Showing 195001 words to 198000 words out of 249515 words
ya rufe hand luggage dinsa, can Maheer yace "When did u see the debit alert?" Ba tare da Usman ya kallesa ba yace "Not long ago" Maheer yace "To yanzu ina za ka?" Usman yace "I contacted my account officer ya sanar min a Abuja ta cire kudin" Da mugun mamaki Maheer yace "Abuja?" Usman dai bai ce masa komai ba, Maheer yace "Yanzu Abujan zaka tafi da daddaren nan?" Usman yace "Yeah" Maheer yace "But... Ta yaya za ka fara tracing nata a garin Abuja that is wide??" Usman yace "Watch and see, i have been waiting for this day dama" Maheer ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya, tun da Usman ya kirasa ya sanar masa Mayraah ta cire kudi a account dinsa yaji wani kwanciyar hankali ya zo masa don the silence is too much, shirun ne yasa duk hankalinsa ya tashi, but tunda har ta cire kudi ya nuna she is fine and doing well kilan kudin account dinta ya kare kenan, Maheer yace "But ya kamata ka fara zuwa gidan Hajja ka dubata har yanzu she is not saying anything, she is really shock" Usman ya kallesa yace "Wani abu ya faru ne da zan je dubata?" Buda baki Maheer yayi yana kallonsa don sarai yasan abinda ke faruwa duk commotion din nan da aka yi throughout yau yana sane amma yaki tofa nasa, Maheer ya mike ya dafa shoulder dinsa yace "Saboda Ammi zaka yi Usman, ni ma ba don Ammi ba i won't involve my self in this, yanzu haka can zan tafi, kayi hakuri mu je tare" Usman bai ce masa komai ba suka fita gidan a tare. Maheer ne ya fara shiga parlon Hajja da sallama Usman na biye da shi a baya, Hajja na kwance an sa mata drip sai bin kowa take da ido tana numfashi sama sama, Mama Ladi na gefenta sai fifita take mata ta tsuke baki, Ammi da idanuwanta yayi jajir ita ma tana zaune kasa har a sannan bata daina kukan da take ba, Aunty Mariya dai tayi tagumi, Abba ma na zaune parlon don ko minti biyar bai yi da shigowa ba su Maheer suka zo, Maheer ya karasa kusa da Hajja yana dubata, Mama Ladi ta fashe da kuka tace "Mashir ni dai da kawai a tafi asibiti a duba min er uwa da kyau, naga kamar karkacewa bakin nata yake kokarin yi, ita kenan gareni a rayuwar nan fa ka rufa min asiri mu tafi asibiti" Maheer yace "Ko mun je asibitin abin nan da nake shi za a mata, in sha Allah zata samu sauki" Shi dai Usman na tsaye bakin kofa, Abba ya sauke ajiyar zuciya yana kallon Ammi for the first time yace "Ina Badiyyar?" Mama Ladi tace "Er iskar na daki in gaya maka Mamuda, wa ma zai bi ta kanta muna kokarin ceton ran er uwata wallahi ko sanin halin da take ciki bamu yi ba yanzu haka, kawai yanzu tunda zaratan mazan nan sun shigo kamata yayi su risketa a dakin da duka ta fadi uban da yayi mata ciki duk mu ji, tun dazu nake ce ma Ammi da Mariya su shiga su tambayeta cikin waye sun ki hankalinsu na kan lafiyar uwarsu" Abba ya sunkuyar da kai yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Sai ga hawaye na sauka idon Hajja, Mama Ladi ta fashe da kuka tana goge mata hawayen da dankwali tace "Tun dazu a haka take, sai dai kawai mu ga hawaye na bin gefen idonta ni dai na shiga uku na lalace Badiyyah ta cucemu" Abba na kallon Maheer yace "Kira min ita" Maheer bai so wannan aiken na Abba ba, don shi kansa tun dazu bai sa Badiyyah a ido ba bai kuma tambayi isilinta ba ya ma zata ta gudu ta bar gidan, amma bai ma Abba musu ba ya mike ya tafi zuwa dakinta, bude kofar yayi ya shiga ya ganta kwance kasa kamar warce ta yi wata uku tana jinya da alama har yanzu ko ruwa bata samu ta kai baki ba, tana ganinsa ta rushe da kuka ta mike zaune da kyar tace "Yaya don girman Allah ka rufa min asiri ka bani magani in cire cikin nan" bata rufe baki ba ya sauke mata lafiyayyen mari yayi ball da ita yace "Ni kike ce ma in baki magani ki cire ciki?" Bude kofar yayi fuskarsa a murtuke yana nuna mata waje yace "Fita ki je ki gaya masu who is responsible kar in kakkarya ki" Jikinta na rawa ta fara rarrafe zuwa bakin kofar don ko tashi bazata iya ba, rakubewa tayi jikin pillar dake corridor din tana kallon mutanen parlon hawaye na sauka idonta, Abba da Mama Ladi sai Usman kawai ke kallonta, don Ammi kauda kai tayi haka ma Aunty Mariya da zuciyarta ke tafarfasa, Mama Ladi na nunata da yatsa tayi mitsi mitsi da ido tace "Allah ya isa tsakaninmu da ke Badiyyah, kaf zuri'a ba a taɓa dauko mana abun kunya ba sai a kanki, Allah ya isa bamu yafe ba, yanzu da wani ido za mu kalli yan ubanmu?" Sai kuma ta rushe da matsanancin kuka tace "Ba don mun zama daya da Mamudan ba shi kansa da wani ido za mu kallesa wannan abun kunya haka a pamily dinmu" Abba na kallon Badiyyah calmly yace "Who is responsible?" Ta kara makalewa jikin pillar tana zazzare ido kamar me nazarin abinda zata ce, Abba ya sake jefo mata tambayar still looking at her, ta daga kai a hankali ta kalli Maheer.
[7/24, 7:34 PM] Khaleesat Haiydar💖: Maheer ya wani hade rai ya daka mata tsawa yace "Baza ki bude baki kiyi magana ba kina bata ma mutane lokaci" Ta fashe da kuka a hankali tace "Wallahi Haseenah ce ta hada ni da shi ni ban san shi ba" Daga Ammi har Aunty Mariya basu san sanda suka juya da sauri suna kallon Badiyyah ba, Mama Ladi da ta gwalo ido tace "Wacece haka? Sunan fa matar Mashir naji ta kira ko dai kunnena ne jama'a? Sanisa dai da duka muka sani?" Cikin kuka Badiyyah tace "Wallahi ita ce ta hada mu, Malaminta ne shi yake mata aiki a Zaria" Salati Mama Ladi ta saki bayan ta ajiye maficin hannunta tana tafe hannu cikin kidimewa tace "Malaminta kuma?" Maheer kam kallon Badiyya kawai yake babu ko kiftawa kamar yanda Abba da Usman dake tsaye bakin kofa ma suke kallonta, Cikin rawan murya Badiyyah tace "Dama bayan an fasa auren Mayraah nace mata ina son Musharraf din ya dinga kulani, shine ta hadani da malamin wai ya iya aiki, shikenan mu ka fara waya da shi na fara tura masa dubu hamsin sai watarana yace in je Zaria zan amshi wasu turarruka da zan dinga amfani da shi, ni kuma sai nayi ma Hajja karya zan je Bichi sai na tafi Zaria wajensa" Tana kai wa nan ta kara rushewa da kuka, Mama Ladi dake ta zare ido tace "Sai aka yi yaya?" Cikin kuka sosai Badiyyah tace "Wallahi ni ban taɓa iskanci ba Haseenah ce ta hadamu da shi, kuma yace min shi ne ma yayi mata aiki har ta auri Ya Maheer, sannan ya bata asiri da ta kai dakin Ammi wai don Ammi taji ta tsani Mayraah, ita ma kuma ai tana zuwa wajensa a zaria sai da tayi aure ne ta daina zuwa wajen sa" Mikewa Mama Ladi tayi ta dafe gwiwa tana kallon Hajja da hawaye ke sauka ta gefen idonta tace "To Allah ya sa dai kunnuwanki basu samu matsala ba kina jin duk abinda marainiyar ki ke cewa, mu dai sai dai mu ce Allah ya isa lalata mana zuri'a da za ayi da shege, yau ga dai Badiyyah da cikin boka" Sai kuma ta fashe da matsanancin kuka ta rike kanta, Ammi ma kukan take sosai wani bakin ciki da takaici na taso mata a zuciya, ita dai Aunty Mariya shock ya sa ko motsi ta kasa yi a inda take zaune sai kallon Badiyyah take, shi kansa Abba kallon Badiyyah kawai yake ko kiftawa babu, can ya girgiza kai ya mike kawai ya fita daga parlon, Usman ya juya ya bi bayansa, Maheer ya kusa minti biyar tsaye parlon da tunani iri iri a ransa, can ya nufi kofa ya fita shi ma, Ammi ta mike ta bi bayansa da sauri har a sannan tana kukan takaici, tsayawa yayi har ta karaso inda yake cikin rawan murya tace "Yanzu Maheer ta yaya za ayi a cire cikin nan? Ya za mu yi yanzu ya fita Maheer?" Da mamaki Maheer ke kallonta yace "A cire fa kika ce Ammi?" Ta fashe da kuka tace "To me zance Maheer? da wani ido za mu kalli duniya? Wannan abun kunyar har ina Maheer? Badiyyah ta cuce mu, ta cuce mu wllh" Maheer ya girgiza kai yace "Ai in ma wani ya kawo shawaran a cire cikin ke me hanawa ne Ammi" Muryar Mama Ladi suka ji da karfi tana cewa "Ashe baki da kai Ammi? Ina maki kallon me ilimi ashe ba haka bane? Wani cikin za a cire? So kike Allah yayi fushi da kaf zuri'ar mu? Ga laifin zina sannan ga na zubar da ciki, to wallahi babu ruwana sai inyi ta kaina in fita daga zuri'ar nan in shiga duniya kamar yanda Mera tayi, babu zunubin shegiyar da zai shafeni ban ji ba ban gani ba, ai tunda taje ta yo cikin dole sai ta haifesa a ba Hajja ko kuma a baki ku yi raino don nasan Mariya bazata amsa ba, ni ma kuma ba ruwana wallahi, da ana canza ma tuwo suna wallahi a yau din nan da na canza pamily bakina alekum na koma wani pamilyn, yanzu zancen da nake maki wllh kunyan Mamuda nake ji tun dazu na kasa hada ido da shi" Ammi dai kuka take ta kasa cewa komai ta nemi dakali ta zauna, Maheer ya fita daga tsakar gidan kawai, a kofar gida ya tadda Abba tsaye alamar dai lamarin nan ya girgiza sa ba kadan ba, shi dai Usman na tsaye jikin gate din gidan har sannan bai ce komai ba, shi fa bai yi mamaki ba ko kadan yasan akwai ranan da za a zo wanna gaɓar in har Hajja ta ci gaba da biye Badiyyah to gashi nan kuwa an zo, Abba na kallon Maheer bayan ya fito yace "I won't decide for you Maheer, duk hukuncin da kaga ya kwanta maka a zuciya game da matarka zaka iya yankewa but... Ka tabbatar baza kayi hakan ba sai kana da kwakkwaran hujjoji da zaka gabatar ma danginta don Badiyyah ba abun yarda bace, a yau na gama sarewa da lamarinta sannan na zame hannu a duk wani abu da ya shafe ta babu ruwana, sannan zan gaya ma mahaifiyarku daga yau bana son Badiyyah ta sake takowa cikin gidana" Abba na kai wa nan ya shiga motarsa ya wuce. Mayraah na zaune kan darduma bayan ta idar da sallan asuba tana azkar dinta idonta a lumshe ta jingina da bango, wayarta ne ya fara ring ta bude ido tana kallon wayar cike da mamakin wanda ke kiranta by this time, Dr Khalil ta gani jikin screen din, ta sake duba agogo taga karfe shidda, picking call din tayi ta kai kunne hade da sallama, ya amsa yace "Good morning, how was ur night?" Tace "Alhamdulillah, ina kwana" yace "Lafiya lau, i just want to let u know ba sai kin shigo hospital yau ba MD na da meeting, but just make sure karfe tara na yi ki tafi gidan Ummi mu hadu a can" Mayraah ta ɗan yi shiru, yace "Are u there?" A hankali tace "Eh ina ji" Yace "Good! Zan kira in ji ko kin tafi anjima nima sai rana zan shiga asibitin" Tace "Toh" Katse wayar yayi ya juya yaga Zainab tsaye kansa tana masa wani kallo, bai ma san ta fito parlorn ba, a fusace tace "To kar ta kuskura ta sake kai kafarta gidan mahaifiyata don wallahi zan mata rashin mutuncin da bazata taba mancewa a rayuwarta ba, ka nemi wani wajen da zaka kai ta amma in har tayi mistake din zuwa gidanmu yau din nan to zata ga ikon Allah, halan ita arniya ce da bata da iyaye har zata shigo garin Abuja namiji ya dinga accommodating dinta, kuma ko bata da iyaye ai bazata rasa yan uwa ba ko yawon bariki ta shigo yi a Abujan ne dama" Dr Khalil dai kallonta kawai yake ya ma rasa me zai ce mata, tace "Naga rainin hankalin ya kai rainin hankali yanzu, wato har kiranta kake da asuba ka gaya mata kar ta ma je asibiti saboda baza ka je ba, duk kwanan nan dama ina ta lura da take taken ka, ga wani gidan Ummi da ka tsiri zuwa kullum tunda ka kai ta can, an mayar da ni wata shashasha to my patient is finished, kuma ka sani babu yarda tsakanina da kai yanzu" Ya mike tsaye yace "Listen Zainab...." Ko sauraronsa bata tsaya tayi ba ta wuce daki kamar zata tashi sama, ya sauke ajiyar zuciya bai ma san yanda zai mata bayani ta fahimci babu komai tsakaninsa da Mayraah ba sae Kasancewarta er uwar sa musulma da baxai so ganin ta fada halaka ba, gani yayi ta fito daga daki da akwati kamar dama ta hada akwatin ta ajiye gefe abinda take jira kenan, da mamaki yace "Ina zaki Zainab?" Ko tsayawa bata yi ba ta bude kofa ta fice daga parlon, ya kalli dakin da twins dinsu ke ciki suna bacci, komawa yayi ya zauna don yasan ko ya bi ta tunda har taki tsayawa a nan ta sauraresa to a wajen ma bazata sauraresa ba sai ma dai kawai su tona ma kansu asiri, he definitely knows ba gidan Ummi zata ba gidan Aunty Rabi'ah zata dama ita ke zugata always. Tara da yan mintuna Mayraah ta fito daga gida bayan Dr Khalil ya sake kiranta yace kawai ta taho asibiti ba sai taje gidan Ummi ba kuma, wajen karfe sha daya ta shigo asibitin ta gaisa da nurses din da ta gani reception ta tafi sama zuwa office dinsa, hijab ne jikinta bata saka uniform ba, zaune ta samesa office din da twins dinsa sun cika sa da surutu shi kuma yana ta aikin gabansa, tun da ta hadu da su a supermarket ranan bata sake ganinsu ba sai yau don bata taɓa ganinsu gidan Ummi ba, ko kilan an kai su bata nan bata sani ba, ta karasa tana murmushi tana kallon kyawawan yaran tace "Su ma sun zo aiki yau ne Dr?" Shi dai kawai yayi murmushi yana ci gaba da abinda yake yace "Ya hanya?" Tace "Alhamdulillah" tace "Ya sunansu?" Yace "Fatima and Khadija, ana kiransu Ashnaah and Ashfah" Tace "They are so cute" yace "Dama zan fita, ke nake jira so u can stay with them here" Mayraah tace "Ohk, Maminsu fa?" Yace "Bata jin dadi ne" Mayraah tace "Toh Allah ya sauwake" Yace "Ameen" Yana kallon girls din yace "Za ku zauna tare da Aunty zan je in dawo yanzu kun ji? Ga cartoon zan kunna maku sai ku yi kallo, do not disturb Aunty" Ashnaah da Ashfah suka kalli Mayraah a tare, dukawa tayi tana masu murmushi ta kamo hannunsu tace "Hello cuties, yanzu Daddy zai dawo, i will keep u company" Dr Khalil ya dau makullin motarsa bayan ya sa masu cartoon a tv dake office din ya kalli Mayraah yace "Ga cornflakes dinsu da abinci a jaka if they need" Mayraah tace "Ohk" fita yayi daga office din zai tafi gidan Aunty Rabi'ah don ya kira Zainab ya fi a kirga bata daga kiran, Da ya kira Ummi kuma normally suka gaisa nan ya gane ba can taje ba kamar yanda ya zarga kawai sae bai ce ma Ummi komai ba, Mayraah bata san yaran are sharp haka ba, don cikata suka yi da surutu ta rasa wanda ma zata amsa cikinsu, bayan tafiyarsa da kusan minti talatin Ashnaah tace "Aunty i want cornflakes" Mayraah tace "Ohk" Ashfah tace "Me too" Murmushi Mayraah tayi ta tafi inda ya nuna mata jakar ta durkusa tana dubo cornflakes din a ciki, bude office din aka yi ta juya da sauri, sosai gabanta ya fadi ganinsa amma lokaci daya ta dauke kai ta ci gaba da abinda take, tana ji ya shigo office din yaran suka je da gudu suka rungumesa ya duka ya ba ko wannensu peck yana kallonsu yana murmushi yace "Where is papa?" Ashnaah tace "He is gone" Yace "And he left u 2 all alone?" Ashfah ta nuna masa Mayraah da ta mike tsaye, ya juya suna hada ido ya wani sha kunu kamar ba shi ke murmushi ba ya mike tsaye ya jefa files din hannunsa kan table din Dr Khalil, tayi gathering courage zata gaishesa taga har ya fice daga office din daga ita har yaran suka bi sa da kallo, tabe baki tayi ta zagayo ta mika ma yaran bowl din cornflakes da ta hada masu. Sai kusan azahar Dr Khalil ya dawo, duk yaran sun yi bacci ta kwantar da su kan kujera, yana shigowa ya ajiye car key dinsa ya sauke ajiyar zuciya yana kallonta yayi kasa da murya yace "Me yasa baki gaida MD ba da ya shigo office din nan dazu, Why pls Mayraah?" Hade rai tayi tace "Ni gaskiya Dr bazan iya aiki a asibitin nan as far as wannan mutumin yana nan, ya tsaneni, how will i greet someone that just disappeared daga gani na, he is just too rude for my liking, sannan ya fiye nagging" Dr Khalil yace "Let me tell u something, in fa kina karkashin mutum dole za kiyi hakuri a rayuwar nan, mu ma nan duk hakurin mu ke, MD is nyc but he have anger issues sannan baya son wasa baya son raini, he is a man of principle, mun yi degree tare da shi ne shi yasa har muka ɗan saba yake daga min kafa a abubuwa