Showing 12001 words to 15000 words out of 249515 words

Chapter 5 - Mayraah Hausa Novel Complete

20 Nov 2024

1497

tace "Ba naji ance za ku je siyayya ba, kuma me za ki je yi gidan Hajja" Mayraah ta ɗan ɓata rai kamar zata yi kuka tace "Ammi na mata alkawari zan je yau fa, kuma ma ai ba yanzu za mu yi siyayyan ba sai da yamma" Ammi tace "Aa ki hakura da zuwa gidan Hajja, ki bari ranan da baki da lectures sai mu je tare" Usman dake kallon Tv ya kalli Ammi yace "Saboda me?" Ammi tace "In zan je sai mu je tare kawai" Mayraah ta sunkuyar da kanta bata sake cewa komai ba amma abinda Ammi tace bai mata dadi ba, Usman yace "Ni ma ai can zan je yanzu, ki bari in ajiyeta sai mu dawo tare idan zan dawo tunda ni ba dadewa zan yi ba, i will be going to Zaria later"
Ammi ta kalli Mayraah don har cikin ranta taji wani iri ɓata ran da tayi, Ammi tayi kasa da murya tace "To ku je tare, amma ki tabbatar kin biyosa idan zai dawo" a hankali Mayraah tace "To Ammi, Nagode" Kallon Usman Mayraah tayi tace "Yaya yanzu zaka tafi?" Usman ya kalleta yace "What is ur business?" Nan da nan Ammi ta hade rai tana kallonsa tace "Kai komai masifa bawan Allah" Mikewa Mayraah tayi ta tafi kan kujera ta zauna bata sake cewa komai ba, Ammi tace "To meye laifi ma don ta tambayeka banda fitinarka tayi yawa" Ya mike yace "To idan bata da lectures din sai ku je tare, sai na dawo" Mayraah ta zaro ido da sauri ta mike tace "Yaya don Allah kayi hakuri" tuni ya fice daga parlon, Ammi ta tabe baki tace "Bi sa ku tafi" Mayraah ta bi bayansa da sauri.... Tafiyar minti talatin suka yi suka iso gidan Hajja, tsabar ba dadewa zai yi ba a waje yayi parking motarsa suka gaisa da mai gadin gidan ya shiga ciki Mayraah na biye da shi, parlon Hajja cike yake da yaran makota sun shigo kallon cartoon, Hajja na ganin Usman tace "To duk ku tashi ku tafi jikana ya zo, maza ku tafi" Babu wanda ya motsa cikinsu kamar basu ji ta ba, Usman yace "Kai ba magana ake maku ba" lokaci daya duk suka mike suka fita, Hajja ta marairaice tace "Ni na gaji da wahala gaskiya, kaga da baka sa baki ba wllh baza su tashi ba, ko na koresu basa tafiya sun maida ni wata mara makabuli, kakanninsu na can suna hutawa ni kuma sai a zo nan a dameni a cika min parlor har da almajirai, tunda suka kyallara ido suka ga Badiyya ta fita duk suka shigo" Hajja ta zaro ido ganin Mayraah tace "Dama tare ku ke, sannunku da zuwa, ai ko kin cika alkawari" Mayraah na murmushi ta karasa ta zauna kusa da Hajja ta gaidata, Hajja ta amsa da fara'a tace "Ina Ammin taki" Mayraah tace "Tana gaisheki" Usman ya zauna yace "Ina kwana Hajja" Hajja tace "Lafiya lau ya aiki" Yace "Alhamdulillah" Bude kofar parlon aka yi sai ga Badiyya ta shigo, Usman ya bi ta da ido kamar zata wuce sai kuma tace "Ina kwana yaya Usman" Yace "Lafiya lau" Mayraah na kallonta tace "Ina kwana Aunty Badiyya" Tuni Badiyya har ta shige daki, Hajja ta girgiza kai murya can kasa tace "Na gaji da yarinyar nan, ko sallama fa bata min ba ta fita, yau da asuban fari naga tana ta hada akwatunanta na kasa hakuri na leka daki nace ina kuma zata, wai zata koma gidanku..." Sosai gaban Mayraah ya fadi tana kallon Hajja, Usman yace "Zata koma gidanmu tayi me?" Hajja ta rufe baki da sauri tace "Kul kar ka sake cewa haka, ba fa bare bace, yar uwarka ce ta jini, don tace zata koma gidanku ai ba wani abu bane, nasan babu abinda Mamuda zai ce kuma bazai hana ta zauna masa a gida ba, tun yaushe ake son ta koma can din don ku sa mata ido ta rage abubuwan da take amma fir taki, tunda yanzu Allah ya so mu don kanta ta dawo tace zata sai a bar ta ta tafi kawai, dama anjima nake son kiran Ammi" Usman yace "Karya take yi, akwai wani munafurcin da take kullawa, banda haka bazata ce zata dawo gidanmu ba" a fusace Hajja tace "O'o Allah mu yi mata kyakkyawan zato mana Usman" Usman yace "Allah ya kawo ta lafiya, dama zuwa nayi in gaisheki na kwana biyu ban zo ba, yanzu sauri nake zan tafi Zaria" Hajja tace "Ai ko nagode Allah maka albarka" Dubu goma ya ciro a aljihunsa ya ajiye mata, ta dinga sa masa albarka, ya mike yace "Ni zan tafi saboda ana jirana bani kadai zan je Zarian ba" Hajja tace "To maza kaje Allah ya tsare, ke Mayraah ai kina nan har gobe ko" Usman yace "Aa tare za mu koma gida yanzu" Hajja tace "Tare kuma? Saurin me take" Usman ya kalli Mayraah yace "Tashi mu je" Mikewa tayi tace "Hajja in sha Allahu zan dawo ni kadai" Hajja dai bata ce komai ba, can ta sauke ajiyar zuciya tace "Wato Ammi ce tace kar ki zauna ko??" Usman yace "Ai ke dama kin iya zarge zarge a ranki" Mayraah tace "Bata ce haka ba Hajja, kawai akwai wani aiki da nake yi na makaranta ne" Ko rufe baki bata yi ba sai ga Badiyya ta fito da akwatunanta uku tana turasu, Hajja ta mike tace "Tafiyar kenan Badiyya?" Ba tare da Badiyya ta kalleta ba tace "Eh" Hajja tace "To ai kawai sai ki bi su Usman su ma gida za su tafi yanzu" Usman yayi saurin cewa "Wani Usman din?" Hajja ta kallesa baki bude, lokaci daya ta hasala tace "Wai me ku ka dau Badiyyar nan ne? Bare ko me? Er kanwar uwarka ce fa uwa daya uba daya, kwata kwata kun dauki tsangwama kun yafa ma yarinya marainiya ba uwa ba uba" Tana kai wa nan ta fashe da kuka, Usman ya fice daga parlon ita dai Mayraah ta kasa motsawa daga inda take, Usman ya leko parlon ganin Mayraah bata biyosa ba yace "Ke me kike jira Malama" Mayraah ta sauke idonta kasa ta nufi kofa, Hajja ta dau dubu gomansa da sauri cikin kuka tana mika masa tace "Gashi bana so ka kara fetur a hanyar Zaria" ko juyawa shi dai bai yi ba har ya fita, Mayraah dai sai bin sa take don bata son yayi mata masifa.....



07087865788

WhatsApp only.
[5/29, 2:29 PM] Khaleesat Haiydar💖: 💖💖 *MAYRAAH*💖💖




By _Khaleesat Haiydar_📚✍🏻





4....

Suna barin layin Mayraah na kallonsa a hankali tace "Amma Yaya Usman da ka daukota just for peace to reign" Usman yace "That peace should neva reign" Mayraah bata kuma ce masa komai ba ta jinginar da kanta jikin kujeran motar har suka isa gida, tsaye suka tadda Ammi a parlor waiting for them furiously, Mayraah na ganinta ta gane har Hajja ta kirata kenan, Ammi ta nufi Usman rai bace tace "Yanzu Usman abinda kayi ka kyauta kenan? Me zai rage ka idan ka dauko Badiyya a motar ka? Kai duk abin magana baka gudunsa? Inda Maheer ya fi ka kenan don da shi ne bazai taɓa yin haka ba, ko ransa bai so ba zai daukota" Usman ya nemi kujera ya zauna yace "Yanzu dai magana ta gaskiya abinda ya faru ya riga da ya faru sai dai kowa yayi hakuri Ammi, dama Allah ya rubuta Badiyya bazata hau motata yau ba" Yana fadin haka ya kalli Mayraah dake tsaye tana kallonsa yace "Go get me my box upstairs" Sama ta tafi zuwa dakinsa, ya mike yana kallon Ammi yace "Kawai zuwa fa zata yi ta dinga saka mutane magana ba wani abu ba Ammi" A fusace Ammi tace "Ina ruwanka? Naga ai ba gidanka bane nan din ko?" Ya nufi Mayraah dake saukowa rike da box dinsa ya amsa sannan ya dawo gaban Ammi yace "Ammi zan tafi ana jirana" Ammi tace "Amma gaskiya baka kyauta min ba Usman don wannan ba karamin magana ka ja min ba wajen Hajja" Yayi kasa da murya yace "Tafiya fa zan yi Ammi, ke da zaki min addu'a kice min Allah ya kiyaye hanya" Ammi ta maka masa wani kallo, ya koma ya zauna yace "Shikenan, sai a fasa tafiyar, bari in kirasu ince suyi wucewarsu kawai" Ammi tace "Ni ban hanaka tafiya ba, kaje... Allah ya kiyaye hanya, ya tsare, ya kai ku lafiya" Ya ɗan yi murmushi yace "Ameen" mikewa yayi ya dau box dinsa ya nufi kofa, Mayraah tace "Allah ya kiyaye hanya yaya" Yace "Ameen" Daga haka ya fita daga parlon, Mayraah ta nufi Ammi tana kallonta tace "Ammi kiyi hakuri, nima ban san me yasa yayi haka ba, kawai ta hau adaidaita sahu ta taho...." Ammi tace "Ni da ta zamar ma dole zan kira Abbanku in nemi izini in je in daukota ai" Daga haka Ammi ta wuce sama Mayraah ta bi ta da kallo.....
Bayan fitar Ammi Mayraah ta wuce dakinta a sanyaye tana ta tunanin dakin da Badiyya zata ce zata zauna idan ta dawo gidan, don dakuna biyar ne a sama, Na Abba wanda ke hade da personal parlor dinsa, sai dakin Ammi still a bangaren Abba, sannan nata dakin, dakin Ya Maheer da Ya Usman duk a sama suke, dakuna uku ne downstairs, Na Umar, sai na mai aiki, da wani spare room, ta san Badiyya bazata zauna downstairs ba, don a da can baya idan ta zo to dakin Mayraah take zama, tayi ta mata abinda ta ga dama da nuna isa a dakin don ma Mayraah na da hakuri, she can't imagine staying in the same room with Badiyya again, bayan kananun issues dinta da nuna isa da gadara ga kuma rashin gyara waje, duk inda ta samu ajiye kayanta take babu nutsuwa, mayar da daki take kamar na mahaukata da tulin kayanta, she is soo unkept, Mayraah ta kalli wayarta dake ringing ganin me kiranta ta daga ta kai kunne, a hankali tayi sallama hade da gaishe sa bayan ya amsa yace "Baki je gidan Hajjan ba?" Mayraah tace "Mun je da Ya Usman, har mun dawo" Yace "Ohk, I will be coming over at 3pm, is that okay by you?" Ta kalli agogo sannan tace "Allah ya kai mu" Yace "Ameen, bye" Daga haka ya katse wayar, kwanciya tayi ta lumshe ido with many thoughts running her mind.
Ba ayi awa daya da fitan Ammi ba Mayraah taji an murda kofar dakinta aka bude lokaci daya, juyawa tayi suka yi ido hudu da Badiyya tana turo Akwatunan ta cikin dakin, Mayraah ta mike tana kallonta a hankali tace "Sannu da zuwa" ko kallonta Badiyya bata yi ba ta karasa shigar da akwatunan ta fito dauko sauran bags dinta biyu, Mayraah ta sauka daga saman gadon ta dau wayarta ta fita daga dakin, lokaci daya mood dinta ya canza, dakin Ammi ta nufa ta sameta tana linke Hijab dinta, bayan ta kulle kofar a hankali tace "Ammi wai dakina Aunty Badiyya zata zauna?" Ammi tace "Dama ina zata zauna banda dakin naki, hakuri kawai za ki yi ku zauna" Mayraah ta sunkuyar da kanta, Ammi tace "Yar uwarki ce, don haka ki bi ta ku zauna lafiya, nasan dai baki da matsala" Da kyar Mayraah tace "Ni zan koma downstairs in bar mata dakin Ammi" Ammi ta mata wani kallo tace "A saboda na kawo maki bakuwa ko kuma na kawo maki bare cikin daki?" Mayraah dai bata ce komai ba, can ta juya ta fita daga dakin ta sauka downstairs ta zauna parlor, ta yi nisa tunanin da take taji Sabira na cewa "Hajiya a zubo maki abincin ne yanzu ko sai anjima" Mayraah ta daga kai ta kalleta tace "Ba yanzu zan ci ba" Muryar Ammi taji tana ce ma Sabira akwai bakuwa a sama ta zuba mata abinci ta kai mata, Ammi na gama gaya mata haka ta koma sama, Mayraah ta mike ta tafi bandakin dake parlorn tayi alwala ta fito, sama ta tafi don dauko Hijab dinta a daki, Badiyya na tsaye gaban press din dakin ta mayar da gaba daya kayan Mayraah gefe daya tana jera nata kayan, duk girman press din nan ta zabi ajiye kayanta tsabar rashin son zaman lafiya, Dama gaban mirror din dakin ma ta mayar ma da Mayraah kayan shafe shafenta da turarruruka gefe daya ita ma ta jera nata uban shirgin a gefe daya, ga jakunkunanta su ma duk ta jera a inda Mayraah ke ajiye bags dinta, haka shoes, Mayraah ta dau Hijab dinta ta fita daga dakin ta koma downstairs, tana idar da sallah ta kwanta kan doguwar kujera.... Vibration din wayarta ne ya farkar da ita daga baccin da ya dauketa, ta mike zaune da sauri ganin me kiranta tana kallon agogo dake nuni da karfe uku da minti sha biyar, daga kiran tayi daga daya bangaren yace "Hi.... I am outside" Ta zaro ido tace "Ohk pls ka bani like 20 mins..." Musharraf ya gyara zamansa a kujeran motar yace "Are you for real?" Tayi kasa da murya tace "Yeah pls" Yace "But na gaya maki ai karfe uku zan zo" Tace "I slept off, zan shirya ne yanzu" Yayi shiru, sai kuma yace "Ohk to kawo min ruwa" Tace "In ba me aiki ta kawo maka?" A takaice yace "No, thanks" Ta turo baki kamar yana ganinta, katse wayar yayi, ta mike tsaye ta sa hijab din da tayi sallah sannan ta tafi kitchen ta dau bottle water daya ta daura kan tray, glass cup ta dauka sannan ta fito daga kitchen din, to ma meye sai ta daura a tray? komawa tayi ta ajiye tray din kawai da glass cup sannan ta fito rike da goran ruwan... Tun da ta fito yake kallonta ta cikin motar don dama kawai sleeping face dinta yake son gani.... Ta bude motar without looking at him tace "Ina yini" Jin bai amsa ba ta daga kai ta kallesa ta ga kallonta yake, alama yayi mata da ta zagayo, ta kulle motar ta koma daya side din kafin ta karaso ya bude motar, yana kallonta murya can kasa yace "Dama kina baccin rana? Nurses don't sleep in the afternoon" Without looking at him tace "Sai Doctors?" ya jinginar da kansa jikin seat din motar yana murmushi yace "Yayanki ke baccin rana kenan" Da sauri tace "Aa ni yayana baya bacci da rana" Yace "Sai ni?" Murmushi me narkar da zuciya tayi bata ce masa komai ba, ya kafeta da ido, Da sauri tace "Sir lokaci na wucewa, ga ruwan" Ya sauke idonsa daga kallonta, kamar baxae ce komai ba sae kuma yace "Ki je kawai ki ma Ammi sallama ki zo mu tafi, ko shirin me zakiyi? Or baki yi wanka da safe ba ne" Ta zaro ido tace "Ni ce ban yi wanka ba kuma?" Yace "To je ki sallami Ammi kawai ki fito" Daga haka ya dau bottle water din hannunta yace "Thank you" Bata ce komai ba ta juya ta koma ciki, sama ta wuce zuwa Bedroom dinta, ita har ta mance Badiyya na gidan don tana shiga dakin da ta ganta sai da gabanta ya fadi, Badiyyar na zaune tayi dai dai saman gado ga plate din abinci a gabanta da malt, tana ta danna wayarta kamar bata san Mayraah ta shigo ba, Mayraah dai bata ce komai ba ta wuce bandaki, Badiyya ta bi ta da wani kallo, ba a dau lokaci ba Mayraah ta fito rike da sabulunta da shower gel sai towel, har ta fita daga dakin Badiyya bata daina bin ta da kallo ba, Mayraah ta tafi dakin Maheer ta shiga bandakinsa tayi wanka, ta wanke bakinta da mouthwash dinsa ta fito, Hijab dinta ta dauka ta saka bayan ta goge jiki sannan ta koma dakinta don daukan kayan da zata sa da duk wani abu da zata bukata, Badiyya bata fasa bin ta da kallo ba, bayan fitarta ta ajiye spoon din hannunta tana nazarin abubuwa iri iri.... Bayan kusan minti goma Mayraah ta fito daga dakin Maheer cikin shirinta, Hijab ne har kasa jikinta tana rike da handbag dinta ta nufi dakin Ammi ta sanar mata Musharraf na jiranta a waje, Ammi tace "Toh Allah ya tsare, sai a kula, kuma kar ki wuce karfe shidda, Abbanku ma yau zai dawo" Mayraah tace "Toh Ammi, Allah ya dawo da shi lafiya" Daga haka ta sauka downstairs, zaune taga Badiyya a parlon da plate din abincin da take ci, Mayraah ta kalleta tace "Sai na dawo Aunty Badiyya" Badiyya tace "Ina za ki?" Mayraah tace "Ana jirana ne a waje" Badiyya tace "Wa yake jiranki?" Mayraah da kamar bazata ce komai ba, sai kuma tace "Baƙo nayi" Daga haka ta juya ta bar parlon, Badiyya ta mike ta nufi window da sauri tana leka compound din gidan amma bata ga kowa ba, sai da ta ga fitar Mayraah daga compound din sannan ta fito har tana tuntube ta nufi gate tana leka kofar gida, sosai gabanta ya fadi ganin motar dake barin kofar gidan, Dr Musharraf! Abinda ta fada kenan a zuciyarta... Bayan sun bar layin Musharraf yace "A ina ake siyar da kayan ne?" Mayraah ta zaro ido tace "How will i know?" Yace "Ke ba er kano bace" Mayraah bata ce komai ba, Yace "kin yi shiru" A hankali tace "Kasuwa za mu je" Yace "Aa bazan je wani kasuwa ba, babu boutique ne irin na mata?" Murmushi kawai Mayraah tayi still bata ce masa komai ba, Idan tana masa wannan murmushin confusing dinsa take, ya gangara yayi parking gefen hanya, Calmly yace "Kin yi shiru" Mayraah ta sunkuyar da kanta tace "To me zan ce?" Yayi kasa da murya yace "Kinsan me zai faru Mimi?" Ta kallesa da sauri don Ya Maheer da Ammi kawai ke kiranta Mimi, ta girgiza masa kai, kana ganinta kasan she is uncomfortable, After few seconds of staring at her yace "I think it will be better in tura maki kudin kayan nan, ku hada a can gida, idan ma kudin basu isa ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login