Showing 189001 words to 192000 words out of 249515 words
yan sandan? Maganar banza maganar hofi, ke kika saci wayar ba kawarki ba" Aunty Mariya tace "Ai mara kunya ce, sam bata da kunya, don in har tana da kunya ma bazata bude baki tayi magana ba a nan, kuma dama duk inda makaryaci munafuki yake za a samesa da daukar abinda ba nasa ba, to kanki kika ja ma abun kunya wallahi ba mu ba, sannan ga record dinki na sata can wajen yan sanda" Hajja dai ta kalli Aunty Mariya ta gefen ido bata ce komai ba, Abba ya mike kawai ya fita daga parlon don shi case din ma kunya kawai ya basa kawai babu yanda ya iya ne yayi involving manyan mutane masu ganin girmansa, ace wai er kanwar matarsa ce tayi satar waya, satar ma a hotel kawai dai bai son bude zancen ne gaba daya sai dai yayi da Ammi but he is highly disappointed don a hotel Badiyyah tayi satar wayar, ga Maheer da Usman suka ki shiga case din suka bar sa shi kadai yana ta fama for one week, Aunty Mariya na ganin fitar Abba kafin Hajja ta samu damar ce mata komai ita ma ta mike ta fice daga parlon zuciyarta na tafarfasa, Hajja na kallon Badiyyah ta mike ta dagota tace "Tashi mu je gida kiyi wanka in samar maki abinda za ki ci, ba komai rayuwa ce, wanda bai zo ba ma jiransa yake" Ammi dai sai kallonsu take cike da takaici wai er late sister dinta ce haka, yanzu da Rukayyah na da rai Badiyyah ai bazata zama haka ba, Allah ya gani tayi bakin kokarin ganin ta ba Badiyyah tarbiyar da ta ba nata 'ya yan, tarbiyar da ta ba Mayraah ta so yi ma Badiyyah amma Hajja tayi ta intruding saboda son duniya da ta dauka ta dora ma Badiyyah don maraici, haka yasa Badiyyah ta daina tsoron kowa ta daina ganin kowa da gashi tunda tasan Hajja zata tsaya mata, ko kallon banza su Maheer suka ma Badiyyah sai Hajja ta ɓata rai, wani lokacin har Ammi hakan ke shafa don sai ta fita harkanta na sati da satittika duk don kan Badiyyah, wannan dalili yasa Badiyyah na cewa tana son Musharraf Ammi tace a hakura a bar mata tunda ita tasan wacece Hajjar, amma at the end duk da hakan bata fita ba, ta dalilin Badiyyah yau gashi babu Mayraah, tunanin hakan yasa hawaye ya kawo idon Ammi, shi dai Maheer ido kawai yake bin su da shi, Hajja na kallon Badiyyah tace "Baki da lafiya ne, naga kina layi? Ko dukanki suka yi a can?" Badiyyah ta marairaice tace "Jiri nake gani, kuma...." Da sauri ta rufe baki tana tsaye inda take kamar wata er yarinya ta fara kwararo amai Hajja ta gigice tana rike da ita tana salati, Ammi ta taso ta nufo su, Maheer dai sai kallonta yake babu ko kiftawa. Mayraah na zaune ita da Hafsat wajen karfe tara da rabi sauran nurses din na ta harkar gabansu attending to patients da suka zo allura, Hafsat tace "Ko energy drink ne ki amso Ilham don kar ki zama weak anjima, naga jinin naki ya ɗan sauka kadan da na duba, kuma akwai operation har biyar yau..." Mayraah tace "Ai ba da ni za a shiga theatre din ba..." Bata rufe baki ba Dr khalil ya shigo Reception din daga meeting room, tun safe da suka shiga meeting sai yanzu suka fito, MD ma ya shigo reception din ya wuce Dr Khalil dake gaisawa da patients, a takaice ya amsa gaisuwar nurses din zai wuce sai kuma ya juya kallon Mayraah, keenly yace "Hey, i didn't see u in any of the 2 meeting, are you a staff in here?" Nan duk nurses din suka maida hankalinsu kan Mayraah, wasu farin ciki fal cikinsu suna jiran jin me zata ce, Dr Khalil ya karaso yana kallon MD yace "Wannan satin ta fara aiki, kuma...." MD ya daga masa hannu yace "She should speak for her self pls" Yana fadin haka ya maida dubansa kan Mayraah a takaice yace "Madam me ya hanaki shiga meeting?" Mayraah ta nuna masa Dr Khalil a takaice ita ma tace "He have said it all" Ba MD ba, hatta Khalil was shock at her reply, Duk nurses din ma suka saki baki suna kallonta da mugun mamaki, Khalil ya dafa shoulder din MD yayi kasa da murya yace "I spoke to you about...." MD ya dakatar da shi yace "Meet me in my office" Daga haka ya wuce sama kamar zai tashi, Mayraah dai ko a jikinta don ko daga kai ta kallesa bata sake yi ba, Dr Khalil ya juya ya bi bayan MD din, Hafsat ta dawo gefen Mayraah tana zaro ido tayi kasa da murya tace "Ke Ilham why did u speak to him that way? Baya son raini fa? He is our boss Ilham" Mayraah ta kalleta tace "How did i speak to him, tambayata fa yayi kuma an riga an basa amsan tambayar da yayi min and he is still repeating the question" Wata nurse na hararanta tace "Kina wasa da aikin ki kenan yarinya, ko baki san shine MD din duk asibitin nan gaba daya ba, ke haka aka koya maki tarbiya a gidanku, kina ganin ya fara maki magana za ki mike tsaye da sauri ba wai ki zauna kina basa amsa ba cikin isa da gadara, who are you? Ke kamar kanki na hayaki daga fara aiki last week ko, to ina me tabbatar maki idan baki yi hankali ba yau shine karshen aikinki a asibiti nan ba dai MD kika ma rashin kunya ba, kin zata su Dr Hamid da Dr Balogun ne masu fasa maki kai wai kin iya aiki ko, to MD no go area ne, da kyar idan bazai yi firing dinki yau ba" Wata nurse din ta amshe tace "Ki kyale ta mana, yara duk sun je private University sun karbi Degree sun zo nan suna raina mana hankali suna maida mu bamu san me muke ba, to wa zata nuna ma iya aiki in ba karya ba" Mayraah dai bata ko kallesu ba balle ta basu amsa, infact kamar ma ba da ita suke ba, kai ita fa ba dole sai ta bar asibitin ta kama gabanta bata son isa da izza ga nurses ma sai raina mata hankali suke, abeg she can't, Can dai ta kalli Hafsat warce da alama duk jikinta yayi sanyi don a kaf asibitin hatta likitocin kaffa kaffa suke da MD har ma fararen fatan, Mayraah ta kalleta as if whispering tace "Wai shine me asibitin ne wannan jaraba haka?" Hafsat tace "Aa, but he is in charge of everything" Mayraah tace "To su waye masu asibitin?" Hafsat tace "Ceo din ba musulmai bane kamar ma ba yan kasar nan bane, but MD is the Managing Director cause he is good at what he does, kowa shi ya sani" Hafsat ta marairaice tace "Ni tsorona kar yace zai yi firing dinki kin ga ko tanka ki bai yi ba ya wuce sama yace Dr Khalil ya bi sa" Mayraah ta kyabe baki ta dauke kanta tana wasa da farcenta, iyaka ta koma Suleja abun ta tayi ta bacci ba shikenan ba. Dr Khalil ya zauna kan kujera bayan ya gama sauraron MD yayi kasa da murya yace "Look Dr, yarinyar bata san ka bane, and satin ta daya kenan da fara aiki a nan, pls pls consider..." MD ya dakatar da shi sounding so pissed off yace "Plss I don't want to see her in this hospital nace maka Khalil, bana son in sake sauka downstairs for any reason in ganta a asibitin nan seriously, banda kai waye kaga yake kawo health worker just like that inyi employing din sa ba tare da an bin proper procedure for the employment ba, ban ga CV ba, babu interview babu komai, infact ita ban ma kai ga ce maka komai kan employment din nata da ka min magana ba kawai ka sa ta fara xuwa aiki without my consent har ka bata uniform Dr, sannan yanzu from all indications naga rude workers ka fara kawo mana asibitin, so she should leave immediately pls, bamu da vacancy" Dr Khalil ya sauke ajiyar zuciya yace "Kai matsalata da kai saurin hawa, ka ma ki tsayawa ka saurareni" MD ya mike ya buga table dinsa yana kallonsa da kyau yace "Bazan saurareka ba Khalil, she have to leave this hospital immediately ko in kira security yanzu su fidda ta" Murmushi khalil yayi yace "Kasan er wacece?" MD ya koma ya zauna calmly as if counting his words yace "I don't care" Khalil ya mike yace "Kayi hakuri ka bata second chance pls, ni kaina nasan bata kyauta ba but she seriously needs this job, nasan kai me hakuri ne don Allah ka janye batun bazata sake aiki ba, idan ya so i can tell her idan ta tafi yau she should stay back home har sai ka bata employment din fully kafin tayi resuming" MD ya mike yace "She should stay back home, i am not employing her at all, i mean my words" Dr Khalil ya juya ya fita daga office din ya sauka floor din da office dinsa yake, yana zaune office ya kira downstairs yace a turo masa Mayraah, ba a dau lokaci ba ta shigo office din nasa tana kallonsa, sai da ya mata izinin zama sannan ta zauna, a hankali yace "Ilham me yasa kika yi ma MD magana rudely?" Mayraah tace "Did my words sound rude? Ni wallahi ban sani ba" Kallonta kawai yake, ta sunkuyar da kanta, bayan few seconds Khalil ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya yace "Yanzu ki tashi ki je office dinsa ki basa hakuri politely, and be careful with ur words pls Ilham, speak to him politely kice yayi hakuri kinyi kuskure baxa ki sake ba, talk to him remorsefully" Mayraah ta zaro ido tace "Office dinsa kuma?" Khalil yace "You have to Ilham, office dinsa na last floor"
[7/22, 8:59 PM] Khaleesat Haiydar💖: Mikewa Mayraah tayi ta fita daga office din Dr Khalil bayan ya bata direction din zuwa office din MD, jingina tayi da bango tana tunanin yanda zata fara zuwa office din nasa, in taje sai tace masa me? bayan few seconds ta fara tafiya zuwa last floor walking slowly, with direction din Dr Khalil ta isa har door din office din wanda bayan shi babu wani office a wajen, tana ta tsaye bakin kofar ta kasa knocking taji an bude kofar ta koma baya da sauri, wani Dr ne ya fito ta gaishesa ya amsa da murmushi ya bar mata door din a bude ya wuce, a hankali ta saka kai ta shiga office din that was extra large, it was damn chill ga kamshin freshner da ya hadu da sanyin office din, everywhere was so organize and tidy, ya daga kai yana kallonta don bai san ta shigo ba, sosai gabanta ke faduwa ta kulle masa kofar kafin ta karaso cikin office din a takaice yace "Get out and shut d door behind you....." Mayraah ta daga kai ta kallesa, lkci daya ta ɗan hade rai ta juya ta fice daga office din ta kulle masa kofar. Ko office din Dr Khalil bata koma ba balle ta gaya masa yanda suka yi, ta sauka downstairs kawai intention dinta tayi wucewarta gida a lkcn don ta riga tayi making din mind dinta bazata sake barin komai ya dameta a rai ba, gwara ta ci gaba da lallaba low bp din da ta samu all of a sudden, she will never allow anything weigh her down cause babu kuma abinda ya rage mata bata gani ba a rayuwar nan, zata tafi inda zata dau jakarta kenan wani Dr ya ganta ya kirata zuwa theatre room, duk nurses din reception suka bi ta da kallo wasun su na kyabe baki, Mayraah na shiga theatre din taga 2 nurses already a ciki, the theatre is already set for the surgery that was going to start soon, ta saka surgeon gown da hula tayi decontaminating hands dinta ta saka gloves with nosemask, bata dai san surgery din da za ayi ba, but she will just be assisting with surgical instruments don abinda likitan ya nuna mata kenan tun shigowar ta, after few more minutes tana juyawa taga MD ya shigo theatre din gabanta yayi mugun faduwa ta dauke kai da sauri don ma dai fuskarta da nosemask, wani Dr that will not be part of d surgery yayi assisting dinsa wajen saka protective wears sannan ya fita, MD ya wanke hannuwan sa, ita dai bata yarda ta sake dago kai ba tayi facing din instruments dake gabanta. Mayraah wished Dr Salim zata dinga mika ma instruments din gabanta not MD, babu yanda ta iya don shine kan surgery din, though su ma da nasu part din da za su yi playing, fatan ta dai bazai gane ita bace duk da bata barin su hada ido take mika amsa duk abinda ya bukata babu ɓata lokaci, after working for long, tsabar yanda ta fara gajiya taje zata maida wani instrument ta dau wani kawai ya fadi a hannunta, da sauri ta durkusa ta dauka ta mayar cikin sauran yan uwansa, ba shi MD ba har su kansu doctors dake wajen where took aback da abinda tayi, nan da nan tayi realizing mistake din gabanta ya fadi, maimakon tayi sterilizing wanda ya fadi sai kawai ta hada da sauran equipment din, contaminating them also, dole aka dauko wasu instruments din nan take don ta yi contaminating dinsu kenan, at last dai suka gama operation din successfully aka fitar da patient din zuwa ward, tana ta Allah Allah ta fita bayan ta cire gown din jikinta da gloves taji Husky voice din MD dake facing dinta yace "Where is ur theatre Hygiene?" Wani Dr ya mata alamar ta sauke nosemask dinta, tayi yanda yace a hankali tana kallon MD din ba tare da tace masa komai ba, sai a sannan MD yasan ita ce a theatre din, after looking at her from head to toes kawai ya fice daga theatre din zuwa office din Dr Khalil. Maheer ya fito daga office din likita da takarda a hannunsa yana kallon Ammi dake zaune da Hajja a reception, ga Badiyyah rungume jikin Hajja tana ta mata sannu, Hajja tace "Wai ba gado za su bata bane Maheer? Tana jin jiki fa, nasan ba komai bane illa cizon sauron inda marasu tsoron Allah nan suka kai ta" Maheer yace "Sun ce ba sai an kwantar da ita ba ya rubuta magunguna za a siya" Hajja tace "To allurai fa" Badiyyah ta marairaice da kyar tace "Ni bana son allura" Ko kallonta Maheer bai yi ba yace "Ku tashi mu tafi gida" Hajja ta mike ta dago Badiyyah, Ammi zata riko Badiyyan Hajja tace "Aa bar ta kawai ki ji da kanki tunda kema ba isasshen lafiyar gareki ba" A haka suka fita Maheer na biye da su a baya, suna shiga motar Hajja tace "Gida kawai za ka kai ni, na sa Mariya taje ta min share share ta daura girkin da zata kawo mana asibiti ban ma san baza su bamu gado ba" shi dai Maheer bai ce komai ba, after 30 mins of driving ya iso gidan Hajja yayi parking, Hajja ta sauka tare da Badiyyah Ammi zata sauka yace "Ammi we need to talk" Ammi ta kallesa sai kuma ta koma motar, Tuni Hajja ta shige cikin gida da Badiyyah tana mata sannu, Maheer ya mika ma Ammi takardan hannunsa, haka kawai Ammi ta ji gabanta ya fadi, ta dinga kallon takardan kafin ta amsa tace "Na meye" bata jira cewarsa ba ta fara warware takardan, sai kuma ta kallesa da sauri tace "Ka gaya min na meye ni ba ganewa zan yi ba Maheer" Ya sauke idonsa kasa yace "She is pregnant.... 4 weeks pregnant" Ammi da gabanta ya wani yanke ya fadi ta saki takardan ta jingina da kujeran motar tana zaro ido tace "Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun, ita Badiyyar??" Maheer dai bai sake cewa komai ba, nan da nan hawaye ya cika idon Ammi ta dinga nanata Innalillahi wa inna ilaihi raji'un jikinta na ɓari, gaba daya ta rikice a motar sai maganganu take daga karshe ta bude motar ta sauka kawai ta shige gidan Hajja cikin tashin hankali, Maheer ya ja motarsa ya kara gaba, Ammi na shiga parlor ta tarar da Hajja rike da Badiyyah da ta kirba amai nan tsakar parlorn, Hajja sai sannu take mata tana cewa "To nace a kwantar dake ance min ba haka ba, ya zan musu, tun dawowarku zuwa yanzu kinyi amai yafi a kirga gashi cikin babu komai" Mama Ladi dake zaune parlon sai yamutse fuska take tace "Yanzu fisabilillahi ita yarinya ce ma da zata sako amai daga tsaye? Ko yaro yaji amai ya san inda zai je yayi" A fusace Hajja ta dakatar da Mama Ladi tace "Ban gayyato ki gidana ba Ladi? Uban me ma ya kawo ki in ba neman magana ba, yaushe rabon da ki tako cikin gidan nan??" Ammi ta fashe da matsanancin kukan takaici tace "Kin cucemu Badiyyah, kin cuce mu...." Aunty Mariya ta fito kitchen da sauri tace "Lafiya Ammi? Me ke faruwa kuma" Ita kanta Hajja kasake tayi tana kallon Ammi jin furucin da take ma Badiyyah, Mama Ladi ta mike da sauri tace "Auzubillahi wani satan ta sake yi kuma?" Ammi na kallon Aunty Mariya cikin tashin hankali duk jikinta na rawa tace "Mariya ciki ne da Badiyyah har na sati hudu, Mariya ki gaya min ta ina za mu fara Mariya" Wani ihu Mama Ladi tayi tace "Ciki fa kika ce Ammi? Cikin ɗan mutum ko me?" Ko rufe baki Mama Ladi bata yi ba suka ga Hajja ta sulale kasa.
Mayraah na fita daga asibitin bayan ta isa bakin titi inda zata je ta samu abun hawa taji wayarta dake jaka na vibrate, ta bude jakar ta ga Khalil