Showing 186001 words to 189000 words out of 249515 words
gama bata abinci sannan ta mike ta fara hada alluran, bude kofar ward din aka yi Mayraah ta juya, sai kuma ta koma gefe tana kallonsu, MD din ne da Dr Khalil dake biye da shi a baya, Matar ta gaishesu MD din na kallonta yace "Hello Ma, is there any improvement?" Da turanci Matar tace har yanzu jikin yarinyar na zafi, sai zazzabin ya sauka sai ya sake dawowa, sannan yarinyar na zabura, MD ya kalli Mayraah dake tsaye gefe yace "Diagnostic procedure?" Haka kawai taji gabanta ya fadi ta dau file din yarinyar da ta shigo da shi ta fara budewa da sauri, lkci daya duk sai ta daburce, Dr Khalil ya amsa file din a hannunta yana dubawa ya sanar masa diagnosis din, Gyara tsayuwa yayi yace "Ita bazata iya dubawa ba sai kai" Dr Khalil yace "We have 19 more wards ahead Doctor" MD din yace "Therapeutic procedure?" Nan ma Dr khalil ya karanto masa within few seconds, MD din yace "Any medical History?" khalil ya sanar masa yana duban file din still, karasawa MD din yayi feeling the girls temperature ya duba ta da stethoscope din wuyansa, bayan few seconds ya kalli Mayraah a takaice yace "Give her the injections" Daukan alluran tayi ta nufi kusa da yarinyar zata yi mata amma sai abun yayi mata kamar bata taɓa yi ma kowa allura ba kamar ranan zata fara ga kuma kukan da yarinyar take ya gigitata, MD din ya kalli Dr Khalil a bit pissed off yace "Why is she so sluggish? Wannan ta san aikinta kuwa?" Dr Khalil zai amshi alluran ya dakatar da shi furiously yace "What for?" Mayraah ta masa wani kallon gefen ido bayan ta ɗan daure fuska, nan dai ta tsaida hankalinta waje daya tayi ma yarinyar alluran, ficewa yayi daga ward din Dr Khalil ya bi bayansa. Karfe biyar wata senior nurse ta sanar ma nurses dake reception da za su yi ma yan evening handing over cewar su jira akwai meeting, yan evening na zuwa to su yan morning za su shiga meeting din da director a meeting room dake cikin asibitin, the next day kuma kafin yan evening su tafi za su yi nasu meeting din. Mayraah ta fito daga wani ward Dr Khalil ya nufota yana kallonta yace "Kiyi tafiyarki gida kawai ba sai kin yi attending meeting din ba Ilham, beside he doesn't even have ur data for now sai na basa, after the meeting i will be coming back home too" Mayraah taji hankalinta ya kwanta don dama tun da Matron ta sanar masu da batun meeting ta rasa sukuni, ita in son samu ne ma bata son ko wani irin encounter ya hadata da wnn MD din har sanda zai koma, kawai taji kwata kwata bai mata ba she don't like him, he is rude and arrogant sannan ta ga alamar ya iya disgi, Ta langwabar da kai tana kallon Dr Khalil tace "Toh shikenan, sai ka dawo" Yace "Hope kina da cash dai?" Tace "Ehh ina da, thank you" Ko minti goma bata kara a asibitin ba ta dau jakarta ta tafi bayan taje tayi ma Nurse Hafsat sallama a injection room, tana fita nurses din reception suka fara kus kus a tsakaninsu ganin ta tafi bayan ance akwai all staff meeting, dama tun da aka lura da yanda wasu daga likitocin asibitin ke yaba mata shkkn aka fara mata hassada kiri kiri don wasu ko magana basa mata a asibitin ita kuwa ko sanin suna yi ma bata yi ba tunda ba wani surutu take ba ko hira, tsakaninta da su gaisuwa shi ma wasun su sai suyi kamar basu ji ba, asibitin da ko kwana goma bata yi cikakke da fara zuwa ba, hatta yanda Dr Khalil ke kiranta office da kuma yanda Dr Balogun ke interacting da ita ya tsaya ma da yawansu a wuya, wata nurse fa'iza tana kallon colleague dinta murya can kasa tace "Wato ita shafaffiya da mai bazata tsaya meeting din ba kin ga ta dau jakarta ta tafi, tabdi bata san MD bane, ta zata irinsu Dr Khalil da Dr Balogun ne ko Dr Hamid dake shining mata hakora, muna nan dake wallahi sai MD ya gane bata shiga meeting din ba, sai in dai basu hadu a asibitin ba wannan mayen, zan ga ko shi ma kwarkwasan zata dinga masa yanda take ma sauran likitocin, Allah Ubangiji ya sa ya disgata gaban kowa da kowa mu ga iskanci, ko su Dr Khalil din da Dr Balogun babu abinda za su iya yi in ba haka ba ya hada da su" Nurse Victoria tace "The thing tire me my sister, ke daga zuwanki sai wani feeling kanki kike kin zo kin samu mutane a waje ki dinga wani ciccin magani kina daga masu kai wai ke me kokari, who does that?" Nurse Bola dake jin su tace "Fatana kawai yana ganinta after all the meetings ya gane bata shiga ba, a nan zata ga ikon Allah" Suna hango Nurse Hafsat duk suka yi shiru. Mayraah na isa gida ta tadda Ummi zaune parlor tare da Zainab matar Khalil da kanwar Ummi warce ake ce ma Aunty Rabi'ah, tun zuwan ta gidan sai ranan taga Zainab ta zo, ta karaso ta zauna ta gaida Ummi da Aunty Rabi'ah sannan ta gaida Zainab din ma, kallo daya Zainab tayi mata ta kauda kai ta amsa, Mayraah ta mike ta shiga dakin da take, Sai da Ummi ta ji ta kulle kofa sannan ta kalli Zainab tace "Wannan wani irin amsawar walakanci ne Zainab?" Zainab tace "Walakanci kuma Ummi, ta gaisheni kuma ai na amsa" Aunty Rabi'ah tace "Wai Ummi har yanzu bata samu gidan bane, last week da na zo ce min kika yi gida take nema fa, wannan ko sabon gidan da aka gama ginawa take so ya ci ace ta samu yanzu dai" Ummi tace "Bata samu ba, kuma baza a samun ba ma" Aunty Rabi'ah ta kyabe baki tace "To Allah ya kyauta" Har bayan magrib Mayraah bata fito daga daki ba, cause impression din Zainab duk sai yayi weaken dinta gaba daya, Mimi ce ta shigo dakin tana kallon Mayraah tace "Aunty Ummi tace in kira ki" Mayraah tace "Toh" Mikewa tayi daga kan darduma ta fita zuwa parlor, Ummi kadai ce zaune parlon, Mayraah tace "Ga ni Ummi" Ummi tace "Naga baki debi abinci ba" Mayraah tace "Ina jiran ayi isha ne" Ummi tace "To ai lokacin ma ya gabato, Inna na tambayarki nace kin dawo kina hutawa ne a daki" Mayraah tayi murmushi dai dai nan aka yi sallama kofar parlon, Ummi ta daga kai tana kallonsa da mamaki tace "Aa... kai kuma daga ina haka? 5 weeks din kenan?" Juyawa Mayraah tayi gabanta ya fadi lokaci daya ta dauke kanta da sauri.
[7/22, 12:58 PM] Khaleesat Haiydar💖: Karasowa cikin parlon yayi yace "Ina wuni Ummi" Ummi tace "Lafiya lau, ko dai dama baka tafi ba?" Ya ɗan yi murmushi yace "Ban tafi ba kuma? Bayan har vid call mun yi 2 days back Ummi" Ummi tace "To na gan ka ne kamar an jefo ka ai" Sai a sannan ya ga Mayraah da kanta ke sunkuye kamar munafuka, lkci daya murmushin dake fuskarsa yayi fading, kallon Ummi yayi ya sake kallon Mayraah, kamar tasan kallon nata yake ta daga kai da sauri tace "Ina yini" Still looking at her yace "Lafiya lau" Ummi na kallonsa tace "Bakuwa ce" Yace "Oh ohk" Barin parlon yayi zuwa dakin sa, yana shiga ya ciro waya yayi dialing number Ahmad. Gaba daya Mayraah ta kasa cin abincin da ta debo a kitchen, duk ta rasa wani tunani zata yi, shi ma wannan mutumin gidansu ne nan kenan? She still vividly remember his face, Maida abincin gefe tayi ta jinginar da kanta da gado tsabar yanda ta zama confuse. Ana idar da isha mai aikin gidan ta zo tace mata Inna na kiran ta, ta mike ta saka hijab dinta ta fita, babu kowa parlor ta shiga dakin Inna da sallama murya can kasa, sosai gabanta ya fadi ganin Zainab, Dr Khalil da shi mutumin da ko sunansa bata sani ba su ma suna dakin inna, ta karasa ta zauna kasa tana kallon Inna tace "Inna ina yini?" Inna tace "Lafiya lau, naji shiru shiru baki shigo kin zubo min sabon ruwa a flask ba shine nace ko kema kin fara canza hali ne, ko kuma yan gidan sun fara canza maki ra'ayi" mikewa mutumin yayi ya fita daga dakin, Mayraah tayi murmushin karfin hali tana kallon Inna tace "Bari in kawo maki" Zainab dai sai danna wayarta take, Mayraah ta dau flask din ta fita daga dakin, Dr Khalil ya mike ya fita Zainab ta bi sa da kallon gefen ido. Mayraah na kitchen bayan ta kunna gas zata daura ruwan flask din aka bude kofa, ta juya da sauri ya shigo yana kallonta yace "U told me admission kika samu a Abuja? Aikin me kuma kike yi a asibiti yanzu?" Kallo daya tayi masa ta dauke kai ta ci gaba da abinda take tace "Admission din bai yiwu ba" yace "Why did u change ur name from the Mayraah u said at the hospital to Ilham?" Ta kallesa tace "Kaga kai ma ba dai dai ka fada sunan ba yanzu haka, so sbda irin wannan issues din yasa ake kirana Ilham most of the time" Yace "Really?" Tace "Yeah" Yace "Ohk, welcome to our home Ilham" yana fadin haka ya juya ya fita ta bi sa da kallo, wani boyayyen ajiyar zuciya ta sauke ta ci gaba da abinda take, ko da ta je kai ma Inna ruwan zafin ta tarar har Zainab da Dr Khalil sun tafi gida, ita ta ga kamar ma shakkar matar tasa yake wai ko magana bai mata ba saboda Zainab din na wajen, Inna na kallonta bayan ta ajiye flask din tace "Kin ga jikana Ahmad ya dawo daga kasar turawa ko, to shi ne babba a gidan kuma sa'annin juna ne da Halilu, shima kuma Halilun ɗan gida ne duk da ba jininmu bane shi amma ya zama ɗan gida, sai wannan mata da ta bari tayi kiba dazu da kika shigo tana zaune can tana latse latsan waya sunanta Zainab yanzu haka tana da yan biyu mata, saboda yabawa da kyawawan dabi'un Halilu, marigayi ubanta ya ba Halilun auren Zainab, kinsan ni na haifi uban nata, Allah dai ya ji kansa, Bayan Zainab sai yan biyu maza Hassan da Hussaini kullum sai su zagaya bayan windan nan su isheni da buga kwallo wai kar in huta, sai figgiyar yarinyar nan Fatima bata da aiki sai raye raye, duk Zuwaira ce ta haifesu, in ma kika ce ba ita ta haifi Halilu ba to ranta baci yake" Mayraah dai sai kirkiran murmushi take don ta kagu ta bar dakin, daga karshe ta samu ta sulale tace mata zata je tayi wanka.
Musharraf na kwance dakinsa da safe Mami ta shigo, yayi mata kallo daya ya kauda kai, mancewa ma yayi bai kulle kofar ba bayan ya dawo masallaci, ta karaso cikin dakin ta zauna gefen gado tana kallonsa tace "Musharraf" Ya kalleta bai dai ce komai ba, ta kai hannu forehead dinsa tayi kasa da murya tace "Yanzu baza ka cire ma kanka damuwar nan ba Musharraf kayi facing reality" Ya ki kallonta balle yace komai, ta sauke ajiyar zuciya tace "Ta shi mu je kayi breakfast" Mikewa zaune yayi ya matsa daga kusa da ita yace "Mami duk ke kika ja wannan abun, u caused everything, da kin bari mun yi aure tun wancan lokacin she wouldn't have gone missing now, yanzu wa yasan halin da take ciki a inda take" Mami tace "Musharraf ita 'ya mace komin rintsi ban ga dalilin da zata bar gidansu ba ko ince gidan da ta taso, bata da wani hujjan da zata ce ta bar gida, ni fa tunda yarinyar nan ta iya tsallaka kafa tayi tafiyarta har aka zo ana zargin ka akayi arresting dinka naji ta fita a raina bazan boye maka ba, who knows the life she's living now tunda ta gwammaci ta shiga duniya tayi rayuwarta..." Musharraf da yaji haushin furucin Mami har ransa yace "Mami kika san wani pressure yasa ta tafi? She is so young for all this that is happening to her, she can't think straight, so ake yarinyar ta kamu da depression, she is just 22 fa Mami" Mami tace "Ni dai in za ma ka cire ta a rai ka ci gaba da harkokin gaban ka is better u do so, don babu aure tsakanin ka da wannan yarinyar just put that in mind, in kuma har ka mance abinda guardian dinta suka mana a police station sai in ji, it's simple idan har zaman kasar ma baka so to ka tafi Canada ka samu Daddy...." Musharraf ya katse ta yace "Waye Daddy? Mami pls ki daina hadani da gayen nan, i have no business with him" Mami tace "Shi ɗan uwan naka zan daina hadaka da?" Musharraf ya sauka daga kan gadon yace "Ɗan uwana that is happy with what i am going through, he is happy with my downfall, ko sau daya bai taɓa kirana duk wannan abubuwan dake faruwa ba" Mami tace "To saboda me zai kiraka, kai kiransa kake Musharraf?" Bai sake sauraronta ba ya fice daga dakin. Maheer na zaune parlon Ammi yayi kasa da murya yace "Ammi yau za a sallami Haseenah daga asibiti, so Abba insisted in kawota gidan nan har ta karasa samun sauki" Hajja da ke zaune parlon hannunta rike da carbi ta dago da sauri tana kallonsa jin abinda yace, Aunty Mariya ma da ta zo jiya da mai gidanta da ya zo yi ma Hajja jaje ta kalli Maheer da mamaki, Hajja tace "Wani gidan? Wai ci gaba da zama da matsiyaciyar nan zaka yi kake nufi Maheer? Ko dai baka da kai ne? Ita Hasinar kake mararin dawowa da ita har zaka kawota gidan nan?" Ammi dai bata ce komai ba, Hajja ta kalleta ta hade rai tace "Ya kika yi shiru Ammi? Kema kin goyi bayan ta dawo ya zauna da er matsiyatan kenan tunda har kika yi shiru" Ammi ta kalli Hajja ta sauke ajiyar zuciya tace "Hajja ba daga ni bane, nima na so nuna ma Alhajin hakan amma yace lallai Maheer bazai rabu da ita ba saboda ɗan matsalar nan da aka samu, shi yasa kawai na hakura na ja bakina nayi shiru" Hajja na gyada kai tace "Eh lallai, dole kice ɗan matsala tunda ba ke aka kai Caji opis ba aka ci ma mutunci aka walakanta ba ko shi Mamudan, ae ni aka taɓa dama ba ku ba, karshen biyayyar da kike ma Mamuda naga sakayya ya maki da kishiya ai, ke uwar yan bin miji, wato baza ki iya nuna masa ke baki yarda ba an ci mutuncin uwarki shine kika yi shiru kika kyale hukuncin da ya yanke, to ba komai ai rayuwa ce" ita dai Ammi kanta na kasa, mikewa Hajja tayi tana kallon Aunty Mariya tace "Ni ai sai in bar gidan, dama banda lalura da damuwar da yayi min yawa ban san halin da yarinyar mutane ke ciki ba ga dangin ubanta sai zarya suke mana me zai zaunar da ni a gidan surki har zuwa yau, ai an san ba halina bane wannan, ki tashi mu je Mariya dama zuwanki kawai nake jira kuma jiyan baku iso da wuri ba" a hankali Ammi tace "Aa kiyi hakuri Hajja yanxu haka fa Alhajin suna hanya da Badiyyar mun yi waya da shi yace an gama komai in Allah ya yarda yau zata dawo gida an rufe case din" Ko rufe baki Ammi bata yi ba Badiyyah ta shigo parlon, Hajja ta saki salati ta fashe da kuka ta tafi da gudu ta rungumeta tana kiran sunanta, Ammi dai sai kallon Badiyyah take ganin yanda ta rame tayi bakikirin kamar ba ita ba, ita kanta Aunty Mariya sake baki tayi tana kallon Badiyyah, Hajja na kallonta daga sama har kasa cikin kuka tace "Sannu Badiyyah, sannu, Allah Ubangiji ya saka maki wannan abu da aka maki, Allah ya saka maki" Aunty Mariya tace "Allah ya saka mata fa kika ce Hajja? Yarinyar da ta dauke wayar mutane me tsada ne zaki dinga yi ma wannan addu'ar? Maganar da sai da na kai zuciyata nesa na iya sanar ma mai gidana saboda kunya, kuma ke nan har kullatata kika yi ban zo ba, sata fa Hajja? Gaskiya wannan ba karamin abun kunya Badiyyah ta ja mana ba ta ja ma kanta, me ta rasa da zata jefa kanta cikin wannan mummunan hali na satan kayan mutane?" A mugun fusace Hajja ta juyo zata yi magana sai ga Abba ya shigo da sallama, Hajja ta koma ta zauna tayi kasa da kai don dama da hijab dinta a jiki, Abba ya zauna ya gaida Hajja, Hajja ta amsa tana masa sannu da kokari, Aunty Mariya ta gaida Abba ya amsa, sannan yana kallon Badiyyah on a serious note yace "Ke bude kunnuwanki ki saurareni" Badiyya dake rakube jikin Hajja ta daga kai tana kallonsa yace "Kin ga sati dayan nan da kika yi hannun hukuma? To ya kamata ya zame maki darasi a rayuwarki, in har baki yi hankali ba a sati dayan nan to ko baza ki taɓa yi ba, da girmanki da hankalinki ban ga dalilin da zaki dau wayar mutane da sunan sata ba, me kika rasa da har kika ji sha'awar yin sata Badiyyah?" Hajja tayi kasa da murya tace "Mamuda kilan dai akasi aka samu, amma ni nasan halin Badiyyah wallahi sata ba halinta bane bata taɓa daukar min ko kwandala ba tun da ta taso" Tana fadin haka Badiyyah ta fashe da matsanancin kuka tace "Abba kawata ce fa ta bani ajiyar wayar ban san sato shi tayi ba" Abba ya daka mata tsawa yace "Wato bakin ki bazai mutu ba, da aka ce ki fadi inda kawar take kin fada a gaban