Showing 78001 words to 81000 words out of 249515 words
she doesn't mean it har ranta...." Kasa ci gaba Aunty Mariya tayi hawaye na sauka idonta tana tausayin yayar tata, Ammi dai ta rike kanta hawaye na zarya a idonta tana jin zuciyarta na mata zafi, har sannan maganganun Hajja ne ke kai kawo a kunnenta, Aunty Mariya ta koma gefenta cike da karfin hali ta rungumota tace "Don Allah kiyi hakuri ki kwantar da hankalin ki Ammi...." Sai a sannan Ammi ta fashe da kuka sosai... Mayraah ta fi minti bakwai tsaye jikin kofar dakinta ta kasa motsawa daga wajen, her eyes were soo dry, lkci daya taji kirjinta yayi mata nauyi sosai kamar an daura mata ƙaton dutse, ta kasa ci gaba da tsayuwa ta lallaba ta koma gefen gado da kyar ta zauna hoping zata samu relieve din kirjinta da ya riƙe, bata ji ya mata saukin azaban da yake mata ba, daga karshe ta lallaba ta daure ta tashi ta tafi gun da Hijab dinta yake ta dauka ta sa, ta ciro Nikab dinta ma ta saka sannan ta dau handbag dinta ta nufi kofa, a hankali ta bude kofar don taji ana ta knocking din dakin Usman, leka corridor din tayi taga Mama Ladi tsaye sai bubbuga kofar Usman take ba kakkautawa, rufe kofarta tayi making sure it made no sound, ta jingina jiki tana jin kamar she is beginning to find it hard to breathe normal, bayan wani lokaci taji Mama Ladi a fusace tana cewa "Kai ya za a dinga buga kofarka ka ki tashi kamar me baccin mutuwa, wannan wani irin baccin asara ne Usman, ina ma ka ga ta bacci gida ya kacame ba lafiya ta ko ina" Mayraah taji Usman yace "Me ya faru?" Mama Ladi ta shige dakin tana cewa "Ba maganar tsayuwa bace ai" ya bi ta ciki sannan ya kulle kofarsa, Mayraah na jin haka ta bude dakinta a hankali ta fito, da sauri ta sauka downstairs ta fita compound, cikin few minutes sai ga ta a bakin titin gidansu, adaidaita sahu ta tare ta shiga bayan ta sanar masa inda zai kai ta... Duk da tafiyar da Mayraah tayi zuwa department din nasu ba wani me nisa bane, amma da kyar ta karaso saboda numfashinta da take ji yake sarke mata, she was so tired, bata karasa har bakin department din ba don ma kar wani ya ganta ya ganeta ta nemi karkashin wani bishiya me dauke da gossip chair ta zauna tana maida numfashi, she sitted there for 3 good hours, amma babu alamar shigowar ko daya daga 3 cars da yake zuwa makarantar da su, ganin it's almost pass 12 tayi karfin halin mikewa, zuwa yanzu ita kadai tasan me take ji a duk jikinta da kirjinta, ga wani jiri dake dawainiya da ita, tafi minti sha biyar tsaye bakin titin makarantar tana tunanin inda zata je, daga karshe ta tsayar da adaidaita sahu ta shiga ta sanar masa inda zai kai ta.....
Bayan tafiyar kusan minti talatin mai adaidaita sahun ya tsaya dai dai inda Mayraah tace masa ta sauka sannan ta basa kudinsa, a hankali take tafiya zuwa gate din gidan, she leaned against the gate for almost 5 minutes kafin tayi knocking, gajiya tayi da kwankwasa gate din don babu alamar za a bude, bata ma san ko da mutum a gidan ba at first, she is soo tired and sick everywhere, kawai daurewa take ga rana me zafi, tana ta tsaye nan don ko inda zata zauna babu, don ma dai tun zuwanta bata ga kowa ba a street din and that made her more comfortable to keep standing by the gate, masallacin dake next street taji ana kiran sallahn azahar, ta jingina da gate din gidan ta rufe ido, ji tayi ana unlocking gate din after almost 15 minutes, ta gyara tsayuwarta ta koma baya da sauri gabanta na faduwa don bata ma san wanda zata gani ba, aka bude gate din at last, kallonta yake kamar yanda take kallonsa ta cikin Nikab din fuskarta, he looks so surprise and perplexed seeing her, ya bi street din da kallo da mamaki yace "Mayraah!" Ita dai bata ce masa komai ba ta sauke idanuwanta daga kallonsa, da sauri ya kamo hannunta zuwa cikin gidan ya kulle gate din ya dage Nikab din fuskarta yana kallonta, ganin yanayinta and how she is beginning to heave yace "Are you okay??" Girgiza masa kai kawai tayi, bai sake cewa komai ba yana rike da hannunta ya nufi cikin gidan da ita da sauri, ko karasawa entrance din parlor basu yi ba Mayraah ta fara ganin gidan na juya mata bata sake sanin inda kanta yake ba daga nan kuma.
Maheer ne tsaye yana kallon Aunty Mariya sounding so pissed off yace "Aunty I think babu ruwan kowa da duk wani harka da ya shafi gidana ko matata, idan ma sakin Haseenah nayi it's my decision and i am old enough to make decisions for myself babu ruwan wani, ai ba wani ya bani shawaran aurenta ba so babu wanda zai bani shawaran yanda zan zauna da ita banda mahaifiyata ko mahaifina, ina ruwan Hajja da abinda ya shafi gidana har zata daura ma Mayraah? I don't think wannan ne kaɗai dalilin da yasa ta zo gidan nan tayi abinda tayi, there is definitely more to that, Kuma in har tace Ammi bazata kara rike Mayraah ba mu za mu riketa don kanwar mu ce har yau har gobe and this is our fathers house, beside ko gidana Mayraah zata zauna nobody is going to question that, dalilina kuma na maida Haseenah gida still remains between i and her, wannan tsakanina da ita ne babu wanda ya shafa, kuma babu ruwan Mayraah a mayar da Haseenah gida da nayi" Usman dai na tsaye ya rungume hannu fuskar nan tasa a murtuke tsabar bacin rai ko magana yaki yi, Aunty Mariya dai sai goge hawayen da yaki tsaya mata take, gaba daya ta ma rasa abinda zata ce, tun dazu Ammi dai ta kama hanyar zuwa gidan Hajja and this is 12pm bata dawo ba, wa ya sani ko zuwa zata yi ta ce mata ta amince babu ita babu Mayraah din kamar yanda Hajja ta bukata, Mama Ladi na tafe hannu tace "Kai in fa za ku fito fili ku buda ma ubanku abinda ke faruwa ku fito, babu wani zancen nuku nukun da za a mashi wannan karan, Hajja ce ta zo har nan da sassafe ko tashi daga bacci bamu yi ba tace zata ɗaga ma Ammi mama idan bata sallama Mera ba ta shiga duniya, fitar Hajja ke da wuya aka nemi Mera ko sama ko kasa aka rasa alamar yarinyar ta ji duk abinda Hajja ta fada a gidan nan, iyakar maganar fa kenan, duk da nasan Mera dole ta dawo duk inda ta tafi tunda babu dangin uwa balle na uba a duk inda za ta, yarinta ce kawai yasa ta bar gidan nan amma nasan tana hango magariba zata dawo shi yasa hankalina bai wani tashi ba, wancan lokacin da ta gudu ai tana ganin babu sarki sai Allah sai gata ta dawo da asuban fari, wa ya sani ma ko a titi ta kwana ranan, to yanzun ma muna zaune za ku ga ta dawo wujiga wujiga wanda ke da dangi ma ya ya kare idan ya shiga duniya balle ita da aka tsinta bakin masallaci a tsumma, sannan a buda ma Mamuda cewa Badiyya ce ta ruguza auren Mera, in ma Shari'a zai yi da ita bismillah dama ya haifi lauyan da zai tsaya masa ai, ita kuma Ammi karshen biyayya idan ta dawo muga tana watsi da kayan Mera titi taga ita ma irin koran da Mamuda zai mata, ai Mamuda ke da iko da gidansa ba ita ko uwarta ba, ko shi da 'ya yansa kadai sun isa su rike Mera, sannan nima nan ban ki in riketa in samu lada ba, sai in koma karaye in tattaro sauran kayana in dawo kawai, Mariya kuma ku bar ganin tana matsar kwalla a nan muna barin parlon nan ita ma zata saɓa gyale ta bi bayan er uwarta zuwa gidan uwarsu duk kukan munafurci take yi a nan, a yanzu gatan Mera Mamuda sai ni da ku kawai" Ficewa Usman yayi daga parlon ya tafi na baƙi don Abba na can, zaune ya tadda Abba shi kadai a parlon, tun bayan fitar Ammi daga parlon zuwa gidan Hajja bai motsa daga inda yake zaune ba don Ammi bata boyesa masa duk abinda ke faruwa ba, bai taɓa tunanin abubuwa will turn out this way at the end ba, da sun san haka abubuwan za su kasance da har ita Mayraah din baza su boye mata wacece ita a garesu ba baza su boye mata ba su suka haifeta ba, iyaka su sakaya suce iyayenta hatsari suka yi suka mutu suka tsinceta ita kadai a motar, and sun yi bakin kokarinsu basu gano relatives dinta ba, da hakan suka yi tun farko da abubuwa sun tafi smoothly, all this while Abba avoiding din Mayraah yake don bai san da idon da ma zai kalleta ba, gani yake daga shi har Ammi failed her, they disappointed her don ta taso da mentality din su suka haifeta amma all of a sudden rana daya taji ba su ne iyayenta ba, she is going through all this because of them hakan na damun Abba sosai, yanzu ko nan gaba aka samu wanda zai aureta tabon nan na rashin asali bazai taɓa goguwa a tare da ita ba, kawai he is just acting like everything is okay but deep down him he feels so sorry for Mayraah and he regret their actions, ya ma ga kokarinta duk da yasanta to be a very strong gal tun tasowarta, to yanzu ga kuma wani matsalan da Hajja ta billo da shi, Ammi kuma duk duniya babu maganar wanda take ji bayan shi da yake mijinta sai Mahaifiyarta, and her mum first in everything.... quite alright ba don Hajja ba da gidan Marayu zai mika Mayraah shi da yan anguwan a ranan da aka tsinceta duk da yanda Ammi ta nace masa a lokacin ya bar mata ita amma yaƙi har sai da Hajja ta saka baki... Bayan wani lokaci Abba ya daga kai yana kallon Usman da ya shigo parlon, Usman ya nemi waje ya zauna, Abba dai bai ce masa komai ba, after few seconds Usman yayi karfin halin cewa "Yanzu a ina za mu samo Mayraah?" Abba ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya calmly yace "Zata dawo, she will come back in sha Allah, babu inda zata je" Usman ya mike yace "But It's over 3 hours da fitar ta gidan nan fa, who knows the condition she is now??" Abba ya jinginar da kansa da kujera kamar bazai ce komai ba, can yace "Sit Usman" Usman ya koma ya zauna, Abba yace "Ga wata alfarma da nake nema gun ka Usman" Usman ya daga kai yana kallonsa, Abba ya nisa, cikin calm voice yace "Usman ina son hada aure tsakaninka da kanwarka Mayraah, i know u will protect her as ur sister, ur wife and as the orphan dat she is"
MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
Ki sauke hakki kiyi karatu hankalinki kwance.....
[6/22, 11:56 PM] Khaleesat Haiydar💖: Mikewa Usman yayi da sauri yana kallon Abba cike da mamaki, tsabar yanda maganar Abba ya zo masa a ba zata kasa cewa komai yayi, can dai yayi gathering courage yace "In auri Mayraah fa kace Abba? Did you mean it? How? Mayraah da muka taso nake ma kallon kanwata Muharramata how zan aureta as wife? This sounds more like an abomination to my ears, it's weird, ta yaya zan auri kanwata da nake ma kallon uwarmu daya ubanmu daya kawai don abun nan ya faru? No pls tell me ta yaya Abba?" Komawa yayi ya zauna ya ciro handkerchief yana share zufan da ya keto masa a forehead, he looks so confuse, yana girgiza kai yace "No Abba, this isn't going to work, Mayraah kanwata ce har yau, har gobe, har abada, bayan wannan babu wani kallo da zan sake mata, kanwata ce ita ta jini...." Abba ya sauke ajiyar zuciya yace "It's okay Usman, i understand you, but we all neva bargained for this, kawai abinda yasa na kawo shawaran nan naga abinda muke boyewa for many years an tonosa ta hanyar da bamu taba zato ba bamu yi tsammani ba, sannan duk wanda zai zo neman auren Mayraah ina da tabbacin tun daga waje za a tsegunta masa asalin wacece ita, my wish yanzu a rayuwa bai wuce ace Mayraah ta wuce gori ba, i want her to live like every other person, kuma nasan ku da na haifa kadai ne baza ku goranta mata asali ba, baza kuma ku kyamace ta ba, za ku riketa ne da amana ko da raina ko babu raina" Abba ya girgiza kai yace "I don't think there is any means da za ace za'a fara neman iyayenta or anything of such a yanzu because it's of no use, ko daga yanda aka yi dumping dinta a wajen nan a ranan ya nuna ba a bukatarta ne kawai, ba a kuma ajiyeta a wajen da niyyar ta rayu har wani ya dauketa ba, a'a an ajiyeta ne kawai ta mutu, ba kuma a jikin masallaci kamar yanda ku ka ji ana cewa aka ajiyeta ba, i don't know who created that rumors, kawai nasan that faithful day na fito kamar yanda na saba zan zuba ruwa a randunan masallaci kafin jama'a su fara fitowa sallahn asubahi, daga inda ake debo ruwan a wani rijiya ne, sai dai babu wani tazara tsakanin inda rijiyar yake da masallacin, a nan gaba da rijiyan aka nannadeta cikin zani har fuskantar sannan aka saka ta cikin kwali kuma aka rufe kwalin da plank ta yanda iskan kirki ma bazai shiga ba, kaga wanda ake son ya rayu ai baza ayi masa haka ba, kuma me imani bazai taɓa yi ma ɗan da ya haifa haka ba, kai koma ba ɗan da ya haifa ba bazai bari ayi ma wani haka ba, tabbacin koma wacece ta ajiyeta bata da imani, bata tsoron Allah sannan azzaluma ce don da niyyar kasheta tayi hakan, ina jan ruwa a rijiyar nan ina jin kamar kukan jariri amma na rasa a ina gashi kukan babu sauti sosai can kasa kasa ake jin kukan, kawai na bayar ko mage ce ke wannan kukan, har sai da nayi sahu uku da ruwan na kasa hakuri na fara duba wajen da torchlight ina neman inda wannan sautin kukan ke fitowa, in takaice maka nafi minti 10 ina dube duben area din daga karshe na lura da kwalin da aka ajiye nesa da rijiyar kusa da wani kwata na karasa na daga plank din, sai ga sautin kukanta sosai, i was shocked don dai anyi wrapping har fuskarta da zani, na kasa taɓa ta gashi babu kowa, duk ana ciki yawanci ba a tashi bacci ba don karfe hudu da rabi ma bai karasa ba a lokacin, tsabar yanda na zama confuse kawai na koma gida gun Amminku, ita ma tana bacci na tasheta nan na sanar mata abinda na gani bakin rijiya, babu bata lokaci ta sako hijab ta biyoni muka dawo wajen, har sannan kuma jaririyar bata daina kuka ba, Ammi bata yi wani tunani ba kawai ta cirota daga kwalin cikin tashin hankali ta warware zanin da aka yi wrapping dinta da shi, a lokacin sai Amminku ta fashe da kuka tana salati, don yanayin da jaririyar ya nuna ba a ma jima da haihuwarta ba tunda ko goge jikinta ba ayi ba, Ammi bata bi ta kaina ba tayi cikin gida da jaririyar nan a hannunta, Ni dai tsabar yanda mamaki da takaici ya isheni jikina yayi sanyi na koma bakin masallaci na zauna ina tunanin wacce azzalumar ce zata aikata wannan abun comfortably babu tsoron Allah a ranta, sannan duniya na kwance lkcn duk bamu san a haifi jariri a yasar shi ba, wannan yasa abun ya tsaya min, ya kuma tsaya ma mutane da yawa a rai, don kafin gari ya waye labari ya karade unguwa har ma da makota an tsinci jaririya a bakin masallaci kamar yanda ake cewa, da Ammi ta gyara yarinyar ta mata wanka sai da nayi kwalla, ita dama tun da ta dauko yarinyar take kuka, fara ce kal jaririyar, she was a cute baby kamar balarabiya, nan dai aka kai ta gun manyan anguwa aka fara shawaran yanda za ayi da ita, kowa dae na tsoron yace zai riketa don ba a san dalilin yasar da ita a walakance ba a bakin kwata, wasu suka bada shawaran a kai ta gidan marayu, a sannan ma gidan Marayun bai yi yawa ba kamar yanzu ina jin ma babu a garin sai anje wani gari, aka dai yarda akaita can gidan Marayun a harhada kudin mota, duk fa ba wai mun san yanda process din yake bane a lokacin sannan bamu sako yan sanda a ciki ba, nan na shigo gida na sanar ma Amminku shawaran da aka yanke akan jaririyar nan, Ammi ta sakar min kuka ta fara hadani da Allah ita dai a bar mata yarinyar zata rike, tunda a sannan Umar was almost 5 years kuma shi kadai ne a gabanmu, after much pleading and begging, har ta hadani da Hajja, Hajja ma ta saka baki a maganar babu yanda na iya ba don raina ya so ba manyan anguwa suka damka ma Ammi jaririyar nan, a ranan kuma tace min ita dai ta saka mata suna MAYRAAH, as at then we were leaving from hand to mouth, nayi ta kokarin nuna ma Ammi baza mu iya da dawainiyar jaririyan ba muma muna fama da kanmu a garin, gashi Ammi ta jima da yaye Umar babu ruwan Maman da zata ba yarinyar which means dole madara za a dinga siya mata kenan, a hakan ma yan anguwa sun harhada