Showing 120001 words to 123000 words out of 249515 words
is soo heartbroken and sad, gashi gaba daya ta kasa kuka ko zata ji sauki a ranta, tun kukan da tayi da safe bata sake ko digon hawaye ba har zuwa yanzu, ji take kamar hawayen nata sun ƙafe ne, babu irin tunanin da bai zo zuciyarta ba bayan sun ajiyeta dazu, da ta tashi zata yi abinda zuciyarta ke raya mata sae ta tuna da furucin Mamin Musharraf ta koma ta zauna a dakin, did she really want her 5 years to go in vain, idan ma ta bar shi ya tafi in vain din zata iya farawa daga farko kuwa? Ƙwaƙwalwarta zai iya daukan karatun nan gaba ma kuwa? All this thought ke sa wa ta kawar da abinda ke running a mind dinta, amma minti goma yayi kadan tunanin zai sake ringing a head dinta, ita kadae ce dakin don roommate din nata ta shiga school wai zata yi karatu, a haka kiran Usman ya shigo wayarta ta fita ta samesa, sae kuma Maheer da ya zo yanxu, ita kanta bata san she is this strong ba sai yau, firgit ta dawo daga tunanin da ta tafi bayan Maheer ya dafa ta cause magana yake mata amma bata san yana yi ba, ta juya da sauri ta kallesa, da damuwa yace "Mimi tunani kuma? I tot u promise me not to, i just caught u now" Tayi resting kanta a shoulder dinsa cikin sanyin murya tace "Yaya tunanin exams nake, i don't know where to start reading from, all the courses are bulky...." Maheer bai taɓa zama uncomfortable with Mimi leaning on him ba sae yau, ya kasa ce mata komai sae gyada mata kai kawai yayi, for almost 5 minutes babu wanda yace komai cikinsu, ita dae kanta na shoulder dinsa, can dai yayi karfin halin cewa "Erm naga kamar ba wuta hostel din ko? let me go and get u rechargeable flashlight yanzu in dawo" Ta daga kai ta kallesa tace "Yaya Usman ya kawo min with fan" Maheer yace "Good, yanzu za ki shiga ciki ki fara karatun ne? i will be calling u every now and then to know how far you've gone" A hankali tace "Ohk" yace "Good gal, go inside and start reading" Mikewa tayi tana rike da ledan da ya kawo mata tana kallonsa tace "Nagode yaya" Murmushi kawai ya sakar mata bai iya cewa komai ba, ta juya ta shiga ciki, sai a sannan ya sauke ajiyar zuciya, for some minutes ya kasa tashi a wajen daga karshe ya mike ya nufi motarsa, his intention was to be with her har zuwa 10 bai yi niyyar tafiya da wuri ba. Yana isa gida wajen karfe tara da wani abu bayan yayi parking ya shiga ciki, Haseenah na zaune parlon sanye da kayan bacci ga fruits da ta aika Musa ya siyo mata ta yanyanka ma Maheer ta rufe tana jiran dawowar sa, yana shiga parlon tun da ya lura ita ce a parlon bai ko kalli inda take ba yayi hanyar corridor ya bude dakin da Badiyyah take, Haseenah ta mike ta bi bayansa, tsaye tayi corridor din ganin dakin da ya shiga, Badiyyah na zaune ta kusa tashi da kazar da ya siya mata tana siɗe hannu yace "Baki bukatar komai?" Tace "Ba a kawo min ruwa ba" Juyawa yayi ya fita, ya wuce Haseenah dake tsaye ya tafi kitchen, Haseenah ta karasa dakin Badiyya tana kallon ciki, Badiyyah na lashe hannunta tace "Ke naga kamar yaya bai siya maki kazar ba ko?" Haseenah ta dinga jin zuciyarta na wani tafarfasa taki ce ma Badiyyah komai sai kallonta take, Badiyyah tace "Ga yanka daya nan ki shigo ki dauka" Sai ga Maheer ya bi gefen Haseenah ya shiga dakin ya karasa kusa da Badiyyah ya duka ya bude bottle water din ya zuba mata a cup ya dauka ya mika mata yana kallonta yace "Hannun ya maki sauki yanzu?" Ta wani marairaice tace "Har yanzu yana min ciwo wllh" Juyawa Haseenah tayi ta bar bakin kofar ta koma parlor ta zauna tana jin zuciyarta na tafarfasa..... Mayraah na zaune kan darduma da handout a gabanta tayi tagumi, tun tafiyar Maheer ta dauko handout din amma ko layi biyu ta kasa assimilating gashi yanzu har kusan karfe sha daya, gaba daya taji kanta ya tushe ga wani ciwo da yake mata, wayarta dake gefenta ya fara vibrate ta kalli screen din ganin Dr Musharraf ke kiranta tayi silencing kiran, yana katsewa ya sake kira nan ma ta kara silencing kiran daga karshe ta sa wayar a flight mode, ta tattara handout din ta ajiye gefe tayi kwanciyarta kan darduman, kuka take son yi amma ta nemesa ta rasa gaba daya, a haka roommate dinta ta dawo daga cikin school ta sameta kwance, Mayraah ta kulle ido kamar bacci take, bayan roommate din nata ta gama shirin kwanciya ta fara tashinta a hankali tace "Sis ki tashi ki hau kan gado" Mayraah ta bude ido tace "Ina son tashi inyi karatu ne anjima kadan ne" Ummi tace "Ki gaya min sanda kike son tashi zan sa alarm in tashe ki, kin ga kasa akwai sanyin tiles" Mayraah tayi shiru, can ta mike zaune a hankali tace "Toh Nagode" Komawa saman gadon tayi tana kallon Ummi ta nuna mata ledojin kajin da su Maheer suka kawo mata tace "Ki dauki daya naki ne, yayana ya kawo mana" Ummi tayi murmushi tace "Toh Nagode sosai, Allah ya saka da alkhairi, karfe nawa zan sa maki alarm din" Mayraah tace "Sha biyu da rabi" Ummi tace "To in sha Allah zan tashe ki lokacin" Mayraah tace "Nagode" sannan ta kwanta ta lumshe ido amma har karfe sha biyu idonta a bushe yake babu alamar bacci, sha biyu da rabi nayi Ummi da bata kai ga kwanciya ba tana revision ta fara tashin Mayraah, duk Mayraah na jin ta amma tayi shiru, daga karshe ta mike zaune da kyar, Ummi tace "It's time" Mayraah ta sauko daga kan gadon ta sake dauko handout dinta ta zuba masa ido kamar hoto, tana ta zaune har karfe biyu saura kawai daga karshe ta tashi taje ta dauro alwala ta dawo.... Sai kusan karfe hudu Mayraah ta kwanta kuma har a sannan ko line uku bata fahimta ba a handout. Ummi ce ta tasheta sallan asuba bayan ta idar ta koma ta kwanta, bata farka ba sai kusan karfe takwas da rabi, sosai kanta ke mata ciwo ta mike zaune da kyar tana bin dakin da kallo, Ummi ta gyara ko ina ta share har wanke wanke tayi, takarda ta gani gefenta ta dauka taga note Ummi ta bar mata kan cewar ga breakfast ta ajiye mata a warmer, akwai ruwan lipton ma a flask ita ta tafi school... Mayraah ta ajiye takardan ta dafe kanta, can ta jawo wayarta da ta sa flight mode tun jiya, bude wayar tayi ko minti daya ba ayi ba sai ga kiran Usman ya shigo, ta daga kiran ta kai kunne, daga daya bangaren yace "Me ya sa kika kashe wayarki?" A hankali tace "Ina kwana?" Yace "Ko ba ki da caji ne?" Tace "Akwai, bacci nayi ne" Yace "To kar ki sake kashe waya malama" Cikin sanyin murya tace "Toh" Yace "Kin yi breakfast?" Tace "Yanzu na tashi" Yace "To yi breakfast din ki fito" Ta daga kai tace "Ina?" Yace "Waje... Kar ki wuce tara da rabi zan tafi aiki" a hankali tace "Toh" katse wayar tayi ta mike ta shiga bandaki, kafin karfe tara tayi wanka ta saka kaya, ta bude warmer din da Ummi ta ajiye mata taga irish ne da kwai, ko kamshin abincin bata son perceiving, ta bude dayan taga kazan jiya ne tayi masa kamar pepper soup, lipton kawai Mayraah ta sha ta saka hijab dinta ta fita waje, zaune ta gansa cikin motar, he was on suit, ya ajiye wayarsa bayan ya ga ta fito, ta karasa jikin motar ta bude tana kallonsa a hankali tace "Ina kwana" Yace "Lafiya lau, how was ur night?" Tace "Alhmdlh" yace "Kinyi breakfast din?" Tace "Nayi" Yace "Karatun fa?" Kai kawai ta gyada masa alamar tayi, ya ɗan yi shiru, ita dai kallonsa kawai take, can yace "Baki bukatan komai?" Tace "Ba komai" Yace "If there is anything ki kirani, zan je aiki yanzu" Tace "To Allah ya tsare" Yace "Ameen, sai anjima" ta gyada masa kai ta juya ta koma ciki. Maheer na kwance parlor idonsa a lumshe kamar me bacci amma ba baccin yake ba, yana jin Haseenah a kitchen tana ta soye soye tun karfe takwas, jin an bude kofa ya bude idonsa, Badiyyah ce ta shigo parlon kamar ba ita ke dingishi jiya ba, ta dawo garas abinta, ta ɗan sosa kai tace "Ina kwana yaya?" Yace "Lafiya lau..." Sai ga Haseenah ta fito daga kitchen da tray din breakfast tayi ma Maheer, kallo daya tayi ma Badiyyah ta dauke kai ta isa dai dai inda yake kwance ta ajiye duk da tun jiya bata ga fuskarsa ba tana murmushi tace "Honey ga breakfast nayi maka" Bata jira me zai ce ba ta bude cooler din ta fara debar masa irish din a plate, Badiyyah tayi hamma sannan ta nufi kitchen, tana shiga taga wayam duk Haseenah ta wanke kayan da taɓata, ta gama dube dubenta a kitchen din bata ga alamar breakfast ba, can ta fito ta dawo parlon tace "Haseenah ni ina breakfast din nawa?" Ba tare da Haseenah ta kalleta ba tace "Ni zan maki breakfast din da zaki ci? Baki san hanyar kitchen din bane?" Badiyyah ta wani hade rai tace "Ban gane ban san hanyar kitchen din ba, dama a gidan nake da zaki ce min ban san hanyar kitchen ba? ina bakuwa dani baza ki bani breakfast a gidan yayana ba kike nufi?" Banza Haseenah tayi mata ta ajiye ma Maheer plate din irish da kwai ga ketchup a gefe, ta bude wani cooler din ta zuba masa farfesun catfish da tayi, shi dai bai ce mata komai ba, ta langwabar da murya tace "Bari in dauko madara in hada maka shayin baby" Daga haka ta mike ta koma kitchen, Maheer ya kalli Badiyyah da tayi wani mitsi mitsi da ido tana huci tana bin Haseenah da kallo, sai da ya ga Haseenah ta shiga kitchen yace "Zo ki dauka ki je ki ci" Badiyyah ta taho da sauri ta dau plate din irish din da bowl din catfish ta tafi dinning area ta zauna, sai ga Haseenah ta fito, sake baki tayi tana kallon Badiyyah, can ta nufeta a mugun fusace tace "Ke Badiyyah ki shiga hankalin ki kar in maki rashin hankali, breakfast din mijin nawa kika dauka saboda baki da saiti?" Maheer yace "To ke ina ruwanki, ba dai ni na bata ba?" Badiyyah na tafe hannu tace "Kuma baki isa ki hana yayana ya bani abinda ya ga dama ba a gidan nan, ta ya ma zan zo gidanki saboda bakin hali ki hana ni breakfast kamar wata yar iska??" Maheer ya mike tsaye yace "Dauki breakfast din ki wuce daki" A mugun fusace Haseenah ta nufo sa tace "Ban gane ba Maheer?" Calmly yace "Kina nufin da yunwa zaki bar sister na ko kuma ance maki bare ce ita?" Badiyyah ta ja tsaki ta dau breakfast dinta ta wuce ta gaban Haseenah har tana neman bangajeta ta wuce daki ta kulle kofa, Maheer yayi wucewarsa daki shi ma ya bar Haseenah wajen tsaye baki bude kamar an dasa ta.... Wanka yayi ya shirya ya fito parlon, sai ga Badiyyah ta shigo parlon ita ma rike da kwanukan da ta shiga daki da su bayan ta siɗe tass kamar dama a yunwace ta tashi, tana ganin Maheer zaune parlor tace "Yaya aiki zaka tafi?" Yace "Ehh" Tace "Don Allah nima sai ka ajiye ni a school, yanzun nan zan shirya" Yace "Ohk har kin warke kenan" ta sinne kai tana murmushi tace "Ehh hannun kawai ke ciwo amma zan iya zuwa school din" Yace "To kar ki bata min lokaci" Haseenah dake zaune kan kujeran dinning ranta a mugun bace ta dinga bin su da kallo, gaba daya ta ma rasa wani tunani zata yi, Maheer na ta jiran Badiyyah a parlor har ta fito, daga ita har shi babu wanda ya kalli inda Haseenah take suka fita daga parlon. Yana ajiye Badiyyah a bakin gate din school din nasu ta kallesa da sauri tace "Aa yaya bakin gate kuma zaka ajiye ni baza ka shiga ciki ba? Da nisa fa department din namu" a takaice yace "Ana jirana a hospital ne" Tace "Toh shikenan" Sauka tayi daga motar ta rufe tana washe masa baki tana daga masa hannu alamar bye bye, ya gyada kai ya ja motarsa ya bar wajen, A ranta tace kai wai ashe dama haka yaya Maheer ke da kirki bata taɓa sani ba?? Ashe ya Maheer is this nyc? Ko da yake dama ita babu abinda ke hadata da shi kuma ko ta gaishesa da can ma yana amsawa, iyaka idan yaga tayi ba dai dai ba yace zai mata fada ita kuma shine bata so, Usman ne kawai ya tsaneta tun asali, kwafa tayi a ranta tana imagining ta tura ma Usman yan daba su rama mata dukan da yayi mata har sau biyu kenan, da sauri ta shiga cikin makarantar tana addu'ar Allah ya sa Dr Musharraf ya shigo school ta samesa a office, sai murmushi take... Maheer kadai yasan yanda yake tausasa zuciyarsa na ganin ya biye Badiyyah ita kuma har ta wani sake jiki da shi abinda ma ke kara ƙona masa rai kenan, da ta san irin mugun haushinta da yake ji da baza ma ta dinga biyesa ba, but babu komai za su ci gaba a haka he knows his target ae, hostel din da Mayraah take ya nufa don sun yi waya da ita not long ago tace bazata je school ba. Da yamma karfe biyar Maheer ya koma gida, har ya iso gidan ma bai sani ba don tunani iri iri suka cika zuciyarsa, ga damuwar Ammi da taki komawa gida duk da Mayraah bata gidan, Abba dama tun jiya da yamma ya bar kanon ya tafi ya ci gaba da harkokinsa ba tare da ya bi ta kan Ammin ba, ga Mayraah kuma da baya jin dadin yanda yake ganinta yasan she is just pretending to be fine karfin hali kawai take, but she look traumatized, he wish yanzu da ne da zai iya rungumeta ya lallasheta sosai ya kwantar mata da hankali amma that is not possible a yanzu kam, handout da tace masa ta karanta cikin dare ya amsa yayi mata tambayoyi bayan yaje wajenta da safe amma ta zuba masa ido kawai with no answer, if things should continue like this yasan zata samu matsala a makaranta, gaba daya yayi confuse ya rasa way out, parking yayi ya shiga cikin gidan, Haseenah na kwance kan doguwar kujera tana danna wayarta, sai ga Badiyyah ta fito daga daki tana kallonsa don ta ji shigowar motarsa, tana huci tace "Wai yaya fa Haseenah bata ma mutane girkin komai ba a gidan nan yau, tun da na dawo da rana babu abinda na ci, gashi yunwa nake ji yanzu...." Ko rufe baki bata yi ba Haseenah ta mike zaune tace "Ke kuturwa ce da baza ki shiga kitchen din ki dafa abinda za ki ci ba" A mugun fusace Badiyyah tace "Kee kar ki gaya min maganar banza a gidan yayana malama, nan din gidan mijina ne da zan dinga shiga kitchen anyhow?? Ba ke ce matar gidan ba, ai ke ya kamata ki dinga ma mutane girki su ci, ko ke a gidanku haka kika ga ake ma dangin miji??" Haseenah ta mike tsaye da sauri tayi mitsi mitsi da ido tana nunata da yatsa tace "Kar ki sake ki sako yan gidanmu a haukanki, kuma bazan yi girkin ba ai ba zamanki nake ba kuma ke din naga ba gurguwa bace da baza ki iya shiga kitchen kiyi girki ba" Badiyyah ta nufota kamar zata tashi sama tace "Ke ni fa ba Mayraah bace da kika rena wllh kika kawo min nonsense zan nakada maki duka a nan kuma babu abinda zai faru, ko kin ga na maki kama da Mayraah? Tun da yaya ya kawonu gidan nan jiya don ya dinga duba lafiyata naga kina bakin ciki, to naga dae ai ba gidan iyayenki na zo ba ko??" Da sauri Haseenah ta kalli Maheer dake tsaye yana kallonsu without saying anything, lokaci daya ta fashe da kuka ta dafe kirjinta tace "Maheer kana jin rashin kunyar da take min kayi shiru??" Maheer yace "Amma ke me ya hanaki girki kin san gidan da bakuwa? Ko dae baki san wacece ita bace in tuna maki?" Badiyyah ta wani karya kai tana girgiza kafa irin yesss din nan, Haseenah ta bude baki tana kallon Maheer with shock babu ko kiftawa, Maheer yace "To ita din ba bare bace, she have all right to ask for food from you in this house, dama don me aka auro ki? In case u don't know my family over everything Haseenah, dole kiyi girki ki bata" Cikin tsawa Haseenah tace "Toh bazan yi ba sai dai duk abinda zai faru ya faru, wallahi bazan girka ma katuwar banza abinci ba, wannan wani irin Fitina ne daga wannan sai wannan? Wani irin aure ne wannan" Badiyya tace "Sae dae uwarki ce ƙatuwar banza ba ni ba" Haseenah ta zaro ido tana kallonta, cakumota take kokarin yi a fusace, Maheer ya dakatar da ita yace "Keee respect ur self" Sai kuma ya kalli Badiyyah dake girgije girgije yace "Dauko Hijab dinki mu je in siya maki abincin" Da sauri Badiyyah ta koma daki ta dauko Hijab dinta, ko da ta dawo parlor taga Maheer har ya fita ya koma mota yana jiranta, Haseenah kuwa na tsaye ta kasa motsi saboda shock, sae zufa take a goshinta, she just can't believe it, Badiyyah na mata wani kallo tana juya ido tace "Yauwa wannan