Showing 141001 words to 144000 words out of 249515 words
za mu share da kanmu, ko ni kadai na isa in share ai" Aunty Mariya da bata ji dadin abinda Mama Ladi ta ma Haseenah ba tace "To meye laifi don tace zata yi shara Mama Ladi?" Mama Ladi tace "Naga jaraba? Mariya taga sa'anninta a nan ne da zata shigo mana wai zata yi shara, ni fa bana son shisshigi wllhi, naga dai ke ba a kiraki ba, ba a kuma ce ki biyomu ba to menene wannan haka ....." Haseenah dai sai ɗan murmushin karfin hali take, Ammi tace "Kije kitchen ki dauko tsintsiyar Haseenah, suna nan kitchen" Juyawa Haseenah tayi zata fita suka kusa cin karo da Maheer, ko kallonsa bata yi ba ta bi ta gefensa da sauri ta wuce, shi kuma ya karasa ciki ya ajiye akwatin Mama Ladi ya juya ya bi bayanta, Mama Ladi na kallon Ammi tace "Wato ke me surka bari ki gwaleni a gabanta ko Ammi? To wallahi tunda nace bazata yi sharan nan ba bazata yi ba, ni kadai raina na isa in tsaftace parlon nam da daki" Mama Ladi ta mike ta kulle kofar ta dawo tayi kasa da murya tace "Toh bari kuji, naje waje yafi hudu a karaye da getso, an min maganganu iri iri ba dadin ji, kuma duk zan zayyanosu amma sae nayi kumallo, kai har suna wallahi an bani kuma za ku sha mamaki in kunji wa enda ke da sa hannu a cakudewar lamarin nan, sannan waje na karshe da naje bawan Allahn ce min yayi idan baki maida hankali kin dawo gidanki ba to wallahi zaki je ki tarar da abokiyar zama" Sosai gaban Ammi ya fadi tana kallon Mama Ladi, Ita kanta Aunty Mariya da taji wani mugun sanyi ya shigeta kallon Mama Ladi kawai take, Mama Ladi ta dafe gwiwa tana kallonsu tayi kasa da murya tace "Wallahi yau sati daya kenan da ya gaya min wannan maganar, to ina ta fafutukan hada kudin da zan bada a bani iccen da zan kawo maku da zai lalata duk wani mugun abu da bamu san kansa ba, kar fa ku ce wajen boka ko matsafa naje, aa wallahi ba ruwana da wannan harkar, irin malaman nan ne salihai masu tsoron Allah da basa shirka, kuma duk inda naje abu iri daya ake ce min, idan na ci na koshi duk zan Kasa komai a faranti, sannan batun Mayraah kuma....." Mikewa Ammi tayi alamar bata son wannan zancen ta dau handbag dinta ta ciro makullin dakinta zata bude, Aunty Mariya ta buda baki kamar yanda Mama Ladi ma ta buda baki suka bi ta da kallo har ta shiga daki, Mama Ladi ta kalli Aunty Mariya tace "Kin dai ga ko? To ba ruwana kuma, kin dai ga alamar uwar ta gama hure mata kunne kuma duk sun shiga sun zauna sun yi daɓas a ranta ko" Aunty Mariya ta sauke ajiyar zuciya ta mike ta bi bayan Ammi, Mama Ladi ta bude jakanta ta dinga fiddo kullin magunguna kashi kashi tayi kasa da murya tana cewa "Dama tun da aka kawo yarinyar nan lullube cikin mayafi ranan hankalina bai kwanta da ita ba, ilai ga maganganu sun fito iri iri a kanta ashe gagaruman yar bin boka ce, shi sa na mata koran kare yanzu, bari dai inyi kumallo a debo min garwashin wuta za a ga fitina a gidan nan yau..." Ba a dau lokaci ba Aunty Mariya ta fito daga dakin Ammi ganin taki sauraronta don ma kamar bata bakinta kawai take, fita tayi daga parlon zata je dauko abubuwan da za su gyara part din da shi, ta hadu da Haseenah dake haurowa sama da sauri, tana ganin Aunty Mariya ta fara matsar kwalla tace "Aunty daga na zo zan taimaka ayi gyare gyare da ni shine Maheer ya dage sai na tafi gida har yana min maganganu marasu dadi" Aunty Mariya tace "To ke ya zaki fito babu izinin mijinki? Dama bai sani ba ki ka taho? To gaskiya ki koma gida tunda umarnin da ya baki kenan...." Haseenah ta kasa cewa komai, sai tayi da ta sanin yi ma Aunty Mariya magana da ta sani kawai direct Ammi ta tafi ta samu, Aunty Mariya har ranta taji dadin da Maheer yace ta tafi don duk wani abu da zai faru a gidan nan yanzu sirrinsu ne bai kamata ace daga shigowar Haseenah ta fara sanin komai kan gidan ba ko ana yin komai a gabanta, it's too early yaushe ma aka aurota, gaskiya hukuncin Maheer yayi mata dai dai don dama tun shigowarsu parlon sai da taji wani iri ganin Haseenah a zaune da Badiyyah, shikenan komai za ayi sai anyi a gabanta basu da sirrin kansu, Aunty Mariya na kallonta tace "Kiyi hakuri ki juya kawai ki koma gida ki bi umarnin mijinki, kuma aikin ma ai ba wani aiki bane ni kadai zan iya komai" Dai dai nan Hajiya Amina ta fito daga ɓangaren Abba that is at the very far end of the corridor sai ma ka kara corner idan ka kai karshen corridor din kafin ka shiga ɓangarensa, tun da Aunty Mariya ta hangota ta fahimci wacece ita, sosai gabanta ya fadi, ta maida dubanta kan Haseenah dake kallon Hajiya Amina ita ma tace "Ki tafi kawai nace, sai anjima" Haseenah bata ce komai ba, Aunty Mariya da ta ɗan fusata tace "Magana nake maki Haseenah" A hankali Haseenah tace "To Aunty amma..." Aunty Mariya ta dakatar da ita don bata son Hajiya Amina ta samesu wajen tace "Baza ki tafin dai ba kenan" Haseenah ta juya ba don ta so ba don ita kanta tana son sanin wacce mata ce ke tahowa daga can bangaren Abba, Aunty Mariya ta kasa ci gaba da tsayuwa don ji take kamar ita ce Ammi tsabar wani daci da take ji a ranta da wani bakin ciki, kawai ta sauka downstairs tun kan Hajiya Amina ta karaso, ita kanta Hajiya Amina da farko da ta hango Aunty Mariya tayi niyyar juyawa amma sai taga kamar hakan bai kamata ba duk da ba wai tasan ko wacece bace a tsaye, kuma Abba bai sanar mata da zuwan kowa yau ba, A haka dai ta karaso tana dab da isowa wajen kuma taga Aunty Mariya ta sauka downstairs kawai, hakan yasa ta karasa dakin da Mayraah take tayi knocking kofar gently, Mayraah na kwance idonta biyu tun dazu take ta jin kamar footsteps kuma ba na mutum daya ba amma ta kasa tashi balle ta fito ta duba, haka kawai gabanta ke ta faduwa tun asuba, yanzu kuma tsoro ne ya lullubeta, ana bubbuga kofar sai da zuciyarta ya buga sosai, ta mike a hankali ta karasa ta bude with throbbing heart, Hajiya Amina ta gani tsaye bakin kofar, Mayraah ta sauke idonta ta gaisheta, Hajiya Amina ta amsa mata da murmushi tace "How was ur night?" Mayraah tace "Alhamdulillah" Hajiya Amina tace "Kin ga breakfast a kitchen kuwa? Na so tashin ki muyi girkin tare da sade sai kuma na tuna exams kika gama kina bukatar hutu yanzu" Ita dai Mayraah kallonta kawai take with a neutral expression babu kuma alamar zata bata amsa, Hajiya Amina ta sauke ajiyar zuciya ta kamo hannunta tace "Is it too early ki saki jiki da ni daughter? Naga kina dari dari tun jiya, I have 2 kids Mayraah, twins... kuma su kenan Allah ya ban kafin babansu ya rasu! kin ma girme su they are just 15 years, ki daukeni kamar mum dinki daughter...." Mayraah ta ki cewa komai tana jin wani zafi a ranta, she still can't believe wannan matar kishiyar Ammi ce, she don't think she will ever like her, kawai kallonta take bbu fara'a a fuskarta, Hajiya Amina ta jawota bossom dinta tace "Take me as ur mother Mayraah, u will gradually get use to me" lokaci daya Mayraah taji wani mugun faduwan gaba bayan ta hango Ammi da ta fito daga part dinta, kallonta kawai Mayraah take kamar yanda Ammi ke kallon Hajiya Amina duk da she is backing her, a hankali Ammi ke tahowa this time around tana kallon Mayraah da Hajiya Amina, Mayraah bata san sanda ta kulle idonta ba zuciyarta na wani irin bugawa, Hajiya Amina ta saketa ta dago kanta tana kallonta tana murmushi tace "Je kiyi breakfast daughter sai mu girka lunch tare kafin Abbanki ya tashi bacci...." Karaf a kunnen Ammi, Mayraah ta hadiye wani abu da kyar ji take kamar kafafuwanta sun kasa daukarta, Hajiya Amina ta juya zata bar wajen suka yi ido hudu da Ammi da tayi still a inda take bata fasa kallonsu ba, sosai gaban Ammi ya fadi tana kallon Hajiya Amina babu ko kiftawa, Hajiya Amina na kallonta amma kuma bata san ta ba, don ko a hoto Abba bai taɓa nuna mata hoton Ammi ba, ta dai tace "Sannu, barka da safiya" Ammi bata amsa ba sai kallonta take kamar ta ga alien, hakan yasa Hajiya Amina ta bi gefenta ta nufi part din Abba kawai, da sauri Ammi ta bi ta da kallo kamar idanuwanta za su fito. Mayraah wished all this was nothing but a dream, she felt so weak and sick at the same time, nan da nan taji kamar zazzabi na neman lullubeta, tsabar yanda abun ya bugeta ta kasa ce ma Ammi komai sai kallonta kawai take, Ammi ta sake waigowa ta kalli Mayraah, Mayraah couldn't say anything, kawai Ammi ta juya da sauri ta koma part dinta, Mayraah ta kulle kofar dakin ta sulale kasa ta hade kanta da gwiwa hawaye masu zafi na sauka idonta, Mama Ladi ta bi Ammi da kallo baki bude ganin yanda ta shigo parlon da sauri kamar an korota, Ammi bata ko kalleta ba ta shiga dakinta, kawai Mama Ladi taga Ammi na fitowa da duk akwatunan ta daga daki wa enda bata je gidan Hajja da su ba, Mama Ladi ta gwalo ido ta mike tace "Ke meye haka? Ko su ma wanke su za ayi sun yi ƙura ne?" Sai a sannan taga hawayen dake sauka idon Ammi, Ammi taki ce mata komai ta dinga shiga dakin tana fito da duk wani kayanta, Mama Ladi ta saki salati ta fita da sauri ta je kiran Aunty Mariya, tare suka dawo dakin Aunty Mariya tace "Ammi menene haka kuma?" Ammi na girgiza kai hawaye na sauka idonta kamar an bude pampo tace "Na gama zama da Mamuda, na gama zaman gidan nan, ya aiko min da takarda ta bayan na tafi kawai" Aunty Mariya tayi karfin halin zama kan kujera don tasan babu tantama Ammi taga Hajiya Amina kenan, cikin sanyin murya tace "Babu inda zaki je Ammi, nan din gidanki ne, babu wata warce zata hanaki zaman gidan nan, babu warce za ki tafi ki bar ma gidan nan ko ki bar gidan saboda ita..." Aunty Mariya ta kasa ci gaba hawaye ya fara sauka idonta tana taya Ammi jin zafi a ranta, Cikin kuka Ammi tace "Ni Mahmud zai yi ma haka akan yarinyar da na ci wahala kanta tun tana cikin dattin haihuwa, ni zai ma wannan walakancin akan Mayraah? Maheer ya cuce ni wllhi da ya bari na tako kafata na dawo gidan nan naga wannan abun bakin ciki da takaici, da nasan abinda zan dawo in tarar kenan bazan dawo ba Mariya har abada kuwa, nayi da na sanin abubuwa da yawa a rayuwata, nayi da na sani wallahi, alkhairi na aikata ya zamar min sharri daga karshe" Kuka Ammi take sosai tana girgiza kai, Tace "Maheer ya san ubansa ya kara aure shine zai je ya takurani in dawo gidan nan? In dawo in yi me kuma? Me zan dawo in masu? Wallahi ya cuceni" Mama Ladi ta saki salati tana tafe hannu jin abinda Ammi ke cewa tace "Mamudan ya kara aure?? A ina kika ji wannan magana haka? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, aure fa??" Ita dai Aunty Mariya hawaye kawai take ta rasa abinda ma zata ce, Ammi ta ci gaba da fiddo sauran kayanta tana kuka, Mama Ladi ta rike kai tace "Huhuhu, ashe Mamudan ɗan iska ne dama bamu sani ba?" Sai kuma ta fashe da kuka tace "Duk Hajja ce ta ja maki wannan jaraba, kina zaman zamanki lafiya gidan mijinki ta zuga ki kika koma ɗan kuturun gidanta ku ka takure waje daya numfashi da kyar, babu wani alawance din da mutum zai sake ya bararraje komai a takure kamar gidan mayu shi sa nake gudun gidan idan na zo kano na gwammace in sauka nan, yanzu ga irinta nan ta cuceki ta sa an dankara maki kishiya kina can kin saki baki, dama an gaya min wallahi, kuma da kika wani kwaso akwati er iskar da ya auro zaki bar ma gidan kike nufi?" Kwankwasa kofar dakin aka yi, Aunty Mariya ta juya tana kallon kofar, can tayi karfin halin mikewa ta karasa tace "Waye?" Hajiya Amina tace "Ni ce" Aunty Mariya ta ɗan hade rai tace "Ana zuwa" Maida kayan Ammi ta dinga yi daki da sauri, tuni dama Ammi ta shige daki, Mama Ladi ma ta mike tana taya Aunty Mariya tura akwatunan da sauri duk da bata san ko wacece ba, Aunty Mariya ta fito bayan sun kai duk kayan daki ta bude kofar, Hajiya Amina ta shigo da sallama.
MAYRAAH is 500 via 3276052019 FCMB Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
*Wato idan kina neman turaruka masu musulmin kamshi, irin turaren nan da komin bacin rai dole ya narke yabi ruwa🫠 kiji kamar kinyi bargo da gajimare. Toh ki nemi Scentmania_by_sana by sana 07065525409 kawai kice ta baki 'The Empress combo'. Irin turaren dake sa maigida ya nemi shiri cikin gaggawa. In kinason kiyi activating din inner gimbiyarki👸🏽instantly wannan combo din shi ya dace dake.*
[7/11, 8:55 PM] Khaleesat Haiydar💖: Hajiya Amina ta karasa cikin parlon ganin Mama Ladi sai bata zauna kan kujera ba ta zauna kasan carpet tana kallonta cikin ladabi tace "Ina kwana Mama" Mama Ladi dake ta kallonta daga sama har kasa ta kalli Aunty Mariya dake zaune kan kujera fuskarta babu yabo babu fallasa tana danna waya tace "Wacece wannan kuma kika bude ma kofa ta shigo mana Mariya?" Hajiya Amina ta ɗan yi murmushi tace "Sunana Amina Mama" Mama Ladi ta yamutsa fuska tace "Amina? Meye kuma Amina? Amina daga ina? Ko dai batan hanya kika yi? To ko dai korar Salibar aka yi aka canzo wata mai aikin Mariya?" Hajiya Amina ta kalli Aunty Mariya dake ta harkarta da waya tace "Ina kwanan mu" Sai a sannan Aunty Mariya ta dago kai a takaice tace "Lafiya lau" Mama Ladi tace "Kin san ta ne Mariya ta shigo mana kanta tsaye ko dai makota zata shiga tayi ɓatan kai? Ko Saliba aka canza" Aunty Mariya tayi pretending kamar an kirata a waya ta mike ta shige daki ta kulle kofar, dai dai nan aka Bude kofar parlon Usman ya shigo da sallama ya karaso ya zauna kan kujera yana kallon Hajiya Amina yace "Ina kwana" Hajiya Amina ta kallesa tace "Lafiya lau barrister" Daga haka ta kalli Mama Ladi dake ta kallonta daga sama har kasa kamar taga abun kyama ta mike tace "Mama bari in baku waje..." Daga haka ta nufi kofa ba tare da ta jira cewar Mama Ladi ba ta fita, Usman na kallon Mama Ladi da ta bi Hajiya Amina da kallo baki bude yace "Ina kwana Mama?" Mama Ladi ta dawo da kallonta kansa, sai kuma ta saki kuka ta rike kai tace "Yanzu Usman kai da nake ganin hankalinka ace har da kai a zuba ido ubanka ya dankara ma uwarka kishiya baka taka masa burki ba? Me zai yi da wata matar gashi da gandara gandaran samari a gida banda son rai da son zuciya irin nasa? Shekara kusan arba'in yana tare da uwarku bai mata kishiya ba sai yanzu kuma kuka yarda da hakan baku tada masa bori ba? Kuma don Allah a ina ya jajibo wannan mata haka sai uban mazaunai? Sannan saboda raini da duniyanci shegiyar sai ta biyo mu har nan daga shigowarmu ko minti daya ba mu yi ba? Ina ruwanmu da ita zata shigo nan idan ba munafurci ba? Ta ina Ammi zata fara kishi da wannan mata haka kamar karuwa, ko kai baka ga yanda take wani juye juye bane?" Usman dai ya mike zai fita Mama Ladi ta tashi da sauri tace mu je ka kira min uban naka, kace Mama Ladi daga karaye na sallama da shi. Duk yanda Aunty Mariya ta dinga kokarin kwantar ma da Ammi hankali tana bata baki Ammi bata saurareta ba don kamar dada tunzurata ma take, sai harhada komai na dakinta take waje daya tana kuka, daga karshe ma ce ma Aunty Mariyar tayi in ta sake mata wata magana zata mareta, hakan yasa Aunty Mariya ta ja gefe ta rasa kuma yanda zata yi ta tsaya duk jikinta a sanyaye, seriously Ammi ke hada sauran kayanta tana goge hawayen dake sauko mata. Mama Ladi na zaune parlon baki sai girgiza kafa take tana jiran taga ta inda Abba zai billo bayan ta aika Usman ya kira mata shi, bayan some minutes sai gashi ya iso chalet din ya shiga parlon da sallama ya zauna saman carpet ya gaisheta da ladabi, Mama Ladi ta fashe da kuka ta rike kai tace "Yanzu kai Mamuda shekaranku 40 da Ammi ba a taɓa jin kanku ba, ba a taɓa sulhunta ku balle a raba ku fada ba sai don wannan ɗan matsalar ya gitta tsakaninku sai ka mata sakayya da kishiya? kishiyar ma kamar daga Tafa ka aurota, Mamuda ka mance yanda Ammi ta zauna da kai kana matsiyacinka cin yau da kyar na gobe daban tsabar talauci, baka da ko kwandalan kanka alhalin masu kudi ne suka dinga sonta da aure taki amince masu ta makale maka kamar me bakin uwa? Ko dai ka mance yanda ta dinga kwana da yunwa ta yini da yunwa duk bamu sani ba tana ta rufa maka asiri a haka har ta haifa maka yaran nan cikin baƙar yunwa?