kasa ta dinga masu kafin ta juya ta bar bakin kofar dakin without saying a word, Maheer ya karasa bayanin da yake ma Mayraah yace "Hope kin gane yanzu?" Ta gyada masa kai, mikewa yayi zai fita ta daga kai ta kallesa, a hankali tace "Yaya dama..." Juyowa yayi ya kalleta yace "Dama me?" Ta sunkuyar da kai, ya dawo ya duka gabanta yace "Talk to me Mimi, dama me?" Ta daga kai tace "Dr Musharraf will be coming" Shiru yayi yana kallonta hakan yasa ta sunkuyar da kanta,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login